SANADIN CACA

...24...

by @sadisakhna

*SANADIN CACA*



Mallakar SADI-SAKHNA



PROFICIENT WRITER ASSOCIATION




*USERNAMES*

FACEBOOK PAGE:Sadisakhna

WATTPAD:@SAKHNA03

AREWABOOKS:@sadeesakhna

PHONE NO:***

________________________________

*Book 1*

Chp[23]




[Sumaimah a mahangar gani]



Shinkafa da miyah nayi niyyar yi,saboda nayi amfani da naman da goje yasaka aka kawo,tun safe yaron da Tunga ya hadani dashi yazo yayimin siyayyar duk abinda nakeso..

Sai wajen shaɗaya kafin na ɗora abincin,wanke wankenmu dan kaɗan ne,tun safe na wanke komai na kwanukan da muka bata,shara kuwa in na share ƙofar inna shikenan saita goje.

Bayan na gama shuru nayi ina kallon abincin dana zuba a cikin kulolin,na tafi tunani naji muryar inna a sama na.

"Wani abune ya faru naga kinyi shuru uhm"

Ashe tana kallon tun ɗazu,so nake da ya fita daga ƙofar tasa saina kai abincin,amma yaƙi fita gashi azahar tana shirin,banaso najene ya gwaleni ya koroni,korar dayayimin ranar danazo gidan har yanzu bata bar cikin kaina ba ina tunowa.

"Inna uhm kina ganin zai yarda yaci kuwa? Baice mu dinga yi dashi ba abincin?"

Dariyar dattawa tayi min kafin tace.

"Karki damu Sumaimah Inshaallah zai karba,kuma abincin yayi daɗi sosai da sosai,Ba kowane zai kauda kai baiciba,musamman ma kinsan maza da son abinci kuwa?? Idan kinga yafara ci saikiyi masa maganar komawarki islamiyya da kika fadamin kinji,amma fah kada ki fada sai kinga yana cikin yanayi mai kyau,kin gane koh?"

Ɗaga kai nayi amma kuma saina tuna naga jiya tace zata fadamasa nakoma islamiyyar meyasa ta sanja ra'ayi.

"Amma inna kince fah zakiyi masa maganar karatunnawa?"

"Uhm uhm da nayi niyyar yimasa maganar,amma inaga kiyi masa maganar da kanki zaifi,ta hakane zaku samu fahimta da kusanci a tsakaninku,sannan in kina tambayarsa da kanki hakan zaisaka ya ƙara gane cewa ke ɗin haƙƙinsa ce kuma kina ƙarƙashinsa"

Maganar da tayin ya gamsar dani sosai,yanda take yimin wasu abubuwan har mantawa nake da itah surukata ce.

Ɗaukar abincin nayi akan tire cikin sanyin jiki na nufi hanyar ƙofar tasa. Tun dawowar innan bamu tab'a yin abinci dashi ba,saboda baya zama a gidan sam,ko mai yakeyi oho. Jiyane dawowar sa yasaka yaro yashigo mana da nama kaman ranar farko.

Na buɗe baki zanyi sallama sai kuma naji yana wata magana...

.......Me kake nufi ne wai,jiya fah na dawo yace na fasa fita aikin,kuma yanzu kace wai na sake dawowa,hakan bazai yiyu ba sam.akwai wani aikin danake so nayi,ba iya waccanne aikina ba. Idan yin fashin ko satar daɗine shiya je yayi mana,in kuɗinkune saina dawo muku da kayanku yana nan ban taba ba.......

Sata fashi..nashiga uku dama fashi yake zuwa idan yayi wannan tafiyar...yaushe yafara fashi?.

"Me kikeyi a tsaye a nan,ko bayan rashin kunyar harda lab'e kika fara yimin"

Saurin tura ƙyauren nayi na shiga ɗakin ina rarraba ido.

A tsakiyar ɗakin na tsugunna tareda ajiye tiren kayan abincin. Da kallo ya bini yana zaune daga shi sai singlet ruwan toka,da kuma baƙin gajeren wando. Ta gefen idona na kulada shigar da take jikinsa,hakanne yasa naƙi ɗaga ido na,fatar bakina rawa take amma kuma na kasa cewa komai.

