FURUCI NA NE

18

by @hauwaausmanjiddarh

*FURUCINA NE* 

( _rikicin babban gida_ )






    



   


             *NA*








*BATUL ADAM JATTKO*




*18*



"wllh k'arya shima bindigan da bullet din su keyi k'arya suke su fasa kan mommyn Nasir tace'' tana ture bindigan a k'eyar ta dariya yayi yana jefawa Khafulan bindigan wasan yace'' wai mommy kina nufin ban iya Acting bane baki tsorata ba".?

murmushi tayi tace''

ai ba aikin ka bane shiyasa ko kyau bai yima ba".

Khafulan yace'' Papa nifa Ball nake so jikina ciwo yake min so nake nayi Execise.' 

dafa kansa Nasir yayi yace''ooo my God son rigima dare ne kaje sama ka kwanta zamuyi magana da mommy good night ".

yaron zai sake maganan Nasir ya d'aga kai yamasa kallo na gaske Wanda idan Zainab ko su khadum yayi wa har fisari suke amma da yake Khafulan shima Theron kan sane jifa yayi da bindigan hannu sa yana turo baki da gun guni yayi gaba mommy dariya tayi tace'' oho de ai kwara da yazo inda ni da karena ne ai baza kaje ba".

Bai juyo ba amma yanda yake yarfa hannun da gani masifa yake 

Nasir ya sauk'e a jiyan zuciya yace'' Mommy yaro nan bashida kunya ko kadan fa".

Mommy tace'' duk waya batashi ai idan ana original copy to Khafulan naka yayi ba ma photon copy ba."


zama yayi Yana dauko Files din da yashigo dashi ya mek'a mata yace'' zaki sa ka hannu anan mommy mommy k'arba tayi takaddun ne na company daya bayan daya tasa hannun shedan ta mallaka masa batare data tambaya meye dalilin sa nayin hakan ba ita de tasan bazai cuce ta ba

jiki a sanyaye yake kallon ta shi yarasa wane irin so da kauna mommy take masa ai ko dan da ka haifa yazo da wannan batun babba za ka iya tsayawa kace meye dalili musamman idan akayi duba da wasan da yamata na yanzu da kuma abin da Dr Hafsa ta kaya mata bai san da afili ya furta" mommy idan ina dake a duniya narasa komai ma zanyi godiya".

d'ago kanta tayi tana cigaba da kallon sa tace'' ina ai bazaka rasani ba banayi maka alk'awarin sai naga jikojin ka ba dan Allah Muhammad ya isa haka kayi aure kai baka ga duniya yana k'erewa bane ga Abbaty nan kanin bayan ku zaiyi aure badan wannan abinda ya faru ba da wata kila matar sa tana da k'aramin ciki amma kai shiru yanzu da mutuwan Agrif da Aiban kaine shikenan watara za amanta ka gaba daya yanzu kaga ko su khadum da Fayyat ba za a manta suba tunda ga Khafulan nan duk Wanda ya gan shi zaice ai su ukku aka Haifa jikoji da tattaba kunne ma sai sunce ai kakan musu ukku aka Haifa amma kai kam b'ata zakayi bat".

a take yanayin sa ya canza cikin b'acin rai yace" towai mommy banji zan iya son yarinyar mutane ba zanyi aure ne bayan nasan bazan iya mata adalci ba ai Annabi yace aure sai kaji zakayi adalci kayi hudu ma amma idan kaji ko dayan ma baza ka iyayewa adalci ba ka hakuri dama sunna ne ba farirla bane".

"haba Nasir buri nane fa kayi kodan ni".

tsaki yaja yakoma Nasuru sa sak yace'' saboda ke zaki zauna da ita ina gaya miki gaskiya kina sake wahalar da kanki."


Cikin b'acin rain itama

 tace

"to Nasir ai naga kana da Wanda zaka iya zama da ita mutane sunfara surutun inda ni na haife ka bazan bari ka kai kusan 36yrs ba aure ba kana shiga 40 fa ka fara zama dattijo kuma naga kana da Wanda zaka iya zama da ita Ina Zuhura yar maiduguri nan tana da kirki zata dace dakai daganin hakurin ta zata iya zama da baud'adde irin ka....

katseta yayi dacewa "mommy bakina da naki na cemiki Ina son ta zan iya zaman aure da ita nifa kawai na ganta da irin zanen kine fa kuma yar maiduguri shine nake dan mutumci da ita shine so".?


