ABBA NE

11

by @mamannusaiba8002115

_*🌻ABBA NE 🌻*_








Hakkin Mallakar


_*Sarat Alk'asum(Maman Nusaiba)*_




_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



_*Littafin na kud'i ne only N300, ku harzarta ku mallaki naku zaku samune ta wannan number +966599791573*_




بسم الله الرحمن الرحيم



1️⃣1️⃣




Gani Inna ina fatan dai ba lefin Iyayena bane zai shafeni" Ta fad'a a sanyaye. Murmishi Inna tayi tace" Mai sunan Jimina ai ni babu abinda kika min sai dai nayi tasa miki albarka, ina fatan Allah yasa kina da babban rabo nan gaba" Murmishi Sanjina tayi tana k'ara k'aunar Tsohuwar tace merci beaucoup ma grande mère, rike baki Inna tayi tace" Kaji wani yare ko? Yo nifa da kike ganina nan ko Larabawan Saudi baza su nuna min Larabci ba,idan kinaso mu canja magana ki min larabci mana kigani.. Mamy tace Gaskiya ne Inna yanzu yaushe za'ayi shagalin bikin? Inna tayi caraf tace Musalle kunji dai wannan Mai kama da Buzayen abinda ta fad'a. Y'ar dariya yayi kawai ya kalli Khalil yace Yaushe kake ganin kana hutu sai ayi bikin? Daure fuska Khalil yayi yace" Daddy ni da zaku bi ta tawa kar ayi wani shagali ko biki tinda an daura auren shikenan" A fusace Daddy Musa yace" Kaji Ja'irin Yaro ko Inna, to taya zakayi aure baza ka gayyato Abokan ka ba su tayaka murna da Y'an Uwa. Kallon Captain Abdul General yayi alamar ya musu bayani" Mik'ewa yayi ya iso kusa da Baba da Daddy Musa a hankali yace" Daddy ku fahimci Khalil tinda yace muku a bari to kar ayi, kun san dai yadda magauta suke neman kaishi k'asa tamkar yadda ake neman arziki ko? Jinjina kai sukayi Baba yace Gaskiya ne kuma naga yanzu ya rame ko me ke damunshi? Dan Murmishi Abdul yayi shi ya san abinda yake sanya Dan Uwan nashi rama amma bazai taba fad'a musu ga binda yake sanya shi rama ba, Kallon su yayi yace karku damu da ramar shi aiyuka ne suka mana yawa yanzu haka yau d'in nan bamu jima da dawowa daga wani daji ba muka kamo barayi sunfi goma" To kunga ai dole kuga wani lokacin muna dan ramewa. Amma yanzu tinda yayi aure kila ko ya rage damuwa da wasu abubuwan.. Daddy Musa ya girgiza kai yana kallon Khalil da yake daurawa Ashma sarkar hannu sabuwa fil, dawo da kallonshi yayi akan su yace" To shikenan kawai abar komai itama Yarinyar kunga baza ma taso ayi ba tinda bata da lafiya. Baba yace gaskiya ne yanzu dai mu samu a shayo kan Inna tabar maganar yin shagalin bikin nan..

Inna ta fasa kuka tana cewa" A ni Indo naga Rayuwa yanzu saboda munafurci yasa kuka had'e kai kuna magana, ni kun daukeni Uwar banza ko? Daddy Musa yace Haba Inna ya kike wannan maganar ,ki bar ma maganar yin shagalin bikin Khalil saboda yana da aiki a gabanshi shine fa Abdul yake fad'a mana. Dena kuka tayi ta kalli Khalil da ya tsare Ashma da idanu kamar ya samu sabuwar halitta, tace" Namijin Duniya zo nan kaji nasa maka albarka. Wani sanyi yaji ya mik'e ya iso ga Inna ya zauna a kusan Sanjina suna facing d'in juna, murmushi ya sakar mata itama cikin jin dad'in ya sakar mata fuska ta mayar masa da martani, da muryar raďa tace" Mai gida. Yar dariya yayi ya nuna mata Inna da idanunshi, langabar da kai tayi tana yin fuskar tausayi, sai kuma ta nuna mishi kanta alamar yana mata ciwo. Waro idanu yayi yana k'ifk'iftawa kamar wani marar gaskiya, nuna mata yayi idan Inna ta gama ta bishi dakinshi. Jinjina kai tayi alamar to sai kuma ta sauke ajiyar zuciya har sai da yaji" Gira daya ya d'aga matayana tambayar ta lafiya? Saitin zuciyarta ta nuna mishi sai kuma tayi Murmishi tasa hannu a saitin zuciyar tata ta nuna mishi tana sonshi" Shima kamar yadda tayi haka ya mata, jin Inna ta juyo kansu yasa sukayi saurin kamewa.. Inna ta dafa kan Khalil ta shiga karanto mishi Addu'o'in neman Kariya ga duk wani abun cutarwa mutum ko aljani ko dabba" Tana gamawa ya d'ago ya kama hannun ta ya sumbata.. Had'e rai Inna tayi tace" Kai bana son iskanci wannan abun fa? Murmishin gefen baki yayi ya mik'e yana cewa" Mamy a kawo min cofi da ruwa haka mai sanyi zafi nakeji...


