15
_*🌻ABBA NE 🌻*_
_Hakkin Mallakar_
_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
_*Last free fage🤸🏻♀️🤸🏻♀️ Yan amana kada ku bari a baku labari domin yanzu aka fara wasan, littafin #300 kacal, ga masu buk'atar cigaba da karanta wannan littafin sai ku tuntubi a no. +966599791573*_
Zaku iya turo kudin ka wannan asusun👇🏻
Account number 0003187186
Name account, khadija Salisu
Name Bank, Ja'iz Bank
_Sai kiyi screen shot ki turo shedar biya ta wannan number 👉🏻+966599791573_
بسم الله الرحمن الرحيم
1️⃣5️⃣
Cikin kidima Mamy tace" Kha..Khalil meya samu Ashma ne? Captain Abdul dake bayan Khalil ya iso cikin palon yana kallon su, ganin Khalil din ba k'arasa shigowa zaiyi ba yasa Sanjina ta k'araso inda yake tsaye da sauri ta amshe Ashma tana kuka ganin yadda ta saki jiki kamar gawa, cikin tashin hankali tace Ma chérie na (Masoyiya ta) meya faru dake haka? Mamy ta kama ta suka kwantar da ita ko wanne jiki a sanyaye suna ta kallon Ashma.. Da k'yar Khalil ya k'araso cikin palon jiki ba lakka" Inna ce ta fashe da kuka tana tab'a jikin Ashma tace Wannan kaddara data fad'a miki Shalele na Ubangiji ya tsinewa Aljannun nan tinda basu da imani, gashi da yake suna da wayo da an soma karatu sai su gudu yanzu wa zai iya auren ki idan aka fad'a mishi lalurar nan taki? Sai kuma ta sake fashewa da kuka har da dafe kai take. Zama yayi a kan kujerar da Ashma ke kwace ya kai hannu yana janye mata gashin kanta da ya rufe mata fuska. Mamy tace Wai Abdul yaushe kuka shigo gari har kuka je Ècole(Makaranta) din su Ashma? Shima zaman yayi duk ranshi babu dadi yace Mamy Wallahi shugowar mu kenan ko gurin Oga bamu nufa ba ,mun dai iso Office d'in mu, ko fita bamuyi ba a motar aka kirani a numéro din école din su Ashma suke sanar damu cewa ai ga Ashma nan tana kurma ihu tana kiran Abban ta ta fita a guje. Hankalin mu a matuk'ar tashe muka tambaya yanzu tana nan suka ce ai basu san inda take ba" Hakan yasa muka kara shiga tashin hankali muka sanya aka watsa photunan ta duk wanda ya ganta kar ya barta ta wuce ya rike mana ita.. Nida Khalil muka nufi hanyar école(makaranta) din nasu muna ta duba ta ko zamu ganta har cen mukaje sai muka samu Malaman nasu a tsaye duk suna jimamin fitar ta, saida muka tambayesu basu ga hanyar data bi ba? Shine wata a cikin su ta nuna mana hanyar data bi, muna ta yawo a gari cen a wani Unguwa muka hango ta zaune a wata bishiya tana kuka, ga kuma wani Mutumi ya tsare ta ya daure mata kafaru da hannu.. muna isa yake ce mana ai yana zaune yaga an nuna ana neman ta ,to ya fito zaije kasuwa sai ya ganta anan zaune shine ya mata wayo ya daure ta. Godiya muka mishi sosai na bashi jika goma san nan muka nufo gida dama tin kafin mu dauko ta da taga Khalil, sai ta shiga kiran shi tana nuna mishi hannunta ana since ta ta suma...
