4
by @halimahz
*RAGAMAR DAMISA*
```FreeBook.```
*©️Halimahz*
*SADAUKARWA GA:-*
Muhammad Kareem(MK)
_for your business advert DM ***._
*(4)*
da magriba Ammi na zaune kan dardumar sallah tana lazimi wayarta tayi ƙara, ta kalli Suhaila da ke kwance akan gadonta, alama tayi mata na ta miƙo mata wayar, Suhaila tayi micici da idanu tana marairaice fuska tace,"Ammi wallahi ba zan iya tashi ba, jikina duk ciwo, sai an kaini asibiti ma".
harararta Ammi tayi ta miƙe taje ta ɗauko wayarta, daidai kuma da katsewar kiran a karo na biyu, ta koma kan dardumar tana ƙoƙarin bin kiran sai ga shi an kira, ta ɗaga tare da karawa a kunne bakinta ɗauke da sallama, daga can ɓangaren Maman Khalid tace da ita.
"Matar Wakili shiru kamar ba ki duniya".
Ammi tayi murmushi tace,"kai matar nan yaushe ne muka rabu a biki".
"ohh kai jama'a ni kuma da mantuwa, wallahi na manta, sati uku kenan ba?".
"ehh fa wallah Amare har sun kusa wata...to ya kike ya iyali?".
"lafiya lau Alhamdulillah, dama nace bari na kira ki na daɗa jin batun rubutun da ake yiwa su Suhail, ana samun sauƙin kuwa?".
Ammi ta kai ƙwayar idonta kan wata baƙar leda da ke ƙasan dressing mirrow nata, taja ɗan numfashi sannan tace,"hmmm Maman Khalid lamarin yarana ai sai adu'a, wallahi kinga duk na tsawon wata huɗun da ake musu ashe basa sha, to gwara ma shi Suhail ɗin ya rantse min yace wallahi ya sha da yawa, shi kuwa uban ƴan zuciyar Allah ne ya matse min bakinsa yake labarta min bai taɓa sha ba yana dai haɗawa baƙinsa lemu, wai kar ya zubar ya sami zunubi tunda ayar Allah ce...to dai kinga wannan ɗin da muka karɓo last Suhail ne kawai yasha leda biyu, shima daga baya yace ba zai yiwu ya dinƙa shan rubutun samun sanyin zuciya ba Rashid ya dinƙa cutarsa...".
Maman Khalid ta katseta da cewa,"kema dai Ammin Suhail sanyinki akan yaran nan yay yawa, soyayyar da kike musu tayi yawa, kamata yay ki dinƙa saka su a gaba kina tursasa su, kuma ki dinƙa daurewa kina yi musu faɗa, amma ace yara kullum suke saka miki ciwon kai da damuwa alhalin su ba ƙananun yara ba, kina fa ji Yara irinsu da yawa an bawa rubutun nan sun sha kuma an sami sauƙi, gaskiya ya kamata ki dinƙa nuna musu ɓacin ranki akan komai ma, sannan idan haka ne kike haɗa musu drinks da shi mana kawai".
Ammi ta sauke numfashi tace,"to sai dai ayi hakan, amma batun tursasawa kam bai taso ba, don bana son ɓacin ran Rashid, kin san zuciyarsa yanzu sai yay fushi".
daga ɓangaren Maman Khalid ta kaɗa kai, tana mamakin Ammi ita kam akan ƴaƴanta,"to Allah shi kyauta ya kuma gyara mana...may be mu shigo garin naku a satin nan, zan leƙo insha'Allah".
"tou shikenan Allah ya kaimu, na gode a gaida yaran".