Mamy tace To Khalil gashi nan zasu kai ma dan duk abinda sukeyi d'azu akan idanun ta sukeyi" Inna ta mik'e tace" To Musalle a gaishe da gida ni zan shiga ciki ina dan jan tasbaha ta saboda ni banyo gadon turawa ba" Murmishi Daddy Musa yayi kawai ya mik'e ya musu Sallama ya fice" Baba da Abdul ma kowa d'akin shi ya nufa, Mamy kuma ta shiga Kitchen ta hado cofi ta mik'awa Ashma tace" Tashi kuje kar Inna tazo ta hana ku kina shiga in kika aje ji dawo sai na miki kitson. Cikin jin dad'i Ashma tace To Mamy san nan ta kama hannun Sanjina suka nufi d'akin Khalil.. a zaune suka sameshi yana danna laptop d'in shi idanunshi sanye da glass ya d'ago yana kallon su.. Ashma ta aje kofin a kusa da shi ta matso ta bashi runguma tace" Abbana me ake cewa ma da turanci taya murna? Yar dariya yayi yace" Congratulations ake cewa ke dai kina son yaren Turanci. Itama dariya tayi tace" Sosai ma kuwa Abba bari naje kitso za'a min Don Allah Abba bari yanzu za'a shigo da abinci ka tsare ta taci, tinda ku ka kawota inba kuka ba babu abinda take.. Khalil ya rike baki yace" Kai ita d'in? Jinjina kai kawai Ashma tayi ta fita da sauri dan kawo musu abincin. Bata jima ba ta kawo musu tana ajewa ta fita ta janyo musu k'ofa" Tashi Khalil yayi ya sanyawa k'ofar key san nan ya dawo ya zauna a k'asa yace" Dawo nan kici abinci.. kamar zatayi kuka tace" Nifa kaina ke ciwo shiyasa na kasa cin abincin" Ta fad'a tana langabar da kai. Da kanshi ya mik'e ya kama ta ya kawo ta gurin abincin ya zaunar, daukowa yayi yace" Bismillah maza bud'e na baki indai kina son jin ciwon kanki ya dena to sai kinci abincin nan sosai.. cikin jin dad'i tace" Da gaske? Gyadamata kai kawai yayi" gyara zama tayi ya shiga bata a baki, sai da ta koshi san nan ta janye bakin ta. Itama da kanta ta bashi tana mai kallon shi dan gani take kamar a mafarki wai itace Matar General Khalil.. suna gamawa ruwan wanka yaje ya had'a mata yazo yace suje ya mata wanka" Waro idanu tayi tace To ai zan iya? ,murmushi yayi bai ce mata komai ba ya sunkuce ta ya kaita toilet d'in" Cikin jin kunya ta ringa kare jikinta idanun ta a rufe, bai tsaya yin komai ba ya shiga mata wanka cike da tausayawa ganin raunikan dake jikinta, bayan ya gama mata ya dawo da ita kan gado doguwar rigar Ashma ya cire mata yace Kisa wannan bari naje nayi wankan nima, sauran abun buk'ata duk suna cikin nan na wuce.. kanta a k'asa har ya shige, Mik'ewa tayi taje ta shafa man shi mai kamshi san nan ta sanya kaya ,kan gado ta dawo bata jima ba bacci ya dauke ta.. Shima yana fitowa ya shirya ya kwanta a gefen ta yana ta tunani kala-kala a zuciyarshi..



