𝑬𝒑𝒊𝒔𝒐𝒅𝒆 22
_________________"Me ke faruwa haka Alhaji?" cikin ƙunar rai Daddy ya ce"bansaniba!!! Hadiza, kin lalata min yaro da baƙar aƙida dan tsabar rashin mutunci ya kalli tsabar idanuna ya ce kar iyayena su dawo hannuna, to baku isa ba idan ba za ku iya zama da su ba,ki ɗauki ɗanki ku ƙara gaba"
Tunda ya fara magana Mami ke kallonsa cikin mugun mamaki, ganin ai yanzu ya ci a ce, shi ya yi wannan tunanin ba wai Abdul-azeez ba.
Abdul-azeez kuwa a zuciye ya bar ɗaki da sauri, ransa na mugun suya, sau biyu kenan Daddy yana marinsa akan villagers ɗin nan.
Kansa ya jinginar da bango ya na huci, a zuciye ya nufi mirror ya zubar da duk kan abinda ke kai, kwalaben da suke kai na perfumes,da su sure duk suka tarwatse a tsakar ɗakin suka fashe, lotions da cream duk suka zube.
Da sauri ya nufi bed ɗinsa cilli ya shiga yi da pillows da blankets ɗin da ke kai, duk ya har gitsa ɗakin sannan ya durƙushe a ƙasa ya hau hauci inanunsa sun firfito tamkar na mayunwacin Zaki, wutar ƙiyayyar su Inna na ƙara ruruwa a zuciyarsa, wani ihu ya kurma yana toshe kunnunwansa.
Mami ta dinga bin Daddy da kallo ta ce"yanzu akan wannan maganar ka dake shi haka Alhaji, sai ka ce wani ƙaramin yaro saboda Allah" Hadiza get out! i said get out!!" Daddy ya faɗa cikin tsawa.
Fita tayi a zuciye ta nufi ɗakinta.
Sintiri ta shiga yi dan neman mafita, "kai wallahi ba zai yuyu ba, tun yanzu ya fara dukan min yara idan suka zo kuma ai sai korarsu daga gidan nan kenan" a sukwane ta ɗauki phone, ta shiga neman layin Fatu.
Hajja Fatu ta fito daga wanka tana shirin fita zagawa dan yin cinikin magungunanta, ta ji ƙarar wayarta ganin Mami ce, ta saki murmishi dan ta san good news ne akan Daddy.
"Ya kika ga aiki Hajiya?" Hajja Fatu ta faɗa kafin ta yi sallama.
Mami ta ce"dallah malama wana aiki, abun sai ƙara gaba yake yi, Alhaji ya ce" akan waɗan nan ƙauyawan sai dai mu rabu" "Innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun ai kuwa ba mu ga ta zama ba, dole mu koma wajen Malam gobe da nisa, ya zai mana haka kuma, shi fa aikinsa kamar yankan wuƙa ne na yarda shi hundred percent to gaskiya akwai matsala,ina layar nan da ya ba ki?" Mami ta ce"au wallahi shaf na manta bansa a bakina ba na shiga maganar" Hajja Fatu ta ce'kash!!! ashe matsalar da ga gurinki aka samu" nan Mami ta shiga sanar da ita abinda ya faru.
Hajja Fatu ta yi mamakin jin har da marin babban ɗa, ta ce 'kai to kuwa shima Abdul ɗin dole sai anyi masa shiri idan ba haka ba kuwa, duk abinda kika sa Alhaji yayi akan iyayen nan nasa, to ko ya amince na tabbata Abdul-azeez zai dinga ware mana aiki saboda shi kinga zai nuna ƙiyayarsa a fili ne, shi kuma Alhaji ba zai amince ba".
Take kuwa Mami ta amince da laifinta na saka baki a maganar ba tare da ta tauna laya ba, ta ce " yanzu dai kinga ba zai bari in fito a yanzu ba, dan Allah ki biyo ta nan in baki kuɗin mota ki je min akan Abdul ɗin, banaso a sami matsala.
Ya daina nuna ƙiyayyarsa a fili komai muyi musu ta ƙarƙashin ƙasa nake so, ko da sun faɗawa Alhaji kar ya amince ya ɗauka duk rikicin tsufa ne kawai"
Hajja Fatu ta sa dariya tana faɗin"hahhhh kai Hajjaju wallahi kin kawo shawara, tabbas haka za'ayi daman shirin fita nake yi, zan je Kurna gidan wasu customers ɗi na da mukayi zaman daɗi da su, lokacin da aure na na huɗu ya mutu har kuka sukayi, na ce kar su damu har gida zan dinga zuwa kawo musu maganin gyaran aure, to yanzu na fasa zuwa can, ganin na yanzu da zafi-zafi ai akan bigi dutse" Mami ta ce"yauwa nagode sai kin zo ɗin" suka ajiye waya.
