FURUCI NA NE

6

by @hauwaausmanjiddarh

*FURRUCI NA NE*

( *rikicin babban gida*)




 *BATUL ADAM JATTKO* 


*rikicin babban gida*



Humairah sai sake maimaita SA'A YAFI GATA take tace wato tana nufin Nasrim y'ar gata ita me sa'a 

ko Wllh sai ta san tayi da y'an halak ba marassa asali butulu ba shikuma ya Agrif kin barshi kenan bari na har abadan Allah zai baki wanda yafishi in Sha Allah zakiga ri ban hakuri".

Izza da zata shigo d'akin K'iran Nasrim taji duk abin da suke fada komawa baya tayi ta tsaya a dan korodo tana murmushi tana danna wayan ta tana ne man hoton Agrif tasamu Wanda yayi kyau sosai ta daura sabon a status dinta ta rubuta 

_samun irin ka zayyi wahala Dan ba a b'ari akwashe d'uka_


sai wani da tasake rubuta 

_sai Dana tace na_

_zab'oka aduniya Kai ne gayya mazaje kubi baya babu rinka na duba duk nahiya_


gashi dama duk ta rufe manyan gidan kafin ta d'aura status ta yanda ba zasu ga status din taba sai su Humairahn da tayi domin su kuma gashi sak'on yaje inda take bukata tayi murmushi a san data ga alaman an bude sabon status din a wayar Humairah 

dan dama basu fita a status din ba tana tsaye sai da taji  Zahra tace'' to ai gawani ma".

 bayan sungani Nasrim ta dafe k'irjinta

 tace ''lalle Izza bata san zafin so ba bata san rad'adin rabuwa da masoyi ba da baza tamin haka ba saide tamin addua duk da gaskiyar ta ba a b'ari akwashe duka hakan bazai hana tamin addua mafi alkairi agun Allah ba tunda Allah yayi duniya da fad'i kuma gaskiyar ta samun irin ya Agrif akwai wahala wacce ta samu dole takira kanta me sa'a kun man ta nida irin rawan kan da nake akan sa azatona Sona yake ai ni abinda nayi ya wuce nata amma yanzu duk wannan abinda yake faruwa bai kamata ba bana son mu samu matsala da Izza dan halinta na kirki da Kamala dan kuskure daya bai kamata kuna mata wannan fassaran ba

ba danni ta daura duk wannan kalaman ajikin hotunan ba giyar so ne kawai ni nasan waye ya Agrif yafara rud'atane da soyayyar sa mezafi amma kar kuyi zaton dani tayi hakan zargine bai kamata ba muyi kokarin dawo da Izza cikin rayuwar mu kamar da muzauna lafiya kada iyayen mu Susa wani abu aran su".

Humairah tace'' haba Nasy ke baki fashimci zafin kalaman ta ba ko? whll habaicine ki duba wannan wanda ta saka na k'arshe nan mana".

ta k'arashe maganan tana mek'awa Nasrim wayan Nasrim ta k'arba ta karanta afili 

 _yanda Allah yaso lamarin sa yabar da mun ku yan da duk ya tsara ba mai iya juya shi_

"kinga me take nufi da wannan su wa abin ya dama bamu k'adai ba har iyayen mu wllh hadin ku suke so bana Izza ba musamman Ummu wllh kowa yagan ta yasan ta damu da abin 

Ita kuma Izza taci gaba ni me iya zuwa na zuga Hajja ce wllh takafa k'aramin yak'i afasa".

dariya Zahra tayi tace kin manta wacece Izza agun Hajja ko"? 

Nasrim tace''nace kubari".

sai asannan Izza ta tura kofar ta shiga bakin ta dauke da sallama cikin nutsuwar ta jefa kanta tayi akan bed a rufda ciki tana murmushi ta d'ago kai tana kallon Nasrim da tarame sosai cikin kwanaki biyu

tace" Nassi kije inji my heart". 

taja my heart din da siririn murya irin yanda Nasrim takeyi a da tana lumshe idon tare da cigaba da murmushin ta 

Nasrim 

bata juyo ba tace'' gaskiya bacci nake jifa nasan ma aiki zai sani kawai kice baki ganni ba".

