FURUCI NA NE

15

by @hauwaausmanjiddarh

*FURUCI NA NE*

('''Rikicin Babban Gida''')   


      *NA*


*BATUL ADAM JATTKO*



'''Marubuciyar'''

*DAMA TA*

*AMFANIN SOYAYYA*

  '''NOW'''

*FURUCI NA NE*



*_________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

***


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


***


*_________________________________*



          



*15*






Mommy bin motan take tana rusa kukan ita akwawo mata y'arta walahi Nasrim tafi k'arfin shiga motan Police tana binsu har kusan babban get tana faduwa tana tashi Barira da mainunau masu ai'kin ta ne suka rik'eta suna ta kuka mainunau tace ''dan Allah mommy kar ki bisu a haka ki bar Adamu yakai ki a mota Allah yana ji yana gani da k'er suke rike ta Allah sarki mommy sai sunbatu take tayi tayi da hausa tayi da turanci tayi da barbarci tayi da asalin yarenta na ibo Barira ce tafito da waya ta kira Dr Hafsa ta mata baya yanda zata iya

Har ambulances na asbitin yazo tafiya da gawar wakin dan ayi musu gwaji daga mutane gidan har ma'aikatan gidan bame ko bakin kuka gaba daya an hargitse suna gani aka dauki su Khafulan da Agrif aka fita dasu itako Ummu jitake ba awannan duniyar take ba gaba daya kwakwalwar ta takasa daukan abin 

 Hajja tace'' inna'lillahi wannan wacece iriyar musifa Allah ya tsaukar a gidan nan bana zaton ko a tashin duniya zamu shiga cikin irin wannan yanayin Abdulmajid me ka haifa mana irin zuciyar kafurai ko ashe kwara da Allah yakashe yara ukku maza da wannan dangin kafuran ta Haifa ashe ba al'kairi bane da sun rayu ba gashi k'anwar su mace ma tayi haka da suna nan da duk sun kashe mu 

me yasa baki kashe iya yaran ki ba dan kirage mana mugun iri kika kashe Haruna da baiji ba bai gani ba nifa dama wllh ba wani gamsuwa nayi da wannan Fanna din ba kawai dan naga Abdulsamad yana sonta ne nabari ya shigo mana da ita cikin zuri'a mu...........

Kamal yace " Hajja ki dena fadan haka baki da wani hujjan da zaki daurawa Nasrim al'hakin kisan nan Nasrim bazata taba iya kisan kai ba musamman yaran ta idan ta kashe Agrif saboda kishi to yaran ta fa?".

"haba Baba na rashin Ima'ni mana bakasan marar Ima'ni kansa ma sai ya kashe ai irin kafurai ce ba bakaji abin da ita kafuran uwar ta tace ba wai ko duk dukiyar da ta tara zai k'are yarta Ko person bazatayi ba ni kuma na dau alk'awarin tare za a jera gawan su a kabari daya ita dasu Haruna ....

jin rin wannan kalaman na Hajja yasa Barira da maimuna suka janye mommy da bata ma cikin hankalin ta zuwa compound dinta suna ta tofa mata duk adduar da tazo bakin su har dr Hafsa tazo ita dawata k'anwar ta da yarinyar ta Amira k'awar su Nasrim ce matar Aliyu abokin Nasir 


Allah mai iko dubi yanda cikin k'an'k'anin lokacin wannan ahalin sun koma kamar basu taba farin ciki a duniya ba tun ba afi 30 minutes da yin abin har abu yazaga duniya abun ka da gidan da dama ansan sa a duniya duk wani kafa na labaru da social

Media da duk wani kafafun yada labarai ba idda zance bai jeba duk inda kashiga a Media to hotunan su da bayanan sune duk da haka wai Kamal yasa masu gadi sun hana kowane yan jarida ahigowa yan uwa ma idan ba najikin 3A full bane sosai to ba kowa ne yake samu yashigo ba


*Dubai* 


Aliyu ne yafara gani a

 fece book cikin dabara yakira gida aka tabbatar masa da gaskiya ne cikin dabara ya kwace wayoyn Nasir ya kashe wayayoyin  

ya samesa akwance zama yayi abakin gadon yace "yade my friend yanzu ba lokacin kwanciyar ka bane yau duk na ganka wani iri very slowly kode aikin ne".

juyi Nasir yayi yana yamutsa fuska yace " gabana yana faduwa kuma kasan me misani 1 pm naga kiran Khafulan ba adadi atunanin na sunyi abinda suka sabane shida Fayyat amma da na kwanta nake ta mafarkin yaran abin ba dadi kuma kasan wayan su games ne ba waya bane basu kai rike waya ba nasa anyi setting na yanda nida A A. kawai wayan zata iya k'ira da nayi mafarkin nayi da K'iran number A'A baya picking Khafulan kuma ba daman na kirashi saide shi ya kira na kira Kamal mommy da Abu da daddy duk bawanda yayi picking".

