20
*DAMA TA*
*NA*
*Batul Adam Jattko*
*Mum farhan*
*Hadim fa bata dauki* *Shawaran kiba*
*Masoyan damata ina kara godiya* 🤝
*Humairan Fandau ta gd*
🌈 *Kainuwa Writers*
*Association*🤝
*20*
A general parlour suka yada zango yaran sunata tsalle dan suna son gidan antymum haka suke kiran Hadim saida sukayi sallah zuhr Hadim takira firseh me aikin ta a bangaren kitchen tace "ga yara kuje su fade abinda suke son ki dafa musu muba yanzuba firseh ta amsa da "ok taja yaran suka fice
Hadim bata ajiye wayan ba tace bari nakira my star naji meya kawo motan sa gida
Nabil da har lokacin yana fadan askin kan Fandau wayan yayi ringing yana zarowa yaga sunan my one yadaga yace "hutawan ki lfy my Queen
"tace Allah yabarmin my prince na tace fasa meeting din kukayine?
Yace "a a mundan fito hutune na kunna wayan ya akayi ne?
Tace to yanaga motan da katafi dashi a gida
Dasauri yace "gida kuma
tace "eh
Yace "ya akayi kika sani?
Zuciya daya tace "ina gidan fa
Hannun sane yafara kar karwa yabude baki amma yaji mgn ma yagagara
Dabara ya fadu masa yace"ok munzo da amjad ne shine muka fitada tasa nabar nawan.
Tace " ok ai muzone da habiba da yaran kwana ma suka kawomana
Yace "ok sai nazo
Tace "ok my sweet
Yana kashe wayan jiki na rawa yatashi yafita babban parlour part din Fandau ya canza security din kofan duk da yasan balalle bane Hadim tashiga amma yayi hakane saboda tsaro.
Yakalli yanda Fandau take. A sugunne tana nishi nagajiya
yace "jekiyi wanka sanan ki samu sabon towel ki daira kisan yanda zakiyi da Wannan kannaki dan bana san ganin sa me kamadana tsohon baya hude karki kara bari naganshi kiwuce kiyi abinda nasaki inajiranki.
Ya fadi haka yana kwantawa akan gadon yana tunanin meyasa Fandau tafi sauran batan da yasani ne ko wannan tsallen kwadon dan yakarewa jikinta kallo yasata bawai mugunta ba shikan sa yana mamaki yanda akayi gangan jikinsa yake yaudaransa akanta,
Allah Allah yake lokacin tafiyanta yayi ko idan yaga bata kusa zai iya manta ta,
Dan yanajin kunyar ranan da Hadim zatagane yanason wani abu ajikin yarinyan amma idan yatuna da ita taja sai yaji tausayin nata yaragu.
Duk dahaka yana tsoron ranan da zata reskeshi,
Yasauke a jiyan zuciya afili yace Ya Allah kacirewa gangara jikina kwadaituwa da wannan yarinyar kar zuciyata ta kasa daurewa itama takarba da ganan na tozarta a idon Duniya dan babban lefi nayi na auri yarinya bada sanin iyayen taba nima nawa basu sani ba nasan ko shari a sai tamin hakuncin hainci da yaudara danayi,
Dukan filo yayi yatashi zaune dan shi yafi ganin lefin gangan jikin sa dan shiya kekai tunanin ta cikin kwakwaln wanshi.
Motsin fitowa tane yadawo dashi daga nunanin ya daka kai yakalli ta daure take da towel kamar yanda yace tayi sai kanta tadaure tamau da wani siriri gele na fakista tsayawa Yayi kallota ya nason yaganta cikin kwalleya da Kananan kaya English weres amma Bata dashi dogayen riguna kawai da fakista hadim tabata a cewar ta ba ado tazo ba karta dauke mata hankalin miji dan komai munin macce idan tayi ado tana kyu
Yana kallon ta ita kuma tasun kuyar da kai tana tsaye a hannu yadan bubuga gadon a laman tazaune ahankali ta zauna ta sake sunkuyar da kai.
Nabil tashi yayi zaune ya nade kafa yasata agaba yana kallon ta hannun sa yasa yadago habanta yakai nasa fuskan dai dai nata a hankali yace "kinyi brush din bakin ki?
Gyada masa kai tayi alaman eh.
