Episode 18
_________________Tafiyar da sukayi ta ɗauke su kusan minti talati dan wani ƙauye ne wanda babu yawan jama'a a cikinsa.
A dai-dai wani ɗan guntun gidan ƙasa suka tsaya, sauka sakayi daga kan machine ɗin, Mami ta biya suka shiga cikin gidan, mutane suka tarar a gidan a zaune a tsakar gida ko arzikin tabarba babu, Mami da ta gaji sai nishi take, ruwa ta ɗauko a jakarta ta buɗe ta sha,gaisawa sukayi da mutanen da suka tarar sun kai su bakwai.
Wata baƙar mace ce ta fito daga ɗakin da yake da labulan buhu, daga ita sai ɗaurin ƙirji, matar Malam gobe da nisa ce.
Washe baki tayi ta ce" lale lale da Hajiya Fatu mai kayan gyara ke ce tafe yau" Hajja Fatu ta ce "wallahi kuwa Sahura kinganmu babu shiri ƙawata na rako" ta faɗa tana nuna Mami wacce ta zauna a kan dutse.
Mami da bata so dare yayi mata anan ta yi wa Hajja Fatu raɗa a kunne, tana ciro kuɗi ta bawa Hajja Fatu, Hajja Fatu ta kalli Sahura ta ce " aikuwa na zo miki da wani abu na musamman matar Malam" Sahura ta washe jajayen dafaffun haƙoranta ta ce " kai tawaje na, hi ya sa nake sonki, higo daga nan" su ka shige cikin ɗakin Sahura, Hajja Fatu ta ce " kinga dan Allah ba ma son bin wannan layin, ungo wannan naki ne" Sahura ta ce " to ce ta higo nan, zan je in masa magana yanzu zai ganku" Hajja Fatu ta ce " kinga daman na tawo miki da wani haɗi na musamman kinsan tun daga ina wannan maganin yake?" Sahura ta girgiza kai ta ce "a'a" Hajja Fatu ta ce " tun daga can Mali yake, dubu biyar nake sai da shi,amma ke ki kawo dubu uku" Sahura ta dafe ƙirji "dubu uku, ina naga dubu uku Hajja Fatu" Hajja Fatu ta ce" to na bar miki a dubu biyun nan ma, ke ai tawaje na ce hahh" ta bata abu ɗan mitsitsi a roba ta ce" turare ne, idan za ki turaka ki shafa ɗan kaɗan, zaki ba ni labari" Sahura ta dinga murna da godiya, ta ce bari in masa magana, yanzu zai ganku" ta fita, ta shiga ɗakin da boka gobe da nisa yake.
Zaune ya ke kan buzu ya kima uban rawani a kansa, ɗakin duk tarkacen abubuwan hauka,irin na matsafa wanda ya haɗar da wuri, kayan askin wanzamai, da ƙoƙon kan jaki da layu da guraye da sauransu.
Wasu mata su biyu ne zaune a gabansa suna zayyana masa buƙatunsu ya na jinsu, ganin Sahura matarsa ta shigo suka dakata da magana.
Sanar da shi tayi yayi baƙi na musamman daga cikin Kano, Malam gobe da nisa mai idon cin naira ya gyaɗa ɗan kansa, da jajayen idanunsa ƴan mitsi-mitsi kamar na aljani, ya ce" ki shigo da su" Sahura ta fita da sauri, kar a ɓata wa Hajiya rai.
Matan da ke ciki, ya sallama, suka fita.
Sahura ta ce "Hajiya Fatu ku shiga" matan da suke layi suka kalli su Mami sukayi shiru, Sahura ta ce "ku yi haƙuri ya san da zuwansu" wata cikinsu ta ce " babu komai" Mami da Hajja Fatu suka shiga.
Sallama Mami tayi, boka ya yi shiru ya na zaune ƙwaryar da ke gabansa cike da wani ruwa, ya kalla, Mami ta zauna kusa da Hajiya Fatu.
Ta ce " sannu Malam ya aikin" ya amsa da kai yana ta kallon cikin ruwan dake gabansa, Hajja Fatu ta buɗe baki zatayi bayani ya ɗaga mata hannu. Alamar tayi shiru.