"To shikenan my son kar ran ka yab'aci ina maka addua wata rana zakayi".

d'aga kafada yayi yana mek'ewa tsaye yace'' shi ke nan 

 mommy ki kula da kanki da yaran".


 Mommy tace'' kai Ina zaka"?.

"Kano". 

Yabata amsa a tak'aice 

cikin mamaki tace'' nan din ina ne".

cikin wasa yace'' gidan kaso ne".

girgiza kai tayi tace'' my Son".

 har yaje tsakiyar parlourn mommy ta mek'e ta kamo hannun sa tabaya tace'' dan Allah Nasir kafitar dani a duhu kagano wani abu ne waye yasawa Hajja guba ina Barira waye yayi belling din ta kana ganin idan aka kama Barira ai asiri zai tonu".

"Mommi komai yazo k'arshe fa kiyi hakuri ko kin koma gidan kar kicewa Barira komai nasan yanda zanyi bana son kisake cewa komai".

"shikenan Nasir nabar komai a hannun ka har cese din k'anwar dan Allah Nasir ka temaki rayuwar k'anwa.......

dakata Mommy wai meye naki na damuwa da wacce y'ar ne ni kadai ma na isheki rayuwa balle ga Zainab ga Khafulan daga yanzu ki lissafata cikin gawar waki dan cikin da yake jikin tane ya hana bamu daukaka k'ara ba dan al amarin yafara bani mamaki har wasu makasan k'awayen ta

 ta fitar acikin gidan prison din da take.....

ajiyar zuciya mommy ta sauk'e ta katse shi da cewa shikenan Nasir yanzu yaushe zamu koma gida dan kwara ina daga can yafi".

"akwai gyare gyare da akeyi a part din ki ne saboda k'ara matakan tsaro zuwa tomorrow ma Ina ga saudia zaki wuce idan kin dawo sai ki sauk'a a can nan inda kike Kaduna ne akwai komai a gidan Sai anjima adamu zai kawo miki girls house akwai masu gadi sosai a gidan".

har juya zai fita kuma yajuyo yace'' amm yawwa Mommy zakiga na kulle general account din ki idan kina buk'atan man yan kudi ki tambaye ni".

gyad'a masa kai kawai nayi takoma tana zama gaba daya tunanin ta ajagule yake meyasa Nasir ya tsani Nasrim haka wane zuciya yace duk lefin ki ne tun yana k'arami zuciyar sa ta ginu da kiyayar ta amma baki kwabe saba gashi yanzu anzo inda shi kad'ai ne zai iya mata maganin abin amma ba zayyi ba saboda yana daukan ta amasayin mak'iya yanzu yazanyi Ina Dr Hafsa tabani shawara ko tana zuwa duba Nasrim nide tun ranan farko bata sake zuwa ba 

da sauri ta mek'e har an bude masa mota zai shiga back seat

yaga fitowar Mommy tsayawa yayi yana sake hade fuska a tunanin sa maganan Nasrim zata masa 

cikin sauri ta k'araso tace'' waya ta fa ?."  

a tak'aice yace'' suna gida".


"to Nasir haka zanyi ta zama inason yin magana da Dr Hafsa".

bai sake ko juyowa ba ya shige mota 

Mommy dafa kai tayi afili tace'' Allah ya shiryamin kai ya kareka daga dukkan Sharri yabaka sa'a da Nasaran rayuwa".

 Komawa tayi ciki 


*******************

*Three brother*


Nasir numfashi yasak'e idon sa akan Hajja yace "ammm Hajja Mommy ta mallaka min komai nata hatta company dinta na shikama nikuma na mallakawa Zainab yar gidan Agrif company sarrrafa Madara nawa na Legos sai yaran Aiban mata guda 3 

tun gafin ya karasa gaban Izza yayi wani irin bugawa !!!!!


yacigaba yaran Aiban Muwadda da umdatu da Musanat na mallaka musu k'aramin company k'arfe da yake Chaina babban company karfe kuma Khafulan 

San nan dama Khafulan da Khaldum da Fayyat suna da kaso 1 bisa 3 acikin nawa hakan yabawa Khafulan daman mallakan rijiyar Mai fetur na Istanbul ma ana na hade masa waje daya kenan nashi da na yan uwan sa da yagada ina fatan kowa yagane".

ya k'arashe maganan yana mek'awa Abu takardun kyautan da yayi kowa yace Kai Masha Allah ka kyauta Allah yakara bude 

Hajja tace'' amma Nasuru banji na Abdulsamad dan wajen Kamal ba".

