MATA TA CE LABARI MAI CIKE DA SARKAKKIYA
TWENTY ONE & TWENTY TWO
by @misshajo
๐ฉโโค๏ธโ๐จโคโ๐ฅ *MATA TA CE*โคโ๐ฅ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
By
*Hajara L Sadeq*
@Miss Hajo
_2023 Gift_๐ฆ
08โ03โ2023
๐ ฟ๏ธ..............*21 & 22*
Hankali kwance nasren ta Tashi lura da mama Batayi baccin kirki ba ya sanyata Kyaleta Tsakar gidan ta fito Bayan ta Gama alwala ta koma ta gabatar da Salla ta na Addu'ar Allah kawo Musu mafita.
Sai wajen 7 mama ta Tashi ta na Gama Salla Dattijuwar da ta saukesu ta shigo da fara'arta ta Ce "sannunku Ya bakunta"Gaisheta Nasren tayi Yayinda suka shiga gaisawa da mama ta na Kara Mata godiya ta ce.
"Bakomai Bar gode mun saidai bansan sunankuba"Nuna Nasren mama Tayi ta ce"ita wannan sunanta Nasreen Ni Kuma suna na Asma'u"Washe Baki Tayi ta ce.
"Masha Allah nasmen "Yar dariya Nasren tayi ta ce"Nasren ne kaka"Ahto ban fada Daidai ba Keenan wannan sunan naki Mai wahalar Fad'a nikuma Suna Na Laure Ban taba Haihuwa ba wannan gidan ma Da nake ciki Na Haya ne D'an Yar uwata yake Biya mum Duk shekara".
"murmushi mama tayi ta ce "Allahsrk Allah biyasa"Tabe Baki laure tayi ta ce "Ameen dai za ace Ai uwarsa Gida ya saya Masa tankamame "a Zuciyar nasren Ta ce"wannan tsohuwa da fitina take"Mama ta ce "Ai Rayuwar yanzunce haka take sai Hakuri".
aikuwadai Yanzu ka nemu na kanka ka dogara da kanka Shi yafi Kinganninan na Tafi shekara 70 Amma Banbar neman na kaina ba ,Duk buge-bugen da Nasan zanyi Na ciyar Da kaina Yi nake Amma sai nake ganin kamar ku Baki NE a garin Nan Naga hausarku ba irin tamu ba"
murmushi mama tayi ta ce"eh Mama mu Bak'i NE Amma gaskiya mun shekara ko Biyu a garin Nan"Allahsrk Niko zanso naji meya fito Dake Da Daren Nan Nasan dai ba qalau ba ".
a takaice mama Ta labartawa mama laure tun zuwansu Kano har abunda ya Faru ya barosu da gidan alhaji"Laure ta Tab'a hannu da salamcewa ta ce
"Amma Anyi lalatacciya matar Nan Daman ance Bata da mutunci Ina Jin labarinta Ai idan nice KE Aura Masa ita zanyi inga ta tsiya"Girgiza Kai tayi ta ce "a a a zaman lafiya yafi zama Dan sarki"nasren ko a ranta ta ce"Kuji itama wannan tsohuwar inyi me dashi".
"Laure ta kame hab'a ta CE "To ita Ina Mahaifinta naji Duk labarin da kikaban banji na Mijinkiba"Mama najin kamar an tabo Mata wani rauni a zuciyarta ta D'aure ta ce"Mahaifinta Ya rasu tun ta na Yarinya".
"Allahu Akhbar kaico Wlh harkun bani tausayi Allah Jikansa inshallah Indai zaku iya Zama Dani Ga Guri Nan muyi zaman mu Tare "Cike da murna Mama Ta ce.
"Amma munji Dadi mama mungode Allah saka Da Alkhairi"ta na Mikewa ta CE "ai yiwa Kaine Bari naje Na fita neman Yan Aikin Nan Naga yau ko a Dace Ga Karin kummallonku chan a tukunya nasmin Saiki zubo Muku'".
"ta na fita Nasren ta kalli mama ta na marairaicewa ta ce"mama kikace Babana ya mutu Bayan kema Kince bakisan Inda yake ba"To Ni kaina bansan Mahaifinki ya mutu ko Yana Raye ba nasren"Tana marairaicewa ta ce "inshallah mama Bai mutu ba Dan Allah ki Fadamun Waye Mahaifina".
"murmushin yake kawai tayi ta ce "Tashi kije ki zubo abincin muci".
Yau kwanansu nasren Biyar a gidan mama Laure tuni sun saki jiki Da ita kamar yanda ta saki jiki Dasu nasren ta dauketa kamar jika Yanzu babban abunda yafi tadawa mama Hankali yanda mama Laure Ke dawainiya Dasu Dukda tasan Bata nuna gajiyawarta ba Amma tasan Dole wataran ta gaji Gashi Yar dubu Biyun ma da ta rage mata sun cinye yauma suna Zaune mama Laure ta leko Ta CE
"To nikuma na Tafi Idan ban dawo da wuri ba nasmen Ki Dora Mana girki Yau dai Ina fatan Allahsa na Dace da wadda zata yarda da kinibabbar yarinyar nan"Nasren CE ta ce"Wai Kaka Ina NE kike zuwa kullum dakin dawo saiki dinga mitar wata yarinya".
