DAMA TA

30

by @hauwaausmanjiddarh

DAMA TA 



      NA




BATUL ADAM JATTKO 



GODIYA TA MUSAMMAN GA WADANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKAYIMIN TA'AZIYYA THOUGH ONLINE NAGODE NAGODE ALLAH YABARMU DA SOYYAYAR JUNA, ANA TARE🤝


  30





Tace ashe yasmin bakida hankali, wanne irin maganane wannan din? Daza kice kinada shakku akan haihuwarta kodazu danaje gidan tana bawa 'yarta nono,


 yasmin tace "Allah inna kiyarda maganata kinsan yanda akayi aka samu ruwan nonon ne shinema yakara sakamin shakku don likita dinda take cikin jirgin takira tace yau kwananta 3 da haihuwa amma haryanzu ruwan nono bai sauko mata ba matar sai tace mata meye dalili sai takalleni tacemin inkoma gurin zamana toh day anan bansan ya akayi ba sai naga tana bawa 'yar nono sai inna zainab tayi shuru cande sai tace wasu daman ruwan nono baya sauko musu dawuri balle ita da kikace randa tahaihu nema, 


Tasake sai tace "toh inna meyasa tace kwananta 3 da haihuwa 

Inna ZAINABU cikin fada takoreta agurin tacemata kedan Allah kitashi kibani guri banason surkullen zance ni bana daukan magananda bashida ma'ana kinsan halina sarai yasmin de tatashi tana zumbure zumburen baki





Nabil tsugunne gaban mama tana fada masa yanda za'ayi amfani da magungunan 

 shiko dayaga bazai iyaba kawai sai yaciro pen yake rubutawa tana masa bayani a tsinake idan yarubuta sai yajefa acikin ledan ahaka tagamama sa bayayin 

 yatashi ya bata salama


Hadim ko ajikin ta da Nabil zaitafi dan tasan Fandau tana jego 

Kuma ma ita haryanzu bata wani dauki fandau din da mushin manci sosai ba 


Fandau ta shafa nonowan ta da sukayin hulu hulu dan cikan ruwa acikin yau kwannan ta 4 da haifuwa amma ciwon ta keji agaban ta yanzu ta dena  

Yanzu cikan nonon ne kawai yake damuwan ta dan jitake 

 Kamar zasu fashe 

Dan matsawa tashi saiga ruwan nono ya tsarto mata abincin y'ar ta dayanzu tananan dashine abin cikta yanzu ko mezasubata inama ko sodaya kun barmin ita nabata amma kuka fikarfina 

Cikin kuka tace kiyafemin 

 y'ata Wllh ninayiwa uwata lefi har kema abinya shafeki inama zan ganki koda sodaya ne wllh da ko karfina zai kare sai kin dan dani abincin ki 

Jin kofa yayi magana ta san shikowa za ayi tasan bame shigowa tunda tasan basa nan akasan 


towaye 

amma da tatuno Nabil yace zaizo 

Kafin tayi yunkurin tashi tasa riganta har yashigo 

Cikin shigan sa kamar kullum black cout ne ajikin sa amma rigan cikin blue ne kamar yanda  yasaba rigan cikin kawai yake sa irin daban 

Idan ba da Hadim zaifita ba inda ita kuwa irin daya duke sawa sai ranan da tace ina yau liffaya zatayi shima yakeyin shigan cout din 

Bata tashiba harya karaso inda take  

Tsugunawa yayi agaban ta dukda idon sa boye cikin bakin glas  

Daganin yanayin sa tasan ba karamin kallo ya ke jefa mata ba 

Towel dinda tayi kasa dashi taja zata rufe jikinta 

Yarike towel din gem yana kallon ta fuskan sa dauke da murmushi me narkarda zukatan mata  

Bata rai tayi ta juyar da kanta daya gefen yasa hannusa yajuyoda ita yace tunanin mekike?

Ko tunani na?

Ko dayake 

Nasani kina tunanin inda yarki take ne datana nanda yanzu zata rage miki cikan suko yayi maganan yana shafa mata boobs dinta  

To kar kiji komai yariya tana wajen Momin ta tana kuma shan nono yanda ya kamata kulawan da take samu bazai misaltu ba.


Idanuwan ta masu haske ta daga ta kalle shi ta tabe baki 


Hada yatsun sa yayi tak yadaki leben ta

 daya 

Taji zafi tayin saurin kai hannun ta kan leben tana murzawa 

yace"barshi yayi jizafinsa kidena murzashi hukuntashi nayi yacika lefi

 bai iya sannu da zuwa basai rashin kunya ko

Koda yake mijin gaske akewa sannu dazuwa ba Mijin wucen gadi bako.