Matsowa yayi ya dawo bakin katifar yana ƙareni da kallo.

"Ɗago fuskarki ki kalleni"

Bin umarninsa nayi ta hanyar ɗago idanuwannawa,akan ginannen ƙirjinsa na ajiye idanuwana,ban ƙarisa izuwa fuskarsa ba,magana naji yafarayi,saidai ba irin muryar danaji yana yiwa mutumin dayake waya dashi bace.

"Me kikaji ina faɗa a waya?"

"Uhm....uhm zancen fashi kuke da sata"

"Dakyau dama na tsani ayimin ƙarya,to kada ki kuskura inna taji wannan zancen"

"Tohh bazata jiba"

Ɗaga kai yayi alamar ya gamsu da abinda nace. Shuru ne ya gibta,ganin baice komai ba yasa na fara bude kular abincin,a raina ina cewa karka hanani karka ce ka ƙoshi.

Ohh Allah ya amshi Addu'a ta kuwa harna gama zubawa baice komai ba,amma inajin idanuwansa a kaina. Cokali na saka a kan plate ɗin na miƙa masa. Kar'ba yayi ba musu yafara garwaya gabansa yana kaiwa baki. 

Ruwa na zuba masa a kofin jug ɗin danazo dashi na sake mika masa gabansa,hannunsa ya kawo zai ɗauka nikuma ban zare hannuna,hannunmu ne ya haɗu dana juna,da sauri na zare nawa ina sake sunkuyar dakai.

"Akwai magana a bakinki meyasa bazaki furta ba,kina bani mamaki,har yanzu na kasa gane kanki,lokacin da banyimiki komai ba kina tsorona,da nayi niyyar yimiki kuma sai kika maida martani"

"Uhm kayi haƙuri a loka......"

"Ahah bance saikin bani dalilinki nayin hakan ba,me yake tafe dake yanzun?"

Dama yana magana haka ta lumana irinna sauran mutane? Tun lokacin dana ke ganinsa a gari kafin zanen ƙaddarata ya ɗinke da nasa ,nayi zaton idan an zo kusadashi kashe mutane yake. Tsaida tunanin danake nayi tareda sanar masa buƙata tah.

"Uhm dama inason komawa makarantar islamiyyah ne,amma ta matan aure"

"Tsawon sanda nake cin karo dake a lokacin baya da kayan makaranta nake ganinki kafin kifara talle,har yanzu bakiyi ya isheki ba?"

Da yayi maganar bansan lokacin dana ɗaga ido na kalleshi ba,dama yasanni yana kallona.

Kaman yagane abinda nake saƙawa a raina,murmushi yayi amma ba mai tsayi ba yace.

"Ohh a zatonki bana kulada mutane ne idan suka ga zamu haɗa hanya suka juya da gudu,ina kulada ke duk sanda muka haɗa ido komawa kike da gudu kibi da wata hanyar,abin yana bani dariya da kuma nishaɗi idan naga mutane suna gudu"

"Babu ɗaɗi da kuma nishaɗi ace kana ɗan adam ƴan adam ƴan uwanka suna gudunka,alamar maƙiyine a gujeshi,kana kuma alamar masoyine a kusanceshi a duk inda ya gifta"

Wuuff nasaka hannuna na rufe bakina ina jijjiga kai,Sumaimah kinga ta kanki meya kaiki fadamasa waɗannan kalaman.

Runtse idona nayi,na ɗanyi wani lokaci,jin bai dakamin tsawa ba ko mari yasa na buɗe idona,murmushi naga yanayimin....wannan bawan Allah menene yashiga jikinsa.

"Yanzu ma kin sake bani mamaki,kece mutum ta farko data fara faɗamin irin waɗannan kalaman bayan inna,zuciyata ta kasu kashi biyu a halin yanzu.....ki tattare kayannan maza ki fitah,batun makarantar kuma zan duba nagani"

Tashi nayi da hanzarina ba bata lokaci na tattare kayan dana shigo na dasu zan fitah,har nazo bakin ƙofa naji muryarsa,inba nasan muryarsa ba bazan ce bane.