Nasir juyowa yayi yana kallon Mai sunan Abban sa dayake zaune a kusa da Mama dan shara 7 yajuyo yasake kallon Hajja yace ai shi yana da uba ni kuma marayu na yiwa".

yana gama fadan haka yamek'a yafita Hajja sai data tabbatar yafice tace'' lalle wannan kyauta na renin hankali ne yoo banda renin hankalin ya zauna Yana mana kyauta na iko wai Fanna ta mallaka masa komai cikin dukiyar ta kuma ya dauka yabawa Khafulan jikanta kaso mafiyawa yo anyi ba ayi ba abude a gindin su ya k'are yo banda ma mutuwa har a dukiya Abdulsamad mutum zai zauna yana min iko Abdulsamad wanda naga dama yake wa kyauta 

Kuma alokacin sa ba nuna ban banci amma shi yaraba bai bawa dan Babana Kamal ba yo banda ma bayahuden banza da bai san darajan mai sunan uba ba ai shi ya kamata ma yafara bawa kyautan yaci darajan sunan uban sa ma mana zonan Abdul ni Ina da gidan gona na baka kaji".

ta k'arashe maganan tana jawo yaron jikin ta 

a wani irin fusace Kamal ya fita a fili yafur ta yau za ayi fallasa acikin gidan nan 


Nasir yana shirin shiga bathroom har yakama handle yajuyo jin an banko Kamal ya k'araso inda yake yace'' Nasir me yasa ka renawa mutane hankali ne kana Abu kamar kai ka haifi gidan gaba daya to wllh kayi hankali a tafin hannu na kake ina ka kai Mommy nasan duk inda Mommy take tursasa ta kayi ta samaka hannun a dukiyar ta".

ahankali Nasara ya saki handle din ya tako gaban kamal dafa kafadan sa yayi cikin jan murya da isa da k'ajinin sa yace'' kamar ne ma ai ni ne babban wa acikin gidan nan shi kuma babban wa ubane sannan ai uwar da ta haifi iyayen gidan ma a gaban ta nayi komai banji tace wani abu ba sai kai Mommy kuma da dukiyar kuma iko nane sai yanda ni nayi".

Kamal cikin bacin rai 

yace'' ba ikon ka bace ikon mijin tane kuma shi yake da ikon duk wani shawaran ba kai ba".

Nasir Karan hancinsa ya shafa yace "to yanzu yakake son ayi maidawa mommyn zanyi ko baka zanyi ka maida mata mijin ta kuma da kake magana akai ya saketa har tagama idda baka da labari ne".  

"naji daddy yasake ta amma ai suna ta y'ar atsakanin su Wanda dukiyar mommyn hakkin Nasrim ne ita kuma Nasrim daddy yana da gadon ta nima dan uwan ta Ina da gadon ta".

Murmushi Nasir yayi yace'' anzusa zuwa wajen Kamaluddeen Baban Hajja Kamal da wayo ba hankali inji Baba yakubu ko ba kirarin ka kenan ba *Kamal da wayo ba hankalin* 

To inba rashin hankalin ba taya dukiyar Nasrim zai zama naka bayan tana da yara". 

murmushi shima Kamal yayi yace'' tana da y'a daya de Zainab 

amma Khafulan ai shege ne bashida gado ba dan sunna bane...........


!!!!!!wani irin bugawa gaban Nasir yayi faduwar gaban da tunda yake a rayuwa bai taba jiba amma cikin jarumta 

yace'' Khafulan ne shegen ya akayi yazama shegen!??".


wani irin Dariya Kamal ya kece dashi yajuya zai fice yana cigaba da dariya sai daya bude k'ofan yafitar da k'afarsa daya waje yajuyo


 yace'' muje suwa Nasir k'aryar ta kusa k'arewa 

 babban shukan da kukayi Kai da Haruna kunyi a idon mak'orwa sai nayi abinda Mommy da kanta zata ce ka maida mata dukiyar ta sai nayi abinda Mommy zata ce ba ita bakai zai ta daure ka da hannun ta saboda kai din ba mosoyin gudan jinin ta bane Kai kasha cewa zaka cusa rayuwar su cikin matsala ita da Haruna kasha cewa k'addaran Nasrim ba mekyau bane Ina da kyawawan hujjojin da idan naga dama wllh a yau baza ka k'ara kwana a duniya ba duk kudin ka da ikon ka amma na bari saboda wasu dalilai ko ba FURUCIN KA BANE a kullum sai ka jefa rayuwar yar uwata cikin matsala to tabbas gidan nan akwai RIKICI d'ana kuma da kaware ba kayiwa kyauta ba Alhamdulillah nima na tara Wanda na tara ma ya isheni nida shi."

