FURUCI NA NE

9

by @hauwaausmanjiddarh

*FURUCI NA NE*

('''Rikicin Babban Gida''')   


      *NA*


*BATUL ADAM JATTKO*



'''Marubuciyar'''

*DAMA TA*

*AMFANIN SOYAYYA*

  '''NOW'''

*FURUCI NA NE*



*_________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

***


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


***


*_________________________________*




*Page 9*




Dama wannan bayahuden shi yamin haka shi ya rabani dakai na shawon sati shida alokacin da nake buk'atan ka akusa dani shiyasa ni dama banga lefin ka ba dan Allah Yaya kane mi wani ai'kin a wani'gu tunda baya sona ka aureni bazai bari muji dadin rayuwar mu ba ai kagani tunda ga yanzu ya turaka aiki adaren furkon mu mun jure yaga ba riba shine yanzu yafito a file yake maka barazana daka sake ni ko".?

ajiyar zuciya Agrif ya sauk'e afile bakin sa yana furta "Al'hamdulillah" tunda bataji kan zancen ba duk da shima hankalin sa atashe yake amma cikin son wantar da nata hankalin yace " come down ki fashin ta my dear ni nafi kowa sani waye Nasir ba zance yana farin ciki da auren mu ba kuma bazance yana b'akin ciki ba dan da baya so wllh yasan hanyar da zai biya yaha auren amma Nasir mutumin kirki ne ba yanda kike daukan sabane".


cikin rashin yarda da maganan nasa tace'' mutumin kirkin ne zai umarceka daka sakeni har kana cemasa zaka d'auki duk sharadin sa ni kawai kagaya min wane sharadi ya gindiya maka har kake masa alk'awarin ko yatsa na bazata taba ba?".

cikin in'ina 

yace

" amm amm dama randa zan tafi Bai San na karbi budurcin ki bane kawai Hajja tasa mommy ta kirashi tana tambayar sa ni anan tagaya masa kina da ciki shine yake fadan na zaliceki wai jikin ki nake so nak'asa hakura har naje na dawo haka na turmujeki da gajiyar biki to danaga ya zauki zafi dayawa sosai har yana gani kamar wata rana zan iya juya miki baya shine na masa alk'awarin dana miki randa zan tafi ai namiki alk'awarin bazan sake neman wani abu ajikin kiba har sai kin shekara agida na dan ki yarda ba jikin ki nake soba abin da yafaru k'addaran ce 

to wannan shine saradin Nasir shi yana fadane akan ki

 ki yarda dani Nasir yak'i yake akanki Nasir masoyin kine na boye ke kike nuna masa k'iyayya".


tabe baki tayi tace'' ummm to Ina ruwan sada rayuwar mu nide wllh ban karbi wannan sharad'in ba".


Agrif yace" nima bawai na karbi sharad'in sa bane ah ah yazo akan gab'an alk'awarin da na miki ne bazan kusan ceki ba in Sha Allah har sai lokacin da na dauka yayi danna nuna miki ke nake so bawani abunaki ba".


Nasrim wani irin kallo ta masa tana tabe baki ta wuceshi 

sai data haye kado taja blanket ta rufe rabin jikin ta tace'' ni kuma ban yarda da wannan alk'awarin ba ni kayiwa lefi kuma nayafe maka saboda isanka a waje na kai harma kafi". 

tana gama fadan haka ta k'arasa jan bargon ta ta shige ciki 

Agrif dube dube yafara da alaman yana nemam inda aka tsak'ala CCcamera ne amma bai gani ba 

cikin muryar shagwab'a tace''

"wai me kake nema ne ".?

diri diri yayi yace

"amm sweetheart ki kwanta kinga kina buk'atan hutu bari ingama shiryawa ina zuwa".


yace tare da ficewa daga shi sai towels akugun sa 

yana taka steps wani message din yasake shigowa Nasir din ne de da sauri ya bude gaban sa yana fuduwa yafara karantawa 

 _banason kabawa kan ka wahala wajen neman CCVT Dan zaka b'ata lokaci kane dan ko da ido dubu aka halicceka bazaka gani ba_

a slow yake takawa 

d'akin k'asa yashiga ya zauna abacin gadon yana dafe kansan


shima 

Nasir abangaren sa rufe laptop din sa yayi ya mek'e yana murmushi yafita da saurin sa yafice direct part din su Agrif ya nufa cikin rashin far gaba saikace gidan sa haka ya haye har sama direct bedroom din da yake zaton anan Agrif din yake yanufa murda handle din yayi ya shika Agrif duk da bai d'ago ba amma yasan Nasir ne dan idan ya doshi gu k'amshin turaren sane yake sallama

karasawa yayi har inda Agrif yake abakin gadon shima zama yayi abakin gadon yasa hannu ya cire tagumin Agrif cikin sanyi murya yace"

My friend banso muka zo wannan matakin da Kai ba naso ka dauki shawara ta tun farko kara bu da ita amma ka nace banso kyakkyawar halak'ar mu takoma haka ba dan kasan kaine abokin shawarata kai kafi kowa sani na duk damu ukku muka tashi Amma kasan bamu shak'u da Kamal kamar kai ba agani na na isa dakai ni me baka shawara ne san nan nafi k'arfin komai awajen ka".?


