SARKI SAMEER

Episode 21&22

by @azeemadahiru

💅SARKI SAMEER......💅

     by ❤xeemat....love❤


      🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


      🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹

                    ﷽

        Bismillah.......🖋

Episode21&22 

          ****************

da wuri saleem yatashi yafara shirin zuwa wajen aikin da zeje yama gama shiryawa yafito ya gaida mama tana yimishi magana ma akam ya tsaya ya fara karyawa amma yace mata aa baya so yayi late da addu'a ta rakasa har bakin ƙofa Azeema ce ta fito da gudu tana cewa yaya wai fita zakayi ina ya qoqari ingma hada maka abun da zakaci dan Allah ka tsaya ya kusafa just give me a few minits dan Allah kaji dan murmushi yayi yace haba auta sokike infara laifi daga zuwa na nafiso inriga kowa zuwa kibari namiki alƙawari koma me kike min ki ajiye min idan nadawo zanci koda ya wuce bata rai tayi tace nifa wlh bazan bari ka zauna da yunwa ba ko ka tsaya ko kuma kaban address din wajen inzo in kawo maka gurin aikin buda baki yayi yace ke rufamin asiri in mutu maza sukaine ba mata ba daga fara zuwa ne sai kawai aga ankawo min abinci kinsan kwa yanda gurin yake da tsaro kiyi hakuri mama ce tace wai ke meye haka din wani sabon kinibibin ne da saunawa yana fita beci abincin ba sai yau zakisashi agaba da shirme kai kuma ka tsaya da tunima ka kusa zuwa, hakan ma da kayi ai ƙara bata loƙacin kake yi ka wuce katafi dan murmushi yaqara yi sannan yace mama ai da sauran loƙaci yanzufa ko bakwai batayi ba zumudine irin nawa kawai amma yanzu tunda tanaso bari injirata ta qarasa idan kuma takai qarfe bakwai da minti goma zan yafi da sauri Azeema tace nayarda wlh mama tace au biye mata din zakayi to nide ba ruwana idan kaje kasamu matsala sai hankalinku ya kwanta ko girgiza kai yayi yace mama in Allah yayarda ma bazamu samu matsalar komai ba in sha Allah kada kai tayi ta koma tazauna tace ai sai kuyi tayi jinjina kai yayi kawai sannan yabi bayan Azeema da tunda taji yace zejirata ta koma kitchen din yana shiga yaganta a tsaye sai faman aiki take da sauri gyaran murya yayi ta dan juyo ta kalle sa tace laa wai biyo ni kayi ai nama kusa kaje ka jirani a falo kaji yace to sannan yajuya yana ce mata sauran ki minti goma tace kafin lokacin ma ai nagama yace Allah yasa tace amin sannan tadan zuba ƙullin dake gabanta dan tabbatar da man yayi zafi yana zubawa kuwa yayi ƙara cuuwwi nan da nan tafara sakin ƙosai da Sauri da sauri tana gama daidai yanda tasan ze isheshi sai ta kashe gas din ta zuba masa a plate sannan ta dauko cup tazuba mishi kunun gyadar da hadashi tundazu tazuba a flax sau yanzu ta tsiyaya mishi daidai yanda tasan ze isheshi sannan ta dora akan faranti tare da cokali sai yar ƙaramar robar sugar ta dora masa duk wannan abun adan ƙanƙanan lokaci tagama komai tafito tace gashi har nagama aide lokacin be cika ba ko daga mata kai yayi sannan yace gsky kinyi sauri me kika yiminne haka akeso sai naci tace idonka yagane maka tunda gashi yanzu zaka gani tana gama fadar haka ta ajiye masa waro ido yayi yace wow gaskiya auta godiya nake kinmin suprise wlh rabona duk son da nakeyi wa abunnan na dade banci ba bansan meyasa ba kwason yinshi tace wlh nima ina so mama da baba basa sonshi shiyasa bamufiya yinshi ba tace yauwa yaya wai har yanzu basu ƙara kiranka yace wlh basu kiraba tace to anjima idan ka dawo sai ka ƙara gwada kiran su kaji me ake ciki yace nima tunanin danakeyi kenan bari idan nadawo din sai inkida tace hakan yayi tace bari inbarka kaci inje in ƙarasa wancan dan kai kadai nayiwa yanzu yace to sannan yaci gaba da cin abunshi hankali kwance duk saurin da yakeyi hakan besa shi cin abincin da sauri ba ci yake kamar yanda ya saba lokacin da yagama bakwai da rabi daidai sannan yatashi ya ƙara gyara jikin shi sannan ya nufi dakin mama da tun dazu tabar falon yana zuwa yayi sallama ta amsa masa sannan ya shiga daga bakin ƙofa yace mama ni nagama zan wuce tace Allah ya kiyaye hanya ALLAH ya tsare hanya yace amin sannan yajuya ya fita da sauri ya dan leƙa kitchen yace wa azeema shi ya wuce itama da addu'a tabishi sannan ta rakasa har bakin hanya saida taga ya hau napep sannan ta juya ta koma ..............


