MATA TA CE LABARI MAI CIKE DA SARKAKKIYA
CHAPTER FIVE & SIX
by @misshajo
π©ββ€οΈβπ©β€βπ₯ *MATA TA CE?* β€βπ₯π©ββ€οΈβπ©
By
*Hajara L Sadeq*
@Miss Hajo
```2023 GIFT π¦
Marubuciyar
ππ½
Auren wata Tara
Ni da Yaya Arman
Komai muk'addari ne
Najmat Abiy
Khadijatul sabren
And now
Mata ta ce```
19β02β2023
π ΏοΈ................*5 & 6*
Washegari Bayan dawowarta school da la'asr Tana Taya mama Aiki a kitchen Taji shigowar zuly fuska Hade ta shako ta Tare da Jan kunnenta ta ce.
"Dan ubanki kodanma Ashe shegiya ce Ba uban Dan Uwarki Bance Idan nayi bak'o ko kafarki Karna Gani kin leko ba eh shine Dan Kinganni da bako kike lekani da window ko?
a matukar rude ta ce "Wlh Aunty Zuly Ina tare da mama wlh Ban leka ki ba ",Ajiyar zuciya zuly ta sauke Dan dama Rigataferiya ce tayi Tana wurgata ta ce
"Ai Dan Karkiyi mtwss "kafin tayi Gaba "girgiza Kai mama Tayi Ta na kamo hannun nasren da Tayi narai-narai da idanu Zatayi Kuka ta Girgiza Mata Kai ta ce ".
"a a a Yan Mata na Karkiyi Kuka kici Gaba da hakuri ki cigaba da toshe kunuwanki Akan duk abunda za ace Maki wata Rana sai labari kinji".
gyada Mata Kai Tayi ta na kirkirar Murmushi "Mika Mata karamar Wayarta tayi ta ce "amshi Maza koma Dakinmu ki kunna radio kiji Nasan anfara shirinki da kike so".
"Murmushi Tayi ta na amsa tayi waje a farfajiyar gidan ta had'u da Ashraf wanda yana ganinta ya taso Duk Irin yanda yake janta da Hira kin sake Masa tayi Labaran Dariya ya dinga Bata Wanda ba Shiri ta biyesa hada Dariya Daidai kunnowar motar abba gidan ko lura dashi Basuyi ba Irin Kallon da Yake watsa Musu ne ya Sanya nasren Shan ruwan jikinta tare da saurin Mikewa Tana in'ina ta ce
"Abba sannu da dawowa"Bai Bata Amsa ba Tayi Saurin wucewa bangarensu A zuciyarta ta na Mamakin me yasa Abba Duk Soyayyar da Yake nuna Mata Amma Kuma Dan Ashraf ya gwada ya na sonta yake nuna Rashin son tarensu karara dukda ba sonshi take ba Amma batajin dadin Hakan Kenan Bai daukeeta dayan ba da Yake nunawa?.
shiru tayi Ta na tunanin tsohuwar rayuwarsu da Mamanta a garinsu na kazaure kafin su dawo Nan Kano Irin gori da tozartar da tasha a wajen dangin mama Kowa na garin ba Wanda Baisan da zaman shegiya bace ba Wanda yasan da ubanta Gashi Mama Bata Isa ta Kare kanta ba Tunda Ita nasren din ta banbanta da kalar Hausawa.
Sosai dangin Mamanta suka nuna Mata kiyayya Karara Gashi Daman Mahaifan Mama basa Raye Abinci ma gagararsu yake Dakyal Da Taimakon Allah ta samu ta kammala primary school Wanda a js one mama ta gagara Karfinta ya tsaya Bata ci Gaba Da Makaranta ba babban tashin hankalin da ya barosu da garinsu Irin yanda maza ke kokarin b'ata rayuwar Nasren din sau Kusan Ukku Allah Yana tsallaketa Gashi duk inda Tayi Ana santin Kyanta Saidai kuma Irin tsangwamar da ta taso dashi na ita shegiya ce wasu Nace mata mayya Har a Makaranta islamiya Wanda dalilin Hakan ya Sanya ta Daina islamiyar saidai mama Tayi Mata Kari Dan mama Akwa ilimin addini Sannan zuwansu Kano ma Saida suka Sha gararanba Kafin Allah ya taimakesu su samu Aiki anan gidan Alhaji Sani Mai chanji babban Dan chanji ne da yayi Suna Mai halin gaske Matanshi biyu Da Yara Da dama Uwar gidansa hajiya lami Bata da mutunci Haka yaranta Amaryarce kawai Mai saukin Kai haka dai suke hakuri a gidan dukda tozarcin Da cin mutuncin da mama Da yaranta suke Musu Dan Maman nasren mace ce Mai matukar hakuri da kawaici Hakan yasa ta jure saboda Alhajin ya na matukar mutuntasu kamar danginsu Haka Yasa nasren makarantar Da yaransa suke dukda Ta Dan girme s s two Yanzu Dan sa'anninta da dama sunyi candy a Halin Yanzu ta na shekara Kusan 20 a duniya Amma a Ido baka cewa takai saboda Rashin sabo da mu'amula da mutane ya Sanya Bata da wani ishshen wayau Musamman fagen magana Dan ko fad'a nasren bata iya ba.
"Dogon Numfashi taja Bayan dawowarta Daga dogon tunanin da ta Lula Tana kwancewa a katifarsu ta kamo gidan radio ta na saurara a Haka bacci ya Dauketa dukda Bata Saba baccin Yamma ba.