Mamy tayi tagumi tana kallon Ashma tace Allah sarki Allah ya baki lafiya wannan ciwo naki mun kasa gane kanshi" Baba da ya shigo da Malam Nafi'u ne yace Ameen. Juyowa sukayi suna kallon su, Baba ya zauna a kusan Mamy yace ku rike ta mu samu ta farfado.. dauko ta Khalil yayi ya kara kunnen shi a hancin ta yaji kamar dai bata numfashi" A firgice ya jijjiga ta yana fad'in" princess! Ashma! ki tashi karki min haka karki sa na kasa cika alkawari Ashma,ki tashi.. Ganin kamar ya fita hayyacinshi yasa Abdul amshe ta yace ba fa mutuwa tayi ba bari kaga a soma karatu zata tashi.. Malam Nafi'u ya gyara zama ya dauko wani ruwa ya soma addu'o'i, bayan ya gama ya watsa a fuskar Ashma. Wani k'ara ta kwalla wanda ya cika palo, Khalil kuwa a zabure ya mik'e ya warce ta daga hannun Abdul yana kallon ta . Inna da tayi jugum tace ka bari a mata karatu ko ta tashi" rungume ta yayi yana kallon Mamy da itama shi take kallo tana kissima abubuwa da yawa a zuciyarta.. karatu aka soma yi mata sai kururuwa take kana jin Karan kasan ba muryar Ashma bace, cen bayan wani lokaci ta saki jiki sai kuma ta soma kuka. Da sauri Khalil ya d'ago shima kad'an ya rage hawayen da suka cika idanun shi su zubo" Cikin wani irin kalar yanayi mai wuyar fassarawa yace" Ashma na! Bud'e idanun ta ta somayi waro su tayi ganin a jikin wanda take, Tashi tayi zaune tana dariya sai kuma ta sanya yatsar ta biyu da ta saba sha ta shiga tsatsa tana kallon Abban nata ba ko k'iftawa, mamaki ne ya kama ta ganin Abban nata .. Malam Nafi'u yayi musu Sallama ya tafi gida. Inna tace Alhamdulillah sannu kinji Yar lelena ya jikin naki? Ashma ta turo Baki duk da yatsun ta na cikin bakin nata hakan bai hanata turo bakin ba, tace Inna lafiya ta lau fa, sai kuma ta kalli Khalil tace Abba yaushe ka dawo? Wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke yace" D'azu nazo my princess tashi kije kiyi wanka sai muci abinci. Mak'ale kafad'a tayi tace ni ba yanzu zanyi ba" Abdul yace Princess wato ma ni baki ganni ba ko? Juyowa tayi ta sauka akan ciyar Khalil ta dawo kusa da Abdul tana dariya tace Papi na sannu da zuwa. Kuncinta yaja yace Yauwa kije kiyi wanka kinji sai muci abinci tare mu duka kuma zamu je wayo dake dani da Abban ki. Ai da sauri ta mik'e tana wash Abba jikina ciwo yake. Khalil yace Ai dama nace kiyi wanka zaki dena ji yi sauri ki fito.. ficewa tayi Sanjina ta bita a baya dan ta fito mata da kayan da źata saka..
Mik'ewa Khalil yayi ya nufi wata k'ofa, ganin haka yasa Abdul binshi yasan halin ne zai soma. Ai kuwa ya sameshi ya kifa hulashi a fuskarshi sai sauke ajiyar zuciya yake yi. Zama yayi a gefen shi yana sauke hular ganin hawaye a idanun shi ya girgiza kai kawai. Cikin dauriya yace Wai kai baza ka dena kukan nan ba Khalil? Kullum sai ka sato jiki kazo nan kayi kuka meye haka kamar ba Soja ba.. D'agowa yayi yana goge hawayen shi yace baza ka gane halin da nake ciki bane Abdul! Ka sani princess amana ta ce bana son na kasa rike amanar da aka bani ne, gashi tana cikin wani hali Kullum damuwa ta guda ce idan har ta tafi école bana iya sukoni sai naga ta dawo lafiya, yanzu ta fita da gudu tana yin wani wajan, ya kake gani ranar da kowa bai ganta ba inta fita? Ajiyar zuciya Abdul ya sauke yace Pardon(kayi hak'uri)Khalil Insha Allah ba abinda zai sameta kuma zata rabu da wannan ciwon kayi hakuri kaji ka dena sanya damuwa a ranka kaga Doctor Ma'aruf yace jinin ka ya hau sosai ka rage tunanin nan don girman Allah" Abdul ya fad'a yana dafashi.. Khalil ya mik'e yace" To shikenan zan rage bari naje nayi wanka. To Abdul yace shima ya koma ya nufi dakin shi....
