6
_*🌻ABBA NE 🌻*_
Hakkin Mallakar
_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚_
_*Littafin na kud'i ne only N300 ne domin karin bayani ku tuntubeni ta WhatsApp number na👉🏻+966599791573*_
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣6️⃣
Kai Doctor dakata! Ta fad'a da karfi" Galala Doctor ya saki baki yana kallon Ashma data zaro masa dara-daran idanun ta wanda yasa shi jin tsoron Yarinyar. Murmishi Khalil yayi ya shafa kanta yace" My Princess d'ina meyasa kika ce ya dakata? allura fa za'a min na samu lafiya." Ko baki so muje gida ne? Ya fad'a yana daura ta akan cinyarshi. Sake had'e rai Ashma tayi sai kuma ta juyo ta kalli Doctor cikin zazzakar muryarta tace" Ba kai bane ka duba Abbana da farko dan haka baza ka tab'a min jiki Abbana ba, ni banga kana kama da Doctor's ma" Waro idanu Yayi jin abinda take fad'a a ranshi yace" Kai Yarinyar nan ko dai aljannu gare ta, Numfashi yaja yace" To ai shi wancen d'in aiki yake shiyasa ni zan mishi allurar ki bari a mishi ko kun koma gida, ko baki so kiga Abban naki ya samu lafiya? Wani banza kallo ta watsa mishi sai kuma ta turo baki tace' Abbana ya samu lafiya kuma sai na kashe duk wanda yake son ganin bayanshi, ko waye mutum idan na gano shi ni da kaina zan masa dukan tsiya ko Abba? Ta fad'a tana kallon Khalil daya tsura mata idanu yana mamakin abinda take fad'a.. Abdul yayi murmishi yana jinjina kai dan shima bai yarda da wannan Doctor d'in ba, cikin bada Umarni Abdul yace" Am nace ba Doctor zaka iya tafiya idan Doctor Ma'aruf ya gama sai yazo ya duba shi, tinda tace baza ka duba mata Uba ba" Ya fad'a yana tsare shi da idanu.. Ai tuni yasha jinin jikinshi sumakai ya fita daga d'akin" Khalil yace" Kefa baki ji ko? Yanzu gashi Doctor ya tafi. A'a Abba ni kawai bana so ya maka allura ne mugu ne shi kana ganinshi bashi da imani, shiyasa nace bazai ma ba. Kallon ta yake Mamy data zuba musu idanu tace Kaji Ja'irar Yarinya ko, ke duka nawa kike da har kike gane mugu da wanda ba mugu ba? Ashma ta koma jikin Khalil ta kwanta abunta ta sanya yatsun ta guda biyu na tsakiya ta shiga tsotso har da lumshe idanu. Khalil ya mik'e tare da ita a jikinshi ya sauko daga kan gadon, sauke ta yayi yana jan kunnen ta yace" Ke dole sai a jikina zaki zauna ne? Indai ina guri to nine abun zaman ki zan fa zaneki Princess. Kwabe fuska tayi ta kalli Abdul tana fad'in" Papi kaga Abba ko wai zai zaneni. Kama hannun ta yayi yace" Ki rabu dashi yama isa ya zane ki muje mu kira Doctor sai mu tafi gida. Harara ta aikawa Khalil tace" Abba yau fushi nake da kai karka min magana kaji! Shan kunu yayi shima yace Nima ba ruwana dake yau" Fita sukayi basu jima ba suka dawo tare da Doctor Ma'aruf, cikin jin dad'i yace" Kai Masha Allah jiki yayi kyau yanzu ya kake jin cikin naka? Khalil ya d'an yamutsa fuska yace" Ba komai rashin kwarin jiki kawai nakeji shima an jima zan warware.. Ashma ta tsaya a gaban Doctor Ma'aruf yatsunta a baki tace" Yanzu wani yazo zai wa Abbana Allura na hana! Murmishi yayi yace wani kuma yaushe to? Yatsu biyu ta d'aga tace" Minti biyu da tafiyarshi ka ganshi kuwa Kamar irin horon nan na television, ni kuma naji bai yarda dashi ba haka kawai yazo yace zaiyi wa Abbana Allura, kila ma mugu ne ko? Ta fad'a tana tsareshi da kallo.. Mamaki sosai