ya k'arashe maganan yana ficewa 

Inna'lillahi dama Kamal yasan da wannan maganan waye ya gaya masa daga ni sai Agrif ne fa muka sani no no Agrif yanda yake tausayin rayuwar yaran nan yake hana nima intona asiri bazai tona ba to ya akayi Kamal yasani wannan rana inda Agrif yana raye sai nafi kowa farin ciki kodan Khafulan yazama d'ana a idon kowa amma yanzu zafi kowa bak'in ciki idan ya tuna girman alk'awarin da yayiwa Agrif

da sauri ya bi bayan Kamal 


Kamal yana sauk"a step Nasir ya cin mashi ya janyo shi har cikin d'akin yarufo 

ya sauk'e numfashin yace'' meye shidan ka na sheganta Khafulan".

dariya Kamal yayi yace" ba wani sheda hasashe ne fa musamman idan mutum ya kafawa Khafulan Ido to zai sheda uban sa yana raye ba maraya bane kai ni Zeenat din ma ban yarda y'ar halak bace Aiban ne kawai dan Agrif kuma ya rasu amma sauran sai ahankali".

ajiyar zuciya Nasir ya sauk'e jin Kamal bai San komai ba zargine kawai

ya d'aure fuska Sosai yace'' idan abinda na bawa yaran Haruna yasa ka zargi wani Abu to zunubi kake kwasarwa kan ka dan sanin kan ka ne Aiban da Haruna sunfi karfin komai a wajena Especially Haruna yayi aiki tukuru a three brother zuciya daya kuma ba abinda ya tsira dashi dan haka dole yaran sa su mori wahala da uban su yayi idan kasa ke ai bata yaran Agrif abin bazayyi maka kyau ba 

a kan k'anrwa ka kuma kayi komai ma Shari'a ba fashi wawa kawai".


ya sakeshi Yana shegewa batdroom dariya Kamal yayi yace'' zaka ga aikin wawanci idan na kafa k'iyayyar ka azuciyar wanda kake takama uwar kace 


*Prison*


cikin mamaki Nasrim take kallon masifaffiyar matar mai kula dasu wanda lokaci daya ta canja mata bawani abu na more rayuwa Wanda bata bawa Nasrim tasa an kai ta special d'aki ita daya mekyau komai na more rayuwa akwai daga kan firiji tv lafiyeyyen gado amma da alama musamman dan ita aka gina d'akin 

san nan yanzu tazo mata dawani batu 

 tace'' ma'am serious dan Allah waye yake gaya miki sirrin gidan mu taya ki kasan yaune birthday din Agrif nasan de dama kinsa mutuwar sa wata hudu ne cif kuma waye ya dauk'o miki waya ta?".

Murmushi bayerabiyar matar tayi tace'' Madam Halima ai sirrin gidan ku bawani boyayye bane kawai inason na baki wayan ki zaki hau duk wani kafafen social Media zaki daura pic din Haruna ki masa happy birthday kinga mutane zasu tuna dashi su masa addua kuma amma daurawa kawai zakiyi cikin 10 minutes ki bani wayan naje na boye".

karban wayan tayi tabbas natane wayan amma a Ina Timona n

ta samu wayan da sauri tashiga cikin wayan pic din Haruna ta fara cin karo dashi sosai take kuka kasa cigaba da duba wayan tayi 

Maam tace'' ok ni zan daura miki wak'ar da pic din nasa kawo".

 tayi maganan tana karban wayan ahannun Nasrim  Nasrim zama tayi tana cigaba da kuka 

tace''dan Allah ma'am kifita da wayan nan ni bazan iya cigaba da rayuwa irin wannan ba kuma dan Allah basai kin daura hoton mijina a media ba hakan zai janyo mutane suyi min wani fassaran na daban kuma a gidan yari nake fa".

