8
_*🌻ABBA NE 🌻*_
Hakkin Mallakar
_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
_*Littafin na kud'i ne only N300 ku harzarta ku mallaki naku, my WhatsApp number 👉🏻+966599791573*_
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣8️⃣
Ya Dafashi yana binshi da kallo irin na ban fahimta ba, Sunkuyar da kanshi Khalil yayi yana had'e rai ganin kallon da Abdul yake mishi, yace" Nifa kasan bana son kallo ko? To ka fita idona. Murmishi Abdul yayi yace" To ba dole na kalle ka ba naji kana maganar wai Princess lefin me ta maka da har kake shiga damuwa irin haka? Khalil ya girgiza kanshi yana d'ago da idanunshi da sukayi ja saboda damuwa yace" Baza ka gane ba a duk Duniyar nan bayan ku itace raunina banaso koda na rana d'aya ta matsa daga inda nake, ina jin tamkar zan rasa nutsuwa ta idan bata kusa dani" Sake da baki Abdul ke bin Khalil da kallo yace" Amma kai dai General ka zama Mahaukaci to baza ka aurar da ita bane? Ko kuwa haka zatayi ta zama kana kallon ta? Shuru yayi yana binshi da kallo jin ya ambaci aure, juya mishi baya yayi yace" Bazan iya bawa wani auren Princess ba kai ma kasan dalilin hakan shiyasa bana so ta had'u da wani Saurayi ma bare su k'ulla soyayya. Wannan ne kuma baka isa ba dole tayi soyayya ina tunanin dai fushin da tayi da kai ne yasa kake fad'in haka, ko kuma ban sani ba yanzu ka soma shan kwaya ne ? Nifa wani lokacin tsoronka ma nake ji, idan mun fita waje ka zama tamkar zaki idan kuma muna gida kamar wani Yaro to bana son iskanci gaskiya" Kaga ba wannan ba ma muje Asibiti wajan wannan Maaikacin. Had'iye damuwarshi Khalil yayi suka nufi mota, yaran shi ne suka iso da sauri aka bud'e musu mota suka shiga sai Asibiti...
Mansoor ya rafka tagumi ya lula Duniyar tunani, duk wayonshi ya rasa hanyar da zai bi dan ya sato Ashma. Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki kwalbar giyarshi ya ringa kwankwada kamar ba gobe, sai da ya shanye tass san nan ya mik'e yana tangadi cikin muryar maye yace" Matata Ashma Y'ar fara kizo gareni mu gudu daga garin nan.. Mommyn shi ce ta shigo dakin ta sameshi a wannan yanayin tace" Mai zan gani Mansoor? ashe dama baka dena shan giya ba? Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un na shiga uku haba Mansoor ya kake neman lalata rayuwar ka saboda wancen mugun Uban naka.. kallon ta yayi sai ya fashe da kuka yana cewa" Mommy ki aura min Ashma Daddy yace wai bazan aureta ba" K'ura mishi idanu tayi san nan ta kama hannun shi ta zaunar dashi ta shiga rarrashin sa tana cewa" Kayi hak'uri Mansoor Mahaifin ka bazai tab'a bari ka auri jikar Umar mai Nasara ba, kasan yadda abin yake ba sai na maka bayani ba. Goge hawayen shi yayi yace" To ni ina ruwana da fad'an su ai ba dani akeyi ba nidai kije ki kawo min ita nan mu gudu. Zaro idanu tayi tace" guduwa fa kace Mansoor idan ka tafi ka barni ina zan saka kaina? Wani kallo ya mata yace" Kaji Mommy da wata magana ai zanke zuwa ina ganinki. Shuru tayi tana kallon shi, sosai D'an nata yake bata tausayi D'anta mai hankali da nutsuwa amma yanzu Ubanshi ya maidashi babban tantiri saboda wani banzan dalilin shi marar tushe,hawaye ne suka zubo mata tayi saurin gogewa tana sauke ajiyar zuciya. Kallon ta Mansoor yayi duk da ba'a hayyacinshi yake ba amma yaji ba dad'i ganin hawayen Mahaifyarshi" Tashi yayi yazo ya rungume ta yana cewa" pardon Mommy na bazan tafi ba na dena. Murmushin k'arfin hali tayi kawai....
