KOWA YA YI DA KYAU.....

Chapter 1 to end

by @ummindaddy77

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai.


KOWA YA YI DA KYAU.......(Gajeren labari)

Da alkalamin Ummulkhair Abba Muhammad.


Please readers ina buƙatar addu'o'inku bisa wani al'amari da na sa a gaba ina fatan za ku sanya ni. Na gode may almighty Allah accept our fasting. Ramadan Mubarak and happy salla in advance.





KOWA YA YI DA KYAU........

(Gajeren labari)

 Da alkalamin Ummulkhair Abba Muhammad.




Fati, matashiyar yarinya ce mai kishin ganin ta yi zurfin karatu a rayuwarta musamman fannin da al'umma za su amfana da ita, a lokacin da take makaranta tana ɗaya daga cikin ɗaliban da ake ji da su saboda hazaƙarta. Babban burinta a rayuwa ta zama ƙwararriyar likita don ta taimakawa al’umma, sai dai kash! Wahalhalun rayuwar da suka tsinci kansu a cikin sanadiyar rashin zaɓen waɗanda suka cancanta da mutane garinsu suka yi, ya mantar da ita wannan burin nata. 


 Ta taso cikin talauci kasancewar mahaifinta ba shi da abin hannu amma akwai shi da faɗi-tashi ganin ya kyautatawa iyalansa, su biyar ne a wurin iyayen nasu ita ce ta fari sai ƙannenta biyu maza da ke mara mata baya sai kuma tagwayensu mata biyu.

 Kimanin shekaru uku kenan da kammala karatunta na secondary amma ci gaba da karatun ya ci tura, kasancewar mai tallafa mata mahaifin nata ya kwanta dama tun bayan wata uku da kammala sakandare nata. Ga fannin da take buƙatar ta karanta akwai kashe kuɗi.


 Tafiya take a gefen titi hannunta ɗauke da baƙar ledar da ke ɗauke da garin kwaki a ciki. Da kyar take iya ɗaga ƙafarta saboda yadda yunwa ke addabar ‘ya’yan hanjinta. 

 Tsagaita tafiyar ta yi saboda jin da ta yi yawun bakinta na neman ƙafewa, cikinta ya fara ƙullewa idanunta na mata dishi-dishi tare da fara ganin wasu taurari na mata gizo saboda tsabagen yunwa, a take ta ji wani irin jiri na ƙoƙarin jefar da ita, ta nemi waje ta zauna na wasu ɗan daƙiƙu cikin hukuncin Allah sai ta ji abin da take ji ya yaye, ta miƙe ta ƙarasa gida. 

 Tana shiga ta hango mahaifiyarta zaune ƙannenta sun kewaye ta suna kukan yunwa, wani irin ƙwalla ne suka fara zirya a tsakanin kwarmin idonta.

 Suna hango ta ɗaya daga cikin ƙannanta zumbur ya miƙe ya je gare ta, tare da riƙe ledar da ke hannunta, "Yaya Fati me kika sayo mana?"

   Ta dalla masa harara"Ban sani ba sarkin tambaya idan aka haɗa idon ka sai ya gani."

 Cikin fushi ya juya ya tafi wurin mahaifiyarsa yana tura baki, ta ce da shi, "Kai Haidar daga ganin mutum sai tambaya, kamata ya yi ka yi mata sannu da zuwa ka karɓi abin da ta zo da shi. Amma abin da ka yi baya daga cikin tarbiyya. Kar ka sake ka ji ko?" Tare da shafa kansa ta kuma cewa, "Yi haƙuri ɗan albarka."

 Sai ya saki ransa ya ce, "Umma, in sha Allah ba zan kuma ba, yaya Fati kema ki yi haƙuri."

 'Yan tagwayen ne suka zo suna mata oyoyo ta sanya hannu ta ɗauke su dukkaninsu biyu ta sumbace su ta ajiye su.


 Mahaifiyarta ce ta ce, "Yarinyar nan ina kika je ne?" Tana sosa keya ta ce, "Umma jarina na gullisuwa da kantun gana da nake ne na ɗauka na je na sayo mana garin kwaki da shi, jiya da daddare ba a ci abinci yau ma sai a wuni haka."

 Ta shiga kitchen don ta jiƙa musu garin kwakin ta ga babu ruwa ko kaɗan, bayan ta fito ne ta ga Hafizu ƙaninta da bokiti empty a hannu yana cewa, "Umma na zaga duk famfuna babu ruwa, kuma duk gidan da na shiga masu famfo da su ba ni ko da bokiti ɗaya ne sai su ce babu."