"Okay".

tace tare da mek'ewa ta fita wayar Nasrim ne yayi ringing da sauri ta dauka ganin my best bro ne wato Kamal cikin sanyin murya ta amsa sallaman sa tace "Yaya yaushe zaka zo"?. My best sister ina Camaro yanzu haka insha Allah yau zan zo daddy ya gaya min komai abin da yafaru da har nayi shirin daukan mataki daddy yace a a ina miki fadan alkairi sis farin cikin ki shine nawa bani da y'ar uwa ko dan uwa ciki daya sai ke abin yabani mamaki shikan sa Agrif dazu dana kirashi har da kukan sa yana cikin damuwa sosai ni sheda ne akan son da yake miki ban san meya sameshi ba amma insha Allah k'anwata kece da nasara babu rashin sa'a ko rashin nasara a 3brother kinji zakiyi nasara ki kwantar min da hankalin ki kafin nazo".

ba tasan sanda ta fashe da kuka ba dan dama ta sabayiwa Kamal shagwab'a sosai lallashin ta yayi tayi 

tana zaune cikin gerdeng akan wani kujeran k'arfe tana sanye da goguwar riga yellow an masa ado da bak'in duwasu ta d'anyi nisa cikin karatun da takeyi dan sunkusa fara exam jin k'amshin turaren sa yasa ta dan shafi hancin ta da hannu amma bata d'ago ba shima kujera yaja ya zauna yana cigaba da kallon ta kusan mintuna 2 sannan ya sauk'e wani ajiyar zuciya me nauyi cinki cool voice dinsa yace

 " Halima. bata d'agoba amma tabar karatun da take kuma da alaman shi take sauraro yasake cewa "Halima".

ahankali ta d'ago fararen idonta ta zuba cikin nasa still yasake cewa "Halima where is you phone".?

batayi magana ba amma ta dauko wayar da yake cinyar ta

 ta nuna masa 

"Ok ok horon har yakai ga haka kin sani a

black list why ? kin san yan da kika azaftar da zuciya ta a tunanina ko meye zaki gaya min bani da kamar ki a duniya bayan uwar data haifeni kisa aranki a mata ba wanda zata kai ki daraja zaki iya sarrafa rayuwata yanda kike so ko zaki min horo da komai kar kimin na rashin ganin ki ko jin muryar ki wllh shine abinci na bana son ganin ki cikin k'unci da rashin walwala shine dalilin da yasa bazan iya auren kiba saboda nasan in akace nine mijin ki wataran zan sab'a miki ayanzu nafison kiyi ingantaccen rayuwa ta yanda duk mijin da kika aure inya tsaba miji zan zame miki garkuwa hakan zaifi duk da kowa yasan ke cousins dina ce kuma ina da daman fitowa auren ki kowa yasan there is marriage between us so confusing people 

Amma but sai de nace kiyi hakuri dan Allah ni ba amatsayin cousins na dauke kiba tamkar yanda kuke da Kamal haka nake daukar ki tamkar Humairah please amma...

"Stop ya Agrif ai nima ban taba cewa ina son ka da aure ba".

 ta dakatar dashi dan Magan ganun sa sunfara isar ta shuri yayi yana kallon ta 

ta numfasa 

cikin sanyin murya tace" hope de ba Izza ta amince ba to ai fatan mu kenan kuma nagode sosai da soyayyar ka nima Ina son ka kuma bazan canza ba ina matsayin cousins din ka zanyi duk yanda kace.....

tana cikin maganan taji kawai yayi wani irin hugging dinta yana wani irin kuka cikin tsoro take kogarin kwacewa amma abin ya gagara "Nasrim ki barni naji dimin jikin ki abin da najima ina rayawa ne ashe na kasance bani da rabo Nasrim tunda na furta bake nake soba ban samu sauk'i ba sai yanzu da najini a jikin ki sai yanzu naji hawaye na yazubu abinda nake mutuk'ar buk'ata kenan na samu nayi kuka ashe kuka ma rahama ne Allah kabani karfin gwaiwar sadaukar ta".?

jin yafara shafata yasa taji wani irin k'arfi yazo mata tunk'ud'ashi tayi kefe da gudu tayi cikin gida 

cikin yan kwanakin Hajja ta matsa sai da aka zo neman auren Zahra da Humairah Zahra Aliyun tane da suke soyyya sai humairah Ayman d'an gidan Dr hafsa Abbaty yayi tsalle yadire shide bai isa aure ba Aiban ko k'asar ma yakasa zuwa agogon sarkin aiki kenan