Wani Matashin Mutum ne ya juya baya da alama waya yake, fuskarshi cike da damuwa yake fad'in" Ranka ya dad'e yanzu haka Yarinyar bata jima da barin nan ba tare da Uban nata kai kaga yadda ya susuce kamar zaiyi hauka! Gaskiya yana mata so fiye da tunanin ka. Shuru yayi yana sauraron abinda ake fad'a sai gyada kai yake yana cewa" To insha Allah zan kara himma akan wadda nakeyi, duk da nasan ana bata tsaro na gàban kwatance amma zan kokarta nima naga komai ya tafi yadda ka buk'ata. Shuru yayi cen kuma yace Holle Madam ki kwantar da hankalin ki zanji da komai babu wata matsala, ina dai tunanin ciwon Aljanu gareta, Shuru yayi sai kuma ya gyada kai yace to shikenan sai anjima daga haka ya kashe kiran...
*Nigeria*
Rufaida ce ta fito daga School waya a kare a kunnen ta tana maganar har da dira k'afa, ko ba'a fada ma kasan da Abie din ta take magana" Cikin shagwab'a tace" Abie Wallahi na sake ganin Pictures d'in shi, sunan shi General Khalil Umar mai Nasara kuma dan Niger ne" Nidai ina sonshi ma kawai tinda yana kama da kai. Dariya tayi sai kuma tace Abie wai baza azo a dauk.. Bata k'arasa fad'in maganar ba ganin Maza biyar a gabanta ko wanne ya rufe fuskarshi da mask sunyi mata banga-banga. A firgice ta kurma ihu tana ja da baya cikin kidima tace Abie wasu sun tareni a hanya kazo karsu kashen.. kafin ta k'arasa wani ya shaka mata fauda tuni ta saki jiki suka dauke ta amma duk da haka wayar na rike a hannun ta gam.... daga cen b'angaren Hisham a matuk'ar razane ya mik'e tsaye yana fad'in Daughter! Waye zai kasheki? Shuru yaji ba amsa a hanzarce ya fito sukayi kicibus da Khalifa a hanya. Cikin mamakin ganin yanayin shi yace" Hisham lafiya dai na ganka a firgice? Ba lafiya ba Khalifa muje School dinsu su Daughter tace min wasu sun tare ta muna cikin magana kuma naji tayi shuru, ina jin tsoron su cutar min da ita.. Da gudu suka k'arasa isa bakin mota ba b'ata lokaci sukayi bar Asibitin...
Suna zuwa school din suka samu ba kowa sai mai gadin shima yana hirin wuce, da hanzari suka iso wajanshi suna fad'in" Baba Don Allah ko kaga wucewar Rufaida Hisham? Mai gadi yace gaskiya ban ganta ba yanzu dai, na ga dai lokacin data fita to sai naji ta kwalla k'ara sai na nufi wajan amma ina zuwa naga ba kowa sai naga alamaŕ gurin kamar anyi kokowa a wajan... Hisham daya gama rikicewa yace Ina ne, jansu yayi ya kaisu har gurin ga kuma sawun mota, ji yayi kamar ya kurma ihu kenan sace mishi Y'a sukayi? Da sauri suka bar wajan tin a mota Hisham ya kira Yan sanda ya fad'a musu an sace Y'arshi, cikin girmamawa suka ce zasu bi lungu da sako sai sun dawo mishi da Y'arshi, godiya ya musu suka nufo gida...
Koda suka zo gida suka fad'awa Ammi da Daddy sosai hankalin su ya tashi Ammi ta ringa kuka da kyar Daddy ya rarrashe ta, Daddy ya kira D.P.O. ya sanar mishi yace nan da Yamma yakeson a dawo mishi da jikarshi, cikin girmamawa yace Insha Allah yanzu za'a binciko koma a ina take... Hisham kamar wani zararre haka ya zama cikin tsananin damuwa ya dafe kanshi to shi waye yake bibiyar Y'ar tashi? Tambayar daya rasa me bashi amsa.. da k'yar Khalifa ya shayo kan Hisham ya zauna a kan kujera" Sako ne sukaji ya shigo wayar Hisham, da sauri ya d'aga. Mik'ewa yayi yana fad'in what! Dukkansu kallon shi sukayi, Daddy yace menene aka turo maka? Mika musu wayar yayi hawaye na zirya kan kuncin shi yace Daddy meye abinyi kalli kaga yadda suka mata.. amsa sukayi suka danna video, Rufaida suka gani a daure an fasa mata goshi da baki sai kuka take tun karfin ta tana fad'in" Waiyo Allah Ammi kizo zasu kasheni! Waiyo Abie dukana suke ni ban musu komai ba! Daddy! Wani suka gani ya d'ago fuskarta yace maza ki musu magana su kawo kud'i inba haka ba mu kashe ki. Rufaida ta shiga girgiza kai tana cewa Abie zai baku ko nawa kukeso ku kunceni muje daku zansa ya baku" Ammi ta rushe ta kuka tana fad'in Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un kidnapping din ta akayi. Wayar ya amshe yana jin zuciyarshi tamkar zata Rabe biyu saboda tashin hankali. Tex suka turò mishi ya karanta, da sauri yace Daddy wai sunce gobe naje da kudi naira million ashirin na kai musu su bani ita.. Daddy yace ko nawa suke so a basu karsu mata komai.. fita Hisham yayi shi da Khalifa duk ranshi babu dad'i da kyar yake iya hadiyar yawu. ..