Aliyu yace'' inaga basu tashi bane amma ai kaima yanzu zakaje 9j din nagama shirya mana kaya har wayoyinka na kashe nabawa P'A danmu samu

mu shiryar dawuri jet na jiran mu tashi mutafi".


 "Nigeria kuma kasan me kake cewa Ali".

Aliyu yace'' Eh zanyi surprise din Ameera ne yanzu muka gama waya da ita take cewa wai ni Inata maka bauta amma da zannemi alfarman lokaci daya baza ka iya min ba sai nace meye alfarman sai tace tana son ganina yanzu idan na isa kuma tana da matsayi shine ni kuma naci mata alwashin bani ba har kaima yau breakfast din mu yana hannun ta dan Allah sir kar ka nuna ban isa da kai ba kamin wannan alfarman mutafi yanzu".

tsaki yaja yace " bani da wani lokacin b'atawa akan wata macce kude da kuka daurawa kanku kuje kuyi tayi wancen shegen ma daga zuwa aikin da baifi na 1 week ba yace dole sai 1 months zayyi kuka duk kan macce ne nasani".

ajiyar zuciya Aliyu ya sak'e azuciyar sa yace inda kasan halinda yake ciki da bazaka ce haka ba 

Afili kuma yace" to ai rayuwar duniya sai da mata shi kansa neman dan suwa mukeyi yanzu de zan samu wannan alfarman"?.

tattare fuska yayi yana mek'ewa yace " ba dole na ba inde ina son amin aiki da nusuwa bayi mata kawa".

"Thanks so much my friend".


ko ajirgi a zaton Aliyu Nasir zai nemi wayan sa amma ina ko tambaya bayyi ba kawai wantar da kansa yayi akan kujera tare da lumshe ido ya sauk'e numfashin a hankali 


Nigeria 

Bayan sauk'an su Nasir amamakince yake min mutanen da suke tare tun farkon layin su da kallo wanda dole su suka sauk'a dan mota bazai shoga ba amma dayake bashida kuzarin da zayi wani masifa kawai sai ya sauka tabbas agidan sune amma to meyake faruwa".

 yayi maganan afilli hannun sa Aliyu ya sake damkewa yace "sorry MUHAMMAD mushiga ciki ko". 

dak'er suke kur tsawa har suka samu nasaran k'arasawa wajen get din masu gadin suna ganin Nasara suka bude kofar ya shiga

da d'ai-d'ai yake kallon mutanen gidan Wanda su Hajja ma har yanzu suna compound duk ana waje a zaune a k'asa Hajja ce kawai take kukan da bama fitowa yake ba muryar ta yagama dashewa Ummu ko tuni ta suma anyi asbiti da ita 

yana jefa idon sa kofar part din mommy yagan ta kwance sai faman shafa mata ruwa ake ahankali yake takawa gaban sa yana faduwa 

ya k'arasa wajen mommyn zuba gwaiwogin sa yayi a k'asa lips din sa narawa yace "mommy meyake faduwa"""?

Mommy jin murya Nasir yasa tayi saurin mude idon ta kamo hannun Nasir ta damke cikin wahalallen murya tace'' sun tafi da ita Nasuru zasu kashe min y'ata zasu kashe ta Nasuru kaine gatan mu ka karbo min y'ata agaban Alhaji Abdulmajid aka jefa min ya a hilux police suka tafi da ita zasu kashe ta wllh Halima bazata kashe Fayyat da Khaldum da Agrif ba tana son su Dan Allah Nas........

"FAYYYYT KHALDUM 

cikin wani irin k'ara da amonsa ya amsa duk gidan yasake cewa "mommy ina Fayyat ina Khaldum kafin mommy tayi magana Khafulan yace " Papa mamy ta shashe su har abbanmu yan sanda sun tafi dasu ni buya yani a toilet Ina ta kiran ka bakayin picking ba papa".