Murmushi matar tayi tana dashi da wayan tace'' duk abinda zasu fada mutanen duniya ai ni shi na bid'a akan aikina nake Nasrim nasan me make inason hankalin mutane yasake dawowa kanki yanzu an fara manta abinda ki kayi kinga hakan zai janyo mutane suyi cece kuce akai".

ta k'arashe maganan tana ficewa 


*Three brother*


Humairah ce ta fara gani dama ita yar media ce na gani gasheni 

Wani uban asher ta maka tace Nasrim kina gidan prison kina daura wak'a mutuwar dan uwana ko shekara banyi ba 

waka ma har biyu na farko cikin sanyin sauci na kayaran murya mawak'iya take rera wakan me tsuma jiki


_Allahu sarki ka kafurtawa mijina wayyo Allah na nayi kukan rashin ka abokin rayuwa ta wayo Allah na wai ni nakashe miji na ya zanyi na kashe mijina ni Sadiya anyi min k'azafi arayuwa ta bazan yafe_


sai daya wanda hotunan tane da kayan prison aka tana kuka wan ita mata masan sanda akayi ba 

_idan na tuna da mosoyi sai inji kwallah nata kwarara idan na nuna da mosoyi sai inji tamkar infasa k'ara nayi kewa nayi k'ewar Mai mini fira_


jiki asanyaye Humairah ta tafi part din Ummu samun Ummu tayi tasa waya agaba tana ta rusa kuka itama Humairah rungume Ummu tayi ta fara 

Kuka Ummu tace'' Humairah bazan iya ba bazan iya ba ankaini bango ya isa daga yanzu zan nuna nima uwace kuma Haruna yana da gata kamar kowane da agun uwa da baifi da ba mutuwar Agrif ko shekara bayyi ba har Nasrim da take gidan kaso ta ware tana daura hotunan su da waka ba shakka wata ranan sakin ta za ayi ta zo ta zauna to ko yanzu meye yayi saura tana gidan prison amma tana da duk wani Freedoms na rayuwa da ganin Nasrim acikin walwalan ta take tunda har tasamu danan daura hotuna".

Humairah tace

"Ummu kiyi hakuri ai ya Nasir yana bayan mu shiyayi duk wani ciku cikun daukaka k'ara kuma wannan abinda tayi ta sake tabo kowa ma duk wani wanda baya koyon bayan ta to zai fito yayi magana muna tare da ya Nasir Kamal ne yake tare dasu ni wllh sai na bar masa gidan sama akan fansan dan uwana kuma ni har shi Kamal din zan shigar k'ara duk wani bayanan da yan sanda suka nema duk yasani kin fada yayi dan kar a kashe masa k'anwar sa tes din da ya Agrif ya turamasa na yazo yaceceshi Nasrim zata kashesa ai gogewa yayi sai a wayan ya Agrif din aka gani".

"Humairah Abu kune yake cewa nayi hakuri shima Abbaty bawani abinda yakeyi Yana bayan Dr Fanna gaskiya yanzu bazan iya ba Nasrim ta cutar dani ta kashe min d'an da yafi yimin biyayya me farin jini ta kashe yaran sa amma anbarta nata rayuwa kamar kowa".


Humairah tace'' Ummu dama hukuncin da aka yankewa Nasrim bayyi dai dai da lefinta ba hukuncin rataya yakamata ayanke mata kawai shima daddy kanin y'ar sa ce bayyi adalci ba wllh wllh sai an kashe Nasrim idan ta haifu".



 Nasir ya shiryawa Mommy zuwa umara yayi Wanda zatayi wata ukku acan kuma idan tazo agida zata sauk'a ranan da mommyn tazo aranan Nasrim ta cika sati da haifuwar dan ta namiji me kama da Agrif sak amma shi farine Abu yazo duba yaron an masa hud'uba da Haruna 

a ranan sunan aranan Madam Timona ta shirya wani Dan party akayi sa'a kuma aranan ne birthday din Nasrim ita Nasrim duk wannan bai da meta ba bata ma tuno yau ne birthday din taba tana tsaka da kuka su Maryama suka zowai sai tafito waje haka firsunoni yan uwanda suka jata ta fito abin mamaki Mp takani suna ta raye raye girgiza kai tayi ta dafe kai zata koma wata ta jata tsakiyar filin alallai wai sai tayi rawa murmushin da yafi kuka ciwo tayi tad'an ged'a kai a laman tayi rawa murmushi tayi tafice acikin filin d'akin ta koma direct tana rusa uban ihu kuka ko zataji sanyi suko sai rawan su suke suna na nata Haruna happy birthday Halima happy birthday tana jin iface ifacen su da raye raye da suke 


ashe duk wannan party da Timona ta shirya dan ta sake daurawa a media ne murnan haifuwa dakuma birthday party Nasrim takeyi a cikin gidan prison abu yasake jakulewa masu zagin Nasrim suka Kara azama tsine mata 


