SARKI SAMEER

Episode 19

by @azeemadahiru

💅SARKI SAMEER.....💅

      by❤xeemat....love❤


      🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


         

Allah ya gafartawa iyayen mu Allah yasaka musu da gidan aljanna Allah yabiya musu bukatunsu na alkhairi Allah yasa murabu dasu lafiya Allah yabamu ikon cigaba dayi musu biyayya  👏


           Bismillah........

Episode 19🖋


        ********************


Azeema ce takalli Ameesha tayi mata alama da ido akan ta tambaya sutafi itakuma sai ta qara make lafada alamar taqidin dadda dake tafaman hada kaya tana kallon su duk abun da sukeyi tana ankare dasu amma ta nuna batasan ma da zaman su adakin Azeema ce ta mike da nufin tatafi amma ba tafiyar zatai ba tanaso taga yaya Ameeshan zata tambaya sutafi dinne kozatayi shiru ne ta barta tatafi ita kadai din aikwa tana mikewa tace dadda nizan wuce dadda tace kigaida maman taku kar kimanta kice mata ina mata Allah sanya alkhairi tace dadda zangaya mata tana fadar haka kuma tajuya batabi takan Ameesha ba tayi waje aikwa a sukwane Ameesha ta mike ta tari gaban tana cewa wai da gaske tafiya zakiyi kibarni tabata amsa dacewa to me kike so inyi nace ki tambaya kinqi kuma kinyi shiru kinqi magana so kike kawai inzauna ina kallonki to ni ina da aikin yi inke baki da shi tana gama fadar haka ta ratsa ta gefenta zata wuce nan ma taqata saurin tare ta tace to tsaya zan tambaya Azeema tsayawa tayi tana kallon sannan tace kiyi sauri kifada acikin minti biyu inba haka ba kuma inta fiyata tace naji to sannan tashiga tunanin ta inama zata fara ganin bata lokaci take qara yi yasata yin dan gaba kadan kusa da dadda sannan ta juyar da kanta gefe tana hade rai tace zanje gidan su besty kinji banza dadda tayi mata hakan kuma ba qaramin qara bata mata rai yayi ba haka dan haka itama sai tayi shiru kuma bata juyo da kanta ba muryar Azeema ce ta daki dodon kunneta da cewa zantafi ba rintse ido tayi sannan tace wai yakike so inyi ne kinajifa nagaya mata tayimin banza AZEEMA tace inkuma bata ji bafa kiqara tambayar ta mana wani irin kallo ta watsa mata tare da wurga mata harara aranta tana cewa yama za ayi ta wani ce batajiba bayan gata ga ita kusa kusa amma ta wani ce batajiba kawai de rashin mutunci dadda take mata qara tamke ido tayi sannan tace zanje gidan su besty kinji nanma shiru tace kinji ta qara maimaita mata dadda dake tafam aikin gabanta tace inbakisan sunana ba sai kitashi kibar min waje ba inda zaki iya qololuwa Ameesha ta kai amma ba yanda ta iya sai ta miqe tsaye kawai ta daga murya tace wai dadda sai wulakanci kike min kawai akan dan wannan abun da yafaru bafa tsoron ki nake ba wlh zan iya qasa qafata infita kuma bazan qara dawowa ba daga gidansu duniya zanshiga daman nagaji da zama dake nagaji nagaji burinki kullum kiganni cikin damuwa ina kuka baki da matsala da hakan saboda bake kika haifeni ba nasan da yar kice da bakiyi mata haka ba to wlh to wlh nagaji ki maida ni inda kika dauko ni inma tsintata kikayi ko akan bola ne to ki maida ni inda aka haifeni tunda daman ance akan titi aka haifeni ni banda uba ni shegeya ce tana sauke maganar taji wani kyakykyawan lafiyayyun maruka har biyu akan kyakkyawar fuskarta wanda suka sata dauke wuta gaba daya kawai ta dafe kumatun ta ta tsaya cak ko motsi bata yi kamar wacce aka kafata awajen dadda ce cikin bacin rai da bata taba ganin irin shiba afuskar dadda hannu dadda tadaga zata qara kaimata duka Azeema tayi saurin shiga tsakanin su dadda da har kwalla ta cika mata ido ta daga yatsanta ta nuna Ameesha da shi tace ke harni zaki gaya wa wadannan maganganun dan ke baki da hankali duk irin dawai niyar danke dake tun haihuwar ki har zuwa girman ki baki gani ba duk qoqarin danake akanki shima ba kya gani to kulawar da nake miki ko yar cikina ban mata hakaba kuma wlh inki qara kiran kanki da shegiya saina karkar yaki agidan nan ni kinsan halin da nake ciki kinsan bakin cikin da yake kwance aqasan zuciyata shekaru da shekaru tun kan kizo duniya nake fuskan tara tashin hankali har kawo yanzu ta nuna kan qirjin ta saitin zuciyar ta tace kinsan meye acikin zuciyar nan taf take da bakin ciki kodan kinga bana nunawa bana son nunawa saboda banason inga kinshiga damuwa tun kina yar qaramar ki duk sanda kika tambayeni bana ce miki zan gaya miki amma saikin qara hankali duk wani abu danasan kina so shi nake qoqarin inga nayi miki duk dan inganki cikin farin ciki na gwammace in rasa koma meye inde ke zaki mallake shi hankalina ze