"ahankali Nasara yamek'a tsaye yana girgiza kai yace mutuwa "Ah Ah baza su mutu ba mommy ki min bayani ta yanda zan gane ya za ayi Khaldum da Fayyat su mutu ban nemi yafiyar suba ah ah mommy ki min bayani ya kalli Dr Hafsa yace Ummyn Ayman meya faru? ".

Mommy tace'' Nasuru nima ban san meyake faruwa ba bana gane komai Fayyat ya mutu khadum ya mutu jikokina dana daura dukkan burina akan su an kashe Aiban da guba banyi magana ba naga illan shiru yanzu gashi makiya sunci galaba a kaina an kashe min jikoki an daura al'hakin kisan akan y'ata mutuwa zanyi Nasir".

"Mommy da gaske yarana sun mutu abokina yamutu". Humairah ce tace'' wllh ya Nasir ta kashe su dama tun da rana tace'' sai ta kashe ya Agrif akan ya amince zai auri Izza ta kashe masa yara har biyu".

cikin wani irin amon murya yace

"tana ina tana Ina wllh idan rai goma Allah yaba bata to duk sai sun fita cikin a zaba wllh zatayi mutuwar wulak'ancin sai na daura ta ajikin mota na jata a kwalta sai nayi pieces pieces din naman jikinta tana ina yayi maganan yana cikumo Humairah yana wani irin gurnani kamar mahaukacin zaki". 

Humairah kasa magana tayi dan yanda ya cukumota ko numfashi ta kasa ja Kamal da Ayman da Aliyu da sarkin gida dak'er suka ceto Humairah sai alokacin Izza tasamu shigowa dan tana asbiti tun dukan da Nasrim ta mata kwanciya tayi a k'asa tafara wani irin birgima tana rusa ihu haka Mama ma sai yanzu tasa kuka Kamal Abbaty da sauran mutane duk suka fasa kuka daddy da Abu jisuke kamar su kashe kansu duniya ta musu k'unci da gudu daddy yayi part din sana Mama ya haura sama rarufe kansa a d'aki yayi yak'i fitowa kawai shi jira yake ace tashin duniya ne kowa ma yamutu ahuta yakeji Abu ne yabiyo bayan sa yana 

buga kofar yace "haba Abdul ka zama namiji mana ka daure kafito mu kwantar wa da matan nan da yaran nan hankali muje 

 station a karbo Nasrim muyi cuku cukun karban gawar wakin mu musu sutura".

cikin tashin hankali daddy yace "Ah ah Abdulrahaman bazan iya fitowa ba kawai kayi duk abin da yadace ba zan iya cigaba da kallon mutane ba y'ar da na haifa ita takashe d'an ka dan uwanta mijin ta Hajja tayi gaskiya kar kayi kuskuren bellin din Nasrim duk Wanda ya kashe ran mumuni da gan-gan shima a kashe sa". 

 Abu yace " yanzu kafito ni kadai bazan iya duk wannan ba ga Nasir ma yazo baya cikin hayyacinsa mu yaka mata mu kwantar musu da hankali".

dak'er daddy ya yarda yafito 

suka dan kwantarwa da matan hankali suka shiga parlou su kuma suka tafi asbiti dan karbo gawa zasu fita yan sanda suma sukazo binciken gidan aka nuna musu part din da abin yafaru

sai da yan sanda suka gama nasu binciken akan gawar wakin doctors sukayi aka batu gawar wakin dan haka ba asamu daman suturan su a ranan ba Saida suka sake kwana 

Nasir sai binciken wane station Nasrim take yakeyi amma yarasa dan bayan magaruba mommy da aminceciyar kawarta Dr Hafsa suka tafi Nasrim tana asbiti hannuwan ta dukka biyi a daure ajikin k'arafunan gadon asbiti a d'aki na musamman yan sanda ciki da wajen d'aki 

Mommy girgiza kai tayi tana kallon yanda Nasrim take fitar da numfashin duk da bacci take amma ba na dad'i bane kallon ta tamaida kan Dr Hafsa tace'' Hafsa yanzu Nasrim ce ahaka y'ar dana haifa da cikina ce ahaka a daure ajikin gadon asbiti wllh Hajja ta cuceni Allah ya isa tsakani nadake Hajiya Maryam ke kika hura wannan wutan wllh ko duk abin dana mallaka zai k'are bawanda ya isa yasa a kashemin y'ata ita kadan nake da Nasir yajuya min baya ".

sosai ta fad'a jikin Nasrim take kuka 

Hafsa tace'' wannan itace mummunan k'addaran ta amma dan Allah Fanna k'in tada hankalinki dayawa in sha Allah Nasrim zata fita cikin wannan yanayi koda biyan kudin diya zamuyi zamu dauki kwararrun lawyer da suka san aikinfu Nasrim ko ita tayi kisan in Sha Allah sai ta fita".

