Episode 20
💅SARKI SAMEER.....💅
by❤xeemat....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Allah ya gafartawa iyayen mu Allah yasaka musu da gidan aljanna Allah yabiya musu bukatunsu na alkhairi Allah yasa murabu dasu lafiya Allah yabamu ikon cigaba dayi musu biyayya 👏
Bismillah........
Episode 20🖋
******************
Saida suka gama komai harta katifar dakin su dagata sama babu komai aqasa komai sun kukkule wanda kuma zasu bayar sunfito dasu wajen tsakar gidan suna gamawa kuma suka fara taya dadda sai da suka gama koamai abun da suka bari awaje kawai wadanda zasuyi amfani dashi ne daga nan zuwa dare suna gamawa kuma suka hadu dukansu suka dora abincin rana saboda Azeema kuma suna da guntuwar fulawa bata qare ba sai sukayi dan wake da manja suka daka yaji Ameesha tace dadda kikawo dari muje musiyo salad da cabbage da sauran kayan hadin sai yafi dadi ko yakika ce besty daga mata kai tayi alamar eh dadda daki ta koma ta dakko musu dari da hamsin ta basu karaba sukayi kowacce tasaka hijabi suka fita atare kamar ya da qanwa saboda Azeema ta girmi Ameesha dan ita akalla zata iya yin ashirin amma bata da jiki sosai shiyasa ba aganin girmanta amma de duk da haka tafi Ameesha dan cika suna tafiya suna dan hirarsu Har sukazo bakin titi suna ahirin tsallakawa sukaji ance yan mata dukansu suka juyo suna kallon yaron da yayi musu magana da murmushi akan fuskar shi yace kuyi hakiri fa na tsare ku ahanya daman wancan mutuminne yace inyi muku magana yafada yana nuna musu inda wata jibgegiyar mota me tinted glass daga ganin ta ma kasan sabuwa ce yace musu wai kuje yana son magana da wannan yanuna Ameesha da hannu gaba dayan su kallon juna sukashiga Azeema ce tasamu qarfin halin cewa kaje kace mishi baza muzo ba yaron da aka aiko yace baiwar Allah gsky bazan iya zuwa ingaya mishi hakaba bakisan ko shi waye ba Sai yanzu Ameesha tasaka musu baki tace mishi ko ma dan gidan uban waye baza mu jeba tana gama fadar haka taja hannu suka bar wajen saida sukayi gaba Ameesha tace kefa ni tsoro nake ji wlh kar muje yayi mana wani abun Azeema tace ke matsalata dake wlh wataran tsoro yayi miki yawa ya isa yayi mana abun da Allah beyi manaba ne irin wadannan yan iskanne masu daukan mutane suje suyi lalata da su to mu ba irinsu bane ni wlh ma hakannan duk da banga mutu min ba naji natsane shi kawai haushin shi nake ta gama fada tare da buga tsaki kawai jitayi anjawo hijabin ta tabaya ashe tun lokacin da take bawa yaron amsa yana lure da ita yana ganin shishigin da takeyi saikace ita akace tazo da beyi niyar zuwa ba saboda daman ba halinsa bane shida duk tarin yan matan dasuke binshi baya kula su amma besan meyasa yarinyar tunda yaganta yaji ta burgeshi kuma shi bada so ma yace akirata ba kawai yanaso yayi magana da ita shiyasa ma yace akirata amma shine wannan banzar yarinyar zatazo tayi mishi hauka abun da yaron yafada mishi shine yasashi fitowa daga motar yana daf dasu kuma yaji still yarinyar tana zaginshi ranshi ba qaramin baci yayi ba dan ayanda zuciyar sa take raya mishi kawai ya jawota ya kikkifa mata maruka amma saide kash baya dukan mata arayuwarsa kwata kwata baze iya kai hannusa kan mace ba da sunan duka hakanne yasashi jawo hijabin ta saboda tafiyar dasuke yi shikuna bayaso yay tabinsu abaya shiyasa yaja hijab dinta domin su dakata da tafiyar dasuke yi,