Agrif sake matse hannun sada yake cikin na Nasir yayi cikin k'unan zuciya yace "Nasir kafi karfin komai awajena nasani shine dalilin na na barmaka NASRIM tun farka a zatona da gaske son ta kake duk da nasan bazan jure rashin taba nima amma na bar maka dan kafi karfin komai awajena ashe kai bason Nasrim kake ba nikuma ina sonta bilhakk'i bazan yarda da abin da zai cutar da ita ba dan Allah Nasir Nasrim taci darajan son da kake min kabari mu zauna lafiya".

girgiza kai Nasir yayi yace' ah ah wllh bazan iya ba Agrif bazan iya kwatan ta maka yanda zuciya ta take min barasaza a kowacce second game da Nasrim bane tayi mugun shiga yaruwata yanda bazan iya kwatan tawa ba wllh bazan taba barin ta 

ta huta ba".

numfasawa Agrif yayi yace

 "Nasir ka bani mamaki duk da nasan halinka duk abin da kace zakayi zakayi da kace bazaka bari nazauna lafiya ba ban zaci ta wannan hanyar zaka bullo ba duk atunani na k'untatawar taka zata tsaya a iya korata a aiki ne tunda Kai ne me campanyn amma ashe abin naka ya zarce nan Nasir ina tausayin ka aranan da zakayi nadaman abinda ka aikata kana musulmi ka aikata zina da matar aure kuma baka sirran tashi ba kanunawa wanda yake auren ta saboda ka isa kasani wllh Allah shine ishehhe Nasir wani irin zuciya Allah yabaka da baka sawa aranka akwai ranan shisabi awai randa ikon ka kudin ka baza su maka amfani ba Nasir ban zaci isar taka har takai ka dauki CC camera kasaka a d'akin aure ba har kana barazana dashi kasani mala'ikun Allah ma idan ma'aurata suka keb'e kansu juya musu baya sukeyi basa ganewa idon su tsiraicin ma'aurata Nasir me namaka ?me Nasrim tamaka? Wllh Nasir ka jefani cikin wani irin k'uci wanda ko fitar rai bana jin yafishi ciwo why".?

ya k'arashe maganan yana dafe goshin sa saboda kansa da yake masa zugin ciwo

Nasir mek'ewa yayi tsaye yana juya baya yana murmushi me dauke da b'acin rai yace

"Agrif duk yanda zaka kwatan ta zuciyar ka bata kai tawa ba wllh nafika shiga cikin k'unci 

Dan Allah ka temaka kar kayi yunk'urin bawa Nasrim kowane 

irin farin ciki a karo na biyu zan zo maka da buk'ata idan kabi insha Allah zaka tsira da mutumci ka idan kayi gardama irin na baya to saka makon zaifi haka muni".

cikin dauriya Agrif yace" me kake buk'ata"?.

sunkuyawa yayi cikin taushin murya yace

" Ina son ko dan yatsar ta kar ka taba har ta haifamin yaro na sannan ina son mahaifar ta yazama a tsarkake yake shine dalilin saka cc camera idan ka k'arya alk'awarin nasani".

Agrif yace

"wannan sharad'in ai nariga na dauka amma dan Allah kacire CC TV a bedroom din mu bazan kusan ceta ba sannan ba maganan na baka yaro Dan koni nabada ayanda Nasrim ta tsane ka bazata baka d'an taba sannan shara'a musulumci ta halak tamin cikin jikin Nasrim".

wani irin kallo Nasir yabi Agrif dashi ya d'aga kafada yace' ai dama Kai zumane sai da wuta to wllh ni dakai zanga me nasara zan tona asiri komai ma yafaru ba uban kowa zanji kunya ko tsoro ba".

shima Agrif cikin b'acin rai yace "amma ai na yarda da sharad'in kana farko bazan hada shimfida da ita ba dan haka kamin uzurin ta haifun idan ta amince zata maka shikenan amma da sunan ni zan maka kyautan sa dan Allah idan kana kaunar iyayen ka kar ka fallasa zaka zubar da mutumcin gidan mu hakan babban abin kuyane zaka janyowa three brother abin fad'a aduniya kasani gidan mu shaharatren gidane aduniya ".

cikin rashin damuwa yace

"ni duk wannan bai dame ni ba na tsabawa mahaliccina ma balle wani abu da wani bawa me zunubi aka zai fada akai na ba wannan ne damuwa taba damuwa ta ka kula da sharadina kawai".