Suna zuwa Asibiti suka samu wannan Maaikacin ya farfado, zama general Khalil da Captain Abdul sukayi a gaban gadon nashi. Gyaran murya Abdul yayi yace" Am Rabe ko zaka iya fad'a mana abinda ya faru? Cije lips d'in shi yayi ya mik'e zaune kanshi a k'asa saboda tsoro daya kamashi da suka had'a idanu da Khalil. A hankali ya soma magana" Yau da kwana biyu ina zuba abinci ina kaiwa customers d'in mu, sosai nake jin dad'i ganin an cika restaurant d'in namu. Lokacin da kuka iso nayi farin ciki saboda ina ganin ku a TV ban tab'a ganin ku a fili ba sai ranar, nazo da sauri nace muku mai za'a kawo muku? Sai Captain yace na kawo muku Pizza da lemon juice kawai ya isheku" Da sauri na juya ina murna yau ni zan kawo muku abinci, ina dauko muku abincin ne sai ga wani Mutum yazo yace min" Inaso kayi min wani aiki zan biyaka da kud'in mai kauri har jika hamsin saifa. Da sauri na kalle shi haka kawai naji ba alkhairi ya kawoshi ba, amma na daure nace" Wani irin aiki ne zanyi maka wanda har zaka bani jika hamsin saifa? Murmishi yayi yace" Ai ba wani abu mai wahala zaka min ba inaso ka zuba wannan maganin a cikin wannan juice d'in da zaka kaiwa General Khalil da Captain Abdul. Tsoro ne ya kama ni sosai jin abinda ya fad'a nace Wallahi bazan zuba ba, ko waye bazan iya ba bare General da Captain wanda nake sonsu matuk'a.. haka yayi ta cewa zan baka jika dari nace A'a yace to dari biyu fa nan ma nace A'a, shine kawai ya shakeni ya rufe min baki ya kaini bayan lanbun dake nan baya" Nidai ban san meya faru ba daga nan sai yau dana tashi na ganni a gadon Asibiti, Amma ina fatan dai baku sha abinda yakai muku ba ko? Ya fad'a hawaye na zubo mishi.. Jinjina kai Abdul yayi yace" Ni bansha ba General ne yasha" Waro idanu Rabe yayi baki na rawa yace" Waiyo Allah amma ba abinda ya sameka ko? Murmishi gefen baki Khalil yayi ya jinjina mishi kai alamar eh.. Abdul yace Zaka iya ganeshi idan ka ganshi? Sosai ma zan gane shi, kana ganin shi dama sumfar mugaye gareshi" Dan Murmishi Khalil yayi jin abinda ya fad'a ya tuna mishi da Ashma.. mik'ewa sukayi Abdul yace" Za'a sallame ka da zarar kaga wannan mutumin to ka sanar dani" Rabe yace To ranka ya dad'e. Kud'i General Khalil ya aje mishi masu yawa yace ka kula da Iyalinka anjima zasu zo ku tafi gida. Godiya sosai ya musu san nan suka tafi.