"Tana Jan tsoka ta CE "wlh samu NE na Gani nake neman rasa shi dubu dari Biyu Ce Nan Nake fafutukar nema"Nasren na zaro Ido ta ce"Kaka dubu dari Biyu Kuma?a Ina ake samu"gidan matar Da nake kaiwa Yan aikine to D'anta ne matarsa ta mutu Ta bar karamar yarinya ita Hajiyar Ma'aikaciyar jinya ce shima d'an ma'aikaci ne shine ake neman Mai kula da yarinyar amma bata yarda da kowa shine Hajiyar ta ce na kawo mata wacce ta yarda da ita zata bani dubu dari Biyu ita Kuma albashin Mai rainon dubu dari da hamsin a wata wlh Ina fada miki yarinyar Nakai mata sunfi a kalla ashirin amma Taki yarda da kowa Amma naki hakura Ina ta gwada sa'a ta ko Allah zaisa a Dace".
"Nasren na zaro Ido ta ce "Kaka dubu dari da hamsin albashi Saikace malamar asibiti"Kaka na wangale Baki ta ce"Wlh Yar Nan yosu a wajensu wannan Ba komai bane manyan masu kudi NE mashahurai Ina Baki labari"Jinjina Kai nasren tayi ta ce.
"wasu kudin kamar anyo yayinsu"Bari Karna biyeki na wuce "Kaka ta Mike"Nasren na Mikewa ta CE"Muje na rakaki"harta rakata bakin kofa ta na tunanin Dubu dari da hamsin din da Kaka ta fada Ranar yini tayi ta na tunanin ace Yarinyar Nan ta yarda da ita ita ko na wata daya ma suka Biya Mata burinta Ta koma Makaranta ta zana waec da neco ta sayawa mama Sabbin Kaya ,haka tayi ta wasikar jakkanta acewarta.
Washegari Nasren ta kasa Daurewa Tana cinyar Mamanta ta ce"Inama Yarinyar Nan ta yarda Dani mama Da kudin wannan Ana ban Zan koma Makaranta na saya Miki sabbin Kaya"murmushi mama Tayi ta ce"nasren kenan yaushe Kika Fara son kudi"ta na Yar Dariya ta CE "Mama Kawai Ina son Kiyi farincikine Nasan Kina son gayu samu ne bakyayi sannan kina son cikar burina na Zama cikakkiyar likita".
"Shafa kanta mama tayi ta ce "iNsha Allahu burinki Saiya cika Y'ata Allah Muku Albarka Yasa ku Gama Da duniya Lafiya"Ameen mamana Amma meyasa Inzakiyi mun Addua kike jam'i Bayan Ni kadaice y'arki"Murmushin yake kawai Mama Tayi batace da ita Komai ba itama Bata sake Wata Tambayar ba.
Yau Kaka ta dawo a gajiye sai mita Take ta na Wannan yarinyar da bakin ciki take Dole dai ta rantse bazanci kudin Nan ba Gaskiya inaga Nakusa hakura yo ko chachar kudin Abun Hawa ma ta isheni"Nasren dake gefenta a tabarma ta ce.
"Kaka Kina Ganin ko Muje Tare mu gwada sa'a kilan in muna Da rabo a dace'"Kaka na Kallonta ta ce "Amma jikata kina ganin Zaki Iya sannan mamanki Ta yarda"Kallon mama tayi taga Tayi kasa da kanta Kafin ta kalli Kaka ta ce.
"Indai mama Ta yarda mukaje Ai gwada sa'a ne Tunda Bai Zama lallai Ta yarda Dani ba"Kaka na Kallonta mama ta ce "Asma'u kina ganin ba matsalar muje"Dan ita Kaka Kyan nasren har tsoratata yake"Murmushin Yake mama tayi ta ce
"Bakomai mama Allahsa a Dace"a ranta Tace bama ta yarda dake ba Dan Ni banason hulda da masu kudi Yanzu "Cikin murna Nasren ta ce "Yawwwa Mama ta yarda Allahsa ta yarda Dani"Kaka na Kurawa nasren Ido ta ce "iNsha Allahu Zama ta yarda dake nakeji a jikina,kinsan sainagama wlh kamar Kuna yanayi da yarinyar itama jawur Take kamar KE dinnan Sak balarabiya Dukda Dana tambayi mamanki ta ce Baku hada Komai da Larabawa ba ko Turawa Amma ita yarinyar Balarabiya ce gaskiya Gaba da baya Uwa da uba haka naji ance".
Nasren na zaro Ido ta ce"Kai ko shiyasa Bata yarda da Mutane,to Daman Akwai Larabawa a kasar Nan?ehmana Amma Basu fiya Zama ba Kije ki kwanta da wuri gobe ki Tashi da wuri"Tana murna ta ce.
"to Kaka " Juyawa tayi Taga ba mama a gurin da saurin ta shiga dakin Zaune ta samtea Tana hawaye Wanda Tana ganinta ta maza ta boye Tana kirkirar murmushi a sanyaye ta Karasa ta ce.
"mama meyasaki Kuka ko bakyason naje wlh Indai kikace bakyaso na hakura"Tana girgiza Mata Kai ta ce"Ina so Mana Nasren Maza kwanta ba Kuka nake ba'"da Addu'ar Allahsa Yarinyar ta yarda da ita bacci ya dauke ta.......โ๏ธ
*ALLAH YA BUD'A MANA BUD'I MAFI ALKHAIRI YAYI MANA ARZIKI NA HALAL YASA MU GINU DA HALAL HAR KARSHEN RAYUWAR MU AMEN*
_*Miss Hajo ce*_๐ค