Da gudu Siyama ta shigo ɗakin" Mami,Mami,Mami!!! Yaya ya na ta buge-buge a ɗakinsa sai ƙara yake yi" ta faɗa cikin tashin hankali ta na kuka.
Mami ta ce" subhanallahi" suka nufi ɗakin Abdul-azeez da gudu, shiga tayi ta ganshi a ƙasa yana kuka sosai, dan wani irin ƙaiƙayi hannunsa yake yi akan ya rama abinda Daddy yayi masa.
"What's wrong with you my son, stop mentality, be a man mana, nasan abinda Alhaji yayi bai kyauta ba, ni zan san abinyi akan haka ka ji?"
Ta na faɗa tana shafa kansa, wanda ya jinginar da shi a ƙafafunta ya fashe da matsanancin kuka, rarrashinsa take tamkar ƙaramin yaro, tana ƙara nuna masa ba'a bayyana ƙiyayya, Siyama ce ta taka kwalba, ta sa ihu tana faɗin "wayyo ƙafata Mami". Bai san da ita a ɗakin ba, jin ihunta ya sa Abdul ɗagowa Mami ta na matsar da Abdul ta nufi Siyama, ta na faɗin Innalillahi, waya ce ki shigo" kamata tayi ta zaunar da ita, duk ta ruɗe hankalinta a tashe.
Abdul ya tashi ya nufi toilet ruwa ya sakarwa kansa, a jiyar zuciya ya shiga saukewa, sai da ya ji zuciyarsa tayi sanyi ya ƙara sa wanka gaba ɗaya.
Kafin ya fito Mami da Siyama sun bar ɗakin, Aina'u mai aiki ya gani tana gyara wajen, ya san wannan aikin Mami ne.
"Barka da fitowa yallaɓai" yarinyar ta faɗa jikinta na rawa, daga shi sai towel a ƙugu.
Haɗe fuska yayi ya kalli ɓarnar da yayi wa kansa, cikin tsawa ya ce" barnan dan uwarki munafukan banza, na tsani duk wani ɗan ƙauye" ya faɗa yana tashi kamar zai rufeta da duka, da gudu Aina'u ta bar ɗakin, gabanta na faɗuwa tunda take bata taɓa ganin Abdul-azeez a irin wannan yanayin ba dan shi magana ma bata dame shi ba.
Bagana mai girki ce ta gan Haule a tsorace, babar mace ce dan ta jima a gidan bata kwana marayu ne da ita, ta kan zo da safe ta yi aikinta sai dare take tafiya.
Ke mene haka?"
Aina'u ta ce " Yaya ne ya biyo zai dake ni, ina ji wallahi ya fara shaye-shaye Bagana" sai ta zube a wajen ta na tausayin Daddy dan kaf gidan babu wanda suke jin daɗin zama da shi kamar mai gidan.
D sauri Bagana ta rufe mata baki, ta ce "kul kika ƙara munana zato ga mutum babu kyau, ki dai dinga kula kinji, je ki kiyi aikin ki" Aina'u ta ce "sai ya fita zan koma"
Bagana ta ce " daman bai kyautu ku dinga shi ɗakin baligi kamar wannan ba alhalin yana nan, dan dai babu yanda zanyi na hana ne" taua
Bagana aiki ta yi, tana ta tunanin akan Abdul-azeez dan zuciyarta ta gama aminta da shaye-shaye yayi.
Shiryawa yayi dan fita daga gidan, Mami ta na zaune ta zabga tagumi abin duniya ya isheta,dan ko sallama da Daddy ba su yi ba.
Ta na zaune ta kasa yin breaksfast kawai jiran zuwan Hajja Fatu take, "ina zaka je son?"
"wajen Bilal" ya amsa breif,Mami ta ce " haba son ya zaka fita haka ba ka ci komai ba, indai akan abinda Daddy'nku yayi maka ne ka yi haƙuri, anriga da an shiga tsakaninmu, sai dai Allah ya saka mana, bari ina zuwa" tea ta haɗo masa, ta zo da shi, yana gani ya yamutsa fuska ya na faɗin "please Mami i can't drink now" Mami ta nufi bakinsa tana girgiza kai alamar a'a dole ya sha, haka ta dinga ba shi da kanta har ya sha rabi, sanna ya kau da kansa.
Daɗi ta ji ganin ya sha, sannan ta ce" kayi driving mai kyau, take care my son" ya tashi fuskar nan murtuk ya fita.