Ya ce " kin zo ne akan matsalar ki to ga dai shi nan, ko kishiya ce ko dangin mijin ne gashi nan dai nagani" Mami ta ce " hakane Malam, dangij mijin je, iyayensa ne har yanzu sun hanani sakat, gaba ɗaya sun magance shi ba shi da zance sai nasu, baya duba ƴaƴana, yanzu ma wai dawo da su gidan zaiyi" Boka ya dinga zane-zane akan ruwa da yatsansa ya ce" tabbas asurce shi akayi, shiyasa ba ya ta taku, zai dawo da su tabbas nagani sai dai abu ɗaya zakiyi domin a ɗauke hankalinsa daga kansu" Mami ta ce " to malam ko mene ne zanyi" ya ce" za 'a sai shanuwa babba guda ɗaya, za'a baww aljanu jinin, za'a sai karnuka baƙaƙe guda uku, wannan na sarki aljanu ne, sai a samu zuciyar damo da bindin barewa da su za'ayi aikin" Mami ta ce " ni ina zan samo waɗan nan abubuwan Malam?" Hajja Fatu ta ce " kawai a faɗa mana nawa ne sai a siya nan kawai Malam" Malam ya ce " dubu ɗari uku ma zai yi" take Mami ta buɗe jakarta ta ciro rapper uku ta ajiye masa.
Wasu ƙullin magani ya ɗauko guda biyu da laya ƙarama ya ce " wannan ki zuba masa a abinci, wannan kuma ki sa a ƙasan filon da yake kwanciya, wannan kuma,duk lokacin da za ki yi masa magana akan danginsa ki sa wannan layar a bakinki, to ko cewa kikayi ya shiga wuta sai ya shiga"
Daɗi ne ya kama Mami ta dinga godiya ta sa a jaka.
Hajja Fatu ma ta yi masa godiya suka fito, sallama sukayi wa matan da Sahura suka tafi.
Mami da take ganin matsalarta ta zo ƙarshe sai alwashi take ɗauka akan su BABA.
Machine suka hau ya dawo da su bakin rafin, suka hau aka haure da su ruwan, ta buɗe motarta suka shiga.
A gajiye suka baro ƙauyen da la'asar liƙis, har gida ta kai Hajja Fatu ta bata dubu goma dan ta ji daɗi sosai.
Abdul-azeez kuwa yana barin gida, ya nufi unguwar Nasarawa gidan Hajiya.
Tunda ya shiga gate ɗin yaga wasu motoci daban daga gani baƙi tayi, maigadi ya yi masa barka da zuwa, shi ne babban jika a gidan. Baƙi ne daga Kura, irin ƴaƴan da suka haɗa dangi ne da Hajiya Ruƙayya waɗanda suke karatu anan, tare da su uncle Hisham suna ta hira,idan ba ce maka akayi daga ƙauye suke ba, babu mai yarda.Sun fara wayewa zama cikin hostel.
Abdul-azeez ya shiga ciki da sallama, Hajiya Ruƙayya ta saki murmushi tana faɗin " to yau an tuna da ni kenan, yau a gari Abdul" Abdul-azeez yayi murmushi ya na ƙarasa shiga ya zauna kusa da Hajiya ya na gaisheta, Uncle Hisham ya gaisar ya kau da kansa dan bai san su Hamidu da Ladan ba, Hamid ya ce " Baba wannan ma ɗan nan ne kenan?"
Hajiya ta ce "a'a wannan ba ɗan nan ba ne ɗan can Mazoji ne" da sauri Abdul ya ce " haba Hajiya me ya haɗa ni da ƙauye saboda Allah, ai sai ki sa su raina ni" Hisham ya kwashe da dariya ya ce " garin ubanka ai nan ne garinka, da alama Yaya Hadiza ta koya maka ɗabi'an ƙin asali"
Ladan ya ce " mu zamu koma Baba, daman Gwaggo ce take ta faɗa akan ba mu san gidanki ba"ta ce " ai dole, a ce kuna Kano anan kuke karatu amma ba kusan gidan Babarku ba anji kunya" Abdul yaga yanda suka sake da Hajiya da Hisham, kuɗi ta ƙara musu tasan ɗalibai sai a hankali.
Su na fita Abdul-azeez ya ce " Hajiya wai ina kika samo wa'annan ƙauyawan?" haɗe rai tayi ta ce " ƴaƴan ƙannena ne" bai ƙara magana ba.