    *S.A.S SPATIAL HOSPITAL*

lokacin da ya qaraso gurin ƙarfe takwas saura minti biyar Allah ya soshi be makara ba inda suka saba zama idan sunzo shi da sauran jama'ar wajen basu dade ba kwa sai ga Dr.shettima ya iso wajen suna ganinshi kowa yafara gaida shi yana amsawa sannan aka bude masa office dinshi ya shiga ciki yazauna bayan wasu yan mintina kuma ya bukaci su fara shiga

daya bayan daya suka ringa shiga suna fitowa duk wanda yafito kuma sai ya wuce inda zeyi nashi trainning ahaka har akazo kan saleem da fara'a a fuskar shi ya shiga ciki yana shiga kuma ya tsugunna har ƙasa ya gaida shi da mamaki dr...shettima yace haba abokina da girman ka zaka tsugunna min ina jinma fa ka girme ni amma ka tsugunna min tashi dan Allah kar wani yazo yaganka ai yama dariya yanzu a wannan zamani ko manyama idan za agaidasu ai ba a tsugunnawa yaƙarasa fada yana yar dariya tare da miƙawa saleem hannu alamun suyi musabaha da farko da ƙnyarda yayi saida yaga dr shettima ya dan yi masa hararar wasa yace kai nifa ba ayimin irin wadannan abubuwan ni kowama nawane inzaka saki jikinka ma kasaki dan atare dani zakayi trainning dinka tun jiya ma na riga nagama da file dinka aiki kawai zamu fara idan nagama sallamar mutane akwai wata patient da za a cire mata appendix dan haka sai ka shirya zaka fara ganin yanda ake farke mutum ko antaba yi agaban ka

yace a'a yaude zan fara gani jinjina kai dr shettima yayi sannan yace zaka gani yau kuma atsarin aikina saudaya nake koyawa mutum abu saboda bana san wasa idan akan harkar aikine dan haka na dauke ka dan naga alama kammar bazakayi wasa ba kuma na yaba da kwazonka shiyasa dan haka to be a careful ka maida hankali sosai kayi aiki kar kasa wasa aciki saleem yace in sha Allahu zan maida hankali nagode da shawarar ka yace ba komai ka dauke ni amatsayin yayan ka duk wani abu da baka ganeba ko ya shige maka duhu kasanar dani karkaji komai ni kuma zanyi maka bayani in Allah ya yarda

Saleem ba ƙaramin dadi yaji ba yace nagode nagode Allah yabiya maka bukatunka yanda ka min kaima Allah yayi maka yace bakomai ai duk yiwa kaine ring din wayar dr shettima ne ya katse musu hirar su duba screen din wayar yayi dan ganin me kiran nashi SAM naga anyi saving dashi akan screen din wani killer smile yasaki tare da saurin dagawa saboda kar wayar ta katse yana dagawa ya kara wayar akunne yana cewa shegen gari sai yau aka tuna dani kullum sai nakiraka amma dan rashin mutunci baka daga wa kuma baza ka kira ni ba ko shiru akayi daga dayan bangaren jin hakan yasashi cewa kaifa matsalata dakai kenan ka kirani kaqi magana kuma nima nayi maka magana amma kayi min shiru wlh baka da kirki ko kadan nide banji me akace daga can bangaren ba kawai de naji yace wai da gaske ko da wasa kai amma naji dadin hakan Allah yadawo mana dakai lafiya kace muyi babban shiri yauwa daman inaso muyi magana kan batun sabbin ma aikata acikin mutane hamsin da wani abun gasky wadanda muka dauka basufi ashirin da biyar ba saboda yawancin su duk basu cancanci adauke suba shiru yayi yana sauraron abun da dayan yake gaya masa sai can kuma yace ok ba matsala ammafa inaganin basai an ragesuba saboda muna bukatar mutane da yawa saboda dayan bangaren da aka bude kuma babu wasu ma aikata sosai aciki inaga kawai abarsu baza arasa abun da zasuyi ba amma inkana ganin arage din sai yafi sai murage din ko yakace sake yin shiru yayi yana sauraron sa 