Ko Ina kale k'a a media bayanan Nasrim zakaji k'arya da gaskiya


aranan Mommy ta dawo Nasir bai koma ba komai na three brother ya tsaya cak hatta aiki 


Mommy jikin a hanyaye ta sake kallon Nasir tace'' to wai ya akayi ta samu wayan ta kuma meya hada gidan prison da kayan kid'a meyasa Nasrim batayi tunanin abinda zai biyo baya ba take haka ko mutuwar Allah mijin ta yayi ai bazatayi haka ba mutuwar sa ko shekara bayyi ba Nasrim ta janyo mana hau da abin fad'a duniya da a gidan nan ."

Nasir yace'' Mommy wannan shi ya tabbatar da Nasrim me lefice kamar yanda kowa yake fada dan haka karma kiji wani abu idan an yakke mata kukuncin kisa".

kuka mommy ta fashe dashi Nasir fe cewa yayi mommy taci gaba da rera kukan ta 


Kamal ne yashigo yana yadin ga zuga Mommy akan Nasir baya kaunan Nasrim tare da hujjoji masu k'arfi numfasawa tayi tace'' nasani Kamal baya sonta nun tana yarinya amma meyasa har yanzu bazai can zaba".

"Mommy saboda yayi alk'awarin bazai taba barin Nasrim taji dadi a duniya ba ko kinsan Nasir ya kulle Dr Hafsa saboda tana zuwa visiting wajen Nasrim watan Dr Hafsa hudu a kule kamar yanda ke kike a kulle bakiga kina can ba mezuwa ba haka Nasrim ma da nake zuwa wllh yahana zuwan kuma idan lawyer bai samu daman ganin Nasrim ba lalle muyi Na sara ba zamu iya samun babban matsala Mommy ki ajiye son Nasir a gefe ki k'waci yaruwar y'arki wllh Nasir baya son Nasrim kema kudin ki yake so daga zaran ya samu zai gujeki duk take taken sa wllh dukiyar yake yiwa k......

Mommy mek'ewa tsaye tayi cikin sauri tace'' Kamal koma baya me kake cewa Nasir yasa an kulle Dr Hafsa saboda mu shiyasa yaki yakawo min wayata tunjiya da nazo nake bin bayan sa ya bani waya ta na kirata yaki kuma ya hanani fita ashe shi Sherri da ya kulla kenan me Dr Hafsa ta masa".?

Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Kamal ya d'aura da cewa

"Mommy abinda nake son kigane kenan duk akan kudi yake yi".


"kudi fa kace Kamal iya na kudin yake komai yana gunsa harrta company shikafa yanzu Yana wajen Nasir". 

Murmushi cin nasara yayi a fakaice 

yasake cewa mommy wllh kinyi kuskure mommyn akwai wani abu da na nake son na bayyana amma sai anje gaban Hajja an Kira family meeting anan zaki gane Nasir k'in gaskiya yake miki keda y'arki".

"Kamal ka kayamin tun anan meye ne dan Allah ".


"Mommy zai iya daga miki hankali sai mun hadu a main parlour 

Sai da safe Kamal yasa aka tara kowa Nasara ne Yanuna bazai iya zuwa ba mommy da kanta tazo ta sameshi tace taron nawane sai katashi kazo".

tana gama fadan haka tafice cikin mamaki yake bin bayan ta da kallo to meyasa mu Mommy  

a haka ya tashi ya bita daga shi sai riyan bacci yana tsaki ya yi sallama daddy ne ya amsa yasamu gu a twositer ya zauna Kamal tashi yayi tsaye yayi addua bude taro ya fara bayani kamar haka 

Daddy kai da Abu nasan abin da zan bayyana ayanzu zai muku ciwo tunda ya shafe ku shine ma dalilin da yasa nayi shekaru 7 Ina boye abin saide cigaba da boyeshin zai iya zama matsala zuwa gaba musamman yanzu da ake neman mafi akan wannan abubuwan da suke faruwa amma dan Allah kuyi hakuri".