Kausar ce ta fito da ƙaton cikinta, da ƙyar take tafiya, Hajiya ta ce " sannu, Allah ya raba ku lafiya" Kausar ta ce" a'a Abdul yau kaine ka zo gidan, tun da na zo banganka a gidan nan ba ashe kana zuwa" ya kalleta duk tayi wani iri, ya ce " sannu aunty Kausar wai har yanzu baki haihu ba, Mami ta ce haihuwa za kiyi tun kafin mu je wancen ƙauyen" Hajiya ta ce " to Allah bai kawo ba, kasan ita haihuwa sai lokaci yayi" Abdul-azeez ya taɓe baki yana faɗin "hakane" Hama mai aikin Hajiya ce ta shigo hannunta ɗauke da moper, dake tsohuwa ce mai barƙwanci sama da shekara ashirin suna tare da Hajiya ta na ganin Abdul-azeez ta ce "a'a yau maigidan ne a gari" ta faɗa ta na fara'a, yaƙe kawai Abdul-azeez yayi sanin Hajiya ba ta son a yi wani abu dan bazai manta wani lokaci a baya ba.
Hama ta shigo irin hakan ta na yi wa Abdul tsiyar maigida ba cafane wannan wana irin miji ne" tsawa Momi ta doka mata, ta ce" meye hakan Hama banason irin wannan wasan gaskiya kowa ya tsaya i ya matsayinsa" Hama ta ce "ayya kiyi haƙuri Hadiza ba da wani abu na faɗa ba" Hajiya ce ta dinga yi wa Mami faɗa akan hakan, tun daga lokacin bata ƙara yi wa Hama wani abu na alkhairi ba, tsakaninta da ita sai dai gaisuwa.
Ita kuma Hama ta kasa dainawa indai Abdul ya zo gidan sai ta tsokane shi tun yarinta har yau bata fasa ba.
Hira suke da Hajiya tana tambayarsa mutanen Mazoji, nan ya fito fili yana sanar da ita irin tsanar da yayi wa AZIZAN BABA, yana bata labari har karara ta zu ba masa, Hajiya ta dinga dariya ta na faɗin, " aikuwa akwai dalili ni nasan yarinyar nan ba zata yi maka haka da ganganba"
Abdul ya ce" wallahi Hajiya banjin yarinyar nan mutum ce, kinga idanunta kamar na mujiya ƙwala-ƙwala, ga ta sirirya inda kikasan tsinke, sai bala'in zance, kuma fa ba wai na barta ba ne, hmmm zata san ni ta taɓa"
Hajiya ta ce"kai da gaske?" abun ne ya ba shi haushi ya ɗauki car's key ɗinsa ya fita a fusace.
Hajiya dai ta dinga dariya har da ƙwallah, ta ce"amma Allah yayi wa yarinyar nan albarka, ina ma anan take da zama tayi min maganin wannan aƙidar taka ta raina talaka" sai kuma ta ce "ko da ya ke Hadiza ce take ɗora ku a wannan hanyar bansan inda ta ɗauko wannan baƙin halin ba"
Sai ta tashi ta na hawa sama. Ganin lokacin sallar azahar ya kawo kai.
Kausar da take waya da mijinta, tana ta mitar cikin ya isheta, idan har sati ya ƙare, Aunty Hadiza ta ce sc za'ayi mata, da ke irin masu shiru ɗin nan ne bai ce komai ba sai, to Allah ya sa ma ki sauka lafiya ba sai anyi cs ba" ta ce " amin" ganin hayowar Hajiya ta yi masa sallama ta kashe kiran.
"har Abdul ɗin ya tafi ne?" Hajiya ta ce" ke ma kinsan ba'a wanyewa da shi lafiya, ya yi fushi ya tafi" Kausar ta sa dariya ta ce " zaku shirya ai faɗan mata da miji ne"
Hajiya ta nufi ɗakinta,kausar ta ƙara bajewa a ƙasan capet ɗin parlour'n saman.
Bai koma gida ba, sai ya zarce gidan su Bilal dan kwana biyu ba su haɗu ba.