"Allah ya kyauta." Shi ne kawai abin da ta iya cewa.

 Fati ce ta shiga makwabtansu ta gan su dukkanin zaune, ta yi musu sallama tare da gaishe da su, suka amsa cikin fara'a suna mai tambayarta lafiyar Ummanta, ta ce da su tana nan kalau daga nan ta roke su idan suna da ruwa ko da rabin bokiti ne su ba ta, ɗaya daga cikin ta ce, "Kin kawo kuka gidan mutuwa. Girki na gagara ɗorawa saboda rashin ruwa, yara sun fita sama da awa ɗaya ko sau ɗaya ba su kawo ba." Ɗayar ce ta ce da ita, "Ga shi can ni ma ɗaka da waje bokiti ɗayan ne ki ɗan tsiyaya ki bar mini sauran."

 Fati ta yi godiya ta je ta tsiyaya a zuciyarta ta ce, "Ruwa sai ka ce zam-zam." 


 Bayan ta zauna ta haɗa garin kwaki ta zuba guntun sukari na sana'ar ta tasa wa kowa a kofi ta ba su, kurɓa ɗaya ta yi ta ajiye ta ji abin baya ma ranta, da ta ji almajiri na bara ta kwaɗa masa ƙira ta juye masa.


 Ɗaki ta nufa ta kishingiɗa, ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mata irin halin ƙuncin rayuwar da talaka ke fuskanta a wannan ƙarnin da muke rayuwa a ciki.

 A zuciyarta ta ce,"Yaushe talaka zai fita daga cikin ƙuncin rayuwa da yake ciki? Yaushe shuwagabannin mu za su canja talaka ya mori romon dimuƙraɗiya da ake cewa. Me ya sa 'yan siyasar mu daga sun ci zaɓe sai su mance da alƙawuran da suka yi wa talakawar su? Su dai burinsu su tara idan za a yi lissafin manyan masu kuɗi a ce suna daga jerin farko. Ba su san wannan dukiyar fitina ce gare su ba, kuma duk abin da suka tara suna ji suna gani idan suka mutu a nan duniyar za su bari, yadda suka faɗo duniya babu komai haka za su ce ga mahallinsu babu komai" Ta share hawaye masu zafi da ke zirya saman fuskarta ta ce, "Ya Allah ka ba mu ikon cinye wannan jarabawar da muka tsinci kanmu ciki. Ya hayyu ya ƙayyum ka fi kowa sanin cikar burina ya Allah ka cika mini burina na amfanar da al'ummata kafin na amsa ƙirarka."


 Fati, mafarkin da take a kullum ta zama likita, a wasu lokutan takan cewa anya wannan burin nata zai cika? Don tana ganin abin da kamar wuya, yayin da wata sashi na zuciyarta kuma kan ƙarfafa mata guiwa tana ce da ita kar ta fid da rai ga rahamar Allah, idan ya ce za ta yi za ta yi. Idan ta tuna hakan kuma sai ta yi murmushi tana mai fatan Allah ya tabbatar.


 Ba don komai guiwar Fati ke sanyi ba sai don sanin a wannan ƙasar tamu duk iliminka duk hazaƙarka duk ƙwaɗayin son karatunka idan har ba ku da kuɗi sai dai a yi babu kai babu mai tallafa maka. Kai idan ma akwai mai tallafa maka ɗin harkar ilimi yadda ya taɓarɓare a jihar su sai dai ta je wata jihar ta yi."

 Da attajiranmu za su dinga bibiyar makarantun 'ya'yan marasa galihu su samu haziƙai su ɗauki nauyin karatunsu da hakan ya haifar da ci gaba a ƙasa.


Wani irin baƙon yanayi ne ya ziyarce shi wanda bai saba jin irinsa ba. Haka kawai ya tsinci kansa zuciyarsa na bugawa fat-fat-fat tamkar za ta tarwatse ta fito.

Yayin da bugun zuciyar ke yawaita, sai ya yi saurin ya dafe saitin zuciyar da ke barazanar tarwatsewa da hannunsa, tare da faɗawa gado ya ja bargo ya lulluɓa, wani irin zazzaɓi mai zafi ya rufe shi yayin da jikinsa ya fara kyarma yana jan numfashi kamar wanda ya tsere a filin daga.

