Chapter 23
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 44-45
Kallo Nur ta bita dashi cike da Mamaki, yanzu ta shigo cikin gidan tana murnan zuwan iyayenta, ko mene ne yasata shiga cikin damuwa Kuma, karasowa Nur ta yi bakin gadon ta zauna, sannan ta sake kallon Bilkisu da har yanzun take share hawaye, wani tunani ne ya fado amta arai, dan haka ta kalli Bilkisu tace, "Aunty dan kinga 'yan gida kike kuka?" Dariya tasoyi Amman idonta na sauka akan takardan take hannun Bilkisu saita hade fuskar acikin zuciyarta tace, "Kamar Aunty Bilkisu nada damuwa da takardan nan, me yasa take matseta cikin hannunta?" Ganin babu mai Bata amsa ta mike tare da cewa "Aunty Bilkisu wai mene ne? batakai ga Bata amsa ba wayarta tai kara, saurin kallon wayar Bilkisu tayi sannan ta amsa kiran, daga yanayin amsa da take badawa Nur ta gane da Yaya Abdallah take wayar, bayan amsa ya jikin da ya mata sukaci gaba da hira, murmushi Nur taga ta yi kadan, dan haka ta fice domin ta bata wuri ta sake da mijinta. Tun daga wannan ranar Nur ta saba da waya da Poul, bayan Bilikisu tagama wayar da Abdallah ko wanne dare Nur zata Kira Poul susha hira, sosai Nur ke sakewa da Bilkisu bata boye mata komai, duk da cewa tun da Bilikisu ta samu cikin ta rage walwala, Mamy da aunty kuwa sai abin da Bilikisu keso ake dafawa a gidan, sosai suke bata kulawa, rashin walwalan Bilkusu be damu Nur sosai ba, domin tanaji ana cewa masu cikin sai a hankali dan haka idan taga ta kwanta ta yi shiru saidai ta dauki wayarta ta kira Poul, sosai suka saba, duk da cewa bata tunanin auren zai iya yuwa tsakanin su.
BAYAN WATA BIYAR
Tuni su Nur suka kammala jarabawa har sakamakon ya fito, dan haka Abba ya fara mata ciko cikon makarantar koyon aikin jinya kamar yadda take so, a yanzu burin Abba be wuce yaga ta fara zuwa makarantar ba, sabo da yanzu ya yadda da nutsuwarta, kuma ya tabbatar eh lallai karatun take so ganin bata taba kawo wani gida da sunan saurayiba, haka kuma bata da waya hakan be taba damunta ba, a yanzun islmiya kawai take zuwa, ita ko Bilikisu cikin ta ya fito sosai yayi girma, sai dai har yanzun bata da walwala ko waya suke da Abdallah hiran tasha banban da ta da.
*****
"Na rasa dalilin ki na kin yiwa Abdallah magana ya turo kudi yariyar nan ta fara zuwa awo, abin da fa baka son a maka karkawa dan wani, yanzun in da yarmu ce ai bazamu so ace ciki har yana dhirin shiga wata na takwas ba batare da an san lafiyarsa ba" Cikin rashin walwala Aunty Saratu tace, "Amman na ce miki kiyiwa Bashir magana ai yazo ya kaita, na mishi magana yace wai mijinta bai sanar dashiba dan haka bazashiba, in da kece kikamai magana ai bazai baki wannan amsan ba"