aikwa a fusace ta juyo dan ganin waye me yimata wannan iskanci hada ido sukayi da mutumin da ya wani hade rai kamar ma be taba yin dariya aduniya ba ashe duk yaji abun da suke cewa ita da tajiyo dan yin masifa amma kuma sa tafasa saboda ganin yanda fuskarsa tayi ba annuri maganar gsky yanzu ta dan tsorata da ganinshi dan ko ba agaya mata ba tana tunanin mutumin da take zagi ne kuma tunda taga haka tasan yaji duk abun da suka fada akansa tana tunanin taji ya kaseta da cewa ke yar gidan uban wacece kinsan waye ni dakike kwatan tani da yan isaka ko ke nace ina so uban me zanyi dake kucaka kawai me kama da zombie ko matan duniya sun qare aka ce miki zan iya kulaki da kike cewa kintsaneni nima ai bance ina sonki ba ni tunda nake arayuwata ma banta jin tsanar mutum ba irin wacce nake miki banza shasha sha mezubin aladu da wata mummunar fuskarki duk wanda ma yasoki wlh yayi asara sa arki daya ke macece nikuma bana dukan mata amma wlh da namiji ne yau sai yagayawa aya zakinta sai na canza miki kamanni Yanda ko uwar da tahaife ki bazata gane kiba itama cike da takaicin maganganun da yake gaya mata harda sako uwarta azancen yasa fusge hijab dinta da be saki ba sai yanzu da ta kwace cikin daga murya itama tace dakata malam karka kuskura ka qara sako iyayena azancenka yace innaqifa ko zaki dakeni wlh idan kika qara magana agunnan saina yi qasaqasa dake
itama daga murya tayi tace anyi din kayi duk abun dazakayi hannu yadaga Ameesha da tun dazu tazama yar kallo saide ta kalli wannan ta kalli wannan takasa magana
dasauri taruqe hannun shi tace dan Allah bawan Allah kayi hakuri ka rabu da ita na roqeka kaji plsss Azeema tace dalla kirabu dashi yayi duk abun da yaga zeyi da sai yayi danasanin taba ni wlh be kulataba kawai Ameesha ce takara cemishi kaji dan Allah plsss tsayawa yayi cak ko motse yakasa kuma bece mata komai kawai yatsaya yana kallonta sai can kuma yamaida idanun sa tare da azasu akan kyakkyawan hannuta yana kallon su ganin hakan da tayi yasata sakin shi ahankali tare da dan ja baya sannan tace I'm sorry sir tare da sunkuyar da kanta qasa shikam ya bushe agun ya kasa magana saida kyar ya iya daidaita kansa sannan yakalli Azeema dasai faman cika take tana batsewa nuna ta yayi da yatsan sa yace kinci darajar me daraja amma wlh da sai na canza miki kamanni marar kunya fitsarar riya shasha sha ballagaza yana kaiwa nan kawai ya juya yabarta yasan ko ba komai ya rama zagin da tayi mishi yatafi yana tunanin wlh da ba dayar yarinyar nan ba sai ya koya mata hankali sai ta kirashi da dan iskan da hujja yana qarasa wa wajen motar sa yabude ya shiga yatayar da motar ranshi na mishi quna da shi har yanzu bedena takaicin abun da tace mishi gaba dayama sai yaji ya tsani kansa duk shi yajawa kansa da ya kulasu da be kulasuba da duk hakan bata faru ba bare wannan banzar yarinyar tagaya mishi magana son ranta kuma ya rabu da ita be dauki babban mataki ba haka yaringa tafiya yana ta faman doka tsaki shi kadai.........
