MATA TA CE LABARI MAI CIKE DA SARKAKKIYA
CHAPTER NINETEEN & TWENTY
by @misshajo
๐ฉโโค๏ธโ๐จโคโ๐ฅ *MATA TA CE*โคโ๐ฅ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
By
*Hajara L Sadeq*
@Miss Hajo
_2023 Gift_๐ฆ
07โ03โ2023
๐ ฟ๏ธ...............*19 & 20*
Washegari nasren ta fito da shirinta na Tafiya Makaranta Abba ya fito Rai hade ya Ce koma Ciki ba inda Zaki ".
"ta na narai narai da fuska ta ce"Abba Makaranta fa CE zani"Nafiki Sanin hakan kin Gama makarantar waec and neco ma zansa a zana Miki ".
"Da gudu ta koma ta na Zuwa ta fada Cikin mama ta na Sakin Kuka ta ce"mama Abba yace ya cireni a makarantar mama Dan Allah ki mashi magana yayi Hakuri ya maidani wlh inason karatun sosai Saida aski Yazo gaban goshi Komai zai jagule mun ".
"Gaban mama na Faduwa ta nanata innalillahi wa inna ilaihiraji'un a fili Bata nunawa nasren din damuwarta ba sai Lallashinta tayi ta ce"Kiyi Hakuri zai hakura Bar kukan Yar lelena"haka mama tayi ta Lallashinta.
Wajejen 1pm nasren ta fito compound tayi tagumi Dan mama ta na ciki ta na Aiki Aunty da ta fito hartayi Gaba sai Kuma Ta dawo ta ce"Lafiya bakije makarantar ba"Tanaji kamar ta fasa Kuka ta ce "Abba ne ya CE ya cireni"Tofa wata sabuwa Allah kyauta"kawai ta fada tanayin Gaba Abunta.
Nasren da kallo ta bita tazata zatace' zata Basa Hakuri wannan Wace Irin rayuwace Ta na Nan Zaune har Ashraf yadawo d'aga office Nan ya sameta kamar yanda Ta fadawa aunty haka ta fada Masa ta na hawaye ta ce
"Dan Allah ka basa Hakuri ya maidani"shiru Ashraf yayi ya na nazarin Abun Kafin ya sauke ajiyar zuciya ya. Ce"karki Damu wife kidaina Kuka Dole Zaki koma Makaranta duka wata nawa ya rage ki kammala zaice ya cireki"Lallashinta ya dingayi har ya samu tayi shiru tanajin dad'i a ranta.
Misalin goman dare Ashraf ya Samu Abba Gaba Daya suna palourn da Maganar komawar sabren Makaranta Hade fuska sosai Abba yayi ya CE.
"na Cire ta din ko da chan Kai kasanya Na sanyata Tukwana ma Wai ban rabaka da ita ba Ta Ina kasan na cireta eh So kake muyi mugun sabawa dakai a gidan Nan Wlh Zan iya Maka Komai akan baka Rabu da yarinyar Nan ba ,Ina gab da koranka a gidan nan".
"ya Karasa fada ya na Nuna sa Da yatsa"Cikin bacin Rai hajiya Lami ta ce "Wai Kai Alhaji saika dinga wani Zazzakewa Da tada jijiyoyin wuya Akan shegiyar yarinyar zaka Kora danka,meye na wani haihakewa Ko aurenta zakayi Wai musan da wata a kasa".
Eh Aurenta zanyi sonta nake ko cikinku Akwai ubanda Ya Isa Ya Hana?Kowa dake wajen Saida ya Girgiza dajin Maganar da ta fito daga bakin Abba Ashraf na Mikewa ya ce"Abba Dan Allah ka Daina Mana Irin wannan Wasan bai kamata ba"
Ba Wasa nake ba Da gaske nake Nasren aurenta zanyi sati Biyu masu Zuwa Dan haka Kuma fara Shirin tarbar sabuwar Amarya ko Haram ne Dan na aureta Eyye kukayi mun wani jugum-jugum"Ashraf Da yakejin Zuciyar sa kamar zata bar gangar jikinsa Baisan Lokacin da ya juya ba ya fita Har baya ganin gabansa"
Wata uwar ashar Hajjiya Lami Ta Lafta ta ce "lallai Alhaji Watau Yanzu na gano Kan Zaren Kana nufin wannan Tsinanniyar yarinyar zaka Hada matsayina da nata Idan ka Isa Allah tsinan wlh baka Isa Ka Auri yarinyar Nan ba na yarda ka Auri Mata sama Da dari Amma Banda yarinyar Nan Wlh kaiko Kunya Bakaji Gaban y'ay'anka da Kowa ka Furta Kalmar Nan Ka rasama wacce zakaso Sai budurwar danka tirrr wlh Kuma saina yiwa yarinyar Nan lilis Wlh sai sun bar gidan Nan Tunda ba na ubansu bane".