Shigowar matarsa Mairo ɗakin ke da wuya, ta hangi mijinta kwance a lulluɓe. Ta isa kan shi tare da yaye bargon, yanayin da ta gan shi ya sanya ta razana ta zaro ido ta dafa shi tare da cewa. “Malam, jikin ne ya kuma tsananta haka? Na shiga uku!"  

Bai iya buɗe bakinsa ya ba ta amsa ba, kawai sai numfarfashi yake, ganin haka ya sa ta fita bakin titi a firgice ko lulluɓi babu balle takalmi, domin ta samu ɗan adaidaita sahun da zai kai su asibiti, amma kash! Babu wata adaidata sahun da ke giftawa.

 Daga nesa ta hango gungun jama'a wasu na tafiya da ƙafa wasu kuma a abin hawa, yayin da suka ƙaraso ne ta fahimci zanga-zangar lumana suke saboda tsadar rayuwar da talakawa suka tsinci kansu ciki da kuma hawa-hawar man fetur. 

 Bayan ta sayar da wani ɗan'adaidaita ne ta shaida masa halin da take ciki, nan ya nuna mata suna yajin aiki ba zai iya kai ta inda ta buƙata ba, ya ja adaidatarsa ya bar ta tsaye. Wani irin ƙunar zuciya ta ji yayin da wani abu tamkar dutse ya riƙe mata maƙoshinta, haka ta koma gida jiki babu kuzari tamkar wacce aka cire wa laka.


 Zaune take tana fuskantar mijinta ta zuba wa sarautar Allah ido, sai ta ji ya fara tari tana masa sannu ganin idonsa ya kakkafe ya sanya ta fita a guje ta garzaya maƙwabtansu domin su taimake ta a kai mijinta asibiti kasancewar suna da mota, da ta shaida musu halin da take ciki, nan maigidan ya shaida mata motarsa ya fi sati bai fita da ita ba saboda rashin wadataccen fetur da ake fama da shi, amma ya ce da ita zai ƙira abokinsa idan ta sa motar akwai mai ya zo ya kai su, haka kuwa a ka yi ta nan aka dace.


  Yayin da suka isa asibitin gwamnati, su ma suka shaida musu sun tafi yajin aikin sai baba ya gani a yau, jin haka ya sa suka garzaya zuwa asibiti masu zaman kansu, (private hospital). Kuɗin da aka buƙaci ta ajiye kafin a fara duba lafiyar mijinta da aka faɗa mata sai da zuciyarta ta buga domin naira biyar mallakinta ba ta wayi gari da shi ba, yayin da da ta ƙiyasta kuwa sai ta ga ko da kayan ɗakinta ta siyar, ba za su kai wannan kuɗin ba, don haka ta yanki jiki ta faɗi ta suma.

 Ta buga nan ta buga can kuɗi ya ƙi samuwa, duk inda ta je da a ba ta ko da bashi ne ta gaza samu, da ta shaida wa mijinta halin da ake ciki ya ce da ita aje ƙauyensu a sayar da gonarsa. Haka kuwa aka yi, kasancewar abu cikin gaggawa ba a a sayi gonar da wata daraja ba, dama haka 'yan'adam muke da mun ga mutum na cikin mawuyacin hali ya fid da abin sa zai sayar tayin wulakanci ke biyo baya.

 Amma Mairo hakan bai dame ta ba, ita burinta ta ceto rayuwar mijinta, ta haɗa kan kuɗin ta kai asibiti, daga nan aka soma duba lafiyarsa da yi masa gwaje-gwaje.


Malam Audu mijin Mairo malamin makarantar Firamare wanda yake matsayin hedimasta, a zaɓen da ya gabata ya taka rawar gani sosai wajen dafawa Alhaji Matawalle wajen ganin ya zama gwamna duk da rashin cancantar shi saboda kawai ya masa romon baka, idan har ya lashe zabe zai ba shi babban muƙami, madadin samun babbar muƙami sai ya tsinci kansa cikin Malam da aka kora a aiki cewar ba su cancanci yin aikin malunta ba.



 MALAM AUDU A SHEKARUN BAYA


 Malam Audu a duk lokacin da kakar siyasa ta yi da shi ake damawa kasancewarsa yana da ra'ayin siyasa sosai, tun ba a san shi ba, a hankali a kwana a tashi har ya yi ƙaurin suna, bisa dalilin haka ya sa duk wani ɗan takara na son a ce Malam Audu na ƙarƙashinsa don yadda yake da mabiya.