*Nigeria*


Tafiya suke a mota Rufaida sai zuba surutu take yi, shi kuma Hisham yayi banza da ita dan ya gaji da surutun nata. Kallon shi tayi tace" Abie wai yaushe zakayi aure ne? Daure fuska yayi yace sai randa kikayi" Murmishi tayi tace" Kai Abie daga tambaya Allah ya kamata kayi aure kar ka tsufa ba mata. Bai ce mata komai ba, sai taci gaba da cewa Abie kasan kuwa wani dan ajin mu yace yana sona" A razane yaja birki ya tsaya yana kallon ta cikin idanu yace" Ban gane me kika ce ba Daughter? Ita kuwa ko ajikin ta dan ba shi take kallo ba tace" Wani yace yana sona. Da sauri yace" To ke kuma ya kika ce mishi ne? Dariya tayi tana juyowa gareshi ta kama hannayen shi ta rike tace" Abie ai ni Yarinya ce ko? To ce mishi naji ni Yarinya ce ban isa aure ba, ya bari idan na isa sai yazo gidan mu.. Ajiyar zuciya ya sauke ya tada motar , hankalin shi a kan titi yace" Daga yau kar na kuskura naji ko na gani kin tsaya da wani Saurayi da sunan Soyayya, koda wasa naji zan zaneki kina jina? A sanyaye tace To Abie bazan sake kula kowa ba sai da amincewar ka. Murmishi yayi yana yin packing a katafaran companyn *Muddansir and Brothers* Rufaida tace wow Abie kace surprise ka min? Murmishi yayi yace Eh mana ai naga kin takura ne sai kinzo shine nace bari na biki bazata. Rungama ta bashi san nan suka fito daga motar, ciki suka shiga inda suka nufi wajan kayan kwalliya da turaruka ya shiga d'ibar mata duk abinda yasan zata buk'ata.. Khairat ce ta biyo b'angaren da su Hisham suke tana zabar wasu kayan kwalliya, idanun ta ne ya sauka akan Hisham dake rike da hannun Rufaida yana dauko wa sai ya nuna mata idan ta d'aga kai sai ya saka a cikin kwandon" Baki na rawa tace" Kan ubancen yaushe wannan Hisham din ta warke daga cutar da ya kamu da ita, kuma yama akayi bai kirani yace yana sona ba? Kai ina dole na sake hiri Wallahi. Takowa tayi cikin iya bariki ta iso gare su tace" Hello" Hisham daya ganta tin lokacin da take kallon shi bai d'ago ba bare ma ya amsa ta, Rufaida ce ta juyo jin da su ake cikin zallar farin cikin da take ciki tace" Heyy. Murmishi tayi tace" K'anwata Yayan naki baya magana ne? Rufaida ta tsuke fuska jin ancewa Abie d'in ta wai Yayan ta, tace Yayana kuma? Khairat tace" Eh ko Saurayin ki ne? Tsaki Rufaida taja tace" To Babana ne,san nan tabi bayan Hisham da yayi b'angaren kayan Maza..

Khairat ta saki baki tana kallon su har suka b'ace mata da gani, a fili tace" Kut Baban ta fa tace? Dama Doctor Hisham yana da D'iya kamar wannan tab, kwafa tayi tuna kallon da Rufaida take mata ta nufi inda sukayi... Hisham ya kalli Rufaida yace" Me tace miki? Sake had'e rai tayi tace Wai dan ta rena min hankali ta kalleni tace min kai Yayana ne ko Saurayina Wallahi ba dan kar ka dakeni ba da saina zabga mata tafi ko sau biyu ne.. murmushi yayi yace" Ba abinda zan miki, kuma ko a ina kika ganta karki sake kulata. To tace ta shiga zabar mishi kayan sanyawa da takalma kamar yadda itama ya mata... Bayan sun gama ne suka iso wajan biyan kud'i, anan sukaga Khairat ta gama biyan kud'in ta. Ko kallon inda take basuyi ba suka biya kud'in su aka dauko musu kayan zuwa mota.


Khairat tayi saurin binsu a baya da sauri taga gaban Hisham ganin Rufaida ta shiga mota, cikin iya barikin ta tace" Haba Doctor sai kace kaga wata babbar makiyar ka ina magana ka shareni. Wani kallo ya watsa mata yace" Ke matsa ki bani guri bana son shirme. Kukan k'arya ta soma tana had'e hannaye tace" Kayi hak'uri da abinda na maka Wallahi nima danaje gida nayi tunani naga ban kyauta ba, shiyasa nake ta kiran ka dan na baka hak'uri amma bana samun ka" Amma plus kayi hak'uri kace kana sona. Tsuwww yayi tsaki cikin fusata yace" Bana son maganar Banza ki bani guri nace ko! Ya fad'a a tsawace, ai bata san sanda ta matsa ba sai ganin tashin motarsu tayi.. Cikin bak'in ciki ta shiga Motar ta ta fice itama. ...Suna isa gida Ya fito yana bin motocin da suke a jere da kallo, Murmishi yayi sai kuma ya kama hannun Rufaida suka nufi ciki. Tin kafin su shiga yaji hayani na tashi a parlo sai yayi mamaki haka dai suka shiga..