A office kuwa Alhaji Aminu dollars ya na duba kayan da zai sa a cikin gidan BABA dan jikinsa na ba shi, za su dawo, shiyasq ya ke duba iron bed dan siya musu,yanda AZIZA ta ke tsananin ɗaukin zuwa makka yasan ba zai sa ta manta da dawowa birni ba.
iri ɗaya ya yi wa Inna da Baba Tabawa komai babu abinda ya banbanta musu har kala, na Baba ne kaɗai ya banbanta dan shi baya son kyale-kyale ko kaɗan.
Ɗakin AZIZA kuwa komai irin na pretty ya siya mata, har inda zata dinga wasan ƴartsana ya haɗa mata,son da yake yi wa ɗan uwansa Abdul-azeez duk ya mai da kan ƴar da ya haifa, ga tausayinta da yake ji na maraici bata san iyayenta ba, kullum sai ya ambaci AZIZA.
Yana jinta tamkar shi ya haifeta, ya rasa mai danginsa sukayi wa Mami take ƙinsu, abun nan yana damunsa sosai, har hawan jini ya samu silar wannan damuwa, sama da shekara goma da doctor ya sanar da shi yana da shi.Amma bai sanarwa da kowa ba, hatta Mami bata san yana da hawan jini ba, sai dai ta ga yana shan magani, amma bata taɓa tambayarsa ko na me ne ne ba, dan a nata haukan irin na gajiya ne da ƙara kuzari haka da yawancin maza ke amfani da su.
Baya ga wannan Aminun Baba ba shi da wata damuwa, tun haihuwar pretty ya so ya ƙara aure, ko zai samu wacce zata taya shi, shawo kan BABA ya dawo jikinsa, saboda tsaron da yake so ya ba su.
Dan ganin yanda wasu suka je har gida suka ɗauke mahaifiyar abokinsa Alhaji Aliko Ammani, duk da ankai kuɗin fansa sai da suka kashe tsohuwar, gawarta aka je aka ɗauko.
Tundaga lokacin hankalinsa ya ƙara tashi sosai sanin ya fi Alhaji Aliko dukiya da jama'a.
Har ƙauye ya je dan tawo da su Inna, Baba ya fututtuke ba zai bar Mazoji ba, anan ya ke ba su labarin abinda ke faruwa ga duk masu hali, Baba ya ce shi ya san wani sukorito(security).Babu inda zai je.
Tun Daddy yana ƙarami yake son ya gaji BABA yayi mata biyu, amma da zarar ya yunƙura zai yi aure, sai kuma ya ji ya kasa, dole ya tattara maganar ya barta a ransa.
Munnir ne ya dawo daga training dai-dai lokacin da Mami ta shigo, da sauri ya yi wajen motarta dan tun safe bai ganta ba, har suka tafi school kuma da suka dawo bata nan, shi ya buɗe mata door yana faɗin" ina kika je Mami?"
A gajiye take liƙis ta ce" inda ka aike ni" ya matsa ta fito ta na shigewa ciki.
Munnir ya bi ta da kallo ƙafarta tayi fututu da ƙura ga kayanta sun ji datti da jar ƙasa.
Bin bayanta yayi yana faɗin "Mami wai ina kijaje kinga kayanki yayi dirty fa" Mami ta ce "zanci ubanka Munnir banson sa ido mtsww" ta wuce da sauri kar wani ma ya ganta ya ɗora daga inda Munnir ya tsaya.
Pretty da Siyama kuwa ba su damu da rashin ganinta da ba suyi ba, dan idan da sabo sun saba, su na ɗakin Siyama su na ta kallo a tictok sai dariya suke.
Munnir ne ya leƙa ya ce musu "Mami ta dawo,amma duk tayi datti kamar fa daga ƙauye take" Siyama ta ce "ina ta je?" kafaɗa ya ɗaga ya baje hannu alamar bai sani ba, ya juya ya nufi nasa ɗakin.
Ajiyar wayar tayi ta ce,zo muje mu gani ina ta je.
Tana ɗaki ta zauna a bakin gadonta ta na ta tsinewa dangin mijinta wai sun hanata zaman lafiya da mijinta.
Turo ƙofar Siyama tayi ta bi ƙafafun Mami da kallo, pretty ce ta shiga da gudu ta na oyoyo Mami, ina kika je ki ka daɗe banganki ba?"
Haushi ne ta tasowa Mami ta tureta, da faɗa ta ce " inda kuka aike ni, ka ji jarabbaun yara" pretty ta matsa ta na niyyar sa kuka, Siyama ce ta ce " tafiyar ƙafa kikayi haka Mami?"...........