Wanni irin kallo Mamy taiwa Aunty sannan tace, "Ai ni bazance ya kaitaba haka kurumba, dole sai an bashi kudi tun da ba hidimarsa bace, ai be dace kawai ace yayi hidimar da ba tashiba, ko Abban su da nace ko zai bada cewa yayi yayi bashi da kudi sabo da yayi hidimar makarantar Nur bashi"
"To a yiwa Baffa magana mana" Aunty fada tana kallon Mamy, saida Mamy ta karewa Aunty kallo sannan tace, "Ikon Allah, to waishi Abdallah cewa yayi bashi da kudinne? Nifa banson iskanci, zan kirashi naci mishi mutunci wallahi"
"A'a Karki kirashi, ki bari zan kirashi" Aunty ta fada tare da mikewa ta nufi daki, Nur dake gafe Mamy tabi da kallo, ganin inda take huci tace "Mamy kiyi hakuri" Batare da tace komaiba ta mike ta shige daki, dan haka itama Nur ta mike ta koma daki inda ta samu Bilikisu na waya da Abdallah, juyowa ta yi domin ta basu waje, wannan karon tana fitowa dakin autny ta nufa, saidai tana shiga ta samu anuty tana kaiwa da kawowa adakin, ganin shigowan Nur tai saurin daukan wayarta ta danna sannan tasa a kunnenta, zuwa can ya sauke tare da fadin "Busy" Nur ce tace "Yaya Abdallah yana waya da Aunty Bilikisu" Waigowa Aunty Saratu ta yi domin sai a yanzun ta gane ashe afili tai maganar ba azuciya ba, zama Aunty ta yi yayin da yanayinta ke nuna tana cikin damuwa, zuwa can wayarta ta fara kara dan haka ta kalli Nur tare da cewa Nur bani waje zanyi waya, mikewa Nur ta yi ta fita tare da jawo mata kofar, haka kawai taji tana son sanin mai aunty zata ce da Abdallah, har tayi nisa da kofar ta dawo a hankali ta tsaya, yayin da ta jiyo ayunty na cewa "Abdallah kwanaki da nai maka magana naga kamar kana nuna bakasan Bilkisu nada ciki ba?" Kara kasa Kunne Nur ta yi zuwa can taji ta sake cewa "Eh mana, tun lokacin datai rashin lafiya nan" A'a dakata mana Abdallah abin ba tashin hankali bane yarintane, nima harda laifina danasani tun lokacin na gaya maka tunda Bashir suna dawowa ni ya bawa sakamakon..." Shiru ta sake yi tsayon lokaci, da alama katseta yayi, zuwa can tace "Innalilahi wa innalaihir raju'un, Abdallah ka rufa mana asiri, tsaya kaji, ai shine nace ka saurareni" daganan Nur Bata sake jin komai ba dan haka da saurin tabar wajen, afalon ta zauna tai ajiyan zuciya, nan danan taji wani irin tashin hankali ya dirar mata, bata gama dawowa cikin hankalinta ba taga wucewar Aunty arikice zuwa dakin Mamy, wannan lokacin bata da kwarin bin bayanta dan haka ta mike ta nufi dakinsu, Bilikisu ta gani rike da waya sai Kara take Amma taki dauka, cike da damuwa Nur tace Aunty ana kiranki awaya"
Cikin wani irin yanayi tace "Bazan iya daukaba Nur, domin gabana faduwa yake haka kawai." Leka wayar Nur ta yi tare da fadin, "Yaya Abdallah ne fa?" "Eh na gani gabana faduwa yake Nur yanzu maka gama waya dashi" Bilkisu ta fada tare da kwantawa a gefen wayar idonta cike taf da hawaye.