Hajja sai data matsawa mommy tace tasa Nasara yasa ranan zuwu

*********************

zuwan Nasir da kwana ukku Hajja ta kasa cemasa komai ganin har yana shiren komawa bayyi maganan Nasrim ba yasa Agrif yasame shi da batun yafito yanemi soyayyar ta kafin yatafi tunda Hajja ta kafe dole da Nasrim za ahada auren Humairah da Zahra da Izza


zaune suke cikin gerdeng su biyu da alamun de tattaunawar tasu batayi musu dadi duk kan su biyun cikin b'acin rai Agrif yace " to wllh baka isa ba wai me Nasrim tai maka a rayuwa har haka da kake son rayuwar ta 

ta dauwwama cikin bak'in ciki".?

Nasir cikin isa yace " tamin abubuwa da dama kuma idan kaga Nasrim taji dad'in rayuwar duniya to nikuma bana raye wllh bata isa ta auri mutum sak kamar kai ko wani gaye da ya amsa sunan sa guy ba shine dalilin da yasa na dakatar dakai kuma na baka umarnin ka nemi Izza dan nasan itace aminiyar ta ko da kagane ba auren ta zanyi ba to baka isa kadawo kana son Nasrim ba amma bawai ni zan aureta ba kafin na gama nazarin wanda ya dace da mummunar rayuwar ta da gan-gan na turaka gun k'awata 

ka gane ko ina son kane kuma ko mak'iyina bazan masa fatan auren Nasrim ba saboda ni nasan me na kullawa rayuwar ta balle kai dan duk wanda yayi kuskuren auren ta to ya gurbata rayuwar sa gaba daya ".


dariya Agrif yayi yace " baka isaba kuma ka dena kiran rayuwar Nasrim da mummunar rayuwa domin ita din bata masan kanayi ba kuma ni Haruna nine mijin ta in Sha Allah ai ba dauramin aure da Izza akayi ba na fasa kuma zaka ga yanda zan canza aure na yakoma kan Nasrim".


 Nasir murmushin sa na gefen baki yayi wanda ya keyin sa idan yaso mugunta ya mek'e tsaye ya dafa kafadan Agrif yace " okay ban hana ka ba amma kasani muddin ka auri wannan yarinyar bakai ba kiran kanka a cikin 3brother bayan nayi fired dinka zan maka sherin da zaka dauwama a gidan prison na har abadan kaga sai tabika kuyi soyayyar a can amma har yanzu Ina warning din ka kafita daga har kanta ba baraza na kena maka ba na kuma Mai maita wa wannan FURRUC NA NE".

shima Agrif cikin fushi yace

"bazan fita a har kan nata ba Nasuru ka koreni a aiki mana ai ba tun yau ba nasan kana ta k'ama da dukiya to kasani Nasrim tafiye min komai na duniyar nan kuma zaka gani ba abin da zai samemu da sherrinka".

Yana gama fadan haka ya kwashi wayoyin sa yayi hanyar fice a gerdeng din 

Murmushi Nasir yayi yace "zan baka mamaki ai ba aiki zan koreka ba dena amsa sunan 3 A full zakayi". 

shide Agrif bai juyo ba ya k'arasa ficewa 


******************

a hankali take takawa daga part din mommy zuwa nasu daga sama taji sauk'ar ruwa me sanyi a kanta cikin sauri ta d'aga ido ta ga wane isheshen ne zaune ta gansa kafa daya akan taya yana aikin zuk'ar taba tsigari gefe da gefen sa yan mata ne fararen fata a tsaye cikin bad dress 

kafin ta gama tan_tan ce waye taji an jeho guntun sigar cikin bakin ta da sauri ta tofushi tana murza leben ta inda ya k'one cikin fusata taja baya dan tagan shi da kyau to waye shi kaman taso ganiwa amma bata ganin fuskan sa sosai gashi yana sama kuma idon sa acikin bak'in glass Wannan din waye shi? tace afili kawai sai tajuya takoma part din mommyn banko kofar tayi mommy tagani a dining room batayi mata magana ba ta fara taka steps mommy tace'' ke Nasrim ina zaki hakan?".