Doctor Ma'aruf yayi shi dai baice kowa yazo ya duba Khaba" Kallon Ashma yayi yace To shikenan tinda ya tafi" Abdul na nazarin Doctor d'in, a ranshi yace zan dawo ko gobe" Gyaran murya yayi yace" Yauwa wanda aka kawo d'in nan ya farfado ne? Doctor Ma'aruf yace ya farfado amma bacci yake gaskiya. Abdul yace OK a bashi tsaro mai kyau kada ka bari kowa ya shiga dakin nan" To Doctor yace san nan ya rubuta musu takardar sallama, Godiya suka mishi suka fito. Koda suak fito harabar Asibitin sai da Abdul ya gargadi Sojojin da su Kula da kyau, suka amsa da to san nan ya shiga motar suka tafi gida... Hisham zaune a Office d'in shi yayi shuru kamar mai tunani, ji yayi an shigo amma bai d'ago ba saboda yasan Mutum daya ne zai mishi haka zuwa biyu, daga Rufaida sai kuma Aminin sa Doctor Kalifa" Ji yayi an dafashi a hankali ya d'ago, cikin kidima yake kallon ta bakinshi na rawa yace" K.. Ke waye ya baki izinin shigo min Office ?kuma Uban waye yace kisa wannan kazamin hannun naki ki tab'a min jiki? Murmishi tayi cikin iya barikin ta ta zauna a kan kujera tana wani kwarkwasa kamar wata Agwagwa" Cikin bacin rai yake kallon ta yace" Fitar min a Office yanzun nan ko kuma kiga abinda zan miki! Ya fada har da buga Table d'in gabanshi.. Tsoro ne ya rufe ta amma ta matse dan yau so take Hisham ya yarje mata ta zama Budurwarshi" cikin iya takun ta tace" Haba Doctor Hisham ban tab'a tunanin wulakanci daga gareka ba, nifa pantie d'in ka ce,ko ka kanta ranar Friday nazo kace ka tashi shine nace zan dawo, to bansamu dama ba sai yau shine kuma za kake min k'orar kare.. inaso ka duba ni bani da lafiya Zuciyata ke ciwo ko bacci bana iyawa shine na samu labarin ka ance Duk garin Abuja kai kayi fice a wannan fannin" Ta fad'a tana mik'ewa tsaye ta dawo inda yake tsaye shima.. jiyowa yayi zaiyi magana sai ta fashe da kuka tana fad'awa jikinshi ta k'ank'ame shi" Kwalalo idanu waje Hisham yayi cikin tsabar tashin hankali yace" Ke sakeni bana son hauka fa, ki sakeni anya ma kina da tarbiya nifa Namiji ne ba Mace ba.. Cikin kukan makirci Khairat tace" Kayi hak'uri na kasa jurewa ne na jima ina sonka da k'aunar ka, amma na kasa samun damar da zan fad'a maka ina sonka" Don Allah kada kace baka sona Doctor zan zauna dakai a ko wani irin yanayi kaji, kaji tausayi na kada ka wofantar da K'aunata a gareka please" Ta fad'a tana sake komawa jikin shi.. wata uwar zufa ce ta zazzafowa Hisham tuni jikinshi ya dauki rawa shi bai tab'a had'a jiki da Mace ba da sunan runguma in ba Rufaida da Ammi ba, Kasa tabuka komai yayi sai kawai ya ringa kallon ta kamar wani sakarai.. Ita kuwa Khairat jin bai hana ta rungume shi ba ,tayi wani murmishi tace" Hmm dani kake maganar zaka san wacece Khairat.. Da sauri Hisham ya ture ta daga jikin shi yana huci, yace" Dan kina sona kuma sai akace miki ki had'a jiki dani ko? Hakan ya nuna min tabbas baki da tarbiya, inda kina da ita baza ki kalli kwayar idanu na ba yayinda zaki fad'a min kina sona.. ki bace min da gani ko yanzu na kakkayaki sha-sha-sha kawai, ni zaki kalla kice kina so? Khairat ta sake fashewa da kuka tace" Haba Hisham yanzu dan nace ina sonka shine kake korata? Ina lefin wanda yace yana sonka? Wallahi ko me zakayi ina sonka kuma saika aureni dole ma' Ta fada tana wucewa daga Office d'in. .