Haka rayuwa Taci Gaba nasren naci Gaba da jure duk wani Kyara da musgunawa Sannan Tana kokarin janye jikinta da Ashraf dukda Hakan ya gagara Duk samarin da suka nuna Suna sonta batama Basu dama Daman ba inda ake barinta zuwa Dan Alhaji yace ko waje Kar a barta ta leka Daga school driver KE kaisu ya maido su Hakan Bai dameta ba saboda Daman abunda take Bukata a Hankali Ashraf ya Fara sace Zuciyar nasren wanda tun Bata sani ba ta afka kogin soyayyarsa.
Soyayya suke a boye Amma in yabata kud'i ko wani Abu Bata amsa haka har suka shiga s s three Wanda Ashraf ya ce jira yake kawai ta Gama Makaranta ya rikice Dole Abba ya D'aura Musu Aure Indai Suna kaunar ganinsa a raye
ββββββ
Belah ta shiga shekara Guda Wanda momy ta shirya Mata gagarumin birthday acewarta Ta cikawa mahaifiyarta burinta dukda aliyu baiso haka ba a Gida Sukayi shagalinsu aka Sha Mata Hotuna a hadaddiyar rigarta da tun Mamanta na Raye ta saya Mata Yanzu tayi kafa yawo ko Ina ga barna ana Gama hidimar birthday din momy ta dauke jikarta tare da yo Mata wanka Ta Goyata Wanda Tuni baccin gajiya ya dauketa
"A Halin Yanzu Abun nan na Rashin yarda da y'an aiki da belah keyi ya Fara damun momy Kwata-kwata Daga ita Sai babanta take yarda dasu Daman ko Baki Basu Isa su dauke ta ba,Gashi Yanzu ya Kamata Ace Aliyu ya koma Kan aikinsa Shekara Guda kenan rabonshi Da compony Yana matsayin c e o dukda Shima zaman Gida ya ishesa Saidai a system yake D'an tattaba abubuwa Kullum Daga d'aki Sai Lambu Shida belah Bashi da aiki sai tunanin matarsa da rainon y'arsa Shi kanshi yanzu ya na son Ya Fara Fitar Amma ba Hali dan momy ta Tafi wajen Aiki Dole shi zai zauna da belah tunda Bata yarda da Kowa.
Yanzunma suna Zaune Suna tattaunawa Momy cike da damuwa ta kallesa Ta ce .
"Na yanke wata shawara aliyu Ina tunanin mai zai Hana mukai belah makarantar raino kaga Lokacin da Zan dawo Daga Aiki saina dauketa kaima Ka koma aikinka zaman ka dinnan bazan haifar da D'a Mai Ido ba fa ".
Numfashi yaja ya ce"Amma momy kina ganin zata Yarda kuwa?inaji a jikina inshallah tunda Kaga Yanzu Ta Fara tafiya dukda ba wata maganar kirki take ba sai gwalam gwalamtu Ta iya fad'ar dad Amma momy ce anyi anyi a koya Mata Saidai Ta ce mata Mah Tun mamy na koya Mata Harta Rabu da ita ta barta a mah din Yanzu ta Kara wayau Da Kyau gwanin burgewa kamar Ka saceta Ka ruga yanzuma ta na Wasanta sai barna take"shawara suka yanke Akan gobe Aliyu ya kaita school din.
A Hankali yake driving Yana kallon hanya Gani Yake garin duk ya koma Masa Sabo Yaushe rabon da ya fito Harya manta belah dake gaban mota itama Tana Kalle-kalle alamun itama Bata Taba ganin waje ba Kallonshi tayi da Yatsarta ke lume a Baki ta na Nuna Masa Hanya ta ce
"Da Dy"Murmushin yayi ya na Kallonta Tare da shafa Mata Kai ya ce "kina ganin gari ko Soulmate"ya fad'a mata sunan da Yake Kiran Mamanta dashi"
Dariya tayi kamar ta San me yake cewa Ta Fara zillo ganin zata iya Faduwa ya sanyashi janyota jikinshi tare da maidota gabanshi Yana cigaba Da driving daidai an tsaidasu kwanar shiga makarantar Kamar ance ya waiga ya juya Motar dake gefenshi ya kalla wani Irin zaro Ido yayi zuciyarsa na Bugawa da karfin gaske Kara murza idonsa Yayi Dan son tabbatar da abunda idanunsa KE Gane Masa idan ba idonshine Yayi karya ba Sak Nabelar sa Yake Gani a Bayan Motar Nan Sanye da uniform "
"innalillahi wa Inna ilaihiraji'un"ya fad'a da karfin Gaske Yana Kara waigawa kozai gaskata abunda Idanunsa ke gwada Masa Saidai me Babu Motar Babu labarinta a matukar rude ya tada Motar duk waige da neman da zaiyiwa Motar ya nema ya rasa Gaba Daya lokaci Guda ya susuce ya fita a Hankalinshi hanyoyi kawai ya dinga bi Ina zai ga Motar Nan Mai Dauke Da Matar sa,Daman Nace belah ta Bata mutu Ba tasan son da nake Mata bazata Taba Tafiya ta barni ba ".
"ya fad'a da karfi ya na Kara bin wata hanyar dukda Sanyin Ac din dake Cikin Motar Bai Hana Shi zufa Ba Ta ko Ina zufa KE Karyo Masa lokaci Guda ya fita hankalinsa Ya firgice kamar bashi ba.........βοΈ
*Hmm wannan Karan salon Wasan da zafinsa Yazo Tofa Daman Wanda ya mutu ya na dawowa Malam Aliyu*??
*Idan Kun Karanta kuyi sharing Sauran groups Dan Sauran su Amfana Na Bati neππbanza ta samu lol* ππ€£
_Allah cika Mana burikanmu na Alkhairi_
_*Miss Hajo CE*_π€