Agrif yace"shikenan naji zan kiyaye amma dan Allah ina son na d'an kwanta na huta". 

murmushi Nasir yayi ya nufi kofa atunanin Agrif fita zayyi sai yaga yasakawa kofar key kuma yazare ya jefa acikin aljihun sa ya tako yana murmushi ya fada bed din yana jan blanket yace "good night". 

ba aja dogon lokaci ba bacci ya dauke Nasir 

Juyowa Agrif yayi Yana kallon fuskan Nasir afili ya furta "anya ko Nasir kai mutum ne kana nufin kwana zakayi a part din mu wannan wacce iri yar rayuwa ce"?


tashi yayi yafara safada marwa a d'akin ba abinda yake tunawa irin Nasrim tabbas yaga sha'awar kasance wa dashi acikin idon ta mezai ce mata bai gama wannan tunanin ba yaji ana murda handle din kofar da k'arfi gaban sane yaji yafadi sanda yaji muryar ta tana cewa Yaya "Agrif anan kake ne dan Allah kabude min wllh bana iya kwana ni kadai tsoro nakeji".

ta k'arashe maganan tana dafe maranta dan wani irin murdawa yakeyi duk kwana kin nan hakuri takeyi ta rasa wane irin abune yake damunta tabbas cikin jikin ta yana da son a sadu ga magunnuna da aka dura mata yau ma Mama sai da tabata wani shiyasa take jin mugun sha'awa 

Ji shiru yasa tace'' dan Allah Yaya kabude"? 

 tayi maganan tana jij-jiga kofar da k'arfi 


bude Ido Nasir yayi yana murmushi yace "kaji jarababbiya ko"? 

Nasrim da sauri ta koma d'akin ta 

ta dauko wayan ta Saida tazo dai-dai kofar da Agrif yake ciki ta danna k'ira dan azaton ta kobaya d'akin ne aiko taji waya yana Ringing aciki amma har ya katse ba adauka ba 

tabbas tasan duk baccin da yake zai ji wannan bugun k'ofar da k'ira da take masa 

Afili ta furta "yaya Agrif me hakan kenufi"?.


Nasir yace'' ka bata amsa da cewa kai kana tare da wata yau ba zaka samu daman budewa ba kana da buk'uwa".


cikin razana Agrif yace" ah ah bazan iya ba Nasir cikin sharad'in mu ba wannan'. 

mek'ewa yayi tsaye yana cigaba da murmushi sa 

 yace "ni zan iya yayi bakin k'ofar 

Agrif bai ankara ba yaji Nasir ya canza muryar sa ya koma irin na mata sak sai ka rantse macece yace "ke balla gaza da baki san waye mijin naki bane to ki koma da jaraban ki tunda har ya gaiyatoni har gida ba zan hakura ba ban saba da kwana ba namiji ba".

cikin k'araji nasrim tace'' wacece ke......?


sakeyin muryar matan yayi yace' keni bani da wannan lokacin idan nagama aikina na tafi ki tambayi mijin ki".

Agrif zayyi maganan Nasir ya fisgoshi yayi bathroom dashi sai da suka shiga yaturo kofar yace "kasan ni ba tsoro nake jiba idan kayi magana ko kamusa to dai dai yake da tonan asirin komai dama ni shi nake jira........


ji sukayi Nasrim tana wani irin buga k'ofar kamar zata karya tana cewa " ya Agrif kasan wacece Nasrim awajen kishi amma kamin haka kashigo min da k'aruwa har d'akin aure na ka manta nace duk randa kaso wata to za ayi biyu babu wllh kashe ku zanyi".

 Agrif yana ji yana gani har muryar Nasrim ya dashe amma ba halin yafita lekawa yayi ta bulin mukuli yaga hannun Nasrim har yakumbura dan bugu jinginuwa yayi jikin kofar yana maida numfashi shi kam Ina ma zai mutu yahuta da wannan rayuwar Ina ma zai iya kisa za zai kashe Nasir kawai ya huta in yaso shima akashe shi sai de shi ko Marin mutum bayason yi balle ya illata mutum ko cinnaka bai taba kashewa ba".


azabure Agrif ya mek'e jin wani irif yana cewa wllh nas...…...  



*To masoya mu kasance cikin pages na gaba 10 Ina jin dadin comment din ku ngd sosai da soyayyar ku*


*Taku b JATTKO*