MATA TA CE LABARI MAI CIKE DA SARKAKKIYA

CHAPTER SEVENTEEN & EIGHTEEN

by @misshajo

๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จโคโ€๐Ÿ”ฅ *MATA TA CE*โคโ€๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ


        By 

  *Hajara L Sadeq*


   @Miss Hajo


_2023 Gift_๐Ÿฆ…


06โˆš03โˆš2023



๐Ÿ…ฟ๏ธ.............*17 & 18*



Abba......Kara rufe Mata Baki yayi ya ce kiyi a Hankali nasren "ta na fasa kuka ta CE "ka Fita Dan girman Allah Abba na shiga ukku Abba ko Kayi mantuwa ne Nasreen CE fa yarka"Cikin Wace Irin Murya ya ce"ba laifi na bane Wlh laifin zuciyata ne da ta kasa control din kanta a kanki Nasreen Tun Lokacin Da na Fara arba dake Allah ya jarabceni Da Muguwar Kaunarki Duk yanda Zan kwatanta Miki Irin son da nake Miki Nasreen wlh nayi karya,Ina sonki son da ban Tab'a yiwa wani mahaluki irinshi ba ,Zan iya Komai a kanki Nasreen Dan girman Allah ki Aure Ni wlh Zan iya Mutuwa idan Baki Aure Ni ba".



"rumtse Idonta sosai nasren tayi ta na Jin kalamar Abba kamar digar darma Cikin Wace Irin Murya Ta takaici ta ce"Abba ka manta da wacce Kake tare Ni kake Fadawa Kalmar so matsayin uba fa na dauke ka?Wannan din ba Komai bane nasren Soyayya ba ruwanta da babba ko yaro wlh da gaske nake aurenki zanyi nasren idan kin amince juma'ar nan ma a Shirye nake a D'aura mana Aure idan ban aureki ba Zan iya Mutuwa saboda son da nake Maki ya zarce misali".


 "Ta na Mikewa Cike da takaici ta nuna mai hanya ta ce"Fita Abba ko nayi maka ihu tun muna mu Biyu Kafin Kowa yasan halin da ake ciki"ya na Shirin riko Hannunta ta fusge tare da fasa Kara ai Kafin ka kifta Ido Abba har ya bar dakin Kuka ta fashe dashi ta na hade kanta Da gwuiwa wannan Wace Irin rayuwace Wai ita Abba zai duba yace Yana so Bayan matsayin uba take kallonsa sannanma yasan Sarai Danshi yake sonta Bata Gama wannan tunanin ba Taji duk anshigo dakin Kallonta Momy da Sury da ihun ya tadosu Dan mama Lami sunaji sukai burus a tare sukace.




 "lafiya dai ihunki muka jiyo"Gabanta na Faduwa ta kallesu Ta na shsheka ta ce"mafarki ne nayi Daman shine na tsorata"Duk ajiyar zuciya suka sauke Aunty ta ce"Addua yakamata Kiyi ba ihu ba Kiyi Addua ki koma bacci sannan karki fadawa Kowa Koma wani Irin mafarkine kikai Saida safe Ta Fad'a ta na yin Gaba ".



"sury zata Fita ta kamo Hannunta ta ce"Dan Allah ki tsaya mu kwana tare wlh tsoro nake ji"Ga alamun kin tsorata a mafarkinnan sosai badamuwa to "ta Fad'a ta na Kwantawa gefenta sai sannan ta danji sassauci tunani cinkushe a kwalwarta sai Wajejen 3 bacci yayi awon Gaba Da ita.




Washegari haka ta Tashi sukuku Ko A Makaranta Batayi karatun kirki ba Kallo Daya zaka Mata kasan akwai muhimmin abunda KE damunta Daman Bata da wata kawa da take sharing problems da ita mamantace babbar kawarta da take Fad'a Mata Komai nata Saidai Kuma a wannan Karin batajin ko ita zata fadawa Wannnan al'amarin da Yazo Mata a Bazata.



Koda ta dawo school bangaren Mamanta ta nufa Dan tayi niyyar Bazata koma ba Kallonta mama tayi ganin Duk tayi sanyi ta ce "nasren lafiya Naga Kin chanza"ta na kwancewa jikinta ta ce "bakomai mama"Bayan Isha i nasren harta kwanta khalifa yazo ya ce"Aunty nasren Abbanmu yace ki dawo za a rufe Gida"tanajin haushin Abba a ranta ta ce "Nan Zan kwana yau"Mamanta tayi Saurin harararta ta ce "Alhajin zai Aiko a kiraki kice Baki Zuwa wuce kiban waje"ta na shagwaba fuska ta ce "mama"Daga Mata hannu tai Wanda ba a son ranta ta bi Bayan khalifa ba.