Ammi ta faɗa tana yanke kiran wayar, kuma daidai da shigowar Suhail ɗakin, yay tsaye bakin ƙofa shi bai yi sallama ba kuma bai shigo ba ya cake a wuri ɗaya rai a ɓace.
ta bisa da kallo har sanda ta sauke ƙwayar idonta akan goshinsa da yay malolo, fuskarsa duk ta kumbura sai huci yake yi, kai da gani kasan yasha wuya a hannun Rashid, ba sau ɗaya ba tasha faɗa masa ya daina biyewa Rashid suna dambe tunda ba ƙarfin su ɗaya ba amma sam yaƙi ji, ga shi yanzu ai duk ya mammauje shi, girgiza kai kawai tayi cike da rashin jin daɗi tare da yi musu adu'a cikin ranta.
bata ce masa kanzil ba ta sauke kanta ƙasa tana ci gaba da laziminta, tana jiyo sautin dariyar Suhaila na fita ƙasa-ƙasa, da alamu ma ƙunshe dariyar tayi tunda tasan matuƙar Suhail ɗin ya jita sai ya bata kashi duk kuwa da irin mugun shirin da suke yi.
kusan minti biyar tukunna ya baro bakin ƙofar ya ƙarasa shigowa ɗakin, da alama gajiya yay da tsayuwar, ta gaban Ammi ya wuce ya shiga toilet yay abinda zai yi ya fito, yana fitowa ta juya ta kalle shi tace,"ban hanaka shigar min toilet ba?, wani ƙato da kai gingirin gin shekaru ashirin da takwas ka dinƙa shigar min banɗaki, karka ƙara daga yau".
ta ƙarashe maganar tare da yin ƙwafa tana buga masa harara ganin ya kafeta da ido, ya ƙara ɓata rai ya wuce ya buɗe wadrobe ɗinta, ita dai kallonsa kawai take yi har sai da taga yana neman burkita mata kaya tukunna tace da shi,"me ka ajiye ne anan wai?".
farko shiru yay mata sai da ta ƙara maimaita masa tambayar tukunna ya buɗe baki yay magana murya a kumbure.
"magani".
"magani?". ta maimaita da mamakinsa.
"ehh".
"to dama wadrobe ɗin kama tayi maka da asibiti ko chemist?, ko kuwa gani kayi ina ajiyar magunguna a wurin?, dilla Malami rufe min wadrobe ka wuce ka bar min ɗaki, in magani kake nema kaje can ɗakin Wakili, ƙaton banza kawai".
"Ammi kullum nine me laifi fisabilillah, kina fa kallo shi ya fara dakar ƙirjina, kuma taya za'ai in ƙyale shi alhalin yana ƙasa da ni".
Ammi tayi tsaki tana ɗauke idonta daga kansa tace,"ni dai ka ɓace min da gani, kaje can kaji da zafin bugun da ka sha, bana son muzuran banza a ɗaki, shi mutum ba ƙarfi ba sai kurin banza da wofi".
ransa ya ƙara ɓaci yay ƙofa gadan gadan zai fita yana faman huci, karaf dariyar Suhaila a kunnensa, tunda ya shigo take kallon muzuran zafin dukan da yasha, fuzgewa kawai yake yi shisa ya rikice ma ya ɓige da neman magani a wadrobe.
juyowa yay a ƙufule yana jifanta da mugun kallo yace,"Sai naci uwarki wallahi, idan ni sa'anki ne zanji".
Ammi tace,"na gode da zagi, kaje don kanka".
"kiyi haƙuri".
dawowa yay ciki ya rutsa Suhaila a ƙarshen gado ya faffaleta da mari, tana ta neman ɗauki a wajen Ammi amma tayi mata banza tana cewa,"ke kika jawa kanki ai".
Rashida ta shigo ɗakin da waya kare a kunnenta tana faɗin,"bari na kai masa gani na shigo ɗakin Ammin". sai kuma ta sake cewa,"laa bama ya nan wallahi, kuma har ɗakinsa ma naje, amma ina ganin ko yaje masallaci ne". tayi shiru kafin ta sake cewa,"to zan faɗa masa".
ta shigo ciki tana zama a gefen gadon Ammi, a sace take kallon Suhail ta gefen ido wanda ya kwanta ya miƙe a gado yana jinyar jikinsa, ya rufe idonsa ya sarƙe hannaye a ƙirji.