Doctor Hisham jikinshi yayi tsanani daga ciwon kai ya wuce zazzab'i hakan yasa bai sake fita ba, Rufaida kuwa kullum tana kusa dashi idan taga yana juya kai alama ciwo wani wajan yake mishi sai tayi ta kuka tana mishi sannu.. zaune take tana kallon shi bako k'iftawa hawaye nata zirya kan kuncinta" Shi kuma baccin wahala yake, Hannun shi ta kama tana fad'in" Abie na Allah ya baka lafiya.. motsi ya soma tayi saurin dawowa kusa dashi tana murmishi tace" Abie ka tashi sannu. Zura mata idanu yayi ganin hawaye a fuskarta shima murmushin ya mata da k'yar ya iya cewa My Daughter! Cikin jin dad'i ta amsa da Na'am Abie. Taimaka mishi tayi ya tashi zaune tasa mishi pilo a bayanshi ya jingina da jikin gadon. Hawa kan gadon tayi tace" Abie bari na goge maka jikin ka kaga baronka da wanka tin ranar da zaka kwanta ciwon nan. Murmishi ya sakar mata ,mik'ewa tayi ta shige toilet bata jima ba tazo da ruwa a cikin wata roba mai dan girma hannun ta d'aya rike da karamin towel d'in shi. Kan gadon ta hau ta aje ruwa a kusan gadon tana murmishi tace" Abie bari a cire rigar ko dan kaji dad'i jikin ka idan na goge ma jikin naka" Waro idanu yayi yace" Riga kuma zaki fidda min Daughter? B'ata fuska tayi tace" Eh goge ma jiki zanyi kaga Ammi bata nan ta fita har Daddy ma duk basa nan Uncle Kalifa ma yace sai yamma zaizo, kaga ni zanyi maka komai" Ta fad'a tana balle mishi mab'allin rigar, rufe idanu yayi ita kuma ta gama ta cire mai riga har ta cikin duka ta cire. Kyakyawar fatar jikin shi ce ta bayana Rufaida ta sauke ajiyar zuciya tana kallon shi ,da hanzari ta dauko ruwan ta sanya towel d'in ta shiga goge mishi jiki. Tana gamawa tace" Abie saura wandon za'a cire na wanke ma kafafuwan ka kalli yadda sukayi baki" Da sauri ya zabura cikin rawar baki yace" Wando kuma Daughter ki barshi kawai zan iya zuwa toilet sai na canja kayan. Kuka tasa tana fad'in" Abie kaji fa duk warin dauďa kake amma kace baza a goge ma jiki ba, nidai ka tsaya na gama ko na shirya ka" Sake da baki yake kallon ta maimaita maganarta yake yana cewa" ko kin shiryani kamar wani Baby?.. wayo ya mata yace" Ki kawo ruwan ki wanke kafata kawai ya wadatar nama ji sauki sosai" Ruwan ta kawo kusan k'afarshi ta shiga gogewa sai cika take tana batsewa wai ya hana ta gyara shi.. shi kam murmishi yayi yana kallon ta har ta gama" Kaya ta dauko mishi masu kyau ta sanya mishi rigar ta aje wandon tace" Bari na wanke toilet kafin na fito ka gama" To yace mata tana shiga yayi sauri ya tashi a hankali ya kimtsa ya dawo ya zauna. Bayan ta fito ta ringa murna Abie d'in nata ya samu lafiya" Kama shi tayi suka fita Palo... zaune suke a gaban Boka sun nutsu kamar wasu wanda ake yiwa nasiha mai ratsa jiki" D'agowa Bokan yayi ya kallesu da jajan idanun shi sai kuma ya kece da dariya dajin na amsa sautin muryarshi. Had'e rai yayi yace" Alhaji Babba meya kawo ku? Cikin rawar Muryar Alhaji Kabeer yace" Muna so a kashe General ne da wannan Yarinyar, kai duka ahalinshi ma duk a kashe su mu dena ganin irin su a Duniya.. Dariya Bokan yayi yace" Bari mu gani, Wata kwarya ya janyo ya soma tsubbace tsubbacenshi ,sai ga ruwa sake fad'in wani kalmomi yayi sai ga Khalil ya bayyana zaune a Masallaci yana jan tasbaha" Boka ya d'ago yace ku lek'a ku gani. Lekawa sukayi suka ga Khalil a cikin kwayar, Cikin jin tsanarshi Alhaji Sammani yace" Shine Boka a kashe shi tinda mu mun k'asa kashe dan iskan Yaron nan mai taurin kan tsiya.. Boka ya bud'e k'ofar hanci yace" Bazai tab'a yiyuwa ba a kashe shi. Da mamaki suke kallon Boka su da sukazo ya share musu hawaye amma yana wata magana" Alhaji Mati yace" Boka kamar yaya kace bazai yiyuba? Dariya Boka yayi yace" Wannan Yaron da kuke gani yana tare da sanya albarkan Al'umman gari da wanda suke rikeshi, kuma kullum Kakarshi sai ta mishi Addu'a neman tsari ga irin ku" Ya fad'a yana sake yin wata dariya. Jinjina kai sukayi Alhaji Kabeer yace To Diyar tashi fa? Shafe photon Khalil Boka yayi ya kawo na Ashma tana kwance tana bacci Inna na gefen ta. Dariyar basawa yayi yace" Za'a iya yiwa wannan wani abun amma fa baza a iya kashe ta ba.. Da sauri Alhaji Mati yace A maidata mummuna kowa yake k'yamatarta" Boka ya zaro manyan idanun shi yace Bazai yiyuba ba ku dai fad'i wani abun. Shikenan a hauka tata kawai nan ma Boka yace bazai yiyuba ba" Alhaji Mati ne yace To Boka ake firgitata kawai kaga sai a dauka ta haukace " Dan Jim Boka yayi sai kuma ya dauko wani ruwa ya watsa a saitin fuskar Ashma dake bacci, gani sukayi ta dan motsa sai kuma taci gaba da baccin ta...
