𝑬𝒑𝒊𝒔𝒐𝒅𝒆 24
_____________Tamkar waɗan da akayi wa mutuwa haka su Mami sukayi jigum-jigum, Abdul azeez ne ya fara barin wajen dinning ya nufa dan yin breakfast, sannan sauran suka bi shi, Siyama ta yi serving kowa, chips ne sai tea da kuma plaintain, da pepper soup ɗin kayan ciki.
Abdul-azeez ya ja plate ya fara ci, Mami da ta ke soke da magani a ƙugunta, ta janyo plate ɗin pepper soup ɗin Abdul-azeez gabanta ta na faɗin " shi ne ta kwashe hantar a naka, mugani" ta shiga juyawa da spoon, dariya sukayi mata, suna faɗin, "kai Mami kinsan dai dokar ki ko, yanka uku ne ƙa'idarki" Mami ta ce " ni bama ci zanyi ba" sai da ta faki idonsu ta ƙasa ta kwance magani ta zuba ta juya.
Ta tura masa abincisa chips da tea ya ke sha,tana ajiye masa ya koma kan farfesun sa.
Cinye wa yayi yana jin daɗin sa sosai, sai da suka yi nak, sannan Siyama ta ce"yau akwai manyan baki, bari in fara shiri tun yanzu" ta miƙe da niyar tashi, Mami ta zaunar da ita ta na faɗin "shirin uban me za kiyi, Islamiyya ma zaku tafi dan wallahi ba za ku zauna jiran zuwansu ba"Pretty ta yi rau-rau da ido, jin za'a turasu islamiyya.
Abdul-azeez bai ce komai ba ya tashi dan wani bacci yake ji. Fita zai yi amma jikinsa duk ya mutu dole ya koma ɗakinsa, gado ya faɗa da takalmi ya kwanta bacci mai nauyi ne ya ɗauke shi.
"Assalamu alaikum" sallamar mahaifiyar Mami su ka ji, da sauri Mami ta amsa ta na mamakin zuwan Hajiyan nasu"wa'alekumussalam Hajiya sannu da zuwa" Yauwa Hadiza" Hajiya ta faɗa ta na ƙarasa shiga parlour'n Hisham ne ya shigo shi ma bayan ya gama parking mota.
"Oyoyo Hajiya, oyoyo uncle Hisham"pretty ta faɗa tana faɗawa jikin Hajiya da murna, Hisham ya zauna ya na faɗin "aunty Hadiza ina kwana ya gida" Mami ta amsa tana murnar ganinsu unexpected.
Aina'u ce ta shigo da sauri hannunta ɗauke da ruwa da drinks har da fruits, ta ajiye tana gaishe su.Cikin mutuntawa Hajiya ta amsa hakama Hisham ta shi tayi dan komawa, Mami ta ce"ki ce da Bagana a ɗorawa Hajiya dashishi da miyar tankwa" Hajiya ta ce"a'a ba sai sunyi mana komai ba, duk abinda akayi wa baƙi zamu ci"
Mami ta ce " wana baƙin zamuyi?" Hisham ya ce " ba yau iyayen Baban Abdul zasu dawo ba" cikin mamaki Mami ta ce" waye ya sanar da ku" Hajiya ta ce" ai shi ma ɗan gida ne, da kansa ya je ya faɗamin shiyasa na zo tararsu" takaici ne ya kama Mami ta yi shiru.
Ganin Aina'u a tsaye ta daka mata tsaya, wuce ki tafi a nan shashasha" da sauri Aina'u ta ƙara gaba.
Hisham ya ɗauki ruwa ya buɗe ya sha, sannan ya ce"ina su Munnir ne?" Siyama ta ce" ya bi Daddy Mazoji"
Abdul-azeez fa?" Hajiya ta ƙara tambaya, Mami ta ce " ya fita amma yanzu zai dawo"
Hajiya ta ce" Siyama ku shige ciki zamuyi magana" to suka amsa suna wuce wa sama ita da pretty, Hajiya ta ce" Hadiza ina so in ƙara yi miki nasiha akan iyayen mijinki, banaso su zarge ki ko su ga ɗansu bai yi sa'ar mata ba ni na haifeki nafi kowa sanin halinki, Hadiza ina so ki yi wa iyayen mijinki biyayya, kinga da ba'a kusa kuke ba babu wanda ya san halin kowa a cikinku.
