ABBA NE

12

by @mamannusaiba8002115

_*🌻ABBA NE 🌻*_










Hakkin Mallakar


_*Sarat Alk'asum(Maman Nusaiba)*_





_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



_*Littafin na kud'i ne only N300 No. +966599791573*_



بسم الله الرحمن الرحيم




1️⃣2️⃣



Khalil yayi yunkurin zuwa ganin Abdul ya isa sai yaja baya ya harde hannayen shi a k'irji yana bin su da kallo, zuciyarshi na tafasa ga wani abu daya tokare mishi makoshi har wani ďaci yakeji a kan harshen sa. Abdul kuwa da mamaki yake kallon Alhaji Ismail cikin had'e rai yace" Kai kasan ita wacece? Kasan D'iyar waye ita? Wanene ya baka izinin yin magana da ita? Alhaji Ismail ya ringa kallon Captain Abdul sai yanzu ya gane ashe dai Sojan nan ne da ake maganar sa shi da Dan Uwanshi" Zaro idanu yayi yana ja da baya cikin rawar murya yace" Waiyo ranka ya dad'e dama ka san wannan Yarinyar ne? Ai ni na dauka D'iyar wani gwamna ko shugaban kasa ce, Dama tinda na ganta ne yaji ina... Bai k'arasa ba Abdul ya sauke mishi tafi a ko wani kuncin, damkar shi yayi yana huci yace" Kace kana sonta? Lalle ka tafka babban kuskure a rayuwarka, Y'ar tawa waye yace ka tab'a mata hannu? Irin ku ne mutanen banza dake lalatawa Yara rayuwa, kenan da ace itama irin ka ce sai ka lallab'a ka lalata mata tarbiya ko? To yau zaka gane baka da wayo" Waya ya ciro a lajihun shi ya danna wasu nombobi, ana dauka yace" Kuna ina haka? D'aga cen b'angaren wanda ya amsa wayar yace" Oga muna kusa daku. OK to maza kuzo yanzu yanzu minti uku na baku" Yana fad'in haka ya katse wayar. Alhaji Ismail tinda yasha mari bai sake sanin inda kanshi yake ba ji ma yayi kamar ya kurumce sosai kunnen shi ke mishi zafi da azaba.. Ashma kuwa kuka take tana goge hannun ta daya damka sai cewa take" Allah ya isa D'an iska kwarto tsohon banza sai Abbana ya maka dukan mutuwa... Khalil ne ya iso wajan ya mika mata ruwa a cikin gora yace Maza wanke hannun" Amsa tayi ta wanke amma sai shinshina hannun take ta kalli Khalil tace" Abba hannuna wari yake inda ya tab'a min, nidai kasa min turare kila ma abinci yaci bai wanke hannu ba shine yazo ya tab'a min hannu. Murmishi yayi yana jinjina kai jakar ta dake hannun shi ya dauko turare a ciki ya fesa mata" Goge hawayen tayi ta kama hannun shi tace" Abba muje gida ice cream din ma na dena sha, Juyowa tayi ga Abdul tace Papi gida zamu tafi.. Abdul zaiyi magana sai ga Yaran nasu sunzo suka dauki Alhaji Ismail suka wurga shi cikin mota wasu na yin bol dashi a haka suka bar wajan" Mutanen dake wajan suka ringa kallon Alhaji Ismail suna tab ka dauko ruwan dafa kanka da kanka, Y'ar General d'in ce ka tabawa hannu wadda ko kuďa bayaso ya rabeta bare mutum, mutum d'in ma kai ka nemeta ta hanyar banza" Haka dai akayi ta surutai kowa na fad'in albarkacin bakinshi.. Khalil yaja hannun Ashma suka nufi mota Abdul na biye dasu har bakin mota. Abdul yace" Wallahi da ka barni sai na kakkarya wancen mitsiyacin"Numfasawa yayi yace" Zan koya mishi hankali, sai ya gwammace kida da karatu. Sanya ta yayi a mota shima Abdul ya shiga yaja suka nufi gida.. Ashma nata yiwa Khalil surutu shi kuma yayi banza da ita yana karanta sakon da Ogan su ya turo mishi. Zabura tayi ta fad'a kanshi jikinta ya dauki rawa tace" Abba naga Mutum da Kan jaki waiyo Allah ka boyeni dariya yake min. Tsaki Khalil yaja yace" Idan kika sake mun maganar shirme saina zaneki. Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya, sai da taji ta dena jin tsoron san nan ta mik'e daga jikinshi ta gyara zama" Har sun kusa isa gida kamar ance ta kalli gefen a firgice ta sanya kuka tana nunawa da hannu ,tace" Abba ka gani ko Wallahi naga Mutum mai tsayi marar iyaka shima kirana yake, Abba ka boyeni. Dariya Abdul yayi yace" Kai Princess Wallahi Allah dai ya shirya mana ke, a ina kikaga mutum da kan jaki dan k'arya? Ashma dai ta makure a jikin Khalil tana sauke ajiyar zuciya sosai tsoro ya shige ta sai k'ara k'ank'ame Abban nata take.. Shi kuwa Khalil bai ma kula da maganar ba dan shi a ganinshi kawai shirmen ta ne data sabayi..


