Episode 22&23
💅SARKI SAMEER.....💅
by❤xeemat.....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
﷽
Bismillah..........🖋
Episode 22&23
******************
Dr.. Shettima Girgiza kai yashiga yi a fili yace kai ba ita bace kawaide gizo ne mema ze hadata da wannan yaron wata zuciyar ce ta bashi amsa da cewa inkuma budurwarsa ce tunda har yadora pic dinta amatsayin wallpaper sa wata zuciyar tace kode qawar sace nanma de girgiza kai yayi yace ai basa kama da qawarsace tun ajiyan zangane hakan in kuma budurwar sace nanma yaron baze kulata ba tunda shi yana da hankali daga ganinsa baze kula irin wadannan matan ba yarinyar daga ganin tama kasan ba abata tarbiya ba agidan su tunda har take iya cin mutunci nagaba da ita shi sai yanzo ma yake tajin wani bacin ran na taso masa wai shi zatacewa dan iska me bin mata alhalin ko ganinshi batayi ba amma take dorarwa waya sani ma ko itace me bin mazan daman ance duk abun da kakeyi gani kake kowama na aikata irinshi arayuwarsa shiyasa ta fadi haka shikadai sai faman saqa da warwara yake yi sai can kuma yasaki wani irin murmushi kamar bashine yake bacin rai yanzu ba ,ba komai yasashi wannan murmushin ba face tunawa da yayi da dayar yarinyar da loqacin da ta ruqe mishi hannu tana ce mishi dan Allah bawan Allah kayi hakuri karabu da ita na roqeka kaji plssss harga Allah hakan da yarinyar tayi ba qaramin tafiya yayi dashiba gashide yarinya ce batafi qanwar qanwar sa ba amma ta burge shi tun ganin farko dayayi mata yaji ta burgeshi shi tunda yake be taba jin yanaso yayiwa wata mace magana ba da nufin wai ta burgeshi sai akan yarinyar nan yar qarama abun har mammaki yake bashi wai shi ya aika yaro yace ayi mishi magana da mace lalle yarinyar nan taciri tuta ta karya mishi record saide bemasamu maganar da ita ba waccen kucakar yarinyar tazo ta bata mishi rai da harma yafasa maganar da yayi niya
gemunshi yadan shafa tare dayin wani murmushin yace Allahn da yahada ni da ita jiya shi zeqara hadani da ita nan gaba in Allah ya yarda zamu qara haduwa dake small girl sunan daya samata kenan tundade besan sunan taba nocking din office din da akayine yakatse mishi tunani iznin shigowa yabayar
wata nurse ce tashigo tace sir we are ready ok I'm coming juyawa tayi tafita shi sai yanzuma ya tuna ashefa zasuyi aiki amma yazauna yana tunanin abun da bashida amfani a halin yanzu agashi har goman ta kusa ma shaf shaf ya gama shiryawa sannan yafito
yana fitowa ba kowa agun sa saleem da yake ta faman jiran fitowar tashi yana ganinshi yatashi da sauri ya miqa hannu dan ruqe mishi lap code din da yaruqo be hanashiba ya miqa mishi sannan yayi gaba shikuma yamara masa baya wani dogon corridor suka mika sai da sukayi gaba kadan suka yi kwana suka shiga wani daki wanda dagani daman kasan titer room ne nurse biyu ne adakin kowa yayi shigar fara aiki cikin kayan aikin su sky blue sai farar hula da farin face marks suna shiga dr shettima ya karbi rigar hannun saleem ya shiga wani daki da yake acikin dakin da suke anware shine daman sboda shiga canza kaya ko wani uzurin privacy sai ka shiga kayi har da toilet aciki bayan ya shiga yagama shirya wa yace wa saleem ma yaje ya shiryo
shiga yayi be jimaba ya fito shima cikin shigar kayan aikwa ba qaramin amsar sa kayan sukaiba yayi matuqar kyau acikin su yana fitowa kuma ya tsaya daga baya saboda shi ba abun da ze taba kawai kallonsu zeyi sai wata yar joter da pen da dr shettima yabashi yace yaringa recognize din duk abun da ya fahimta abun da yake da tambaya idan angama sai yayi yace to sannan yafara aikin dan shine zaiyi aikin sauran dan tai maka masa zasuyi da wani abun cikin kwarewa da kwazo irin nashi yafara gaba tar da aikin saleem ya tattara duka hankalinsa da nutsuwarsa kan abun da akeyi yana yi yana rubutawa kamar yanda akace kuma yana fahimta Yanda ya kamata...........
Yau nashiga busy da yawa kuyi maleji da wannan da babu gwanda ba dadi
_________________®___________________
Announcement
SANARWA!!!
wasu sunacemin wai typing dina nayin yawa musamman yan facebook to amma kafin inrage yawan inaso inji ta bakin ku
Kowa yafadi albarkacin bakinsa
wadanda sukafi rinjaye akai
Idan wadanda sukafi so arage suka fi yawa to zan rage
Idan kuma wadanda basa so arage su sukafi yawa to saide kuyi hakuri zanci gaba da yanda nake .......
INA SAURARONKU sai naji daga gaereku saboda daga gobe nakeso incanza
___________________®________________
#comment
#share
#likes
#vote
story & writing ..........✍
by
❤xeemat....love❤