MAZOJI
AZIZAN BABA kuwa ta nufi gidansu A'in mai kalwa kamar yanda ta faɗa, Baba mai kalwa tana zaune akan tabarma, taga AZIZA ta shigo.
"Assalamu alaikum" Mai kalwa ta amsa "wa'alekumussalamu a'a AZIZAN BABA ke ce cikin ranar nan" AZIZA ta sa dariya ta ce " eh Baba ina Ai" Baba Mai kalwa ta ce "ayya ai sun tafi suna tun da safe ita da uwarta" AZIZA ta ce " kai shi ne suka tafi na ce mata fa zanje ta ta tsaya ni,amma shi ne innarta ta sa sukayi tafiyarsu" Baba mai kalwa ta ce" sai kuma su zauna haka har rana tayi uwarsu ɗaya ubansu ɗaya fa da Atine da maijegon" AZIZA ta ce "shikenan zata sani kuma ma mu birni zamu koma kuma har ɗakin Allah zamu je alkur'an sai na karta mata rashin mutunci" ta juya a fusace ta bar gidan.
Baba Mai kalwa ta bita tana faɗin "ya ki nan AZIZAN BABA, zo mana ai nima yanzu zan tafi gidan sunan zo mu je" ina AZIZA ta miƙi hanya, Mai kalwa ta koma ciki, tana gudun haɗuwar Ai da AZIZA dan idan akayi faɗa sai hankali ya tashi.
Har gida BABA yake zuwa yayi musu tijara da cin mutunci in ma bai dangana ga wajen maigari ba.
Duk yaron da ya ga AZIZA a wannan halin ba wanda yake kulata, Fatsima ce ta ɗauko tallan gyaɗarta marau da tuɓus ta ciro fanteka, ta ci ɗammara fuskar nan ta sha jar hoda, AZIZA customer ce.
Fatsima ta hau washe mata baki tun daga nesa, AZIZA ba ta ko kalle ta ba, ƙwafa kawai take yi, Fatsime ta sha gabanta ta ce " dalla sai fara'a nake miki kinyi min banza, ko ba za ki siya ba in tafi"
Ture fantekar tayi, gaba ɗaya gyaɗa ta zube rabi duk a cikin kwata rabi a gefen kwata, ta kwasa a guje ta yi gida.
Fatsime ta kurma ihu ta ɗora hannu aka tana kuka, sanin innarta maigyaɗa sai ta zaneta akan hakan, wallahi bazan yarda ba sai an biya ni" kuka take ta na tattara gyaɗar da ke gefen kwata.
Yara suka fara taruwa suna tsinta suna guduwa suna ci, Fatsime sai kuka take ta na binsu, da duka, kafin ta gama kwashewa yara sun cinye sauran gyaɗar.
Gidan sun AZIZA ta nufa tana kuka, AZIZA na can tana rigimar sai sun tafi birni a yau, ai suma suna da ƴan'uwa.
Baba Tabawa ta dinga tambayarta meke faruwa, ta ƙi faɗa, Inna Gaji ta ce "sai ki bari Malam ɗin ya zo, ki gayamasa ni kam kin dame ni da wannan kukan naki na jaraba" Baba Tabawa ta ce "haba Yaya meyasa kike hakane, ai kinsan akwai abinda akayi mata" kukan Fatsime ne yayi musu sallama. "wallahi sai an biyani gyaɗata"
"ihum ni nasan da walakin wai goro a cikin miya,me ya faru?"
Fatsime ta ce"AZIZA ce ta zubar min da gyaɗa ta cikin ƙwata" Inna Gaji ta hau tafa hannuwa tana salati" la,ilaha'illalahu ke kalle ni nan, ni sa'ar ki ce,a ina ta zubar miki da gyaɗar tunda ta dawo daga makaranta ta ke nan zaune, ko a makarantar ta zubar miki iyee?"
Fatsime ta ce "yanzun nan a hanya wallahi ko wa za'a tambaya" Baba Tabawa ta ce "ke yi shiru a ina ta zubar miki?"
Fatsime ta ce " a faƙo"
Ta nawa ce gyaɗar?" Baba Tabawa ta faɗa.