Suna packing Abdul ya fito ya bar su a ciki, Kallon ta yayi a hanci yace Zaki tashi ko sai na zaneki? Kinga Princess bana son shirme fa. Fashewa tayi da kuka ta tashi daga jikin nashi, da sauri ta fito ta kwasa a guje hannun ta akai tana k'arawa kukan sauti haka ta shiga palon.. Mamy dake zaune tayi saurin mikewa tana salati ganin Ashma takalmi da Dan kwalinta a hannu tana kuka, Riko ta tayi tace" Y'ar Abban ta lafiya kike kuka? Sake sakin wani kukan tayi tace" Mamy ABBA NE" Kallon bakin k'ofa Mamy tayi kafin tayi magana sai ga Inna ta fito zanen ta a hannu, bata zarce ko ina ba sai wajan Ashma ta riko hannun ta suka zauna akan kujera sai ga Khalil ya shigo.. Inna ta k'ank'ace idanu cikin masifa tace" Khalilu shin wannan Yarinyar da Uwarta ta mutu ba cewa tayi ka rike mata ita amana ba? Ko ita Uwar tata ba auren soyayya kukayi ba? Ka fita idona fa zan ballaka a nan katon banza katon wofi, gaka nan narkeken Namiji Amma sai hankali kamar na rakuma.. Khalil dai baice komai ba ya wuce dakin shi, ita kuma Ashma da k'yar Inna ta rarrashe ta tayi shuru, sai fad'a take tana zagin Khalil wai ya shiga hankalin shi zatayi maganin shi inya sake.. Abdul kuwa Dariya yake sosai har Inna ta dawo kanshi ganin zata kawo mai ciwon kai ya wuce ciki.. washe Gari Abdul da Khalil suka nufi Barikin Sojoji cikin wani gida suka nufa, Hon yayi aka bud'e musu get, suna yin packing wani Soja yazo da gudu ya bud'e musu k'ofa, suna fitowa ya sara musu ya kame" Murmishi Khalil yayi ya mik'a mishi hannu yace" To kai wai bance ka dena bud'e mana ķofa ba idan munzo? Shima murmushin yàyi yace Ranka ya dad'e ai kun cancanta ne shiyasa. Ciki suka nufa daret dakin da aka Kai Alhaji Ismail suka nufa" Done hanci Abdul yayi jin wani waro ya bugo shi, wani Soja ya kira yace maza su fito dashi harabar gidan, san nan a tabbatar an gyara d'akin" Cikin girmamawa yace OK Sir" fito dashi sukayi aka zaunar dashi a k'asa.. Khalil ya janyo kujera ya zauna yana kallon shi tuni suka canja mishi kamanni saboda yasha casa kamar gero, sake had'e rai Khalil yayi ya zaro bindigar dake kugunshi ya sanya mata alburusai, saita kan Alhaji Ismail yayi yace" Kace kana Son Y'ata ko? Alhaji Ismail ganin an daura mishi bindiga ya shiga rawar jiki yace" Don girman Allah kayi min rai Wallahi tsautsayi ne yasa nace haka, amma Insha Allah ko haduwa nayi da ita bazan kalli inda take ba. Tsawa Khalil ya daka mishi gani yake kamar yanzu ne ya kaiwa Ashma damka, daukeshi yayi da mari har sai da ya kifa saboda azaba" Cikin tsawa yace" Yi min shuru mutumin banza shi neman rungumar ta da kayi fa? Shima duk cikin soyayyar ne? Ya fad'a yana take mishi hannu har sai da yayi k'ara san nan ya dauke kafarshi. Ihun azaba Alhaji Ismail yayi yace" Natuba kayi hakuri bazan sake ba, don Allah ka sakeni naje gida Y'ata bata da lafiya kuma Mahaifiyar ta ta rasu ni ke kula da ita, kayi hakuri zanje na duba lafiyarta.. wani kallon banza ya watsa mishi ,yace" Yanzu misali ace wannan Yar taka da kake ji da ita kamar tsoka d'aya a miya, in kaga wani yana yi mata irin abinda kaso yiwa Y'ata wani mataki zaka dauka? Goge hawaye yayi kanshi a k'asa kamar yana gaban wani surukin shi yace" Pardon Soja in naga haka sai inda karfina ya k'are kayi hakuri don Allah na tuba ba dan ni ba dan halin da Y'ata take ciki ka min rai" Ya fad'a yana kama kafafuwan Khalil... Captain Abdul dake kallon su yaji ba dad'i jin yace Y'arshi a gida shi yake kula da ita, a fili yace Gashi ka Jawa kanka dan indai Khalil ne azaba wannan mai sauki ce yake ma, ganin ba zai sakeshi ba yasa ya iso gurin da suke, Kama hannun shi yayi ya tashi yace maza ka tafi gida ga motar ka cen. Godiya sosai Alhaji Ismail yayiwa Abdul ya kuma ce Insha Allah ya dena abinda yake" Jinjina kai kawai yayi sai yace" Zaka iya tafiya ne ko mu hadaka da wanda zai kai ka Asibiti? Zaro idanu yayi yace" Wallahi zan iya nagode maka Yaro, da hanzari ya nufi motar tashi cikin karfin hali yaja motar yabar gidan..