"Mommy mommy".

 su kaji Nasrim tace da sauri mommy ta d'ago 

" My daughter gani meye how you feeling now me kike ji yanzu ajikin ki".?

"Mommy ina Agrif ina Fayyat ina Khaldum".

"Nasrim kin kashe su kin kashe Fayyat da Khaldum da Agrif Nasrim meyasa kika mana haka idan kin kashe Agrif saboda kishi su yaran me suka miki me jikokina suka miki gashi kinsa zan rasaki ai da kin barmin su zanji sauk'i ".


"Mommy da gaske sun mutu? Mijina yarana duniya ta kuma ake zargin na k'ashe su meya ke faruwa dani da gaske ni na kashesu mommy".

Mommy tace'' Nasrim kece mana duk bincike ya tabbatar kece Khafulan yaganki kina wasa wuka kuma yace kafin sannan da kuma wukan da yaga kin wasa dashi kikayi kisan duk kuma dama kinyi furucin hakan".

mommy idan ni nakashe su mommy wane hukunci za ayanke min".

"Kisa mana Nasrim ke ba lawyer bace kinfini sani ai".

Murmushi Nasrim tayi tace'' mommy a yau ayanzu yaka mata ayanke min hukunci inason a kasheni yanzu inason naje inda Fayyat d'ana me sona yaje na tambaye shi waye ya kashesu Ina son naje naga mijina na tambaye shi waye ya kashe sa mommy a cikin daren jiyan bayan fitan ya Kamal saida Agrif yaje mukayi magana na fashimtar juna mun sasanta dashi munyi dashi zamu tafi mubar zaman Nigeria mommy meyasa to na k'ashe sa bayan mun sasanta ya yafemin yankan dana masa a hannu ya tabbatar min da mak'irci aha hada bashi ya d'aura hoton ba amma yaga Wanda yadaura hoton dan duk Wanda yayi amfani da wayan sa yana ganewa saboda wayan yana daukan hoton duk wanda ya taba amma nayi nayi ya gaya min yace" hakan bai dace ba amma yasamu munafikin ya tabbatar masa kuma ya nemi yafiyar sa yafe masa dan haka basai yagaya min ba mommy Dan Allah akai ni kotu yanzu zan amsa nina kashe su a kasheni gwara rad'adin mutuwa da kuncin yaruwar da zan fuskanta idan ba Agrif acikin yaruwa ta".


Mommy tace'' Al'hamdulillah kina nufin bake kika kashe suba ".

"Mommy kisa aranki ni banyi ba amma afili ki barshi anice".

Mommy ta girgiza kai tace'' Nasrim bazan bari ba bazan bari akashe minke ba kokina da lefi balle baki dashi sai kin fito sai me lefin yafito da kansa".


murmushi Nasrim tayi tace'' mommy wai meye acikin mutuwa ne duk gudun da zaka yiwa mutuwa zai zo duk tsawon shekarunda mutum zayyi a duniya baya wuce dubu to da mutuwar yanzu dana wata shekaran duk sunan su mutuwa kowane rai sai ya dan danni mutuwa ban damu na mutun ba mommy".


Doctor din da yake kula da Nasrim ne yashigo zubewa yayi har k'asa yace ranki shi dade an wuni lfy ya mukaji da wannan abin da yafaro".

mommy ta juya tana kallon sa tace

"Yawwa Dr suleman kaine akanta ko dan ALLAH akula sosai idan Muhammad Nasir yazo kar abari ya ganta inde ba Daddy ta ko yayanta Kamal ba banason kowa ya shigo".