Dan nasan da Wannan mekama da barorojin kika aura da kinmasa sannu ko?


Fusge towel dintayi a

Hannun sata ta daura zata meke


 yada kafa fuwan sa ya danne guiwowun ta daya sa a tsakiya tasaki dan k'ara tasake zama 

Yadago haban ta yace "badan halinki baya yajikin ki? 


Cikin dakiya tace"

  kazo daura tukunyan ko har goben tayi 


Cikin basarwa

 yace" mama ta bada sako akawo miki shine dalilin zuwana 

Kuma ina miki albishi Bagana ta haifu danta namiji shekaran kija.


Cikin sauri 

Tace" dan ALLAH ina kasan yangidan mu.

Yace"bakiji nace miki nariga ki sanin yangidan ba 

Ina kasan su me mamata ta maka idan kasanta meyasa baka cuci sauran matan masu yara dayawa ba sai ita me biyu kuma makahuwa. 


Yace" rashisani ne yajanyo amma banso kaddara ta hauta kanta ba 

Kuma karki kara cewa mama makahuwa dan yanzu tafiki lfy da jindadi 


Cikin sauri tace da gaske tasamu lfy  

Kuma bagana wata aura.

Shima cikin jinda din sakin fuskan ta yace "wannan sada ka yallan da aka so hada ku mana 


Tace"Shattima 

Yace "Yees  dan haka kicire shi aranki kar kikara tunanin sa kinji  

Keba mashiba kowane namiji ne 


Itako bata maganan sama take ba taluma cikin murnan warkewan maman ta saide dan tasake tabbatarwa tace"dagaske tawake tana gani ras harta bada sako akawo miki 

Nabil ganin firan mama da bagana yana sa Fandau cikin farin ciki yasa yakudiri niyan wannan mawani daman ne 

Da zaisa ta cikin farin ciki kozai ragewa kansa alhaki 

Hannuta yakamo yace da gaskene mana bari nayi wanka nafito zakiji sauran bayanan muje kimin wankan danni mata ta ita take min wanka mikewa wayi yace "shikenan bakya son jin komai na mama haka yaja hankalin ta tabishi suka shiga wankan ko acikin bathtub dinma bawani wanka take iya masa bashide ya janyota jikinsa yana faman jagolgola ta 

Danwani kyau ta kara masa kamar ba ita ta haifu ba

Saida yagama jagolgola ta yace tafita zaiyi wanka 

A kunyace tafita a bathtub din ta dauki wani towel din ta daura tafito  

Shikuma duk yana binta da kallo komai nata sha'awa yake bashi yasauke ajiyan zuciya yasaki ruwa yasake tara wani ruwan yayi wankansa yafito yasameta har tagama gayunta cikin wasu English wears masu dan karen kyu 

Sunfuto mata da Heep's dinta sosai ga boobs dinta da suka yi tsage tsage acikin rigan wow yafurta yana binta da kallo takawa yayi har inda take ya jata jikin sa yasauke ajiyan zuciya cikin kunne ta yarada mata 

"kirage wannan gayun ba yanzu ba karki sana kauce hanya.

Dago kanta tayi ta kalle shi tace" ina  labarin mama ta  


Yace"na aika ayimin ordern abinci ina jin ya iso ma bari nasa kaya na karbo abinci saimu yi firan mama ko  

Daga shi sai towel din yawuce part dinsu 


saida yagama mata bayanin komai tace "da'gaske wanan daga hannun mama yafito  

 Bai mata magana ba yadauko wayan sa yashiga gallery ya shiga nuna bata hotona mama da kuma wanda suyi selfie da maman 


Ai Fandau bata sanyanda tawarce wayan ba 

Wllh mama ce itace 

Wllh 

Tana maganan idon ta yana zubar da hawaye kamar ansaki kan fanfo 

Mama wannan da kikayi hoto dashi mama ba masoyinki bane harkina dariya akusa dashi mama kin manta niko harkina dariyan ki bayan kin rasani aduk kan alamu kinfini jin dadi kamar yanda yafada kin canza 

Fusge wayansa yayi a hannun ta 

Tace"dan Allah kamani bangama magana da ita.

Yace" kingama tunda kika cemin ba masoyin mama ba bayan baki fine sonta ba kingujeta akan wanda bai taba furta miki kalman soba Allah ma yatemakeki kin fada hannun nagari da kuma idon sani da wlh kin gama bata.


Tace" Naji nayi kuskure kaban hoton nagani  


Yace"naki nabaki kinamin kuka.