Dafe kai Hisham yayi yana fad'in" Astagafurullah ya rabbi, A'uzu billahi minan sheďani rajim meye yake shirin faruwa dani, wai ina nake kallo har wata Mace ta tab'a min jiki? Mik'ewa yayi ranshi a dagule ya fita Zuwa gida.... su Khalil na isa gida Dakinshi ya nufa dan yayi wanka, da gudu Ashma ta rigashi shiga d'akin ta shige toilet" Murmishi yayi yace My princess gidan rigima zama yayi yana jiran ta fito yasan ruwan wanka ne zata had'a mishi" Yana nan zaune sai gata ta fito tana wani cin magani ita ala dole wai tayi fushi dashi. Dariya yayi yana girgiza kai ganin ta nufi Wardrobe d'in shi tana dauko mishi kayan da zai saka. Mik'ewa yayi ya shige toilet ita kuma tana gamawa ko zaman data saba na jiran shi, in Ya shiga wanka batayi ba ta wuce wajan Mamy... A parlo ta samu Mamy na jerawa Khalil abincin irin na marassa lafiya" zama tayi tana cewa" Dama ai ba sona ake ba shine aka dafa abinda bana ci, kuma sai na fad'awa Inna. Kallon ta Mamy tayi tace" Indai Inna ce yanzu zata k'araso garin ai sai ki koma wajanta ma" Mamy ta fad'a tana hararar ta. Tsalle Ashma tayi tana fad'in" Wow kai naji dadi Inna zata zo nan zan koma dakinta dama" Ta fad'a tana fad'awa kan kureja duk da bata tab'a ganin Innar ba amma suna waye sun shaku sosai da ita, shiyasa take son ganinta..
Baba yana murmishi ya iso parlon ko kafin ya zauna yaji kira yana shigowa wayarshi" Dubawa yayi ganin number Inna ce yace" Kai Inna ce ke kira, Da sauri Ashma ta dawo kusan Baba tace Baba ka bud'e volume naji muryarta.. Baba yana d'agawa Inna ta rushe da kuka, cikin kidima Yake fad'in" Inna lafiya kike kuka? Daga cen b'angaren Inna tayi rashe-rashe akan carpet ta face majina tace" Yo ba dole nayi kuka ba Yusufa ko me kake kazo yau din nan kai ko ba takalmi ne kazo Bakori ka daukeni na koma Niger bazan iya zama ba ana cin min mutumci kamar wata almajira, yo to almajira mana saboda Allah Yusufa wai Amadu ne ya tattaro min kayana gaba d'aya yace nabar mishi gida, ka ganni nan a bakin titi da katuwar akwatina kamar wata shegiya na zauna a k'asa" Ta fad'a tana sake rushewa da kuka sai kuma ta tsayar da kukan tace" Uban waye ya haifi Amadu? Waye ya dauki nauyin cikinshi wata ďai-ďai har tara cif-cif da kwana tara rass? Nifa na shayar dashi kusan shekara biyu garass yanzu Kai Yusufa ko wani yace ma Amadu yayi min haka zaka yarda? Baba cikin kunshe dariyarshi yace A'a Inna wai shi Ahmed d'in ne ya miki haka? Lalle kuwa ni da kaina zan mishi hukunci' Ya fad'a dan tayi shuru da maganar.. Inna ta jinjina kai tace Allah ya tsinewa wanda ya kawo turanci duniya, yo ni ko baturan ma nake gani tass zan mishi, wai ni yau Arufullah yake Zagi da turanci, kuma Ubanshi yana kallo amma baice komai ba haka ake rayuwa, yo ko daga haihuwar Amadu Bola na kaika na jefar ai baza kamin cin mutumci haka