Khalil ya kalli Abdul ya sake daure fuska yace" Waye yace kace mai ya tafi? Tsaki Abdul yaja yace" Yo ko marin Ashma yayi iya abinda zaka mishi , kuma kaga yayi nadama mai zai sa mu tsareshi bayan ga abinda yake fad'a maka Y'arshi a gida ita kad'ai.. Khalil baice komai ba ya mik'e ya nufi mota, ganin haka yasa Abdul yin murmishi ya bishi suka wuce a gidan...


*Nigeria*



Layla ce ta shigo palon tana kuka kamar wadda aka jefo ta" Da sauri Ammi ta rikota tana fad'in" Ke Layla lafiya kika shigo mana gida kamar wata sabuwar kamu? Zama tayi tana maida numfashi cikin tashin hankali tace" Ammi na shiga uku Daddy yace wai aure zai min ni kuma na kawo mishi wanda nakeso, amma yace bazai bani wanda nakeso ba wai Yaya Hisham zai aura min, Don Allah Ammi ki bashi hakuri" Ta fad'a tana k'ara sakin kuka... Wani sanyi Ammi taji saboda hankalin ta ba'a kwance yake ba ganin yadda Hisham ya shiga damuwa da auren nan, amma a fili tace" Haba Layla Yayan naki ne bakya so? Kin san kuwa me kike fad'a? Jinjina kai tayi tace" Ammi kiyi hakuri nasan baza kiji dad'i ba a matsayin ki na Mahaifiyar Yaya Hisham, amma na k'asa daurewa ne ina da wanda nakeso fa.. Ammi ta numfasa tace" To waye shi wanda kike son? Kanta a k'asa tace Abokin Yaya Hisham Doctor Khalifa shine wanda nakeso Ammi kiyi hakuri nasan kece kawai zaki dakatar da maganar nan..