Bangaren su Azeema kuwa da ta gama cika da haushi harda kuka wai yazo yaci mata mutunci alhalin shine da laifi amma yayi mata haka Ameesha itama fuskarta da damuwa tace dan Allah kiyi hakuri ki manta da komai shima watakil ranshine ya baci akan zaginshi da kikayi kuma yajiki shiyasa shima yayi miki haka dan ya huce haushin shi tace kuma sai yaringa zagina ni irin haka nayi mishi basai ya rama da abun dana yimishi ba harda cemin fa ballagaza menayi mishi ko yaganni ina yawo da mazane ko ya ganni da wata shiga da bata dace ba Ameesha tace dan Allah kibar wannan maganar yafada ne kawai dan yabata miki rai kinsan daman ramuwar gayya tafi ta gayya zafi shiyasa tun farko nace miki murabu lfy muje kikace kar muje Yanzu gashi nan yazo yabata miki rai yabata mana lokaci dan Allah muje kar dadda taga mundade janta tayi zuwa inda me kayan miyar yake suna zuwa suka bashi kudin Ameesha ta gaya masa duk abun da suke bukata shikuma yabasu Ameesha tasa hannu ta karba suka juya suka nufi hanyar gida suna tafiya Azeema nacewa wlh in Allah ya yarda sai ya hadu da daidan sa ahanya sai ya hadu da wanda zeci mutun cinsa fiye da yarda yaci mutuncin ta itade Ameesha banda bata hakuri ba abun da take yi mata har suka qaraso gida Azeema bata dena mita ba da sallama suka shiga dadda dake daki ta idar da sallar la'asr ta amsa musu sallamar suna shiga basu je ga shiga dakin ba Ameesha ta wuce ta dauko roba da wuqa da zasu yanka salad din sannan suka shiga dakin suna shiga dadda tace sai yanzu Sai kace an aiki bawa garinsu ina kuka tsaya kukuwa Azeema mace tace wlh dadda wani dan rainin hankali ne yatare mu yaci min mutun ci kuma yatafi Allah zesaka min takara sa maganar da kunbura fuska sai kace dadda ce tayi mata laifin dadda da mamaki take kallon su tare da son qarin bayani dan bata fahimci komai ba Ameesha ce ta gayra zama ta bata labarin duk abun da yafaru dadda kwa ita abun ma dariya yabata amma sai tayi qoqarin riqe abarta bata bari ta fito ba saboda yanda taga Azeema tasan ranta yabaci idan kuma tayi mata dariya zata fi jin haushi ma sai kawai tace ayya Allah sarki gaskya be kyauta ba kiyi hakuri Allah ze saka miki kuyi sauri ku gama kuci danni har na ci nawa danaga shiru tunda mungama komai idan kuci sai kuje can gidan din saikiyiwa maman tasu sallama da to Ameesha ta amsa sannan taci gaba da yanka salad din da suka suyo bawanda yaqara cewa komai har tagama taje ta wanko ta dawo sannan taqara komawa ta zubo musu ta kawo komai da zasu bukata harda ruwan sha sannan takalli Azeema tace mata bismillah kai ta girgiza mata alamar baza taci ba hararar ta tayi tace wai ke baza kicire wannan abun aranki ba shi yana can yana uzurin gabansa ya manta dake amma ke zaki tsaya kina sawa kanki damuwa abanza a wofi shiru tayi mata bata ce mata komai ba kuma bata sa hannu a abincin ba
Saida dadda tasa baki sannan ta fara cin abincin bawanda yayi magana har suka gama ita kuma dadda nata faman gyangyadi alamar bacci take ji sai Ameesha ta gama kimtsa wajen sannan tayo alwala tacewa Azeema taje tayo tazo suyi Sallah bayan sun idar da sallar ne Ameesha ta sake shirya wa tasa doguwar rigar atamfa da dinki yayi mata das kamar ajikin ta aka dinka shi sai ta dora mayafi akai Azeema de na zaune tayi tagumi tana kallon ta har ta gama sannan ta tashi sukayi wa dadda sallama suka fita ahanya made bawan da yace komai saboda Azeema taqicewa komai shiyasa itama taja bakinta tayi shiru suka ci gaba da tafiya sunqun sunqun kamar
raquma har suka qarasa gidan dasuka shiga nan made Azeema taqi sakin jikin ta har saida mama tagane bayan sungama gaisawa da Ameesha sai ta tambayeta me yafaru da Azeema ne nanma de labarin abun da yafaru tabawa mama