"Mommy wani d'an iska ne a sama ya zubo min ruwa ya jefa min guntu sigari shine zanje na duba d'an uban waye shi".?

cikin tsoro mommy tace'' Nasrim Yayan ki nefa".

"Mommy Yayana kuma? ni kaf cikin yayuna ba mahayin taba ba mane min mata wasu turawa nagani da bad dress a sama....

sauran maganan ne ya mak'ale mata saboda wani irin shak'a da taji a mak'ok'oron ta 

"mommy cikin in in na tace'' dan Allah my Son kayi hakuri bata san kai bane afuwan".

"cikin dakiyar murya irin tasa yace "ai shine yanzu nake son ta sani tasan ni d'an uban waye na kuma tabbatar dani D'an iska ne"..

Mommy tace dan Allah kayi hakuri nace".?

"Wllh mommy yau sai tasha giya tasha taba sannan na hadata da alade ta kwana dashi kinga ta zama cikekkiyar y'ar iska ko".

da k'er har Saida mommy tasa kuka ya hakura ya barta amma yace zasu sake haduwa ta guji haduwa na biyu dan baya yafiya". 

Mommy tace'' insha Allah baza ku haduba yanzu mafa data shigo sai da nacewa Barira tace bana nan kar ta bari ta shigo ai idan kana gida bana bari ta shigo kayi hakuri kaji my Son".

sakin ta yayi ya juya ya haye upstairs cikin b'acin rai 

Nasrim ma cikin b'acin rain tace "mommy dama kina gida kika ce ace bakya nan saboda wani banza mommy na bar masa ke nikuma har abadan bazan k'ara ahigowa part din ku ba".

dagudu ta juya ta fice  


**************

Aiban da Agrif 


"Aiban dan Allah kaine kadai zaka iya temakona kamin wannan alfarman". 

shiru Aiban yayi can ya sauk'e numfashi yace'' haba Agrif meyasa da kasan Nasrim kake so kace Izza yanzu Koda nace inason Izza ai iyayen mu bazasu yarda ba kuma yazama kamar wasa da hankalin sune ai".

Agrif yace"ni amin cewar ka kawai nake buk'ata nasu me sauki ne zuwa zakayi gaban Hajja kazube kana kuka kace ai Izza kake so nasan tana sonka zata amince kuma amincewar ta shine amincewar kowa nikuma idan aka tambayeni zance na sadaukar maka da ita zan tafi karatu course  na watanni tara kafin nazo kunyi aure kuma kafin nazo nasan yanda zanyi na shawo kan Nasrim".

Aiban ya girgiza kai

 yace "zanyi hakan saboda farin ciki ka amma ba dan Izza tamin ba".

**************

Hakan ko akayi Aiban yazube gwaiwoyin sa a gaban Hajja yana kukan shi idan bai aure Izza ba zai mutum Hajja uwar son jikoji kodan basu da yawa nan danan ta gigice ta tara mutanen gida ta tambayi Agrif zai iya hakura ya barwa k'anin sa da gudu ya amsa eh 

 Hajja tayi ta sawa Agrif albarka akan sadaukar 


Izza zaune a d'akin Baban ta tace'' Baba kaji shawaran da suka yanke ko".?

Mustapha yayi shiru 

can yace " eh Izza amma abin da yafi bani mamaki akwai maganan aure tsakanin ki da Agrif ga kuma shima Aiban za ayi auren abin yana rudani har yanzu na kasa tan tance wa gashi de ina gani har da rabon haifuwa a tsakanin ki da Aiban to na kasa gane yanda Agrif ma yake ta k'iftawa ta tsakani".

Izza tace " Baba kawai Ina ga maganan da d'in kake gani".


gir giza kai baban Izza yayi yace' ah ah bana baya bane akwai rud'adi sosai amma kar ki damu zanji da komai".


Izza tace" nifa Baba hakan yafiye min ma Aiban yanzu na gama gane Aiban yafi kowa aiki dukkan account din dukiyar gaba daya yana hannun sa dan shine aban garen kudi sai yagani yake turawa Nasara ma ni shakan ma yafi dan kana ganin Aiban gaka Naira".


dariya Baban yayi yace' ai ni nayi aiki akan Wanda yafi kudi yazama shine mijin ki yanzu de abin da yafi damuna wannan maganan Agrif din".