"KE Dayake gidan Ubanki ne ba Lami Ki daki yarinyar Nan Ki daki igiyar aurenki wlh Kika sake wani Abu ya sameta Akanki zai Kare"Fada Lami Da Abba Sukayi sosai Wanda Aunty koke da bakinan Dukda Maganar ta soketa Amma A zuciyarta tabar Abun Daman ta jima da Ganewa Alhaji Kanshi Yake ma Fada Yaranko ba Wanda baiji bakin Cikin Wai babansu zai Auri nasren Har sury Da suke Shiri Saida Taji nasren din ta fita a ranta.
.washegari karfe bakwai Batayi ba su nasren sukaji Bugawar kyauran dakin su Da karfin gaske Ba Shiri suka Mike Kafin suyi wata wata an banko kofar Gaba daya Yan matan gidan ne tare da Lami a gaba idan aka cire Yaran Aunty Dukansu Kan nasren Sukayi suka rufeta da duka.
Mama Kuka ta fasa ta na rikesu ta ce"me Y'ata tayi Muku da Zaku hallakamun Ita me mukayi Muku?mama Lami na huci ta ce"bakaken munafukai watau Daman A munafurce kuke Zaune damu amma ai laifinmune Daman ance tsintacciyar mage Bata mage Watau an samu waje har kike Shirin Aurawa mijina shegiyar yarki mun Muku Rana ku Mana dare ko? to Bari kiji na rantse da Allah Auren y'arki da Alhaji Tamkar Ranar Mutuwar y'arki ne Tun wuri Ki tanadi likkafani da tabarmar kaba Dan nafi krgin nayi kishi da banzar yarinyar Nan Taki Mai Ido ya na mujiya,"
"Gaba Daya Kan mama ya kulle Kuka take Tana turesu subar Dakar Mata 'ya Kafin ta kalli mama Lami ta ce"Dan girman Allah da darajar fiyayyen halitta Ki Musu magana karsu Halaka mun y'a na yarda kome kikeso zamuyi Amma karku illatamun y'a".
"wani shu'umin murmushi mama Lami tayi ta ce "Ku dakata "Saida suka Kara jibgarta suka kyaleta Da gudu Mamanta ta rungumota Dukansu Kuka suke ba karamar jigatuwa nasren tayiba tunda take ba a Tab'a dukanta haka ba Jikin Mamanta ta shige ta na shsheka.
"idan Kina son Cigaban Rayuwar y'arki to ya Zama Dole yau yau dinnan ku bar gidan Nan,KUYI nesa Damu ku tattara ku koma inda Kuka fito idan kukayi haka Kun taimaki kanku Kun rufawa kanku asiri idan ba haka ba wlh kinji na rantse Saina Zama ajalin y'arki"Hankali tashe mama ta ce.
"Zamu bar gidan Nan kamar yanda Kika Fada Nasren ta fiyemun Komai da Kowa duniyar nan Amma Ina son ki Sani Arziki Da Rashin sa duk na Allah ne ba asan me gobe zata haifar ba mungode da Irin taimakonku garemu Allah saka da Alkhairi".
"Kafin ta kalli nasren Dake jikinta ta ce "Tashi mubar Musu gidan su nasren"Daka kalli fuskar mama kasan ta na Cikin Tsananin fushi A gaggauce ta hada Musu Komai nasu a ghanar su Suka Sanya Hijab ta Kama Hannun yarta Suka fito".