Ammi tace da ita,"kin sauke abincin?".
"ehh".
"to duk wanda ke jin yunwa ya zuba nasa, Ɗan gidan Wakili yaci?".
"ai Ammi shi na shigo nema, ya fita ya bar wayarsa anata kira".
Ammi ta miƙa mata hannu don karɓar wayar tana faɗin,"wane ya kira shi?".
"wannan ɗan ajin nasu na jos".
"ohh Allah sarki".
Rashida ta waiga bayanta tana kallon Suhaila tace da ita,"munafuka".
ita kuma ta murguɗa mata baki tana faɗin,"ni ba munafuka ba ce sai dai in kece munafuka".
ta faɗa kanta tsaye saboda ta san tana da me tare mata a kusa duk da sunyi faɗa, aiko ba shiri Rashida ta haye kan gadon zata kai mata duka Suhail ya buɗe idonsa yana doka mata tsawa da cewa,"wallahi kika taɓata sai na ɓallaki a wurin nan, shegiya me fuskar ƴaƴan aljanu". ya faɗa yana yin ƙwafa.
ta haɗe gira tana cewa da shi,"amma Yaya kana ji fa rashin kunya tayi min, munafuka fa tace min ni sa'arta ce?".
ya galla mata uwar harara yana cewa,"ke munafurcin uban me tayi miki da zaki fara kiranta da hakan, in rainin ne ma ai ke kika so ta raina ki tunda bata kula ki ba tun shigowarki...sauka akan gadon nan ko in wulla ki da ƙafa".
Rashida ta zumɓuro baki gaba tana ƙunƙuni ta sauka akan gadon, ta fita daga ɗakin kamar zata yi kuka, sai dai idan basu je kwanciya ba amma sai ta daki bakin yarinya.
idanun Suhail akan Suhaila yace,"zo nan".
ta ɗago daga duƙen da take tana shashsheƙar kukan dukan da yay mata, tasowa tayi a wurin ta dawo kusa da shi ta zauna, ya miƙe zaunr yana sa hannu ya goge mata hawaye yace,"sorry ƙanwalle, please daina kukan kinga tun ɗazu kike kuka kanki zai yi ciwo".
taja majinar hanci tana faɗin,"Yaya wayata".
yaci gaba da lallashinta yana faɗin,"kiyi haƙuri zan siya miki wata kinji, shi da ya fasa miki alhalin baki masa komai ba yaje don kansa, ai akwai Allah".
Ammi ta sako baki tana cewa,"taya kuwa yarinya ba zata dinƙa shan duka ba bayan kana sakata a gaba kana koya mata rashin kunya".
sannan ta kalli Suhaila ɗin tace mata,"karki daina rashin kunya kici gaba, kece kullum a wahale tunda shi dai fita yake yana barinki da su a gidan...kuma tashi ki fita ki kira min Yaya R".
Suhaila ta ƙwalalo ido waje tana neman ruɗewa tace,"Ammi duka na fa zai kuma yi".
hararar da Ammi ta banka mata yasata rufe baki tana miƙewa cikin sauri ta fita ta bar ɗakin tana faman dukan ƙafafu a ƙasa. Ammi ta kaɗa kai tana faɗin,"Allah ya shirya min ku gaba ɗaya".
har kusan sallar isha'i Suhail na ɗakin nata, ita dai ko ta kansa bata bi sabgogin gabanta kawai take, shima kuma tun ɗazun bai ƙara magana ba ido kawai yake binta da shi a duk abinda take yi ɗin, yana dai jinta tana magana ƙasa ƙasa kuma sarai ya san da shi take.
turo ƙofar ɗakin suka kai idon su wajen, Rashid ne ya shigo yana ƙarasa saka riga, suna haɗa ido da Suhail yaja tsaki yace da shi,"ka daina kallona".
ya faɗa yana nunasa da yatsa, Suhail ya diro da ƙafafu ƙasa yana cewa,"an kalleka Rashid Wakili ka ɗauki mataki"..