Dan Allah ki riƙe su bisa amana ki ɗauke su tamkar su suka haife ki"
Mami ta ce "to Hajiya in sha Allahu zan yi duk abinda kika ce" Allah yayi miki albarka, yanzu ki shiga kitchen ki taya masu aiki asamu a yi musu komai akan lokaci" Mami ta ce "ni da kaina zan shiga kitchen?" Hajiya ta ce" to ke ɗin wace ce, Hadiza ranki zai mugun ɓaci fa"
Ta shi Mami tayi ta na ba da haƙuri ta nufi ɓangaren kitchen.
Kamar tayi kuka, wayarta ta fara dubawa dan kiran daddy ko sun tawo.
Alokacin ba su taso ba, ya sanar da ita inda yake.
Ba dan ta so ba,ta bawa Bagana da Aina'u umarni a yi abinci mai kyau dan ganin Hajiya ta zo gidan.
Cikin lokaci kaɗan suka gama aikin, Mami ta koma tarar da Hajiya da Hisham su na hira, ganin ta fito, Hajiya ta ji daɗi, ta ce"angama Hajiya bari in je in yi wanka" Hajiya ta ce"nima sallah zanyi, Hisham ma ya tashi ya nufi masallaci, Mami na hawa sama ta hau su Siyama da faɗan ba su shirya ba har biyu saura, Uniform su ka sa, kowacce ta sauko.
Hajiya da ta idar da sallah ta ga sun sauko.
Hajiya ta ce" ba za ku jira kakannin ku su zo ba, haba Siyama" da sauri pretty ta ce "ba Mami ce ta ce ba za mu zauna ba sai munje makaranta ba" Hajiya ta ce" ku koma ku shirya kuma babu inda za ku je" da murna suka juya, kowacce ta sa kayanta masu kyau.
Su ka dawo wajen Hajiya, Mami ma tsaf ta fito cikin shigar lace pink colour tayi kyau sosai.
Ganinsu haka ya sa Mami ta ce"makarantar kenan?" Hajiya ta ce" ni na ce su zauna su tari kakanninsu"ba dan Mami ta so ba tayi shiru.
Abdul-azeez kuwa sai da yayi baccin awa uku sannan ya farka, kamar anyi masa mugun duka haka jikinsa yayi, toilet ya shiga yi wanka sannan yayi sallah azahar.
Ƙasa ya sauko, ganin Hajiya a zaune ya saki murmushi yana faɗin "ƴar tsohuwata ke ce da kanki, ko dai mafarki nake yi" Hajiya ta ce " bansaniba watukun kai ma ba za ka iya kira na ka sanar da ni yau su Alhaji za su dawo ba ko"
Abdul-azeez ya ce" Daddy ai tun shekaran jiya ya dawo, two days kawai yayi a Osun state" Hajiya ta ce"kai dallah shashasha, mutanen Mazoji nake nufi" sai Abdul- azeez ya yi tsaki ƙasa-ƙasa ya bar maganar dan har cikin ransa baya son mutanen nan, yanzu abun har ya fi da, sunan garin ma da Hajiya ta faɗa, ji yayi tankar ta watsa masa ruwan dalma a zuciya.
Ana ta jiran ganin zuwan su Daddy, har akayi la'asar, basu iso ba, Lubuna ƙanwar Mami ce ta kira Hajiya, nan take ji tana gidan Hadiza taran surukanta za su dawo gari.
Lubuna ta yi murna, tana faɗin ita ma tana nan tafe yi musu sannu da zuwa, kamar Mami ta zageta haka ta ji, ganin Hajiya ya sa ta ce "Allah ya kawo ki"
Shigowar Motar Daddy da horn ɗinsa ne ya sa suka san Ƴan Mazoji sun iso Kano.
AZIZAN BABA, da tayi amai ya fi goma kafin azo, duk ta ɓata jikinta.
BABA ne ya fito yana faɗin "Alhamdulilah ma sha Allah mun sauka lafiya" Tabawa da Inna Gaji sai kalle-kalle su ke dan rabon da su zo gidan har sun manta.
Daddy ya kamo hannun AZIZA ya na faɗin "sannu mai aman mota"
Sun kuyar da kai tayi tana murmushi.
Mai gadi da ma'aikatan suka zo suna ɗiban gaisuwa BABA, sai washe baki yake, ya na faɗin "kai Aminu wannan gida uwa a aljanna, kai ai sai mutum ya ɗauka ya mutu ne alkur'an ya samu rahama" Munnir kuwa ya ƙyalƙyale da dariya, masu aiki kowa sai ƙara sun kuyar da kai suke kar suyi ɓaranɓatama.