Izza tace'' kai Baba rabu dashi ayi abin da zai fita a rayuwata in ma sona take".


***************

a ranan aka sa ranan daurin auren Aiban da Izza Humairah da Kamal zahra da Aliyu sati biyu kacal dan Aiban yace bazai bar k'asan ba har sai an daura auren 

Nasir yakoma Agrif ma haka fadan shagalin da akayi a bikin b'ata lokacine Agrif yazo bikin amma Nasir bai zoba Agrif tun a na shagarin yake ta faman tura kansa wajen Nasrim amma ba fuska acikin gidan aka ajiye Izza da Humaira dayake Hajja tace duk ka jikokin ta 5 anan zasu zauna da matan su dan haka gidan Izza da Humairah ajere suke Aiban bayan gama cin amarci yakoma India yabar Izza saboda makaranta Izza kam ta taka matakin da take so aburin ta dan Aiban me bushasha ne motocin da ya saya mata ma abin kallon ne tana fasa kai yanda take so cikin k'awaye fiye da yanda Nasrim takeyi 

******************

*bayan wata 2*

Izza ta kalli Nasrim tace'' haba my sister amma idan kikace haka bakiyiwa ya Agrif adalci ba kuma akaran kan ki maki duba mun tashi mu hudu duk kan mu ukku munyi aure ban da ke."

Nasrim tace'' lokacin kune yayi nikuma ahalin yanzu bani da wani space da zan ajiye namiji kingane musamman Agrif bana buk'ar sake jin wannan ke da mijin ki kune masu yimin wannan dan ya Kamal tun so daya da yakawo min yaga ba fuska bai kara ba amma ya Aiban da ya Abbaty sun nace min har nadena mude message din su".

Izza tace

"to naji dan Allah tunda yace alfarma ya nema kimasa alfarma Koda na iya gaisuwar ne gashi ma a falo dan Allah ki fito".

da k'er Izza ta shawo kan Nasrim ta samu Agrif a falo Agrif kam awanan Karan da k'arfin sa da kalamai masu zafi yazo bai sha wani wahalan shawo kan Nasrim ba duk taurin kai irin nata 


Numfasawa tayi tace'' shikenan amma kasani ina da dokoki".

'ki fadi ko wacce iri yace inde zaki yarda ni Agrif ina son ki".

 tace

"na farko deni ina da kishi duk mijin da ya auri Nasrim to yasa a ransa tamkar ya auri mata hudu ne dan daga ni ba k'ari ina da kishin azaba wanda ni kaina ban san iyakar sa ba".

Murmushi yayi ya sauka daga kujeran yazuba guiwowin sa k'asa yace" inde wannan ne mai sauki ne ba mata hudu ba na sawa Raina ke a masayin mata dubu kike a rai na ke daya ce azuciya ki rik'e ki aje ".


murmushi tayi tace'' Allah ya Ag wllh ba dan ina mutuwar son kaba wllh ba zan sake yarda da kai ba dan ina da kishi sosai a gabana kece kai Izza k.....

rufe mata baki yayi da tafukan hannu sa yana dariya  

*************

Hajja tace'' ikon Allah ai ni dama nasan iskanci ne irin na yaran zamani amma Agrif ai na Nasrim ne kunji irin iskancin da yadinga min ne wai wllh shi de cikin satin nan ya keson adaura masa aure daddy yace "gaskiya Hajja ba wani abin da yarage banda a daura auren me za a saya jira a take aka sa ranan auren wata 1 

Nasir bai ji ba sai a status din Kamal ya gani alokacin ma ko suna tare da Agrif din a Dubai cikin riki cewar yanani yake kallon Agrif yace 

"Agrif bakaji gargadin dana maka akan yarinyar nan ba ko Wllh auren yariyar nan shine mummunar k'addaran ka na gaya maka ba matar ka bace ka nace".

Agrif cikin b'acin rai yace'' ni kuma na gaya maka baka isa ba Ina son Nasrim kuma baka isa hanani auren taba".