"Ok ma'am amma muta ta fama da yan jarida". tace

na gayawa police din kar abari su shiga ayanzu bata cikin nutsuwar ta".

sai can dare Dr Hafsa da mommy suka bar asbiti har lokacin gidan tamkar nara kuma ba adena koke koken ba mommy part dinta ta yawuce direct ita kuma Dr Hafsa tace bari taje gunsu Hajja da dawo a falon sama ta samu Nasir ya daura Khafulan a cinya yana da aikin lalashin sa dan shide akawo masa su khadum kallo daya tayiwa inda suke tayi hanyar bedroom din ta 

Khafulan yace " Papa Allah itace ta kashe su da kayan data shiga ta mana addua da zamu kwanta dashi ajikinta ta kashe su kuma ta rofe fuskan ta har hannun tasa safan hannu dogo baki da dogon shijab ina tsoron nima kar da kasheni tunda tayi ta buga kofar naki na bude tayi da turawa da karfi kofar yaki buduwa ta nemo key tayi ta gwadawa ni kuma sakata nasa ".

shiru Nasir yayi can yace sorry my son baza ta kashe kaba ina tare da kai kuma idan zan koma tare zamu tafi kaji". 

yaci gaba da lalashin yaron har yasamu bacci ya daukeshi ya kaishi bedroom din sa ya kwantar dashi ya fita knocking yayi a bedroom din mommy batayi magana ba yashigo samun ta yayi atsakiyar godo tazuba uban takumi

hannun sa zube cikin aljuhon wadon ya karasa inda take 

Mommy bata d'ago ba tace'' kai ma ka yarda Nasrim zata iya kisan kai ita ta kashe su ko".?

Cikin b'acin rai yace" to idan ba ita bace waye waya kashe su wayayayi FURUCIN zayyi kisan kai idan ba ita ba"'

Nasir ba ita bace ba ita bace Nasrim bata kashe su ba ta fadamin gaskiya".



 " Eh mommy zakiyi kareta because y'arki ce amma nikuma jinin yarana bazai tafi abanza ba Ina nan Ina binciken asbitin da aka kaita wllh wllh awannan daren da zan ganta zan dinka yan kan naman jikin ta sai nayi piece piece dinta a tattara naman ta a binne danasu Fayyat". 


Mommy sauk'owa tayi akan gadon tazuba gwaiwoyin ta a k'asa a gaban Nasir ta hada hannayin ta cikin tsananin damu tace'' Dan Allah muhammad katema kamin Nasrim ta fita cikin wannan k'alubalin zan iya shiga matsala idan narasa ta dan Allah Nasir kadubi soyayyar da yake tsakani na da kai kamin a dalci muhada karfi da karfi mu ceci rayuwar Nasrim uban da ya haifeta ma bai koyi bayan ta ba kuma bata dalefi".

 "Juyawa yayi zai fita da sauri mommy ta kamo k'afafuwar sa tana kuka tace'' katema min".

girgiza kai yayi a hankali ya furta "impossible".

ya janye kafar sa mommy tana kuka tana k'iran sa "MUHAMMAD kai kadai ka ragemin Nasir kar kamin haka". Bai ko jiya ba yafice 


washe gari k'arfe 9 nasafe akayi musu sutura ansha fama da Nasir da za afita da gawar wakin dan sunbatu yadin gayi dan Allah kar kukai min abokina wllh yafi kowa sona da rufamin asiri na Agrif ko mutum na kashe zai rufa min asirin dan Allah kar ku binne min Khaldum da Fayyat kubar su surayu su girma na nemi yafiyar su wllh idan muka hadu awajen Allah bazasu yafemin ba ni me lefini awajen su nasa sunzo duniya bata hallaceciyar hanya ba inaso sugirma in nemi yafiyar su".

Mutane basu wani tsaya sun fashimci abinda Nasir yake fada ba dan duk muryar sa adashe basa jinsa daddy yace a jan shi asani a d'aki ba aje mak'abarta dashi ba  


 Abu ya hana zaman makoki na mata da maza gaba daya wanda ya kama dole ya musu gaisuwa yana zuwa idan yayi musu soke sallaman shi


washi garin ranan 

Izza da Baban ta

 tace'' Baba wai dama wannan mutuwar kagani kace gidan zai hargitse wllh Baba gida ya hargitse gaba daya Hajja ta dauki lauyoyi ciki harda ni zamu gobza Shari'a kuma kasan me akotun daddy kasan shine na biyu a najeri daga shi sai high court babban kotu na k'asa dan haka Nasrim Baban ta ne zai yanke mata hukuncin kisa yanzu yau yan sanda zasuyi minciken su na k'ashe daga nan su mek'a cases din court insha Allah zamuyi wining".