Gidan dai yau ba'a tashi da farinciki ba, Hajja Fatu ce ta zo, yawan zuwan da take yasa maigadi ya santa, da fara'a aka buɗe mata gate ta shiga, da sauri Mami ta tare ta ta ce "yauwa taso, taso mu je ki tafi kar kiyi rana" har ɗakinta ta kaita, Hajja Fatu ta dinga kallon yanda aka kashe dukiya a ɗakin, hankalinta kawai ya na kan daular da Mami take ciki yake, take hassada ta shiga zuciyarta, ta ji inama ita ce, a wannan daular.
"Hajja Fatu kina jina kuwa?" furgigit ta dawo tunaninta.
Yaƙe tayi ta ce'ina jinki Hajiya ai naji duk abinda kika ce yanzu zan nufi tasha in hau mota,indai ina nan ba zan bari ki wulaƙanta ba" Mami ta ɗauko kuɗi ta bata, ta na faɗin "ki yin sauri, sai kin dawo" Hajja Fatu ta tashi ta tafi tasha ta nufa, tana ta saƙe-saƙe a ranta dan son shiga gidan Mami ne a matsayin matar Alhaji Aminu Dollars ta ji take yi.
Da buƙatu biyu ta nugi garin Ɗanbatta, na farko a yi wa Mami aiki akan dangin mijinta sannan ayi mata aiki akan Daddy, ya aureta karo na biyar...........
MAZOJI
Sosai Inna Gaji da Tabawa suka ƙara sa ido akan AZIZA, suna haɗa kaya suna yin sallama da mutane.
Yanzu su Baba sun daina yi mata wanka, kuma suna ƙoƙari wajen hanata zama haka.
Abun ya fara shiga jikinta.
Tafe take da allo a hannuta ta na tsalle-tsallenta, Amina ƴar gidan Maigari ta gani da markaɗen kayan miya a hannunta, sa'ar AZIZA ce, kamar abin arziki AZIZA ta ce 'lah Amina"Amina ta ce "AZIZAN BABA bala'i daga makaranta kike tab, ni na daina zuwa ta malam Ɗahuru, Islamiyya kawai ta isa" duk bata san kalmar bala'i da ta je fi AZIZA da ta ba, ta ɓata masu hira, ba tai aune ba AZIZA ta shaƙo wuyan Amina, "ni kike ce wa bala'i, yau zakiga bala'i ba ƴar maigari ba, ko Uban Maigari ne sai na suburbuɗaki" ta shiga jijjiga wuyan Amina, ƙafa ta sa ta yi ball da markaɗen Amina, tuni suka hau dambe, Amina na kuka anzakagi Babanta kuma an zubar mata da markaɗe, AZIZA ta san ta kan faɗa, ta taɗe Amina, ta jefar da ita, ta dinga lugudarta.
Yara aka taru ana kallo, Salisu yayan Amina ne ya zo da sauri ya shiga rabasu.
AZIZA tana ta masifar ba zata yarda ba,tunda aka ce mata bala'i, Amina ta na ba za ta yarda ba tunda AZIZA ta ce Uban maigari kuma sai an biyata markaɗenta, tana kuka, Salisu ya ce "ke AZIZA Maigarin kika zaga" cikin rufewar ido da masifa ta ce " uban Maigari na zaga, na rantse bazan yarda ba, tunda ta ce min AZIZA bala'i sai ta ga bala'i" Salisu ya kwaɗa mata mari ya shigarwa ƙanwarsa, aikuwa AZIZA ta fashe da kuka ganin sun tarar mata, Salisu ya ce "dan uwarki ubanmu sa'anki ne da kike zaginsa" saukar dutse ya ji a bakinsa, ta jefe shi ta diba a guje tana kuka, da matsanancin ihu ta shiga gidan, da sauri suka yo kanta suna "ke mene ne?" Baba Tabawa na duba jikinta.
Ba Salisun Maigari ba ne ba, wayyo Allah na shiga uku"gabansu ne ya faɗi, Inna Gaji tace "me yayi mik?"
Baba Tabawa ta na wallahi ba zamu yarda ba, ina mace ina namiji" AZIZA ta na shiɗewa ta ce " shi da Amina ne suka tarar min sukai ta dukana, ji bi jikina ya sa dalbejiya ya dinga dukana kamar Allah ne ya aiko shi" ta zuge zip ta na nuna jiki, babu komai na duka kawai tsantsar sharri ne, idanunsu Baba Tabawa ya gano musu layi-layin gaibu, take suka yarda.