Ita kuwa Rufaida bayan sun sanya ta ta gama yin magana d'aya daga cikin su ya dannawa wata number kira, Ana dauka yace ranki ya dad'e gata mun kamo ta fa mun fad'a mai duk abinda kika fad'a.. dariya tayi daga cikin wayar tace so nake ku mata rashin mutumci wanda har abada Uban nata bazai manta da hakan ba, ku mata faďe iya son ranku idan kuka gama ku jefar ta a inda kukayi zaku had'u, amma fa sai kun dauki kud'in zaku jefo musu ita.. Cikin ladabi yace an gama zamu sha shagali nan ya kashe kiran" Kunce mata daurin sukayi Ogan nasu yace akai ta ďaki, daukanta sukayi tana kuka suka jefata kan gado. Ogan nasu ne ya shigo ya kulle k'ofar yana lashe baki, ja da baya ta shiga yi tana cewa A'a, A'a don Allah karka cutar dani za'a baku kud'in da kuke so, ihu ta sanya ganin ya fad'o kanta, a gigice ta hankada shi ta mik'e da gudu tabi wata k'ofa ta kulle.....
*Niger*
Mansoor na labe bakin dakin Daddyn shi yana jin abinda yake fad'a, a matuk'ar razane ya zaro idanu jin abinda yake fad'i, a guje ya fito Mommy na magana amma ya arce yana cewa zan dawo Mommy yanzu" Daret École din su Ashma ya nufa hankalin shi a matuk'ar tashe sai cewa yake lalle Daddy nine ajalin ka indai har yaran ka suka kashe min Ashma na..
Abdul ne ya shigo Office d'in Khalil bai tsaya yin komai ba ya damki hannun shi yace maza muje Yanzu nake samun labarin an tura wasu zasu kashe Princess kuma kasan tana École ga yau masu tsaron nata basu je ba. A kidime Khalil ya mik'e suka shiga mota, a 380 Abdul ke jan motar hankalin shi gaba d'aya baya jikinshi, wayarshi dake kafad'a ya ciro ya danna ana dauka yace Hello Captain ke magana maza kuyi sauri École d'in su Ashma idan kuna wajen, To sukace ya katse kiran...
Suna isowa Mansoor yana isowa, suma Wanda aka turo sun iso tuni wani ya saita k'irji Ashma amma idan zai harba sai ta juya wani gefe. A guje Mansoor ya iso tin kafin yazo yake cewa Ashma maza ki tàshi na kaiki gida, ki tashi karsu zo su kashe ki.. Abdul ma a guje ya nufi inda yaji ana kiran sunan Ashma suna isowa sukayi ido Hudu da Mansoor da yake cewa ta tashi kar su kashe ta. A guje Khalil ya nufe ta ko kafin ya iso tuni mai harbi ya sakarwa Ashma alburusai har sau biyu daya a kafad'a d'aya a gefen ciki.. wani kalar kara Ashma ta kwalla ta zube a k'asa yaraf" A k'arfe Khalil yace A'a Princess! Ashma! Ya fad'a da karfi yana k'arasowa inda take....
_TOFA WASA FARIN GIRKI YANZU MA AKA SOMA WASAN._
*Shin Ashma ta mutu ne?*
*Shin Rufaida zata iya Kubuta daga hannun Azzalumai?*
*Wani hali Khalil zai shiga?*
*Shin Mahaifiyar Ashma da ta Khalil suan raye kuwa?*
duka wannan amsoshin sai ku biyo Maman Nusaiba domin samun su, Littafin naira N300 ne only Hajita karki bari a barki a baya
_*Nice taku har kullum Maman Nusaiba*_