"Abincinki yayi daɗi,nagode"

Ehh juyawa nayi duk da yacemin na tafin,kallonsa nayi ya saka hannayensa akan kunnuwansa,idanuwansa kuma a runtse kaman yana cikin ciwo,meyasa lokaci ɗaya yakoma haka saikace bashi ba?

Nidai fitah nayi daga ɗakin zuciyata cikeda mamakin ganin sabbin halayen gojen.


[Goje a mahangar gani]



Ina cikin wayar naji alamar motsin mutum a bakin ƙofah,nasan babu wanda a yanzu yake zuwa ƙofar tawa sai Sumaimah,dan haka itace a wajen.

Jikina ne yabani cewa taji abinda na faɗa,aikuwa dana tambayeta hakanne,jinta bai dameni ba,kawai inna ce bana so taji,shiyasa nayi mata gargaɗi.

Lokacin da take zubamin abincin haka kawai na tsinci kaina wajen zuba mata ido,gashi dai bata ɗaya daga cikin yarana,amma kallonta a tsugunne tana zubamin abincin saina jini tamkar wani sarki,gashi cikin nutsuwa take zubawa duk da yanda jikinta yake rawa.

Bayan ta miƙomin loma na ɗiba nasaka a bakina,ba laifi yayi daɗi sosai,ba kaman wanda ake na siyarwa ba.

Ganin ta zauna tayi shuru tana motsi da baki yasa nagane akwai abinda takeson tambaya,domin a dan zaman danayi da itah wata ɗaya da satuka na gane hakan.

Islamiyyah takeson komawa itakuma? Toh.....ban wani mamaki ba,dan dama tun sanda nake ganinta akan hanyar zuwa makaranta muke cin karo. 

Bayan mun ɗanyi magana,amsar data bani saina tsinci wani bangare na zuciya ta yayi na'am da amsar,amma mafi akasarin raina kuma so yake na tsinketa da mari saboda maganar da tayimin. Karo na farko a rayuwata kenan bayan inna na ƙi amincewa da muryar da take bani umarni. Sanadiyyar hakan saina farajin ciwon kaina yana barazanar zuwa da ƙarfi,hakanne yasa nace tattara kayan abincin ta tafi. Harta zo fitah bakina yasamu faɗamta cewa Nagode....wai mai yake damuna ne,nafi kowa sanin kaina idan na farantawa wasu ni saina baƙantawa kaina,ko kayan abinci dana kawowa su inna sai nake ganina kaman baniba.

Farkawa nayi naga duhu yafara ta windown ɗakinnawa,kutt kaddai bacci nayi kai har magriba ta kusa.

Tashi nayi daga kan katifar na fito,alwala na gurgurza na fice waje.

Masallaci na shiga nayi azahar la'asar da kuma magriba,daga nan na wuce duk inda ta garamin.

Lokacin dana dawo da daddare na samu Sumaimah ta ajiyemin abincin dare,banciba na sake fita,saboda ban saba da cin abinci a gidaba,dan nayi full tank a waje..

Da safe soyayyar doyah ta kawomin a ƙaramin kwanon jiya,wannan karon bata nuna alamar tsoro kaman jiya ba,kayan dana saka na zuba a gefen ɗakin ta tattara tafita dasu tareda abincin daren data kawo banci ba.

Babu wanda yayiwa kowa a magana a tsakanin nida itah bayan gaisuwar datayimin ta safe na amsa.

Kai tsaye makarantar garin na tafi ALBAYAN,Babbar makaranta ce sosai,anayin islamiyyah da kuma boko,sannan ba iya ta yara bace hadda manya. Nasan hakanne saboda yanda nakejin labarinta,danni bansan wacce waina ake toyawa ba a cikinta.

Makarantar ana faɗan iliminta da kuma tsadarta,amma ni ba wannan ne damuwata ba,ita kaɗai nasani manya suna zuwa shiyasa na je naji mai yake wakana.

Tun daga shigata makarantar idanuwan mutane suke dawo kaina,banga lafinsu ba wanene zayyi tsammanin ganin goje a makaranta.