Haka Abdallah yaita kiran wayar Bilikisu har sau Babu adadi taki dauka, kwanciya ta yi cike da damuwa, hakama Nur take kiyasta abin da ke shirin faruwa cikin zuciyarta, saidai tana korewa domin ko a mafarki batason hakan ya kasance, haka gidan ya wani Babu wani walwala, adaren ranar Aunty Saratu ta shigo dakin Nur, bayan sun mata sannu ta ce da Nur ta jirasu a waje zasuyi magana da Bilikisu, mikewa ta yi ta fita, sai bayan kusan awa guda sannan Aunty ta fito, lokacin da Nur ta koma dakin samun Bilikisu ta yi Cikin kuka sosai, dan haka ta zauna a takure, daren ranar cikinsu babu wadda ya runtsa, lokaci bayan lokaci Nur na jiyo ajiyan zuciyar da Bilkisu take yi, yayin da hakan ke jefa Nur cikin damuwa, tare da kara yin nisa da tunaninta dan haka bacci ya gagareta saidai ta juya ta kalli Bilkisu sannan ta hadiyi yawo saboda makogoronta dake bushewa, abin da take tunanin yana shirin faruwa take ayyanawa akanta dan haka damuwarta gaba yake karawa ba baya, washegari bayan Nur ta gama shirin islamiyya ta fito domin yiwa su Mamy sallama, babu kowa acikin gidan dan haka ta nufi falon Abba, tukafin ta ksa taji muryan Baffah na cewa, "To ai wata takwas kenan da auran, wannan kawai so yake ya jawo mana kananan maganganu, sai ya bari ta haihu kafin yace wani abu, ai yanzun dama cikin be isa haihuwaba ko?" Muryan Abba taji yace "To ai shi cewa yayi ma gaba daya be kusanceta ba"
"Innalilahi wa innalaihir raju'un" Baffa ya fada yayin da taji Muryan Yaya Bashir yana cewa "Ba yace sati biyu ya rage ya dawo ba, ni inaganin a bari ya dawo" Adaidai wannan lokacin Nur taji kamar motsi a bayanta, dan haka ta karasa tare da sallama, amsan sallama suka yi cikin sakin fuska har ta gaidasu ta yi musu sallama bataji an cigaba da maganar ba, bayan ta dawo gidan ma shiru tajishi, Bilikisu kuwa cikin tsananin tashin hankali ta sameta, kuma tana kula har yamma Yaya Abdallah be Kira Bilikisu cikin waya ba kamar yadda suka saba, a daren ranar Nur na zaune adakinsu wayar Bilikisu ta dauka da Nufin Kiran Poul domin jiya Bata samu sunyi waya ba, number ta saka tana kokarin kira taji muryan Kaka kamar daga sama, cikin daga murya take cewa, "Ina take tazo ta tafi gidan iyayenta, bazamu dauki kazanta da ba namu ba, yau na tabbatar da mutanen gidan nan basa kyaunar Abdallah, yariyar tashigo gidanshi da ciki kuce Wai yayi shiru? To idan shi kun Isa dashi ni baku isa daniba" a firgice Aunty Bilkisu ta mike tsaye cikin tsananin rudewa, ganin haka Nur ma ta mike tare da ajiye wayar hannunta, tuna irin masifar da Kaka tai mata kwanaki akan Abdallah yasa tai saurin nunawa Bilkisu bayi tace "Kisha Bilikisu" batai musuba ta shige ciki yayin da Nur ta kulle bayan ta cire key jikin kofar sannan ta koma gadon ta kwanta, batajimaba taji an turo kofar, Kaka ce su Mamy na bayanta suna Bata hakuri, Amman sai masifa take yi, neme nema ta fara adakin tare da cewa "Ina tantiriyar take?"
Cikn nuna halin ko in kula Nur tace "Bata muku sallama ba? Yanzun Babanta yazon ya dauketa, ajiyan zuciya Kaka tayi tare da cewa "Yafi masu su je ce su karata, ashe sunsan yarsu lalatacciya ce suka lika mishi, Allah ya Isa tsakaninmu dasu, wato badan Allah ya dubi Abdallah ba dan wani zamu ma bauta acikin gidan nan, yanzun sai ku kara tabbatar da cewa gemon nan nashi bana banza bane, juyawa tayi kansu Mamy ta rufesu da fada ta inda take shiga batanan take fitaba, sannan ta fice adakin tana cigaba da tsinewa Bilikisu da iyayenta,, bin bayanta Many ta yi, Itako Nur suna fita ta bude Bilikisu cikin matsancin damuwa take zubar da hawaye, wannan karon harda shashshekar kuka ahaka su Mamy suka dawo suka sameta, lallashin Bilkisu suka kayi tare da kara kwantar mata da hankali, suna nuna mata rikicin tsofa ke damun Kaka amman ta bari Abdallah ya dawo za'a samu mafita cikin sauki, saidai duk kokarinsu nason su kwantar mata da hankali be gamsar da Bilkisu ba domin ko bayan fitansu kuka taita yi, Nur ma tun fitan Kaka take share hawayen tausayin Bilikisu domin idan har Abdallah yace cikin ba banshi bane to na waye? Juyawa ta yi ta kalli Bilkisu dake matsancin kuka, sam bata ta rawan kai ko kadan, tunda Abdallah yabarta agidan kuwa za'a iya kirga fitan da ta taba yi Kuma duk inda zasu tare suke zuwa, bata da rawankai ga kirkin dake gareta, kuka Nur take tsawon lokaci, zuwa can ta saurara tare da kallon Bilikisu tace "Ki yi hakuri ki daina kuka"
Kara rushewa ta yi da kuka tare da cewa "Ta Yaya zan daina kuka Nur? Ina mai bakin cikin iyayena suji wannan mummunan labarin, ina rokon Allah ya dauki raina kafin muyi ido biyu dasu ina cikin wannan halin, Nur Babana, ina tausayin shi, bansan me zanyi ba, narasa in da zansaka raina Nur, bani da bakin da zan wanke kaina, amman ni ba yar isa bace, sadai ba abin da na sani da zan fada ya wankeni, Nur zo ki taba kirjina kiji yadda yake yi, Nur bayan bugawa da yake inajin kamar zaiyi tsalle ya fito."