Sannan yace ok zan qara bincikawa badamuwa yauwa sai kuma....

Begama fadar abun da yakeso yace ba yaji wayar tayi ƙara ƙit alamun ankashe wayar kenan bin wayar yayi da kallo sannan yasaki murmushi yace hmmm baza ka taɓa canzawa ba Allah yashirye ka ace mutum baze taba jiran kagama magana ba shi inya gama tashi maganar shikenan sai ya katsewa mutum waya yana magana yana kallon saleem da yayi shiru yana sauraronsu sai can kuma yace kayi hakirifa ina ta waya nabarka da kai kadai saleem yace bakomai wlh naga alamar kamar ma baka ji dadin kashe wayar dayayi ba dr shettima yace wlh banji dadi ba ban gama magana ba yakashe kuma daman halin sane yasaba yiwa mutane haka bashida mutunci wlh ko kadan gashima kuma nan da two weeks zedawo shikenan mun shiga uku sai ya takurawa kowa da masifa kaima wlh kayi hankali dashi dan abu kadan zakai mishi ya koreka daga aiki any mistake game over saikabi a hankali jinjina kai saleem yayi sannan yace shine me asibitin kenan

Yace eh shine wlh amma wlh yaba da wuyar sha'ani sai ka koyi zama dashi zaku zauna lfy

Saleem yadanyi murmushi tare da jinjima kai sannan yace to Allah yabamu ikon iyawa dashi Allah yasa muhadu dashi lfy mu rabu lfy ƴar ƙaramar dariya yayi sannan yace aikwa da ƙyar ace kuhad ku rabu batare da wani abu yahadaku kawai de kayi addi'a Allah yasa matsalar tazo da sauƙi danshi mutum ne wanda ba a iya mishi haka de sukai ta tattaunawa akansa kafin daga bisani dr shettima yacewa saleem kaga muata batawa mutane lokaci kaje ka jirani a waje kafin infito sai muwace yace to sannan yatashi yana ƙara yi mishi godiya sannan yafita yana fita mutane suka ci gaba da zuwa har yagama dasu gaba daya sannan yatashi yafara shirin fita teaiter din da zasuyi ƙarar waya yaji akan table dinahi da mamaki yajuyo tare da ƙarasowa kusa da wayar sai kuma ya tsaya yana kallon wayar to waye yabarta anan begama tunani ba yaji anyi noking yace come in dasallama saleem yayi sannan ya ƙaraso inda yaji wayar tashi na ringing yace afuwan dan Allah wayata namanta yafada yana ƙoƙarin daukar wayar sai kuma ta katse girgiza mishi kai dr shettima yayi tare da dan matsawa dan yabashi damar daukar wayar aikwa saleem na dago da wayar idon dr shettima ya sauka akan hoton wellpaper din da yake kan wayar saleem ƙara zaro idon yayi domin tabbatar da abun da yagani gaskiya ne ko kuma gizo ne amma da maida idonsa kai saleem har yasa wayar a luck yajuya ze fita da har ze tsayar dashi amma ba halin yin hakan saboda saleem har yariga da ya ƙarasa fita tunani ya shiga yi inbe manta ba hoton da yagani kamar fuskar yarinyar da suka hadu jiya tazage shi.........


https://arewabooks.com/chapter?id=6402f6f8a3c025c58dc9f42c


#comment

 and

#share

   #likes

More comment more typing.....

No comment no typing.................

    

                ❤xeemat.....love❤