Ammi tace" To shikenan yanzu dai abinda Za'ayi kije cikin dakinshi yana nan ki fad'a mai komai tinda Abokinshi ne zai amince ya janye maganar aurenki dashi.. zaro idanu tayi tace" Amma Ammi kina gani bazai koroni ba? Murmishi tayi tace A'a ba abinda zai miki maza jeki.. Duk abinda suke fad'a akan kunnen Rufaida taji dad'i da Layla tace bata son Abie d'in ta tinda shima dama biyayya ce zaiyi ya aureta. Tana shiga dakinshi da sallama ta sameshi zaune yana duba wasu takardu" D'agowa yayi da mamaki yana kallon ta sai kuma ya saki fuska yace" A'a Layla kece yau a D'akina? Murmishi tayi ta zauna tana k'arewa d'akin kallo. Aje takardun dake hannun shi yayi yana kallon ta, saboda duk yaji abinda suke fad'a ita da Ammi, yasan raba mutum da abinda yakeso abu ne mai matuk'ar ciwo dan haka bazai bari ya raba wannan soyayyar ba.. zatayi magana yace" Ba sai kince komai ba Layla duk naji abinda kika fad'awa Ammi. Cikin rawar murya tace" Don Girman Allah kayi hak'uri Yaya Hisham Abokin ka shi nakeso ba wai dan bana son auren ka bane ba, ni kallon Yaya nake maka kuma Abokin Mijin da nakeson aura. Murmishi yayi ganin yadda ta durk'usa a gabanshi sunkuyawa yayi ya mik'ar da ita, hannu yasa ya share mata hawayen yace" Ya isa haka ki dena kukan ni da kaina zanyiwa Daddy maganar har shi Kawun ma, kuma Khalifa shi zaki aura karki damu kinji K'anwata. Cikin jin dad'i ta fad'a jikin shi tana kuka tace" Ka gafarceni Yaya Wallahi na kasa ne kuma Khalifa zai ke mana kallon maciya amana tinda kaima kasan muna soyayya, ina maka fatan samun Mace tagari mai hankali da nutsuwa. D'ago ta yayi yace" Ba komai Insha Allah Abokina zaki aura kinji ba abinda Kawu zai miki kar kiji tsoro ni zanje na mishi magana.. godiya sosai ta mishi san nan ta fita" Rufaida dake Palo tayi dariyar jin dad'i dan ba karamin jin dad'i tayi ba da za'a dena auren Abie d'in nata, tace" Anki Abie na ko Anty Layla? Murmishi itama Layla tayi ta fice a gidan ranta fess Hisham ya fahimceta..



_Niger_



Bacci take amma tana juya kai alamar dai mafarki takeyi" A firgice ta farka tana zare idanu, gefenta ta kalla sai taga wata katuwar Mage" Ihu ta sanya ta diro daga kan gadon ta fita a guje ta wuce Khalil da su Mamy a palo" Cikin tsananin Mamaki da Al'ajabi Mamy tace" Kai maza ku bita wannan bata hayyacin ta. Da sauri suka fito ita kuwa tuni har ta kusan isa bakin get,Da karfi Khalil yace" A'a kada ku bari ta fita maza ku rike min ita" Ya fad'a hankali a matuk'ar tashe...







_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_