ba shiri Ammi ta miƙe tana cewa,"a'a a'a ku tsaya in aiko a yi muku waje da kayan ɗakin yanda zaku fi samun space ɗin dambatuwa, amma a haka ai ba zaku daku yanda ya kamata ba wurin yay muku kaɗan kam, ba kwa kallo a indian film ƙaton fili ake bawa Actor yay duka son ransa".
tayi maganar sa'ilin da take shiga tsakiyarsu tana ƙara faɗin,"Boss da shegen taurin kai Actor kuma da shegen zafin zuciya da rashin haƙuri, kuma Actor ya jibgi Boss ƙarshe a barsa da muzurai da ciwon jiki...yanzu dai ni tunda ɗakina bana madambata ba ne ku muje in raka ku ɗakin Wakili, can yafi girma nesa ba kusa ba, ga Ac ga fanka kuyi abinku cikin jin daɗi, amma ni nan ai sai ku tarwatsa min ɗan mudubin da aka siya min da ƙyar, gashi ba uba gareni ba balle in kai masa kukana yaji tausayina ya siya min sabo".
duk su biyun suka sauke dogon numfashi haɗe da ƙwafa me ƙarfin gaske, tana jin hucinsu har saman kanta, tabbas ta barsu sai anyi faɗan da yafi na ɗazu, and idan tayi maganar baji zasu yi ba, Ubansu ya jiyo su kuma duk ya kai su station a daren nan, so is better ta yiwa tufkar hanci, still tana tsakiyarsu bata fita ba ta kalli kowannen su da kumburarriyar fuskarsa tace,"ku nemi wuri ku zauna".
Kowa yay carko carko kamar basu jita ba, ta rarumi hand fan da ƙyar ta iya ƙwalawa Rashid a kafaɗa tana cewa,"ba magana nake muku ba".
kowanne na faman fankama ya zauna a gefen gado, ta shiga toilet ta barsu a wajen, bayan few minutes ta dawo ɗauke da ƙaton roba, ruwan ɗumi ne acikinsa tasa gishiri da dettol sai ƙaramin towel a hannunta.
ta ƙaraso wajen su tana kallon tazaran da suka bari tsakaninsu, ta ɗaure fuska tace,"ku raba ni biyu to". sannan kowa ya shiga matsowa har suka haɗe.
towel ɗin ta tsoma cikin ruwan ta fara gasawa Suhail fuskarsa zuwa kafaɗarsa, sai fama take yi da shi akan ash da wash wai zafi, idan ya ture hannunta ita tasa hannu ta bige shi, a haka har ta gama da shi tukunna ta koma kan Rashid shima ta shiga gasa masa nasa, shima leɓensa duk ya farfashe yay ganda, yana jin zafi sosai amma saboda kar Suhail yaga ragwancinsa haka ya daure bai ko irin runtse idanun nan ba.
ita dai Ammi adu'a kawai take yi musu cikin ranta har ta kammala, ganin har lokacin basu saki ransu ba haka basu bar faman huci ba yasa tai ƙasa da murya a raunane tace.
"kuyi haƙuri wataran ba zaku ganni ba balle in hanaku yanda kuke so kuce na takura muku".
Rashid ya tsayar da idonsa akanta yana faɗin,"ina zaki je?".
"babu wani waje da zanje, ina nufin idan rai yay halinsa, kunga idan na mutu ai ba ruwanku da takura sai kuci karanku babu babbaka".
a tare suka yi jikinta suka rungumeta, Suhail me ƙawa zucin uwa yace,"ba zaki mutu ba Ammi". ya faɗa idanuwansa a runtse yana girgiza kai yana jin wani zafi a ƙasan zuciyarsa.