Baba yace "ba nagaya miki ba akwai babban rigimar da zai taso wanda yafi karfin tsafina ba

 yanzu ya cikin gidan yake dan naji shiru".


"Uummmmm Baba cikin gidan nan bakyau Abu da Ummu de basuce komai ba har yanzu amma Daddy yana bayan Hajja  

Kamal Kai ma kasan ida yake gida ha hargitse yanzu yau Hajja zata sa daddy yasaki mommy ta bar gidan kai rigima fa gaba ta kama ita mommy tana Shirin daukan lauyoyi taci alwashin ba wanda ya isa ya yakewa Nasrim hukuncin kisa".


da yammacin yaran yan sanda suka zo gidan gaba daya a main parlour na Hajja suka taru dakka mutanen gidan tambayar farko Kamal sukayi wa suka ce 

"Kamal bincike yanuna akwai tes message da Haruna marigayi ya tura maka da misalin 2 na pm ka boye baka nuna mana shiba a binciken farko da muka maga 


ga tes din kamar haka 

_kamal kazo dan Allah da gaggawa ashi Nasrim bata hakura ba gashinan zata kasheni tace ta kashe min raya_ 


fashewa da kuka Kamal yayi yana girgiza kai ya dafe goshi ya fara kuka 


Sannan dan sandan yace " kayi ne Dan ka rufawa yar uwar ka asiri ko ita ma tayi kokarin haka dan ta CC TV yakamata muga komai amma an goge abinda yafuru daga 1 na dare zuwa karfe ukku darabi amma daga abinda muka gani na k'arfin hudu na yamma zuwa 12 na dare ya gamsar damu ita tayi kisan dan cc tv yanuna tun 12 taso ta kashe sa bata samu da ba ta kashe CC TV kafin taje tayi kisan saide marigayi Haruna yayi mata video a wayar sa alokacin da zata kashe sa tana sanye da likaf sai 

Lokacin da zata Kashi yaran akwai yaron da yasamu ya tsira shima yayi video din a sanda ta kewa yan uwansa yan kan rogo amma abinda bamu gane ba shine meyasa ta kashe CC TV bayan da farko ta nuna bawani boye boye acikin aikin ta meyasa ta bari Haruna ya mata video meyasa ta sanya likaf bayan ita a bayyane take cewa sai ta kashe sa kuma yanzu ma duk tambayar daza amata cewa take ita ta kashe su dan haka gobe za a turaku kotu gomnati ta dauki nata lauyoyin sannan daga yan uwan mamatan ma sun dauka". 

bayan tafiyar yan sanda Hajja tace " insha Allah gobe iwarhaka itama tazama gawa wllh sai de idan Legos din naki zaki kaita ayi jana'izar ta amma ba d'ana daya da zai mata sallah ban yafe ba".

Mommy tace'' in Allah ya yarda baza ma ta mutu ba nan da 50yrs Nasrim tana nan".

"Hajja tace'' ke tubebbiya ni zaki gayawa magana to abinki ya isheni ina gama da hadin bakin ki y'ar ta ki tayi aika Kai kan na

 Abdulmajid idan na amsa sunan uwa a gurin ka ayanzu ba sai an jima ba kasaki wannan tobebbbiya taje can ta k'arata yanzu nake son ka saketa".

A tare Humairah Mama Ummu Abu suka mek'e har Kamal suna cewa subbahanalla Hajja abin har yakai haka

" yafi ma zaka sake ko sai na tsin.....

da sauri daddy yace "ni Abdulmajid Haruna nasaki matata Fanna emake saki daya".


"to kinji kifita kibar mana gidan mu ni idan kina ciki gidan hankalina bazai taba kwanciya ba".

dariya mommy tayi tace'' nafita fa kikace ai sai de nafitar daku kin manta gida nawa ne 

Hajiya Maryam kinyi kuskure da kin bar auren d'an ki akai na dalilin auren d'an naki Ina iya raga miki amma yanzu nida ke ba komai a tsakanin mu yanzu zaki ga aikin tubebbiya kum.......

wani irin mari daddy ya zuba mata yace "ashe baki da mutumcin". 

Mommy tace'' dani daku zaman shekara 32 bakusan bani da mutumcin ba sai yau akan y'ata ba abinda bazan iya ba".