Nasir 

mek'ewa yayi tsaye cikin b'acin rai yayi taku ukku ya k'arasa Inda Agrif yake cikin sanyi murya yace Wannan shine Warning na k'arshe da zan maka Haruna kar ka auri Halima rayuwar ta ba shida kyu idan kasa taurin kai abin ba zai muku yau ba".

"Ai kai ba ubana bane da zaka sani gaba kana gayamin wannan Nasrim ce nan da sati biyu tazama matata". 

gyad'a kai Nasir yayi yana

murmushi yafara takawa na barin gun

tun daga wannan rana Nasir bai k'ara nuna cewa baya son aure ba har taya Agrif shidimar biki yake saura kwanaki biyun adaura suka sauk'a a k'asar da dinbin abokan su 

Dr Fanna kam awanan Karan tafito tanuna eh Nasrim y'arta ce kuma tayi rawan gani 

Safiyar jumma'a dinbin al'uma suka sheda auren 

Haruna Agrif Abdulrahaman da Halima Abdulmajid Nasrim

Justice Abdulmajid yatara mutane sosai 


da dare bayan sun kwanta Humaira da Izza yau a part din Mama zasu kwana saboda shidiman biki zahra ma tazo shine suka samu daman cewa anan zasu kwana dama daga ita har Izza laulayin ciki sukeyi shiyasa duk suka gaji 

Humairah tace'' nasy K'iran fa ake 

Nasrim da har tafara bacci tace'' kai wllh Ya Agrif bashi da hakuri tashi tayi zaune tace wai ni dukka aure haka yake ko nawa mijin ne bashida hakuri wllh dazu da mukazo a wajen diner dak'er na kwaci kaina awajen sa acikin mota ba dan nayi da gaske ba wllh komai zai iya faruwa shine fa yanace wai yanzu yanason ganina kuma wai a part din mu da akayi jere ina tsoro wllh me yasa bazayyi hakuri a kaini goben ba".

dariya Humairah da Zahra da Amira da Izza sukayi Zahra tace'' ai ko dole kije kinsan ya Agrif da rashin hakuri wllh zaki iya ganin sa anan ba da jimawa ba".

ma'rairaicewa Nasrim tayi ta kalli Amira da yake budurwa ce tace '' Amira zaki rakani kinga idan a gaban kine bawani abinda zayyi". grgiza kai Ameera tayi tareda jan blanket k'iran wayan ne yasake higowa Nasrim ta d'aga kai ta kalli agogo 11 30 na dare ahankali ta dauki wayan 

muryar Agrif taji yace "please waiting my wife wllh wasu abokai nane zasu tafi jirgin su zai tashi 12 dan Allah zakuyi sallama ne dasu".

cikin rawar murya tace "promise sallama kawar zamuyi na dawo ko".

 tsaki yayi yace "Because gani kura ko? har sai namiki alk'awari bar shi kawai nace baza ki samu daman fitowa ba". cikin sanyin murya tace

"Sorry my lovely husband gani".

ta mek'e da wayar ahannu tasaka shijab har k'ar akan rigan baccin ta  

ta fito ta k'ofar baya tabi tun daga nesa ta hangoshi yana sanye da k'ananan kaya t-shirt bak'i da yellow din wando duk da wajen bawani wadatar haske yana kallon ta har takusa ya lumshe idon tareda bud'a hannu ya mata alaman ta fado jikin sa 

hannun ta biyu tasa tadan tura k'irjin sa yadan yi baya yana murmushi yace " yarinya kinyiwa kan ki dan wllh bashin gobe ne".

tace'' naji nayi ta cin bashin ai bashi hanji ne yanzu ina bak'in?".

nuna mata cikin gidan yayi da yatsa 

cikin tsoro tace'' haba Yaya kana nufin cikin gidan zamu shiga.?'


"to meye acikin ba gidan mu bane".?