Daren ranar ma Saida Abba Yazo Mata Yana Mata sambatun maganganu Shima Saida ta kusa Masa ihu Kafin ya Tafi.



Tun daga ranar nasren Bata da walwala Dan kullum Abba sai yazo Mata ya na sambatun Irin son da Yake Mata kwata-kwata a halin Yanzu Hankalinta a tashe Yake Gashi Mama Taki yarda Ta dawo wajenta Saboda kimar Alhaji da take gani nasren har wata Rama tayi Saboda Rashin isashshen bacci Dan kullum da fargaba take kwana Yauma Ta na Zaune Bayan Isha'i taji anturo kofar cike da tsoro ta Mike a zatonta Abba ne juyowa yayi ya na Hade hannayensa ya ce



"sorry wife na tsorataki nine"ya Fad'a ya na Karasowa bakin gadon ya zauna"cike da fargaba ta ce "Nidai Ka Tashi karkaja A ganka Ayi Mana wata fassarar Dan Allah Kar kajamun Matsala"calm down wife Basunan Daga Mama har Abba sunje dubiya kinsan kwanannan Nayi juriyar kewarkifa"Yana ganin yanda ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya Ta ce"Ina yini"Hira ya dinga janta Da ita Tare da Bata wayarshi Tayi kallo tuni ta wartsake har Batasan dare yayi ba Saboda dauke Mata Hankali da Kallon yayi Kamar d'aga sama suka ga an banko kofar ba nasren ba Hatta Ashraf Saida ya tsorata mama Suka ga tsaye tare da Abba tsawa Mama ta daka Masa ta ce



 "Dan ubanka Daman baka Rabu da Shegiyar yarinyar Nan ba Shine Har kake Lallabowa So kake ta Bata maka tarbiya na rantse da Allah Ashraf baka Rabu da yarinyar Nan Komai Zan iya maka Kafin ta maida Kallonta ga Nasren data tsure ta ce "To farar munafuka ta Nan Kuma Kika bullo ,to wlh ki Sani Ashraf yafi karfinki yanda Jirgi yayiwa Keke tazara To haka D'ana Yayi Miki Kinyi maitarki ki Gama Amma Dana yafi karfinki banza marar Asali da galihu irinki ki cigaba Da nacewa Dana kiga Abunda Zan Miki Yar matsiyata".



Ta na Maganar ne cike Da tsantsar Masifa Abba ko Shima Masifar ce take cinsa Baisan Sanda ya gansa Tsakiyar dakin ba Daga hannu yayi ya Shararawa Ashraf Mari Kowa dake wajen Saida ya zaro Ido Har Aunty Dake Shigowa Karon farko Da Abba ya taba Marin Ashraf Dan kaf Cikin Yayanshi shine Star dinsa Kafin yayi wani yunkuri ya Kara shararesa da Mari Cikin Tsananin bacinrai ya shakosa ya CE "Dan Ubanka me Nace make game da Ganinka Da yarinyar Nan ,ban rabaku ba Watau ka nuna ban Isa dakai ba To kaji na rantse wlh wlh na kusa tsine maka Akan Baka Rabu Da nasren ba Gwara kabi duniya na Daina ganinka stupid".


 "Kafin Ya juya wurin nasren ya daka Mata tsawa ya ce"KE Kuma tunda bakijin magana Nasan Meye maganinki"Mama CE ta ce "Haba Alhaji Kuma saika Maresa a gaban kaskantacciyar yarinyar Nan fisabillahi dukda Nasan ciwon da kakeji Dan inaji nafika jin Haka Amma ai Kai kaja Ka koresu Mana Dasu asirce Mana d'a y'an Aiki gasu Nan burjik A gari"tsawar da ya daka Mata CE ta sanyata hadiye Sauran magananganunta hanya ya nuna Mata ya ce"Get out stupid"Ba Shiri Duk suka sabe har Aunty Da Bata karasoba Daman Ashraf ko Cikin Tsananin bacin rai ya ce"Abba Ni ka Mara Dan kawai Ina son nasren Abba meyasa bazakumin adalci ba ku tayani son abunda nakeso wlh Abba Ina son nasren Meye aibunta Dan nasota?Tsawa Abba ya daka Masa ya ce"Get out my friend"ya Fad'a Yana rumtse Ido"Cikin Tsananin bacin rai Ashraf ya fita har baya Ganin gabansa Saida yaga fitarsa Kafin ya koma wajen Nasren Ya na riko gashinta da tayi parking ta baya ya ce.