Mai da mata da rigar suka yi, suna faɗin "mu je wajen maigarin dan masifa mu da zamu bar garin ma, nan da jibi, ba za su bari ayi rabuwar arziki ba" su ka sa AZIZA a gaba , aka nufi fadar maigari, kowacce tana huci.
Shiru AZIZA tayi tana tsakiyarsu ko takalmi babu, tana girgiza kai na masifa.
Salisu kuwa kafin ya ankara AZIZA ta gudu, bakinsa ya yi suntum leɓe yayi fushi ya haye, jini ya na zuba, Amina na kuka ta ɗauki bokitin markaɗenta ta nufi gida, faɗar a cike take da manyan unguwa BABA na zaune yana ƙara sanar da su jibi za su tafi, ana ta jajanta tafiyar da zai yi.
Amina ta tawo da kuka , ke yaki nan ke da waye faɗuwa kika yi ne?" Inusa yaron maigari ya faɗa.
Amina ta na kuka ta ce "ba AZIZAN BABA ba ce ta zubar min da markaɗe kuma ta zagi Maigari".
La'ilaha'illahu muhammadurrasulullahi(S.A.W) AZIZAN?" mutanen wajen suka haɗa baki wajen faɗin haka, BABA kuwa jin abinda Amina ta ce ya ce "kai Amina ki ji tsoron Allah, yau she zata iya zagar Maigari, yarinyar da ko unbola(daƙuwa) ba ta iya ba"
Salisu ne ya tawo yara suna biye da shi, ana yi masa sannu.
Maigari ya ce "kai kuma me ne haka?" Salisu ya ce "AZIZAN BABA ce ta jefe ni da dutse"
BABA ya ce "haba ashe tarar mata kukayi zaku kassarata, kai ƙaton gardi da kai me ya kaika faɗa da mace iye salon cin zali, to ta Allah ba ta ku ba"
Maigari ya ce " Inusa a je a tawo min da AZIZAN BABA"
"Angama ranka ya daɗe" ya na shirin ta shi, ya hangosu sun tawo a sukwane.
Ya ce "ga sunan ma ai" duk aka juya aka ganosu ƴar ficiciya a tsakiya.
Suna zuwa suka zauna daga ne sa akan shimfiɗar mai gari " ranka ya daɗe, mun kawo ƙarar ƴaƴanka ne Amina da Salisu, sun rufarwa marainiya da duka"
Jikinta ruɗu-ruɗu da tsimanya sai ka ce sun sami jaka"
BABA ya miƙe da sauri ya na salati ya ce" saboda Allah ko ni ba na dukanta da tsumagiya ku kama ta da bugu, Allah ya sa ma barin garin zamuyi"
Maigari ya ce" AZIZAN BABA ya akayi kuka yi faɗa?" AZIZA ta ce " Amina ce ta ce min AZIZAN BABA bala'i shi ne muka kama faɗa, sai Yayanta ya zo, ya shigar mata suka tararmu suna ta dukana" Maigari ya ce"ya akayi kika zubar min da kayan miya?"AZIZA ta zare ido cikin mamakin nan ta ce"ni yaushe, ko markaɗe banga ni ba,ba ni na zubar mata ba" Salisu ya ce" Baba zaginka tayi fa" AZIZA ta fashe da kuka ta na faɗin" inna kuna gani ana yi min sharri, ban zage shi ba, ban zubar mata da markaɗe ba" Maigari ya ce" Salisu kar ka ƙara shiga faɗan yara, ku wuce ciki, a ƙara gyara wasu kayan miyan akai".
Amina da Salisu suka shige gida, BABA ya ce "ku tashi mu tafi, za mu kai ƙara kotun Allah" Maigari ne ya ciro naira dubu ya ce " BABA ayi haƙuri ga wannan akaita wajen Idi mai chemist"BABA ya ce"a'a bar shi mungode ranka ya daɗe babu komai"
Inna Gaji ta taɓa jikin AZIZA, ta ji ɗan ɗumi, ƙwafa tayi, ta tashi Baba Tabawa ta ce "mun barku lafiya".
BABA tunda ya shiga gida yake jawa Salisu Allah ya isa, AZIZA kuwa ta ƙara narkewa a dole an jigata ta.
Bata warware ba , sai washe gari, ranar da ƴaƴan gidan suka zo dan yin bankwana da su. Gwaggo Aliya da su Maimuna da Gwaggo Zainabu duk anan za su kwana.
Ganin gidan ya cika da jama'a ya sa AZIZA ta wattsake, kayan wasanta da suke a haɗe ta ɗauko ta baza su a ƙofar gida dan ayi wasan bankwana a ƙauyen Mazoji........
𝒁inariya ce✍🏻