Hannansa yasa yaja lips dinta na sama yabude haske masa ido fararen hakoran ta jerarru sukayi bai san sanda yace wow
Dama datti ne yadafar dashi kenan
zuba mata ido yayi yanason yaga munin ta amma sai a sannan yake ganin wasu sirrikan boye na kyunta da mutum bazai iya ganewa ba har sai yanusu hancinta bame tsawo bane kuma bana nen neba ne daidai misali fukanta yanada dan fadi kadan gawani kwantaccen gashi a gaban goshin ta yazo mata har wajen kunnenta sai ka ratse megashi ce dan man askin iya kanta ta shafawa idanuwan ta suna da girma da haske shide Nabil ko jurewa kallon su bayayi Fandau doguwace bata da jiki ban bancin suda Hadim kenan ita farace tas shuwaa amma gajerace ga jiki.
Ajiyan zuciya yasauke afili yafurta yarinya kinada kananan kyu wanda yafina manya daukan hankali ya sunanki?
Fandau wani haushi taji ace mutu yana amfanuwa da jikin ta tsawon watani bai san sunanta ba.
Ahankali yafurta kigaya min mana
Fur taki mgn gashi bayason matsa mata dan yafi son tasaki jikin dashi
Jikinsa ya
Jawota yace "niko fushiki dani ko nasaki tsallen kwado ko bari namiki tausa ciwon zai tafi. Ya nayin yanda yayi magana cikin sanyi kaman bashiba yasa ta dago kanta ta kalle shi ido daya yakashe mata shiru tayi ajikinsa yana mammasa mata cinyoyi ta tuntana jin ciwon har tane meshi tarasa daganan salon ya canza.
Haka ya wuni yana cin bonus injishi da fada🤣🤣
Wuni guda ajima bini bini abu daya tana manne ajikin sa,
Ba abinda yake rabasu sai sallah
Abinci ma kayan
Fruit kawai suke sha sai ruwan tea
Nabil yayi hakane dan yaji ko yarinyar zata iya gunduran sa amma ina sai mawasu surukan da dabai saniba da suka sake nunkuwa
Akan nada.
Sai kusan 10 na dare yakira oucera wani yaran gidan sa yace yazo general parlour yadu ba masa Hadim tana ciki.
Yazo yaduba yace "bata ciki
Harzai fita yajuya yakalli Fandau yace "zan siyo miki man da zaki shafa akan ki da kuma wanna zaki shafa ajikin kida sabulun wanka mai kyu kidena wanka da wancen bashida kyu amma zaki samu inda zaki boye idan kika kuskura matar gidan ta gani sai nacikin jahannama yafiki jin dadi.
Yayi shiru can yata ko gaban ta yasa hannu yamekar da ita ta tsaya yasa hanunu ya tallaho kumatunta biyu duk da hannun sa biyu idon sa cikin nata yace "sai me'kikeso da bukata na sayo miki kwace fuskan ta tayi tazame jikin ta danasa tace" wajen mama ta nake son naje
Wannan bazai samuba zakije idan kingama mana aikin da muka daukoki.
Fandau fashewa tayi da kuka ta fada gado.
Baki ya tabe tareda daka kafadun sa yafice da sauri sai da yaga yafa da kan kujeran general parlour sannan yaja ajiyan zuciya yana murmushi wayan sa yazoro yakunna yakira Hadim yace "na dawo
Tace "kana in yace ina babban parlour tunda kince gidan da baki tace "ai har sun kwanta ni ina daki kashigo kawai yace"ok my dear
Hadim da yau ita da habiba sunsha jike jiken suna na mata Nabil kawai ta ke jira yana shigowa da godu ta fada jikin sa shima rungumota yayi sosai yana ajian zuciya na karya kamar gaske yayi missing nata
Tace "kasamu meeting ka manta dani nasha iran ka awaya soba adadi barufe
Yace" meeting ne yayi zafi yaraba jikinta da nasa yawuce toilet tabi bayan sa cikin zumudi dan magani na aiki ajikin ta
Saida suka gama duk shirin suna kanciya Nabil yana sane da ita yaja blanket ya kwanta yau ko janyo tan bai yiba data dame shima juya mata maya yayi.
Da sauri Hadim taja wutan ta kunna my star mekenan hakan nizaka zuyawa bayi yajuyo yace "wayyo my one dan Allah kibarni nayi Baccci wllh agajiye nake kinsan fa wuni nayi a meeting.