"meyasa kikeson azabtar Dani Da soyayyarki nasren kinsan Irin zafin radadin da nakeji idan na ganki da wani namiji kuwa,wlh ji nake kamar na kashe kaina Saboda Tsananin kishinki da nake ,Dalilin da yasa na killaceki a Gida Ko Ma'aikatan gidana maza banason suna ganinki,Ina son Na Gina Miki rayuwa Mai inganci,Amma kin tsaya Kina sakarci me zakiyi da wani Ashraf ga ubanshi Mai dukiyar gidan Gaba Daya Nasren Ina sonki Kuma saina Aure ki Dole wlh Banga mahalukin da ya Isa Ya hanani Aurenki ba a Halin Yanzu bank'i Kowa yasan Irin Soyayyar da nake Maki ba Dan Wataran gawata Za a tarar sonki da kishinki na iya hallakani"


Kukan ta ta karawa volume ta ce "Ni wlh Abba bana sonka bazan aureka ba Ni Kallon uba nake maka "idanunsa harsun sauya tsabar bacin Rai ya ce "Tamkar dirar darma Haka naji kalmar bana sonka Daga bakinki ,Ni Kuma Ina sonki Kuma dole na Aure ki nasaka Ranar Aurenmu sati Biyu masu Zuwa zanga ubanda ya Isa ya Hana Kuma ki sake Bari na ganki da Ashraf kiga abunda zai faru'"


fuuu ya fita ta na ganin fitarsa ta Mike ta na Kuka Tayi waje Aunty da KE Zaune a palour tayi jugum ta binta da wani Irin kallo da gudu ta Fad'a dakin da Mamanta take harta Fara bacci ta hayeta ta na sakar Mata kukan da Bata Karasa sakinsa ba Hankali tashe mama ta ce "subahanallah nasren lafiya meya Faru"Ta na shsheka ta ce "mama Dan Allah mubar gidan Nan"Ta na Binta da wani Irin Kallo ta ce "Kamarya mubar gidan Nan nasren gidan da suka tallafemu suka inganta Miki rayuwa Gidan da Suka Mana Abunda Danginmu suka gagara Mana zakice mu Bari muje ina to?tukunama a wani dalili"?



ta na Kuka ta ce "mama Allah ya na sane Damu shizai cigaba Da tallafa Mana Nidai wlh mubar gidan Nan "a wani dalili"ta na shsheka ta ce "Mama Wai Abba ne Yace yana Sona zai Aure Ni Kuma wlh Mama Daman Duk dare saiyaje Yana cewa Yana Sona Nidai wlh mubar Musu gidansu,"Tana fiddo Ido waje ta. CE"so fa nasren kinsan abunda kike cewa kuwa?Alhajin ne zaice ya na sonki bayan matsayin y'a yake daukarki"Banason karya nasren idan kina so mubar Gida kuma saiki Masa sharri"ta na Kuka ta ce.



""Allah mama ban Masa sharri ba Sannanma duka sun rabamu da Ashraf Nidai Mu Tafi kawai"ta na harararta ta ce"Yanzu naji Batu watau sun rabaki da dansu shine Zaki Masa sharri ko nasren yaushe Kika Iya sharri haka bansaniba eh to wlh tun wuri ki bude kunnanki da kyau kiji Babu Inda xamu Daga Nan gidan Bamu da wajen Zuwa "Tana kuka ta ce "wlh Mama ba sharri nake Masa ba"Duk yanda taso tayiwa mama Bayani kiyawa tayi ta ce sharrine zata Musu "tare suka kwana Saida tayi bacci Tukwana mama tayi tagumi ta na nazarin maganganun nasren tabbas Indai Hakan ta faru tabbas akwai babbar Matsala sai Kuma wata zuciyar tace haba karya ne Taya alhaji zaiso nasren Bayan matsayin Diya ya dauke ta ko ita alhaji yace Yana so bare nasren Yar Cikin sa........โœ๏ธ



*ALLAH RABAMU DA SHARRIN MAKIYA,MAHASSADA KAYI MANA TSARI DASU AMEN*




  _*Miss Hajo CE*_๐Ÿค™