Murmishi sukayi Alhaji Sammani yace Yanzu ba abinda Za'a yiwa Khalil din boka a dai bduba? Boka yace Kuje bayan sati biyu ku dawo lokacin na samu wata hanyar" Cike da farin ciki suka tashi har zasu tafi Alhaji Kabeer yace Kai munyi mantuwa ,Boka D'an mu yana son wannan Yarinyar a cire mishi sonta muna so ya kashe ta da hannun shi" Sake dubawa yayi yace" Shima bazai yiyuba ba na raba soyayyar da yake mata saboda ba daga sama ta fado mishi ba so na gaskiya yake mata, maza ku tafi La'anannun Allah sai bayan sati biyu ku dawo. Juyawa sukayi suka bar dajin kowa na ta saka da warwara...
A guje ta fito harabar gidan kanta ba dan kwali ,wata Mata ce ke binta da dorinar, tana fad'in" Ni zaki kunyata Sanjina? Duk jin dad'in da kike yi a gidan nan shine ki rasa wa za kice kina so sai General Khalil to yau saina kashe ki kowa ma ya huta, har kina da abinda General zai kalla a jikin ki yace yana sonki bari ki gani.. Wata sandar karfe ta dauko ta shiga maka mata tana cewa" Ni zakici amana Sanjina Musulmi zaki ce kina so Shi wanda muka Zaba mikin uban waye zai aureshi iyee? Kuka sosai Sanjina keyi tana fad'in Mama kayi hankuri nidai shi nake so shima yana sona" wani wawan Mari Maman nata ta sauke mata akan kuncin ta wanda yasa taga wucewar taurari. Janta da ringayi tana ci gaba da dukan ta har bakin k'ofar waje ta kawo ta, hankada ta tayi tana huci ta koma ciki" Jakar kayanta ta dauko mata a jefo mata tana cewa" Kije cen gidan su sai ku zauna indai shi kikeso ba mu ba ke karki kuskura kizo inda muke kinji na fad'a miki.. Hak'ura ta shiga bata amma Maman nata tace Sam baza ta yi ba daga karshe ma Yaran Unguwar ta kira tace su Kora ta har sai tabar Unguwar gaba d'aya" Su kuwa Yara sun samu abinda sukeso tuni suka ringa jifanta suna tile ta da k'asa. A hankali take tafiya tana kuka yaran na binta har ta kusan zuwa karshen layin gidan su san nan suka kyaleta. Zama tayi a gindin wata bishiya tuna wayarta yasa ta duba ta kuwayi sa'a Maman nata ta hado mata da ita.. number Khalil ta dannawa kira, yana dauka ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma rai. Khalil dake zaune yana shan iska ya d'aga kiran nata jin kukan ta ne yasa Yace" Hello Sanjina kina jina? Lafiya kike kuka ? Waye ya tab'a ki? K'arawa Kukanta Volume tayi da k'yar ta iya cewa" Mama. ....
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_