Abu yace" au Dr Fanna duk kawai cinda nake miki agabana kikace haka to wllh za a hukunta Nasrim kamar kowa tunda duk bayanai sun nuna ita tayi kisan".


Mommy tace'' hakane mu hadu a court kawai ta

fice da sauri Kamal ne yabi bayan ta Saida suka k'arasa har parlour yace

"Mommy kinga Shari'a nan fa gobe ne kuma lauyoyi kusan ukku gomnati ya suba sannan ga shi acikin gidan nan an dauki kwararrun lawyer har 5".

shiru mommy tayi can tace'' to Kamal yanzu kana ga ya zamuyi?.

"mommy dama ai dazu na miki magana Barrister Lawan Zakar 

da kuma Barrister Ishak Hamza suna da kwarewa insha Allah zamuyi nasara" .


Kuka mommy tasaka tace'' na gode Kamal Kai da mahaifiyar ka kun zame min garkuwa arayuwa".


"Mommy saide Barr Ishak ya gayamin Nasrim zata iya basu matsala dan jiya kusan wuni yayi awajen ta duk tambayar da yamata kawai cemasa take ita fa ita takashe mijinta da yaranta biyu akashe ta wannan shi zai iya sawa muyi rashin nasara". 


Kutu  

Court tacika makil har waje yan jarida ko ba amagan iyalan three brother sun hadu awajen makil bayan maga takarta ya gabatar da Wanda suke kara da wanda ake k'ra 

wanda take k'ayar itace Hajiya Maryam Habubar Dardum 

 tana Karan Halima Abdulmajid wanda ta kashe mata jika da yaran sa 2 


mommy kuka tayi alokacin da aka wuce da Nasrim da handcuffs a hannu yar sanda macce ta rike hannun ta taja mayafin ta rufe fuskan ta dashi Dr Hafsa tace "please Dr 



My Mai shara'a ya nemi lawyer me kara ya gabatar da kansa 


 "sunana Brr Zayyat Inuwa atare dani akwai Barr Izzatu Mustapha sai Brr Alfa Ibrahim da kuma Barrister farida moddibi duk baris tocin sikayi gaisuwa ga court 

sai lawyern wanda ake k'ara "sunana Barrister Ishak Hamza atare dani akwai Barr Hawwa Adamu sai Brr Lawan Zakar mune lawyer Wanda ake K'ara bayan suma sunyi gaisuwa aka buk'aci lawyer me kara 

Izza ce tafara fitowa 

tana gyara riganta na lauyoyi ta k'arasa gaban Nasrim ta dafe dan d'an gajeren d'akin katakon da Nasrim take ciki ta cefa idon ta cikin nata tace'' HALIMA ABDULMAJID HARUNA ko ?

gyad'a kai Nasrim tayi 

Izza tace'' baki zaki bude kiyi magana".

Nasrim tace" Eh nice".

"Ok yanan 7 ga watan 3 da misalin karfe hudu na yamma kin bude status din mijin ki Haruna Abdulrahaman kin kaga ya d'aura hoton wanda zai aura da kallama kamar haka

 _ko rana da wata zasu dena haske gimbiya ta sai ke soyayyar ki har har abada_

 kin bude status din da misalin 

karfe duhu da rabi 

Kika masa Ripley da 

_lalle kam zaka dena ganin hasken ayau_


sannan kika dauki hoton sa dana wanda zai aura kikayi kansil  kika saka R I P 

yana komawa gida kin gaba wasa wukar ki kamar yanda danki ya bada shida kika fara masa barazana bayan yabaki hakuri ya kwanda kika je kika kashe yaran sa shima kikaje kika kashe sa ta hanyar luma masa kuka har sau ukk...

cikin zafin rai Brr Ishak Hamza ya tashi yace objection my load 

Lawyer me kara nata son daurawa Wanda nake karewa lefi bayan zargin ta ake fuskan ta arufe yake a sanda ake zargin tayi kisan dan haka ba kai tsaye ba me cewa ita tayi kisan".

Alk'ali yace 

"Brr ki canza salon tambayar ki".


agurguje de anyi gobza Shari'a kamar lauyoyi zasu dambatu daga k"ashe de lawyer me kara sukayi nasa ra 


Kotu tayankewa Halima Nasrim hukuncin..............





*kuyi hakurin jina shishur jiya sorry*



*Batul jattko*