''eh ai ba akawoni ba kawai su fito nan muyi sallama shikenan Allah bacci nake jin".

shafa suman kansa yayi yana mata wani kallo yace "wannan dan k'aramin bakin fa najima ina da haushin sa". 

ya k'arashe maganan yana sama da ita ya nufi ciki sai turesa take tana masa gunguni 

A main parlour ya direta yana dube dube kamar me neman wani abu sai kuma yaciro wayan sa ya dan kira yace 

"na shigo ban gan kaba fa ok gani".

yace yayi hanyar k'aramin parlourn 

Nasir yasamu zaune k'afar sa daya kan daya acikin kujera ya raje hasken parlourn

 Agrif dukan kafadar sa yayi yace " big brother gata can na gawo maka ita da fatan bazaka razanar min da ita da wannan fuskar shanun naka ba amata nasiya a hankali wanda zai shiga jiki ni badan tafiya zakayi ba ai nasihar nan ba yanzu ba".

Nasir bai dago ba yana danna laptop din sa yace "please ga abin sha nan kafara kai mata kafin na dan gama wani dan abu".

Agrif ya kalli drink din yaga yakamata ya kai mata ko zata dan war tsake yayi murmushi yace  

"Ok ba lefi naga da bacci ma a idon ta ko tadan wartsake".

ya k'arashe maganan yana daukar kwalin drinks din yafita 

tana hangosa ta mek'e tsaye tana cewa ''suna ina ne".

Dariya yayi yace "Nasy wai me kike gujewa ne bakiji ance duk wayon amarya ba".

 ya k'arashe maganan yana mek'a mata lemon hannu sa kallon sa tayi sannan ta k'arba ta ajiye a kan table murmushi yayi yajuya ya dauk'o cup akan fridge ya dauki drinks din ya dan siyaya yasha yana kallon yanda take wani kame jikinta alaman tsoro yace '' to kin ga ni nafara sha sai ki cire shakkun ko nasa miki wani bu karbi ki sha". 

ya dire maganan yana d'aga mata giransa daya 

Murmushi tayi tace'' haba Yaya ai nasan bazaka cutar dani ba har abadan ta karba takai baki tasha sosai dan taji dadin sa har tasake kallon kwalin milik ne amma bata san sa ba kodan ita dama kayan shaye shayen bai dameta ba 

cikin wani irin hamma yace "ko ak'aro ya k'arasa maganan yana cilla kansa kan kujera ita ma dafa kanta tayi tana hamma ta bude baki da niyar zatayi magana da ganan taji shiru 


"why why why Muhammad Nasir meyasa baka kashe niba dawan nan tozarcin da kamin ai kwara ka kasheni Nasir ka lala tamin rayuwata kaci zarafina kaci amanar yar dan da namaka Nasir kayi zina da matata ta sunna aranan da aka daura min aure da ita ko sanin ta banyi ba ka rigani shiga d'aki da ita ka dauke min budurcin ta acikin d'akin aure na Nasir koma dame kake ta k'ama Wllh sai na dauki fansa baka isa ba kai mayaudari ne maci amana.....


Murmushi Nasir yayi yana mek'ewa tsaye tare da zuge zip din gaban wandon sa yace please Haruna nifa banci amanar kaba tun farko na gaya maka zaka tafka kurkure idan ka nace ka auri Halima dan nagaya maka bana son meson ta dan ita k'addaran ta bame kyau bane na tsara yanda zatayi rayuwa cikin k'unci wanda zata ce dama ba ahalito taba

Amma baka jiba ka nace wannan shine dan k'aramin taku acikin takun dana adana muku Agrif nayi warning din ka baka jiba rahama ne Allah ta'la ya nuna maka mak'iyinka sannan wawanci ne ka kasa tunanin kare ganka daga sharrin sa naso ka da rahama na sanar dakai abinda zai zama cuta agareka ai ni ban so kasha juice din nan ba sonayi nayi komai agaban idon ka amma sai nasamu kana bacci naso kagani dan nasan zaka tsane ta tsana na har abadan ita oganniyar ce bana son tasani ayanzu har sai na gama aiwatar tar da nufina akanta shiyasa na fitar da ita a hayyacin ta amma ina maka albishi da matar ka komai yayi zam zam ba wai kyan fuska da sura kadai Allah ya bata ba tana da sirrin boye wanda yafi na zashiri in ganci sannan k......


wani irin cakuma Agrif ya kai masa yafara dukan sa ta ko ina yana kuka yana Allah ya isa Allah ya isa Allah shi zai mana shari'a da kai a lashira".