Mama tace maganinki kenan ke meyasa zaki zageshi bayan kinsande ya girme ki gwara da yayi miki hakan ni wlh yayi min daidai Azeema jin hakan yasa ta tashi daga gurin ta koma daki dariya mama tabita da ita tana cewa Allah ya shiryeki sai da tayi shiru sannan Ameesha ta sanar da ita cewa dadda tana gaida ita kuma tace tana tayaki murna Allah yasanya alkhairi da Ameen mama ta amsa mata sai Ameesha ta dora dagaya mata zasu tashi itama mama batajin dadi ba dajin tashin nasu haka tayi musu fatan alkhari bayan sungama kuma itana ta tashi tabi bayan Azeema tana shiga kuma taganta kwance ta kifa kanta tana ta faman kuka da sauri ta qarasa inda take tare da dago ta ta rungumeta tace haba besty wai meye haka ne kikeyi sokike kisawa kanki cuta akan abun da be taka kara ya kar ba Azeema tace dole kice haka mana tunda bake aka zaga ba tafada tana kwace jikinta daga jikinta Ameesha itade taga takanta dan ita wlh abun harma yafara bata haushi daman ita Azeema haka take kwata kwata bata iya fushiba zata dade batayi ba amma idan tayi anshiga uku kullum cikin mita take
Dan haka kawai sai tacewa Azeema ke ni wlh nagaji bari inzo intafi gida tunda abunnan yafaru sadi baki hakuri nake amma kinki hakura bansan kuma me zan miki ba tana gama fadar haka ta miqe zata fita sai kuma Azeemar tayi saurin ruqeta daka tawa tayi da tafiyar sannan ta juyo tana kallon ta tace wlh inde bazaki dena ba tafiya zanyi
Daka tar da kukan da take yi tayi sannan tasa hannu tana goge hawayen tace nadena wlh abunne sai nayi qoqarin in manta sai kuma inqara tuna wata maganar tasa maganganun sa sai yawo sukeyi min narasa dalili Ameesha tace ki manta kawai gyada mata kai tayi sannan tashiga bathroom ta wanko fuskarta sai ta zauna ta goge fuskar itama Ameeshan zama tayi suna fuskan tar juna tace ko kefa dan Allah wlh har kinyi kyan gani bakya kyau da danuwa bare kuma kuka murmushin dole ta qaqaro ta aza a fuskarta sannan tace ai baza kigane bane amma de yanzu in sha Allah komai ya wuce tace yauwa koke fa..........
nande da wasa da wasa Ameesha ta shawo kanta sai kuma suka barke da hira kamar ba gobe kiran sallah ne ya katsesu suka ankare wai har lokaci yaja haka dasauri Ameesha ta miqe tana cewa kai besty wai har lokaci yaja haka nayi magariba awaje Allah yasa dadda kar tamin fada Azeema ma tace wlh nima nayi mamaki muyi sallah to sai inrakaki tace shaf shaf suka idar da sallar sannan suka fito falo mama bata nan daki suka leqa Ameesha tayi mata sallama sannan suka qara fito wa sukayi waje Ameesha tace laa nikam kinga har zantafi bamu hadu da yaya saleem ba Azeema tace wlh kuwa saide ingaya masa idan yadawo niban ma san me yazaunar dashi awaje ba har yakai wannan lokacin tace to shikenan kya gaya masa haka sukai ta hira har suka zo inda zasu rabu sannan sukayi sallama kowa ya nufi hanyar sa Ameesha sai sauri takeyi kamar zata tashi sama abu biyu ne suka sata saurin na farko tana tunanin kar dadda tayi mata fada na biyu kuma kar yaya bossay yazo bata nan aikwa adan mintina kadan ta qaraso gida da sallama ta shiga cikin gidan dadda bata waje dan haka kawai tashiga dakin tana shiga taga dadda na lazumi guri ta samu tazauna har dadda tagama sannan Ameesha tace dadda kinga nayi dare ko wlh muna daki bamu lura da lokaciba sai da mukaji kiran sallah dadda tace to ai shikenan tundade kindawo gida lafya sai a kiyaye gaba kuma tace in sha Allahu dadda daganan dadda ta dora mata da nasiha akan zaman rayuwa sosai kwa nasihar ta shige ta har aka kira sallar isha'i sanna ta tsaya dayi mata alawala Ameesha ta qara yowa tazo tayi sallah itama.....
Abude kamar wasa har goma ta wuce amma shiru kake ji ba labarin zuwan bossay tun Ameesha na hakuri har takasa tace dadda kinga fa har yanzu yaya bossay bezoba anya kuwa zezo tafada fuskarta cike da damuwa
Dadda tace tunda kikaga haka watakil wani uzurin ne ya riqeshi ya hana shi zuwa kije ki kwanta kawai sai gobe idan Allah yakaimu tunda yanzu kinga har shadaya ta kusa bazuwa zeyiba kije ki kwanta da to ta amsa mata jikin ta asanyaye ta ta jawo katifar da suka daga dazu
ta sauke ta ta dauko zanin ta shimfida da filo sanna ta kwanta tayi luf kamar me bacci ita kadai tasan yanda takeji aranta saboda ta kwallafa rai akan yau zata bar gidan amma sai gashi Allah beyiba haka ta kwanta ta ringa tunani dan bata jin zata iyayin bacci yau................
#comment
and
#Share
More comment more typing.....
No comment no typing.................
Pls likes more
by❤xeemat.....love❤