Daddy yayi murmushi ya ce" mu je BABA"
Sandarsa ya dogara ya na saɓa babbar riga suka nufi ciki.
Yana ɗaga sanda tana ƙara dif-dif.
Baba Tabawa ta na riƙe da ledar kayan wasan AZIZA.
Masu aiki suna riƙe da kayansu suka biyo su dan ajiyewa, "Assalamu alaikum" Daddy ya fara sallama , sannan BABA ma ya yi, Wa'alekumussalam sannunku da zuwa, Alhaji sannunku da zuwa" Hajiya ta tashi tana ta rawar jiki. Mami da idanunta ya ciko da ƙwallar baƙin ciki, aikin gama ya riga ya gama.
Abdul-azeez ko kallonsu bai yi ba, kamar ya kashe su yake ji, babu wanda ma ya kula da shi a parlour'n.
AZIZAN BABA ta na maƙale jikin Baba Tabawa tana kallon gidan, Mami ce ta galla mata harara, AZIZA da tasan ba ƙaunar su take ba ta, ta ɗauke kanta.
Baba Tabawa ta ce "ina ne bayi?"
Mami ta ce to za'a fara ƙazanta min gida mtsw, duk a ranta ta faɗi hakan.
Daddy ne ya ce "ga shi can, Siyama nuna mata"
Baba Tabawa ta ce" ta shi ki sauya kayan" tana taɓa AZIZA, Munnir ya ce" me aman mota hahh"
Hajiya ta ce"ayyah amai tayi a she, oh sai ka ce ƙanwata Amina tana ƙarama ita ma haka take da aman mota" Siyama ta ce" kai Hajiyan Pakistan ɗin?" Hajiya tayi murmushi ta ce " ita ɗin Maman Sahil da Sahal ba"
Mami ta ji mugun haushin wannan labari da Hajiya ta bayar, gani take ta rage musu ƙima, bata taɓa nuna tasan hanyar ƙauye ba.
Anan sukayi sallah, aka zauna a dinning cin abinci, BABA ya ga ana jan yo chairs ana zama.
Inna Gaji ta taɓe baki ganin Abdul-azeez a kwance ya rufe fuskarsa da p-cap.
Bacci ne ya ɗauke shi a hakan wanda bai san lokacin da yayi ba.
Mami ce ta ce " Inna ku taso mana"BABA ya ce"a'a mu kam dai akai mu masaukin mu do Allah"dan AZIZA ce ta raɗa masa hakan, dan mutanen gidan ba su ƙarɓe su yanda ya kamata ba.
Mami ta taɓe baki ta ce "bari a kira shi" tana duba three seater ta ga Abdul,"a'a son, my son lafiya kake kuwa" BABA ya ce" au Abdul-azeez ɗin ne a nan amma shi ne ko ya zo ya gaishe mu"
Mami ta ɓata rai ta ce" ba shi da lafiya ne BABA,bai san ma kun zo ba"
Cikin tausayawa su Inna suka ce " me ya same shi?"
Banza tayi musu, Abdul-azeez ya tashi ya na ya mutsa fuska.
BABA ya ce" gawa ta ƙi rami sannu"
Daurewa Abdul-azeez ya yi ya yi musu sannu da zuwa, sannan ya nufi sama ransa a ɓace, AZIZAN BABA ta kalle shi.
Ta taɓe baki.
Abinci Mami ta ɗibar masa ta nufi sama dan bawa ɗan lelenta, yana wanka ta shigo, ajiyewa tayi ta sa maganinta karo na biyu sannan ta nufi kiran Daddy dan ya zo, ya fitar mata da su BABA, ganin Hajiyanta a wajen ne ma ya sa bata jona borner ba, a ce warta parlour'n warin tsoffi ya ke mata.
Clashing sukayi ta ce" sun ƙi zamaaɗ su ci abinci wai a kaisu masauki"Daddy ya yi murmushi ya ce" to sai a kai musu can ai, mu je a kai su su huta"Mami ta ce " bari naga jikin son, ba shi da lafiya" Daddy ya yi gaba yana faɗin "okay"ko kallonta bai yi ba.
Da harara ta bi shi ta nufi ɗakin Abdul-azeez, yana kwance ya ƙurawa silim ido, duk jinsa ya ke a hargitse, Mami ta taɓa shi ,tana faɗin son meyake damunka?
A hankali ya ɗago ya na faɗin...........
Zinariya ce✍🏻