Murmushi Nasir yayi yasa hannu ya kwace wuyar sa a hannun Agrif yana murmushi yace "ba sai kajira lashira ba ai Baban Halima ma chief justice ne na fison ka fallasa komai kaga kowa zai san ayanzu Nasrim ta haram ta agare ka hakan zai min kyau ni kuma".

ya k'arashe maganan yana kama handle din kofar 

cikin kuka Agrif yace koton Allah yafi na kowa shi zan kai ka lefin ka yafi k'arfin sha'ria da kai a duniya kuma idan nayi haka na tozarta gidan mu a idon duniya na tozarta rayuwar Nasrim daga nan burin ka yacika dan haka ba wanda zaiji ko ita bazan bari ta sani ba".

Nasir yajuyo cikin b'acin rai tabbas bai ji dadin yanda Agrif yanuna bazai fallasa ba 

Cikin d'acin rai yace to shikenan ni inada idda na akan Nasrim in har bata gama idda ba ko hannuta ban yar da ka taba ba yin kahan zai iya gurfanar dakai agaban kotu ina son sai tayi wata ukku kafin kayi zaman aure da ita san nan kasa aranka akwai b'acin ran da yafi wannan agaban ku....


yafita tare da bugo masa kofar 

ahankali Agrif yaja bargon ya k'arasa rufe Nasrim yakifa kansa ajikin gadon yana cigaba da kuka yanaji ana kiran sallah sannan yayi addua yana kallon Nasrim da take shirin bude idonta Nasrim yink'urawa tayi da k'arfi asan data fuskanci inda take wani irin zafi taji kamar ana yanka Naman k'asan ta wani irin rikicecen kuka tasa ka tana fisge hannun ta daga nasa "Agrif meyasa kamin haka? aure de an riga an daura hakuri kwana daya ka kasa har sai ka tozar tani kanunawa duniya wani abin jikina kake so bani ba sha'awa ta kawai kake har ka kasa hakurin akawo maka ni amatsayin mata nayi kurkuren auren wanda dama bawani soyayya ta gaskiya a zuciyar ka kacu ceni Agrif amm....

ahankali ya dauki hannun sa da yake jin yamasa nauyi yarufe mata baki cikin wani irin murya yace" wait my sister ban san da bakin da zan baki hakuri ba sai de ina neman alfarman gafara agareki dan Allah ki daure ki dauki wannan a matsayin k'addaran mu wanda yake fadowa dukkan mutum batare da mahukunci k'addaran yayi shawara damu ba saide yana sauki ga masu Ima'ni irin ki tabbas wannan k'addaran muce ki bar cewa na tozar taki kedin halaliya tace annabin mu ya ubarcemu da cewa matayin mu gonakin mune mushiga alokacin da muka so amma kibar cewa ni Haruna sha'war ki kawai.....

cikin tsawa ta dakatar dashi dacewa ''ah ah idan ba sha'awa ba mezai sa kamin haka ".

shima cikin wani irin b'aci rai yace" saboda ke halaliya tace ko baki san a d'azu din bin mutane suka shafa sheda ke matata ce ba".

itama wani irin kuka ta sake fashewa dashi sai kuma yaji tausayin ta shima jiyake kamar ya d'aura hannu aka yayi ta kukan irin na d'azu amma ina bazai iyayi a gabanta 

ta gani ba dan haka cikin sanyi jiki ya zauna abakin gadon yace "sorry my wife wllh wani tafiya ne yataso min na gaggawa yanzu haka jirgin mu zai tashi k'afe biyar na asuba kuma da alaman aikin zai iya daukana wata guda kuma kinga ke kina school bazai yiwu naje dake ba shiyasa nayi hakan kinga ba kowan ne ango bane zai iya jure ganin macce kamar ke ya tsallake ya tafi amma dan Allah kiyi hakuri haka de yayi ta lalamin ta har yasamu shawo kan  


Agrif tunda yafita masalacin sallan asuba bai koma gidan ba airport ya wuce ba tare da ya tsara ga k'asan da zai jeba 


acikin gidan kam.......


*To masoya muje zuwa sai mun hadu a page 7 muji yanda LABARI zai canza salo* 

*da gaske ne idan Agrif ya kusanci Nasrim Nasir zaiyi k'aran sa sai naji*

*comment din ku* 

*wannan FURRUCIN* *Nasir ne*


Bj 🖊️