ya k'arashe maganan yana zuwa gaban tv memory ya fitar yasaka acikin DVD ya kunna tv take Nasir da Agrif suka bayyana danna stop yayi yasake yace wa "daddy wannan video ne na daukeshi aranan da Hajja tak'ira Agrif akan yazo Nasrim tana da ciki ai su biyu suka zo idan baku manta ba suna zuwa direct a gerdeng suka tsaya nima Ina cikin akusa dasu bayan bishiyar kwaiba daganan ya danna pl duk tattaunawar da Agrif da Nasir sukayi wanda yanuna k'arara yara na Nasir ne gashi a filli ya bayyana har gargadin da Nasir yakeyi wa Agrif na idan bai saki Nasrim ba rayuwar baza ta tabayin musu kyu ba

 kowai gashi ashi a bayyane


wannan shiya tabbatar wa iyayen yara na Nasir ne 


Hajja ce tabara kwallah Kara tana ihun kuka suma su daddy kukan suka fara haka Humairah Mama Ummu hatatta Izza yau abin ya girgiza ta sai kuka tayi ita duk masifan da take tsammanin zai balle batayi zaton zayin haka ba daddy da Abu suma kukan suke suna maimai allahuma gafurni'walhamni 

gaba daya dasu da yaran kuka suke ba me lallashin wani 

cikin kuka Ummu tace'' Nasir Allah ya isa tsakani na dakai da Nasrim da ita uwar munafukan Dr Fanna ashe kwara da gaskiya ta bayyana na dena yiwa shegun yara kuka haba dama da alaman tabbaya yanda sukayi kaman nan kaman ma har ya b'aci ni nasa wannan araina tun randa FAYYT ba shida lafiya jinin kowa bai masa ba sai na Nasir za a saya a saka yace kar a sawa d'an sa jinin saidawa gashinan zuwa aranan yazo kuma nasa jinin ne yayi mun dauka duk a zumunci yakeyiwa ashe yaran sane 

Allah yajin k'an Haruna ya mutu da bak'in ciki mafi girma wllh ita ma Zainab din tashi ce banzan karbeta amasayin jika ba harshi wannan jaririn duk da ban ganshi fili ba a hoto fari ne bazan k'ar ba ba bajinin Haruna acikin su balle Zainab da itama kama daya sukeyi sak ai shegiyar ce....


 Mommy cikin Wani irin zafi ta dashi ta shak'e Nasir iya k'arfin ta dace da gaske ne nace da gaske ne Nasir Allah yagani ni da al'kairi na soka nace da gaskene ban yarda da wannan video ba gayamin gaskiya duniya abin tsorone za a iya hadashi amma ka fadamin da bakin ka.....

ta k'arashe maganan tana sakin sa zubewa Nasir yayi agaban iyayen nasa yace'' Mommy sharrin shedan ne da k'addaran ALLAH ya rubuta dama rayuwar su Khafulan a haka zai zo amma Aiban Zainab da wannan jaririn wllh yaran Haruna ne ni sodaya tak habin yafaru ku yada dani kumin duk hukuncin da yayi dai-dai dani".

"girgiza kai mommy tayi tace'' Nasuru kafi shedan iya hada tuggu kuma Nasir Allah ya isa ba wani hukuncin da zamu yanke nida kai sai agaban Allah".

Hajja tace''towai Abdulmajid Abdulrahaman ku ba abinda zakuce ne bazaku dauki madoki ku fasa kan shege ba wannan ba jinin Abdulsamad bane tabbas an can zasa Dr Fanna sai muyi Shari'a dake wannan wani shegen d'anki kika Haifa yazo dai-dai lokacin da Halima zata haifu kika dauke namu kika sako naki kuma kika samu nasaran shiga cikin gidan kika reneshi ni dama najima ina tunanin ya akayi yaron nan yake kama dake ashe dan ki ne ban yarda ba sai kin nemo min jikana na asali wannan ba jikana bane wllh Shari'a zamuyi da gan_gan kika kashe Halima bawani wasiya da tabada na ki auri mijinta yama za ayi hakan ta faru kawai dan kin karbi haifuwar ta dan yayi kama dake sosai ni dama Ina zargin wani abun yau ayanda kuke kama dashi wllh ban karbi Nasir ba kamar yanda Amina tace bata karbi Zainab da wannan jaririn da akasawa sunan Haruna ba cikin kuka ta k'arashe maganan zan iya cewa tun da family nan suke basu taba shiga cikin tashin hankali irin wannan ba dan atake Abu ya yanke jiki ya fadi daddy da Abbaty sukayi kansa amma Ina da alaman ya gamu da paralysis cikin sauri daddy da Abbaty ne suka dauke sa zuwa asbiti mommy taci gaba da newa nazama makafuwa dama Dr Hafsa ta gayamin kaine kaine naki yarda yanzu Kashi kayi abinda hankali bazai taba kawoshi ba Nasir na tsaneka ina son ka dawo min da dukiya ta ko sadaka nayi dashi yanzu nake son kadawo min da komai nawa Nasir yanzu zan bar gidan nan bana son ganin ka tsakani na da kai sai alashira.....