Gud'a Lami ta rangad'a ta ce "Allah raka Taki gona sai a tari wani sarkin ass tsiya tabar Mana Gida"girgiza Kai kawai mama ta tayi ta na goge hawaye ta ce"hmmm Kaico rayuwa Allah Bamu Ikon cinye jarabawowin Nan"
Saida Sukayi nisa da gidan sosai Kafin su zauna su huta nasren na shigewa Jikin mama ta ce"Ki kwantar da hankalinki mama Allah Yana tare Damu Ni farinciki ma nayi da barin mu gidan Dan Allah karki Damu kinji mamana Kinsan KE Kadai Nake dashi"ta na Kallonta ta ce .
"Dole na Damu nasren Ina kike tunanin zamuje Yanzu Bamu da wurin zuwa "ta na goge hawaye ta ce"Mama mu koma kazaure Mana"girgiza Mata Kai tayi ta ce "Bazamu koma Gida ba nasren Ina son Nayi nesa dasu kamar yanda suka bukatar basa kaunar ganin mu na tozartar dasu na Bata Musu sunan zuri'a Ina son rayuwarki ta inganta kamar ko Wace y'a Amma Kuma Kash Kaddara ta rigayi Fata Ashe gaskiya kike fadamun Da gaske Alhaji zai iya cewa Yana sonki Gaba Daya Rayuwar tazomana a baibai sai Allah ya taimakesu Kaddara ta risko"
Tana Goge Mata hawaye ta ce"Kiyi Hakuri ki Daina Cewa haka mama Dan Allah ki manta Komai Indai inaganin kukanki Nima Zan iya shiga wani Hali"Gyada Mata Kai tayi ta ce"Allah Muku albarka nasrenTana murmushi ta ce"Ameen mamana"Saida suka Gama hutawa Kafin suyi Gaba Tafiya suka dinga sha Batare da sunsan Inda Zasu nufa ba nasren Duk ta Gaji Har Isha'i suna Gararanba Yanzu babban tashin Hankalinsu Wajen kwana sunsan yanda Rayuwar Nan take da Rashin yarda ba kowanne zai tallafemu ya Basu masauki ba".
dakalin wani gida suka Zaune suna sauke gajiya pure water da awarar da mama tasai Mata a hanya ta sinta ta Fara ci kamar wacce Bata tabacin Abinci ba Ta na Gama ci ta kwance cinyar mama baccin gajiya ya kwashe ta Kallonta mama ta dingayi ta na tuna rayuwa Yanda tayi da ita tabbas Rashin uwa babban tashin Hankali ne D'anta tabbatar da mahaifiyarta na Raye da bazata shiga halin Nan Da take ciki ba Haka Mahaifinta adduar Allahkawo Musu mafita kawai take.
Kamar d'aga sama Taji an dallosu Da fitila a tsorace ta firgita ta na kallon Yar Dattijuwar da ta fito Zata kulle Gida ta na Dan lekowa waje ta ce "bayin Allah Lafiya kuke Zaune Nan dare ya kusa latsawa"lura da matar kamar ta na da mutunci ya Sanya mama cewa "Dan Allah taimako muke nema Da wajen Kwana Kafin gobe Mu Kara Gaba mu Baki NE"ta Jima ta na kallonsu Ta na nazarin Maganar mama Tare da dallesu da fitila a Zuciyar mama Addua take Allah sa ta amince Chan Taji ta ce
"Badamuwa ku shigo Dukda duniya ta baci Mutane ba Abun yarda bane Kayi Musu Rana su maka dare haka nandai zanyi shahada ku shigo nayi Dan Allah"Cike da farinciki mama Ta ce"nagode Allahsaka da Alkhairi Kafin ta tada nasren dake Cikin gigin bacci suka shiga madaidaicin gidan na kasa Wani daki ta nuna Musu ta ce.
"Ku shiga Nan dakin ku kwanta Saida Babu katifa Amma akwai tabarma"godiya sosai mama ta sake Mata suka shiga dakin Wanda suna shiga nasren ta baje Kan tabarmar ta na Kwanciya Mama ko Bata iya bacci Tunanin Mutane Biyu masu matukar mahimmanci A Cikin rayuwarta Ta dingayi sai Gabannin asuba baccin Wahala ya dauketa cike da mafarkai barkataiii.......โ๏ธ
_*Miss Hajo ce*_๐ค