Tasabayan hannun ta tagoge hawaye 

Tace to kabani 

Wani mugun tausayinta yaji yanda tayi maganan  janta yayi jikin saya rungume ta yana shafa kanta 


Cikin sarkewar murya 

tace" kace Bagana ta haifu ko meta shifa 

Yace namiji ne 

tace kaganyi ne?

Girgiza mata kai yayi 

 baka gayamin inda kasan mama ba? 

yace "zaki kisani da sauran lokaci 

Tace "idan lokacin yayi zaka samin alluran mantau din?

Shiru yayi yace "bar wannan mujira lokaci banace kiciga bada addua ba 

Tace inayi ai yace yawwa kida ge 


Tace ina yariyar ya akayi take shan nonon wanda bata haifuba 

Har yabude baki zai gaya mata kuma yatuno kar hakan yazame mata sheda ko hujja wataran.

Yafada 

Afili yace"wannan bai shafeki ba 

Kidauki kayan da mama ta aiko miki da mushin manci ki fara amfani da shi 


Sai asannan ta juya tana kallon kayan ita har taman ta dashi ganin hoton mama 

Dasauri ta kwace ahannu sa tafara bude laidojin tana ruguman su wai yanzu wanan daga hannun mama yafito to dasunan waza akawowa tasande bada sunan taba   


Cikin kuka 

tace"ni tace akawowa tasan inda nake ne? 


Murmushi yayi yace "taya zata san inda kike 

Anan yagaya maya yanda yayi yakarbo amma bai gaya mata dangan takar suba.

Kuka fandau tasake fashiwa dashi

  

Yace"idan kina kuka banace bazan karamiki baganan mama ba 

Cikin sauri tace "nadena 

Ahaka yayi ta mata firan mama ganin tafi sakewa idan yana mata firan mama da Bagana 

Wani wajen tayi kuka wani tayin mamaki labarin dayafi dadi nasamun idon mama ne

Ahaka suka kwana tana like ajikin sa duk da bai nemeta ba dan ba hanya amma yayi wasanni masu gamsarwa da ita 

A washe garin suka bar kasan shida dimbin abokan sa 

Sun iso ran gobe suna 

Fadin shidiman da ahashi da shagani bata lokacine anko na mata da maza iri daya Hadim taci makeup kamar wata amarriya kyukam harsun kaji 

Kyuta sunsha shi ba adadi Hadim kam har gajiya tayi da karban 

 kungiyar sun bawa hajara kyutan kofi irin na yan ball dinnan karshe a sada na farin golne wanda sadan sa yakai rayuwa wani babban mekudin ma   (BBC) (CNN) (ALJAZEERA)  (France 24 )da sauran kafafun yada dalaru sun yada aduniya 

Balle kasan mu duk ida kaji zancen sunan ake  

A *shid* *hotel* akayi taron amma duk girman shid dayawa basu samu shiga ba 

Su yasmin sune manya awajen Inna ZAINABU sai washe baki take idan taduba wanan dinbin mutanen nan suntarune dan saboda Nabil sai taji dadi da son Nabil kamar acikin ta yafito takeji 


Kwanan bakin Nabil ukku a garin meduguri suka tafi 

Nabil yashigo yasamu Hadim tana bawa fujjirat nono yazauna abakin gadon 

Yana cewa"maman mama yane

 tace "akwai damuwa fa wllh wannan shidima sunan yayi yawa ko ina kashiga social media da kafafun yada labaru banda labarin mu bawani yarmu ta shiga Duniya ina tsoran bakin yayiwa babyn illah fa


Nabil yasa hannun yadan daya nonuwan Hadim da sunyiwa bakin baby wani ragajaf jaf yace kinga kidena shan maganin sauko daruwan nonon nan ya isa harya mata yawa kuma jiya banaji ummi tana cewa kidinga rikewa idan zaki bata ya mata nauyi ba idan ba haka ba tazama me katon baki.


Hadim tace "Wllh nadena sha 

Yace "maganan bakin mutane kuma ba abin da baki zaiyiwa jinin Muhammad Habubakar damasak  

Dan ni jinina da baki yataso yazama jinina ba abinda zai sameta.