da sauri Nasir yace'' Mommy kuskure daya nayi zan nemi yafiyar Nasrim Agrif ya yafenin mommy kibabi dama na gyara kuskure na dan Allah Mommy ki dena FURUCIN na bazaki yafemin ba yayi tsanani akaina mommy cewa fa kikayi KIN TSANE ni mommy ke nasani bane da kowa ke kar kimin haka ki naji Hajja tace'' bata karb'eni a jikan ta ba dan gidan Abdulmajid ba ke bai kamata kimin haka ba ki yarda kedin kece uwata kamar yanda ta fad'a ke nasami mommy mommy ke nasani mommy".


cikin wani irin tashin hankali Mommy tace'' ban taba tsanan wani Abu aduni sama dakai ba Nasir bana son ganin ka zan karbi kakkina ko agaban Shari'a ne".

da sauri Nasir ya fice duk wani file da yasan Yana hannun sa yakwaso da sauri harda woyoyin sa da laptop din sa ya dire agaban momny yace'' Mommy inde abin duniya ne ni na barmiki su halak dinki ne mommyn ban taba tsammanin makiyan mu zasuyi nasara akan mu ba nayi zaton mune zamuyi nasara mommy makiya sunyi Nasara akan mu mommyn akwai abinda ake kullawa acikin gidan nan kar ki zauna acikin dan ba aikin mutum daya bane mak'ircin gidan nan mommyn kuma nasan keda NASRIM!!!!!! ne zaku fi fad'awa ciki amma Isha Allah daga wannan bazasu cutar daku ba zan dauki mataki mommy zan tafi kamar yanda kika buk'ata amma nasan zaki nemeni Mommy kwana kusa zaki ne meni 

zan tafi hatta takadduna na makaranta ba zan dauka saboda agidan nan na samesu zan nemi komai da gumina Mommy Allah wadaran abin duniya da zai shiga tsakanin mu Mommy iya kayan jiki na zan fita dashi Naira biyar din gidan nan bazan dauka ba haka ga komai na bar muku zan nemi halak dina yasa hannu acikin ajihun wandon sa yafitar da dukka al'jihun waje alaman bazai fita da komai ba ya juya sai da yakusa fita yajuya yace Mommy dan Allah kije wajen Baba Nasuru kice masa zaki he Lagos kiji abinda zai ce miki yana gama fadan haka yafice da sauri mommy tana kwallah masa K'iran kazo ka zauki shegen yaron ka wazaka barwa su".

 juyowa yayi ya mata murmushi ya fice


masu gadi da ma'aikatan gidan suna mamakin ganin yanda Nasir yafita a k'afa suna daga masa hannu sai da yaje fita daga babban get yajuyo yayiwa gidan kallon k'arshe ya fara takawa cikin sauri 


Mommy da sauri ta k'arasa part din Baba Nasuru cikin sauri tace'' Baba Nasuru ni zanje Lagos". 

azabure ya tashi yace'' Lagos Lagos ki kaini zoki ki kai ni wajen Emaka zan karbo y'ata ZANNA FANNA Emaka muguwa ce a a Sherri akamin ta yarda zata sa y'ata ZANNA FANNA ta tashi arniya dan Allah ki kaini ai kece Halima ko FANNA yan biyun HALIMA ce zan je Lagos na karbo yarinyata maiduguri zamuje FANNA EMAKA FANNA EMAKA 


wani irin runguma Mommy tayiwa Baba Nasuru cikin kuka tace'' BABANA.............


*wai ya batun su Abu a hospital ne*


*To masoya muje zuwa rikicin babban gida yanzu aka fara fa da gaske ne Hajja bata yarda Nasir jikanta bane ya Ummu za ta dauki Zainab da jaririn Nasrim mu hade cikin pg 19 insha Allah*




*Bj*