Kara fashe Nur tayi da kuka, haka suka raba dare suna abu daya, kafin safe gaba daya idonsu yayi luhu luhu ita da Bilikisu gaba daya, ciwon Kai ya hana Nur zuwa makaranta, halin da Namy da Aunty suga Nur aciki be basu Mamaki ba, domin suma cikin damuwa suke, tunda ga ranar abincima saidai adancishi fan dole acikin gidan, Nur ko har tafi Bilkisu ramewa sabo da ta saka damuwar a ranta duk da cewa Bilkisu Koda Yaushe cikin kuka take Nur kuwa tsabar tunane tunen da nemo mafita tasa a azuciya dan haka duk ta fige, a daddafe aka cika sati biyun da Abdallah yace zai dawo, be dawo a ranar ba sai Washegari da tsakar rana, Bashir ne ya daukoshi kasancewar gidan babu yara masu oyayoto basusan da shigowanshi ba Saida sukajiyo Muryanshi shida Bashir afalo, mikewa Nur ta yi ta fara kokarin fitowa domin gani take Yana dawowa komai zai warware, tana fitowa suka yi Ido Biyu dashi Yana zaune yayi wani irin fari tare da tara kasumba fiye da baya, kananan kaya ne ajikinshi dan haka sosai taga ya canza, kallo daya ya mata ya kauda kai, gefen Yaya Bashir Nur ta Isa sannan tace "Sannu da zuwa Yaya Abdallah" kanshi ya juyar wani gefen batare daya amsa ba, har sau biyu Nur ta Kara mishi asannu da zuwa be amsa ba, dan haka ta juya ta koma daki, Mamy na lura dashi saidai damuwan dake gabanta ya dame wannan, dan haka batabi takai ba, abincishi yaci sannan suka fita tare da Bashir, Misalin 8 na dare yana kwance a dakinshi na gidan Mamy Abba ya kirashi cikin waya, bayan dauka yace yazo falo suna jiranshi, mikewa yayi ya fito anan ya cika da mamaki ganin falon cike da mutane ciki har da Baban Bilkisu da kanninsa, zama yayi akasa wannan karon jikinshi yayi sanyi sosai, Baffa ne yace "To Abdallah mun hadu ne anan dominku ku biyu kaida Matarka, ga iyayenka anan, ga nata, sabo da muna son mu tabbatar da adalci, tun kana can kace Bilkisu ta tafi gida mukuma munga hakan ba daidai bane, dan mun tambayeta tace ciki naka ne, to yanzun gata gaka ga Kuma iyayenta ga naka, kace ba naka bane; tace naka ne"
Sunkuyar da kai Abdallah yayi tsayon lokaci, zuwa can yayi gyaran murya cike da nutsuwa ya ce, "Baffa ina son zan mata tambaya daya zuwa biyu."
Gaba daya falon aka hada baki wajen fadin "Kana da damar yin hakan."
Juyawa yayi ya kallin Bilkisu yace, "Bilkisu har muka cika kwana shidda na kusance ki?"