Tace "Gaskiya my star ka binciki lafiyan ka dan da bahaka kake ba dada ko ball kabuga baya hanaka yin kamai balle wani meeting nide zamuje wajen doctor baka da lfy ina gama shiyasa ka kasa bawa yarnyar nan ciki dukka canza kamar ba star dina ba.
Shide baiyi mgn ba Baccci karya mayayi.
Da safe duk tare sukayi breakfast dasu habiba
*Bayan wata 1*
Fandau tana jin canjin ajikin ta dayake bawanda zata gayawa saita jure abinci ma bako wanne take ciba ga saurin jin yunwa kocikin dare saita tashi tane mawa cikinta abinda zata ci
Gawannan ciwon maran nan da tayi tun ranan da Nabil ya fara satan zuwa yananan gaba daya maranta jinsa take kamar andaure mata baye ma ranan da Nabil bai samu shigowa ba dan yanzu ba abin data keso irin abinda Nabil yake mata,
Yanzu ma tsaye take a kitchen sai cije hanunu take duk abinda ta dafa takasa ci dan jitayi
Tana mugun son shan kunun tsamiya ga bagarin balle wani tsamiya.
Nifa my star inaga kamar yarinyar nan tasamu ciki dan da bata kara ko kwana daya ba amma yanzu gashi har two days Gaskiya idan mu kayi sa a burin muzai cika wannan karon takara she zancen cikin farin ciki.
Nabil yace "inko hakane my one zanmiki kyutan da banta bamiki irin saba zan jidake sosai.
Tace "ai nice yakamata nama kyuta amma bari da safe zamuje wajen doctor tukun
Zaro ido Nabil yayi yace ta yaya zamu kai ta wajen doctor?
Tace ba ita zamu kai ba fisarinta zamu garba sai naboye idan na masa bayani kaman yanda musu ciki sukeyi idan yace na iyo fisari sai nazuba natan.
"Yeeees yace tare da tafa mata.
Fandau tana tsaye haryanzu tana tunanin bayan kunnu tsamiya ko mezata iyaci taji muryan shigowa su hamdala tayi azuciyar ta dan tana muradin Nabil din ma sosai da sauri tafito dan kar tayi lefi zubewa tayi kamar yanda tasaba gaishesu Hadim ce kadai ta amsa Nabil ko inda take bai kalla ba yawani sha mur kamar yanda yakeyi idan agaban Hadim ne.
Hadim tace yawwa muje bandaki ko takamo hannun Fandau suna shiga bathroom din dan roba tameka mata tace gashi kiyi fisari anan kibani Fandau hannu narawa ta karba dan tana tsoron Hadim.
Doctor Muktar yazuba wa Hadim ido yace" meda me kikace yana damunki yamutsa fuska Hadim tayi kamar marar lfy tace tashin zuciya yawan ciwon kai bakina yawu yana taruwa
Cikin happy doctor yace "dan Allah da'gaske abin damu ka dade muna son jine amma bari nakira nurses kuje a gwada firarin ki yabuga waya yakira nurse din tana zuwa ya hadata da Hadim din suka fita wani dan roba tamekawa Hadim tace kishiga toilet kiyi fisari ko Hadim ta karba tana shiga ta bude roban ta siyaya fisarin Fandau a ciki tafito tamekawa matar saka makon yana fitowa tamekawa Hadim tace ta kai wa doc
Hadim tana kawowa tamekawa doc
Hannu narawa Muktar yakar bi pepper suma Nabil da Hadim gaban sune yake faduwa doctor yana budewa ko gama karanta wa baiyiba yajefar yayi kan Nabil yafada jikin sa cikin happy yana cewa "my friend congratulatins
Hakan yanuna musu akai ciki kenan Nabil bai san sanda yature doctor ya rumgumo Hadima suka fara kukan farin ciki atare sunjima a haka.
Kafin doc yakatse musu nunani dacewa ni fabaga ma yarda ba sai namiki scenning
Yafadi hakan yana tunawa Hadim dagon da yake scanning din
Atare cikin sauri Nabil d Hadim sukace scanning kuma
*To fa abin nema ya* *samu amma ya zan cen scanning* *zai kasan ce*
*Zaiyuwu kuwa*
*Karin gdy gamasoya*
*B Jattko*