Tun kafin na isa office ɗin shugaban makarantar labari ya isa gareshi,fitowa yayi bakin office ɗin yana jirana har na ƙariso.

Wuceshi nayi na shiga office ɗin na zauna,biyoni yayi fuskarsa a razane.

"Goje mai kuma yakawoka makarantar mu,wani abu akayi maka wanda ya shafemu?"

Jijjiga kai nayi tareda sosai ƙeyata da makullin mashin ɗina,karewa malaman da suka shigo office ɗin nayi da kallo,wai sunace wani tawayen nazo yimusu?

Hhhhh harsun bani dariya ma,nuna ma principle ɗin kujera nayi ya zauna.

"Zauna mana shugaban makaranta,niba tawayene ya kawoni makarantar ka ba,koka ganni da sanda kai?.

Matata nazo sakawa a makarantar nan,ayimin bayanin tsarin naji"

Bashi kaɗai ba ni kaina nayi mamaki dana faɗi abinda yakawonin.

A diririce yafara bani bayanin makarantar,na uniform ɗinsu bangaren islamiyya da kuma na boko. Dubu goma a shekara islamiyya,boko kuma dubu ishirin.

Damin kuɗi na cire a jakar hannuna bansan nawa bane na ajiyemasa.

"Gashinan kudin makarantar ta harta gama,ku ɗinka mata uniform sannan intazo tayi muku bayanin ajin da take so tashiga. Inda sanji ku riƙe,in kuma basu isaba ku saka sorry. Nizan tafi,gobe ku tabbatar komai da take buƙata na karatun tanadeshi,idan naji labarin ba'a bata wani abuba saina babbake makarantar nan"

"Bakomai bakomai goje zata iya zuwa sai muji inda ta tsayah,komai daya kamata duk za'ayi mata,inkana so ma har malama za'a ɗauka mai nuna mata yanda zatayi. Batun ƙudi kuwa sunyi yawa ma a yanda ake buƙata."

"Wannan kuma ku ta shafah,in nayi karo da wani kuskure ko kaɗanne ta ƙaremuku,saina tashi wajennan dukka"

"Ahh goje ga wannan takardar ka kaimata ta cika,ta nanne zamu san a wanne mataki take,ta haka ne zamu san wanne abubuwan take buƙata na karatun"

Da bazan karbi takardun ba,nizasu aika dan sun rainani,saikuma dai wata zuciyar tace na karba ɗin.

Dana fita daga makarantar ba gida na tafiba,wani meeting na tafi wanda zamuyi na siyasa.

Sai wajen azahar kafin na koma gidan,kicibiss mukayi da itah zata fito daga ɗakina takaimin abinci.

Har ya wuceni zata tafi na tsaida ita.

"Kee"

"Na'am"

Tafaɗa tareda dawowa tana sunkuyar dakai,takardun na miƙa mata batareda nace komai ba.

Ganin ta tsaya tana duddubawa yasa nace.

"Takardar makarantar kice,ki duba ki ciccika duk abinda kikaga kina buƙata,nabiya kuɗin komai harki gama,dan haka inkinje zasu baki gobe"

Ƙiƙƙifta ido naga tanayi,hawayene yake zuba daga idonnata,kaddai bata son wannan makarantar kai,naji ance kowa so yake ace a itah yake karatu.

Tsugunnawa tayi takama ƙafafuna ta rike.

"Nagode nagode nagode mijina,kayimin abinda bazan taba mantawa ba a rayuwata,bantaba zaton zaka saurari magana taba bare harkayimin irin wannan abin,daga yanzu zanyi komai domin faranta maka,wannan alƙawarine daga gareni. Bari naje na faɗawa inna"

Tashi tayi da gudu tana share hawayen tayi hanyar ƙofar innan dagudu.

Jijjiga kaina nayi tareda ɗaga kafaɗa,wannan lafiyarta ƙalau kuwa??.......

  


Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.


3131951977

Auwal Sadiya

First bank


Ko katin mtn ta nan

***


VTU ta nan

2347068390570


Shaida kuma ta nan

***


Ƴan niger ku tuntubi wanann number.

+227 97 21 16 15

----------------------------------------------------


Sadi-sakhan ceh

***

Share please