ba, wai ma abun haushin har da wannan doguwar Matar tashi mai hankalin Rakuma suke min dariya. Itama fa har tayashi ta ringayi Narkekiyar kazama kawai,suna turance ni dan Uban Nasarar Wallahi Yusufa idan baka zo ka daukeni daga Garin Bakori ba to gawata za'a kai ma, kamar wadda bata da galihu a watso ni bakin titi fisabilillahi, to yayi da Y'ar banza, nima fa na iya rashin mutumcin bazan sake zuwa inda suke ba suci kansu.. Baba da Mamy da Ashma har Khalil da Abdul duk sunyi shuru suna sauraron Inna tana rattabo bayani kamar an jona ta" Baba cikin kwantar da murya yace" Yi hak'uri Inna dama sai da nayi tace miki ki dawo nan Niger mu zauna amma kika kiya, to gashi yanzu kin zauna a titi ki koma ciki kin san dai Nigeria ba'a sake yanzu sai kiga yan kidnapping sun dira kanki..
Inna tayi saurin mak'ale wa a jikin gadon ta jin abinda Baba ya fad'a" Maza kuzo ku daukeni bazan iya zama a k'asan nan ba, dama naci na yasa na zauna" Yauwa Yusufa kace a jirgi zan tafi ta wani gari zanbi? Amma dai ba wannan gardawan Sojojin zasu zo daukana ba ko?
Baba yayi murmishi yace" Katsina mana cikin gari yanzu dai kinga ga K'awarki Ashma tana so ku gaisa.. Washe baki Inna tayi tace" Ashatu ina kike. Ashma ta tab'e baki tace" Nifa kinga ko Inna fushi nake da Abba dan haka kina zuwa a dakin ki zanke kwana, kuma Papi ma yana nan a zaune suna miki dariya wai sunce Y'an kidnapping suna kan hanyar dauke ki" Ta fad'a tana yiwa Abdul da Khalil gwalo..Muhammadu rasulullahi salallahu alaihi wasallam, ashe dama ba K'auna ta kuke ba ? To gaba daya sai naci Kundun uban ku zaku gane wacece ni, rabu dasu kinji K'awata da naje zan baki tsarabarki. Ashma tace Yauwa Innata shiyasa nake sonki dayawa sai kunzo" Inna ta mik'e kafafuwanta tace mai kawai zan shafa naji mota a k'ofar gidan zanzo karki damu" To Ashma tace san nan ta mik'awa Baba wayar. Baba yawa Inna sallama san nan ya kashe kiran, kallon Ashma yayi yace" Ashma wai fushin ne har yanzu? Cuno dan k'aramin bakin tayi tana murza idanu tace" To ai ABBA NE yake jan min kunne na saina fad'awa Inna da tazo" Ta fad'a tana fashewa da kuka.. Khalil tagumi yayi yana kallonta ganin hawayen ta yasa yaji duk baya jin dad'in hakan" Mik'ewa yayi yabar parlon a sanyaye ita kuma ta bishi da kallo. K'arawa kukan ta volume tayi tana cewa" Ka gani ko Baba wai ya dena min magana. Rarrashin ta Baba ya shiga yi har tayi shuru tana tsotson yatsun ta har bacci yayi gaba da ita..... Hisham na isa gida ya fito fuuu ya shige ciki yana huci" Bai samu kowa ba a parlon sai Rufaida tana game ta d'ago tana kallon shi, ganin kamar yana cikin damuwa sai tayi saurin aje wayar ta bishi zuwa dakin shi dan taji menene ya sanyashi shiga wannan yanayin, saboda bata tab'a ganinshi a wannan yanayin ba.......
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_