kwanta kigaya min abun da nake miki na bata miki rai ko kuma kigaya min abun da kika taba nema kika rasa inde ina da halin yi kinsan ba abun da bazan miki ba amma ke kullum da kalar tashin hankalin da zaki zo min dake saide in lallabaki inbaki hakuri bantaba daga muki murya ba bantaba dukan ki ba kuma bawai dan bakya min laifi ba kawai ina rabuwa dake ne saboda banason kina yawaita tunani wani abun amma duk da haka banyi miki ba ni kike kira da kingaji da ni ko in maida ke gurin da na dakko ki to bazan yi hakan ba in kin cika yar halak kije kiyi duk abun da zakiyi duk matakin da kika ga yadace da rayuwar ki kije kiyi duniya ce ta isheki riga da wando wanda bezo bama jiranshi take bare kuma wanda yake cikin ta bazan qara hanaki abun da ranki yakeso ba inde harkinga hakan sai yafi miki dadi akan zama dani kina da wanda yafini aduniyar nan kuma kina ganin gwara kiyi nesa dani to qofa abude take kuma kisani daga yau ko kitafi kinzauna ni hadizatu ba abun daze qara hadani dake zan zare hannuna akanki zan zuba miki ido bazan taba saki ba ko in hanaki bare kiringa ganin na takura miki kiyi duk abun da kika ga dama daman kice zaki bi bossay to inyazo kibishi ni ba inda zani kibar ni a inda kika ganni idan na zauna ba ke ai ba mutuwa zanyi zanci gaba da rayuwata har zuwa ranar da numfashi na ze qare inkoma ga mahallici na ta qarasa fada tare da sa gefen hannun rigarta tana goge hawayen da take riqewa amma saida ya zubo Ameesha da jikinta da gaba daya yamutu ba ita kadai bama hatta Azeema saida taji wani iri gaba daya abun be mata dadi ba Ameesha ce tashiga daga qafarta da tayi mata nauyi tashigawa takawa ahankali zuwa gaban dadda tana zuwa kuma ta ta rungumata kamkam tare da fashe mata da wani irin kuka me tsuma zuciya cikin kukan tashiga cewa dadda ta dan Allah kiyi hakuri kiyafe min wlh sharrin shedanne nasan nima kaina nasan wasu abubuwan danake miki be kamata ba amma nima wataran bada son raina hakan take faruwa ba nima bansan me yasa nake yin hakan ba amma nasan kina qoqari dani kin riqeni kamar yanda iyayena zasu ruqeni amma nima dan Allah kifahimce ni dole fa indinga tunanin iyayena ba wanda zezo duniya bega iyayen saba kuma ba ace mishi komai akan suba kinsan dole ya shiga damuwa da tunani iri iri amman tunda ba kyaso daga yau in Allah ya yarda bazan qara yi miki maganar ba bazan qara cewa komai ba akai inde har hakan zeyi miki dadi nikuma nayi alkawari bazan qara taso miki da maganar ba kiyi hakuri dan Allah in Allah yarda daga yau bazan sake yi miki duk wani abun da ba kyaso ba shiru tayi taci gaba da kukan da takeyi dadda dafa bayanta tayi tare da dan bubugawa sannan ta dago ta daga jikinta tana share mata hawayen ta sannan tace kukan ya isa haka da sauri Ameesha ta girgiza kai alamar baza ta dena ba tace dadda kice kin hakuara kin yafe min sai inde na dadda tace na hakura Allah ya yafemana baki daya nima kiyi hakuri da maganganun da nayi miki rainane yabaci da har yasan gaya miki haka amma badan son raina ba Ameesha tace ni ba abun da kikai min nasan kowaye ma aka yimishi haka abun dazeyi kenan tana gama fadar haka tajuya tana kallon Azeema da suka manta da ita agurin tana tsaye tazama yar kallon tan kallonsu cike da tausayawa zataso taji me yasa suke rayuwa haka sukadai babu kowa atare dasu Ameesha ce ta katse mata tunanin ta da cewa besty kiyi hakuri dan Allah nabata miki lokaci kije kawai nazo wataran murmushi Azeema ta qaqalo tare da cewa laa besty wlh ba komai nim daman ba tafiyar zanyi ba dan wuni natambayo agida danna ji kince zaki ne shiyasa amma yanzu tunda kin fasa shikenan muyi zaman mu anan tare da dadda


Ameesha tace to shikenan ma na gode besty dadda ta katsesu da cewa me yasa zaku fasa kuje mana ba komai ai komai ya wuce 

Ameesha tace a'a wlh dadda ba inda zan sake tafiya inbarki inde ba makaran taba ko kuma kin aikeni amma ba inda zanje ina tare dake ako da yaushe 

Dadda tadanyi murmushi sannan tace to ai shikenan nima daman nafison hakan yanzu kuzo ku qarasa awannan aikin kusa min duk abun da kukaga naware shi ta nuna musu inda ta ware wasu kayan tace kusakamin su acikin bakkon nan da to suka amsa mata ita kuma tace bari taje ta hade kayan tsakar gida tana gama fada ta fita

Suma zama sukayi suna ta aikin da aka sasu bawanda yaqara cewa komai a tsakanin su kowa da abun da yake tunani.......





#Comment

  and

#share


More comment more typing

No comment no typing

    Pls Likes  

   

      

              ❤xeemat.....love❤