"mutuwa ai ta zama dole Suhail, zan mutu dole kam, zan yi nisa da ku ta yanda ba zan dinƙa shiga rayuwarku ba".
tsam suka ƙara rungumeta furucin nata na tsuma su, Suhail kawai ke faɗin ba zata mutu ba shi kuwa Rashid ma ya kasa cewa komai, haskowa kawai yake a idanuwansa yanda rayuwa zata kasance musu idan babu ita. saukar ruwa me ɗumi akan ƙafarta yasa ta ɗago kawunan su tana kallon su, ko da ace bata ɗago da su ta kalle su ba tasan ruwan hawayen waye, Suhail baya kukan fili sai dai yay na zuciya, shi kuwa dama Rashid sai in ba ita abu ya shafa ba.
"Ammi bana so mu rasa ki, don girman Allah ki daina faɗa mana cewa zaki mutu ki barmu, kiyi haƙuri indai faɗa ne mun daina".
da haka dai ta haɗe su tayi musu nasihar da ta saba yi musu a kullum, kuma kamar kullum ɗin suka karɓa har suka ware suka shiga sabgarsu kamar ba waɗanda su kai faɗan a mutu ba ɗazu, dama idan ka gansu zaka zaci Hassan da Hussaini ne, musamman in suna good time.
bayan sallar isha'i sun gama cin abinci Ammi ta kalli Rashid tace da shi,"tashi muje ɗakinka".
miƙewa yay yabi bayanta suka wuce, suna shiga ta buɗe wadrobe ɗinsa tace,"ka kwashi kayan da kake so sai akai masa sauran, askin kuma sai ka bari sai da safe sai kaje ko tunda yanzu dare yayi, kuma Daddyn ma ya shiga ɗaki".
Rashida na jin hakan ya haɗe rai ya kauda fuska gefe, bai ko tanka mata ba kuma baida alamar zai tanka ɗin, ya zuba hannayensa a aljihu sai hura hanci yake yi.
itama bata sake cewa da shi komai ba ta shiga fito da kayan nasa duka daga cikin wadrobe, sannan ta shiga ware waɗanda ta san yana son su sosai, saboda duk wasu kaya nasa inda yasa yana faɗa mata irin son da yake musu, har ma sai ya tambayeta idan sun masa kyau tukunna yake iya fita da su, amma idan bata ce sunyi masa kyau ba ko da a wasa ne to duk kyan kayan da tsadar su ya rabu da su kenan har a bada.
lokacin da Ammi ta gama fidda masa da waɗanda ta san yana so ta ɗauko trolly ta saka su aciki ta kulle ta taka stool ta ɗora can saman wadrobe.
"ga waɗannan na ware maka nan nasan kana sonsu, wannan kuma bari na kai masa".
tayi maganar tana tattara kayan nasa, shi dai yana tsaye yana jinta kuma haka bai waigo ya kalleta ba.
"akwai abinda zaka ƙara yi ne karka koma ka zauna a parlon kuma a sami co'incidence ɗin shigowarsa".
bone fuska ya ƙara yi ganin tana kallonsa yasa ya juyar da fuskarsa side ɗin da ba zata kallesa ba. tayi murmushi tana faɗin,"ni dai babu ruwana idan akwai wurin aski da asuba ka taimaki kanka kaje ka aske kafin kaje gaisuwar safe".
"gaskiya gaskiya ni Daddy yana shiga gonata, gani da ɗan ƙaramin kai haka kawai sai inje inyi aski, kan fa dawowa yake kamar an sammin, ni gaskiya babu abinda zan aske hula zan ta sakawa har ya tafi, shima da yana saurayi ai ya tara, Hajjo ma ce tayi da iron yake goge nasa tsabar gayu".
sosai Ammi ta shiga yin dariya, ana cikin hakan Daddy ya turo ƙofar ɗakin, ya watsa musu wani kallo su duka sannan yace da Ammi.
"ajiye masa kayansa". za tayi magana ya ɗaga mata hannu ya dakatar da ita,"ki ajiye kawai nace, kiyi ta ɗaurewa yaro gindi yana son ransa, kima rasa da wanda zaki yi autan sai wannan ƙaton banzan da babu hankali a tare da shi, to ki basa kayansa ya biyo ni da shi, kuyi sallama don daga can station zan kai shi abi min hakkin dukar min ƴa da yay".
salati Ammi taja jin furucin Daddy, shi kuwa Rashid da sauri ya isa gabansa yana faɗin,"Daddy laifin me nayi?".