Da sauri Fatsime ta ce "ta jaka huɗu ce"
Baba Tabawa ta shiga ɗakin ta ɗauko dubu ɗaya ta na miƙawa Fatsime, wafcewa Inna Gaji tayi ta na faɗin " wallahi ba za'a biya ba, ta zo tayi wa yarinya ƙarya kin kama kin hau ba za'a bayar ba, za ki tashi ko sai na mangareki anan, ƙatuwa da ke da aurar da ke akayi yanzu da kin yi ƴaƴa biyu ko uku, amma kin ɓige da biyo yara da herri"
BABA ne ya jiyo hamayani tun daga zaure, "to,to kai wai me ne hakan ne kun cika gari da hayaniya" ganin sunyi cirko-cirko AZIZA na zaune a ƙasa, ta na ta kukanta ba ta su Inna ma take ba, baƙincikin tafiyar su Ai ne kawai ke cin ranta, ta tamawa zuwa sunan ƙanwar Innar Ai sosai.
BABA ya nufi AZIZA da sauri " ke da waye?" ya faɗa yana zama dan ɗago ta cinyarsa.
Inna Gaji ta ce " herri wancen algungumar ta zo yi mata har gida"
BABA ya kalli Fatsime ta na ta share hawaye ya ce " me tayi miki kika sa ta kuka?".Fatsime ta kora bayanin abinda ke faruwa.
Inna Gaji ta ce "ƙarya take malam tunda ta dawo daga makaranta babu inda ta je tana nan zaune" Baba Tabawa ta ce " a'a fa Yaya da gudu ta shigo gidan nan, kin san ta fita bayan ta dawo, kuma kinsan dai zata aikata ki kawo a bata kuɗinta ta tafi kawai" BABA ya ce"ke ki ɗauko ki bayar ba za ta bayar ba" BABA ya tashi ya ɗauki sandarsa ya ce "matsa in bige ƴar jakar uba" a guje Fatsime ta fita, ta na kuka.
Baba Tabawa ta ce"ba ni kuɗina to tunda kun ƙi gaskiya"
Inna Gaji ta ce "ungu tsiyarki mtsww"
AZIZA ta ce "ni sai mun tafi birni tunda Ai suka tafi sunan ba su tsaya ni ba, BABA ka taso mu tafi bazan ƙara kwana a gidan nan ba" ihu ta ke ta na dole a tafi birni.
Hankalin BABA ya yi masifar tashi, Inna Gaji ta ce " Malam dan Allah ka kira Ɗansu ya zo a tafi ni wallahi kukan nan yana ɗaga min hankali"
Baba Tabawa ta ce" AZIZA kin zubar da gyaɗar yarinya kin zauna kina faɗin a bar gari, idan ka ci haƙƙin wani duk inda kika je sai Allah ya kama ki,ni dai babu ruwana" BABA ya ce " anyi ɗin Tabawa ki kiyaye ni, akan AZIZA zan iya rabuwa da kowacce a cikin ku, ki bi ni sannu sannu tom" Inna Gaji ta ce "ayiririiii yau ga amarya ana mata togaciya, ko haka ansan lalaɓawa ake da wata a gidan nan" Baba Tabawa ta ce "alkur'an ko saki na Malam ka yi bazan bar gidan nan ba sai ka bunne ni ko ni na bunne ka wallahi na zame muku ƙarfen ƙafa duk ɗan baƙinciki sai dai ya mutu alkur'an"AZIZA ta kalle BABA ta kalli Inna ta kalli Baba Tabawa taga kowa yana huci BABA ya kafe Tabawa da ido, mamaki ya kashe shi,sai ta kwashe da dariya, ga hawaye ga dariya.
"Tabawa fata kike min na mutu?"Baba Tabawa ta juya ta shige ɗaki, AZIZA ta ce " ba fa fata tayi maka ba BABA, kawai ka kira Baban birni ya zo mu tafi can, mu kaɗai, ni zan dinga dama maka fura ai na iya" Inna Gaji ta ce " ƙafarku ƙafata alkur'an tare za mu tafi, ba zan zauna da wannan makirar ba, a kassaramin rayuwa" BABA ya ce"gaskiya ne Gaji, dan a gaban idanuna ma ta nuna jira take ta bunne ni, AZIZA ɗauko sailula ki kira min Aminu yanzu".............
Zinariya ce✍🏻