Parlon zaune suka sàme su Ammi da wasu Mata biyu sai wasu Y'an Mata guda uku dake gefen su, gefen d'aya kuma Daddyn su da wasu Maza biyu da alama dai Yan Uwan Daddyn nashi ne.. k'ara rike hannun Rufaida yayi ya jata suka zauna kanshi a k'asa yace" Kawu sannun ku da zuwa, Mama sannun ku da zuwa. A tare suka amsa mishi ko wanne fuska a sake yayinda Y'an Matan ko wacce take son ta birgeshi suka ringa gaishe shi" A takaice ya amsa lafiya" Hakan yasa suka gane yau Y'an Miskilancin ne a kanshi.. Daddy yace" Yauwa Hisham dama akan maganar ka ne muka taru" da sauri ya d'ago yana kallon su yace" Daddy ban gane ba? Ko nayi wani lefin ne? Murmishi Daddy yayi yace" Ko d'aya sai kuma yace" Hajiya ku bamu guri ko. Mik'ewa sukayi dukkansu amma banda Rufaida da yaki sakin hannun ta ya rike gam" D'aya d'aga cikin Kawun nashi yace" To ita Y'ar taka baza ka bari ta tafi bane muyi maganar. Sake had'e rai Hisham yayi dan ya tuna ko me suke son mishi magana akai, yace" Kawai kuyi magana karku damu da Daughter kome nawa ya shafeta.. Jinjina kai sukayi, Daddy yace" Yanzu Kai Hisham baza ka fito da Matar da kakeso ba? Har sai na fusata na aura maka wadda baka so, nafi so ka kawo wadda kakeso dan ayi auren cikin jin dad'i amma kai fir kaki kawowa, kai daga Asibiti sai kai wannan Futsararriyar Y'ar taka shoping ko yawo haka kawai, to indai har yanzu baka da wadda kakeso zamu yanke hukunci.. zabura Rufaida tayi ta kalli Hisham wanda fuskar shi ba rahama, a hankali tace Abie tinda baka da ita ka amince kar suce ka rena su. Kallon ta yayi sai kuma ya kallesu yace" Nifa bani da wata budurwa ku zaba min wadda kuka yarda da tabiyarta.. Kawun nashi yace" To shikenan zamu aura maka Layla Yar wajan Kawun ka Muntari. Ajiyar zuciya ya sauke kawai a takaice yace To shikenan Daddy zanje na shirya inason zuwa Asibiti.. Albarka suka sanya mishi san nan ya mik'e ya kai Rufaida d'akin ta da kayan ta" zatayi magana yace Ki bari idan na dawo zamuyi maganar. Badan taso ba tayi shuru ta koma ta zauna...



*Niger🇳🇪*



Da sauri Wani Babban Mutum ya sha gaban ta yana murmishi har da shafa gemu" Harara ta watsa mishi tace" Malam lafiya ka wani tsareni? Gyara zaman Babbar sa yayi yace" Wato Yarinya tin ba yau ba nake ta ganin ki kina zuwa nan wajan kina shan iska, da zarar zanzo wajan ki sai naga masu tsaronki sun kewaki to yau dai na samu dama baki zo da kowa ba, nidai sunana Alhaji Ismail Babban dan kasuwa ne ni, gaskiyar magana ina matuk'ar sonki kuma da aure nake sonki" Ya fad'a yana lashe baki ya matso kusa da ita kamar zai kai mata runguma.. da sauri taja baya tace Kai dallacen matsa ka bani guri in zauna Wallahi idan Abbana ya ganka zaka gane baka da wayo impossible kawai" Tinda ya soma magana Khalil yake tsaye yana kallon.. Sake matsowa yayi ya kai mata cafka ihu ta kwalla jin ya damki Hannun ta" Abdul daya nufo su ganin abinda yake faruwa kamar wani zaki sai gashi a zakiyar Ashma da Alhaji Ismail cikin shigarshi na bakar riga da wandon Sojoji... ..





*😂😂Alhaji Ismail ka tabowa kanka bala'i*




_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_