"wa kuma ya doka Daddy?, ai yau duk ma bai zauna ba a gidan". cewar Ammi cikin kalar tausayi.
"Uwata ta kaina". Daddy ya ƙwala kiran Suhaila, kamar jiran kiran take yi dama sai gata a gabansa tana jan ƙafafu hawaye duk ya wanke mata fuska, tsabar sharri irin nata ko tsayawa ta kasayi wai tayi karaya a ƙafa.
Ammi da Rashid suka buɗe baki suna kallonta, Rashid ya tamke fuska cikin ɗaga murya yace da ita,"tashi tsaye ko inyi ball da ke, munafuka ba ɗazu kika gama zuwa yawonki ba shine yanzu zaki ce kin karye saboda baƙin sharri".
sai ya kalli Daddy yace da shi,"Daddy wannan ƴar fa baƙar munafuka ce, sharrinta yafi na wuta, ka bani dama in zane mata jiki yanzu zaka kalla ta miƙe da ƙafafunta".
har ya kai aya Daddy na banga masa wata banzar harara, ya ƙara ɓata masa rai, lura da hakan yasa Rashid shafo gashi yana faɗin,"Sorry Daddy".
Daddy yace da shi,"ai tunda zaka zagi Uwata a gabana to kuwa kafi ƙarfina Rashid, wannan lamarin kam sai dai in dangana shi da hukuma, Uwa ai bata fi Uwa ba, ban sani ba ne ko don na zagi taka ɗazu shine kake ramawa yanzu, to wuce muje zan kai ƙararka gaban hukuma".
ya shiru kafin ya buga masa tsawa yana sake faɗin,"nace ka wuce muje ko, kai da ba zaai maka magana sau ɗaya ba kaji".
Rashid ya duƙa ya ɗebi kayansa, yay gaba yana faman daɗa cin magani, Ammi dai nata bawa Daddy haƙuri, a parlo Daddyn yabi Suhail da kallo yace da shi,"kai baka duketa ba ne daka nemi wuri ka zauna ka harɗe ƙafa kamar gidanka".
Suhail ya miƙe yana yin ƙasa da kansa, Daddy yace da Ammi,"ki rufe ƙofarki don ba lallai a samu belin su ba a daren yau".
"kayi haƙuri don Allah Daddy, dama fa yanzu yake da niyyar ya kawo maka kayan, askin kuma dama ni nace ya tsaya zan raka shi, dalilin da yasa yay dare kenan, amma ita me sunan Hajjo ɗin ai laifi tayi shisa ma suka ɗan bugeta kuma ba wani bugu suka yi mata ba".
bai ko waigo ya kalli inda take ba yace,"a'a wannan bayanin naki kuma ki adana shi kya faɗesa a gaban alƙali, ki kuma rufe ƙofa shine abinda nace da ke".
a compound su Suhail suka tarar da almajirai su kusan goma sun bi layi, sai Umar, Usama, Bilal a tsaye a gefen mota, Suhail ya ɗan kalli Rashid kafin yace da shi,"wai yaran nan ba'a hana su shigowa da daddare ba".
Rashid yace,"gidanka ko gidansa?".
"gidansa".
"to naka ido tunda ba kai ne kake rasa hutun ba".
suka isa bakin mota daidai da fitowar Daddy daga part ɗin Hajiyarmu, ya dubi Rashid yace da shi,"ka rabawa yaran can kayan kazo mu tafi".
Rashid ya tafi ya watsa musu kayan yana cewa da su,"ku ɗauka kuyi waje, kuma kar in ganku a ƙofar gidan nan".
#MssAnyway
#Gamjiwriters
#Repost
#wattpad:-mssanyway
#arewabooks:-mssanyway