 Fujjirat tanada kwana 20 wani tafiya yasamu Nabil zuwa Bangladesh sunada wasa acan fur Inna ZAINABU tace idan yarinya bata yi watanni 3 ba bakasan daza sake maida ta sai idan shika daizai tafi 

Dan haka Nabil bai so rabuwa da yar babyn saba haka yatafi kuma dasunan idan suntashi shida yan kungiya London zasu wuce wannan ne damuwan Hadim dan tasan da Fandau agidan wanda wata kila ta gama biqin 

dan ita matun gwanaki maman ta takamaya tana sallah dan aboye takeyin sallah  

Sai jitayi tace "Hadim irin bik'ina kikeye danni ma bana jimawa inada kwana 15 ko14 nake fara sallah  

To tunda garanan tafara sallahn ta afili  


Tana suron idan yaje ya jone da Fandau  

Koza ayin tafison da saninta  


Tace "wllh bana son zuwan ka London dinnan dan ina gudun kar kaje agarin rashina kayi sha a'wan Waccen yarinyar 


Yamusa furka yayi yace"wacce yarinyar kenan 

tace" wacce muka ajiye mana

yace "wllh zakisa ma inazuwa na sallah meta 

Tace" haba impossible dan kasan naka bukatan yabiya ko 

Agogon hannun sa yaduba yace"ana jirana makarasa ta waya 

tace"aide baza ahanani rakiya airport bako  

Waneni inhana baby da Mom dinta rakiya airport  


Nabill kwance amakeken gadon hotel din a kasan ta Bangladesh sai juyi yake shide yasan bawai gajiyan wasan bane yahanashi Baccci dan yasha maganin da yakamata yasha yasamu Baccci amma ya kasa daukan sa  

Yana rufe idon sa suffan ta kadai yake hangowa yayi saurin dude idon dan bazai iya jure rufe sunba dan yarasa yazaiyi dan zandan girma ma cewa yayi bazai kwanta ba jiya ma haka yakwana 

Wani bangaren yace anya bazan fita innemi wanda sata yimin magani ba 

Da sauri yagirgiza kai dayatuno da dazu yagama ganinsu daga su sai pant da bra amma baiji sha awan kowane daga cikin suba sai ma kyamar su kuma koyanzu daya tuno su haushi yaji jiyake kamar yacire gangan jikinsa yajefar yadena kawata masa wanda yasan mazai samuba 

Amma ina Nabil nusuwa ya dauke masa 

Tunowa da wani dabara yasa yayi saurin rarumo wayan sa 

Sani yakira yadaga yana 

cewa allah yajan jamanin Abu fujjirat wasa yanzu nayi niyan kiranka amma dana duba sai naga ku acan dare yayi sosai nabari sai dasafe congratulations ALLAH yakara dauka ka amma sir nagajikin ka asanyaye afilin lfy kuwa 


Ajiyan zuciya Nabil yasauke yace "gaskiya sani ba lfy ba 

"Subahanallashi meyake faruwa  

Sani ina son ayau zanshirya maka tafiya zuwa London kadauko min wannan yariyar kakawomin nan dan wllh jinake idan ban kasan ceda itaba Bazan iya. 

 samun nusuwa ba 


Angama sir amma ai nakega jegotake ko? 

Yafadi haka yana dariya dan Sani aboko ne awajen Nabil kafin yazama yaron sa 


Nabill yace"kaide kayin yanda nace kawai dan ina cikin wani hali 


Cikin mamaki Sani yace wai duk akanwan nan yariyar  

Nabill yace"wai fa abin kunya shiyasa banason kowa yasani koda Hadim ce 

 Sani yace "ai bawani abin kunya ai kabar rena allura dan karfene  

Amma kabari adan kwana biyu dan naji anacewa idan macce ta haifu batayi arbain ba aka koma mata to mashaifan bai gama komawa yanda yake baza iya samun ciki wanda hakan zai iya janjo konika


Nabil yace "ai idan zatayi konika zamufi kowa murna dan tayi saurin fita acikin yaruwan mu nima nayin saurin mekata iyayen ta dan idan nasan bazan sameta ba dole zan hakura 


Sani yace "amma ni sir wllh bangama gamsuwa da amata alluran dazatayi losing memory taba aganina kaman ba amata adalci ba. 


Numfasawa Nabil yayi"yace rashin adalci kam anriga anyin tunfarko 

Iya adalcin kuma da zanyi in mantar da itan shine mafita dan kare mutumci na

Amma yanzu duk bamuzo nanba 

Abinda nace maka shine damuwata 


To sir yanzu tunda har kake jinta haka zaka iya rabuwa da ita ne 

Cikin fusata Nabil yace "Sani kayi abinda nace kawai 


 Sani yace sorry sir amma fa ina tsoron yanda zan tauko ta idan ta ganta awaje ta nemin ta zille minfa ko tanemi taramin jama a 

Ayanda tasha wahalan wajen shekara adaki akulle nake ganin idan taganta a wajen dawuya idan zata kara yarda da bina musamman idan kaduba nina kaita   



*Tofa kode DAMAN KUBUTA NE YAZOWA FANDAU*




*To masoya zakumin hakuri dawanan dan hakan ma agurguje nayinsa* *dan kuna rainane*

*dan munacikin makoki ne*