Yayin da guguwar siyasa ta kaɗa, 'yan siyasa suka zama tamkar zakuna wajen neman tagomashin masu kaɗa musu ƙuri'a. Nan Mal. Audu ya kuwa yi kane-kane a cikin lamuran yaƙin zaɓen Alhaji Matawalle Mainasara, ya zamana shi ni ne sahun gaba wajen yaɗa manufofinsa a kafafen yaɗa labarai na zamani duk da kasancewarsa ba celebrity ba, amma saboda iya naƙalto labari ya rubuta a kafafen sada zumunta ya sanya shi samu mabiya sosai wanda ko wani shahararren ma ba shi da shi, a duk lokacin da ya yi posting to fa za a fara ruwan comments da sharing na post kuma duk inda aka kewaya maganarsa ke yawo. Kullum yana cikin posting ɗin gwaninsa da kuma yaba halayyarsa da yaɗa manufofinsa na kawo ci gaba da zai yi muddin ya haye karagar mulki, ya saye zuciyoyin jama'a da yawa har 'yan adawa ma suka fara marawa gwanin nasa baya. 

 Sunansa ya rikiɗe daga Malam Audu ya koma Audu na Matawalle ko ina ya ratsa da haka ake kiransa, daidai da hula ko p cap idan ya sanya za ka ga an rubuta Audu na Matawalle.

 Alhaji Matawalle da ya riƙi Malam Audu duk abin da ya buƙata kai tsaye yake ba shi.



 Malam Audu, sai ya bushi iska yake lekawa makarantar firamare da yake kasancewar shi ne shugaban makarantar babu mai ƙalubalantarsa.


  Kuma ana sa lissafin kiris ya rage masa ya rabu da aikin wahalar nan, saboda babbar aiki ce za ta samu. Sabuwar duniya sabuwar rayuwa sabuwar daula ita za ta tabbata, saboda honourable ya yi masa alƙawarin ba shi babbar muƙami kuma zai ɗaukin nauyin ci gaba da karatunsa.


 A duk lokacin da suke tare da mai ɗakinsa kuwa Mairo sai ya cika ta da surutun muddin suka yi nasara Ubangidansa ya lashe zaɓe zai gina musu katafararen gida na gani na faɗa, Hajji da Umura kuwa sai ta gaji da zuwa, haka yawon buɗe ido sai ƙasar da ta zaɓa.


Irin waɗannan burika da wasunsu da su Mal. Audu ke kwana yana tashi.



Kullum burinsa bai wuce ya ga Ubangidansa ya yi nasara ba, duk wani lungu da sako sai ya ratsa don tallata Alhaji Matawalle. Kasancewarsa yana dabarun iya siyasa da kuma ƙwarewa wajen jawo hankalin jama'a tuni mutane suka dinga goyon bayan abin da yake so don duk inda ya je sai ya faɗi irin ci gaban da Ubangidansa zai kawo a jihar muddin suka yi nasara, jama'a sun yi na'am da huɗubobinsa ya kasance a jihar babu ɗan takarar da jama'a ke yi sama da gwaninsa.


  


 Zaɓe ya tunkaro saura kwanaki ƙalilan Malam Audu ya shiga busy ya zage dantse rai da buri bisa ganin sun samu nasara. Shi ne kan gaba wajen kawowa mutanen unguwa kayan masarufi domin jan hankalinsu. Kuma shi ne lambawan wajen jagorantar matasa wajen ƙaddamar wa 'yan adawar da ke hamayya da su. 



 Alhaji Matawalle na jin daɗi sosai yadda al'amura ke tafiya babu cikas.


Ranar zaɓe Mal. Audu bai zauna ba ballantana ya huta. Shi ne zirga-zirga tsakanin rumfa zuwa rumfa domin neman nasara. Cikin tsakar dare aka kammala tattara sakamakon zaɓe aka sanar da cewar gwaninsa Alhaji Matawalle ne ya lashe zaɓe, nan ya hau rawa da murna

Haba! Wannan rana ta zama na musamman gare sa saboda mafarkin rayuwar jin daɗi da ya daɗe yana yi za ta tabbata.


 Saboda farin ciki ko runtsawa bai yi ba a wannan daren, ashe bai sani ba, tsugunne ba ta ƙare ba. Wannan murna da yake kuka na zuwa domin Alhaji Matawalle Mainasara zaɓen tumun dare ne, kumurcin maciji ne wanda kul badaɗe kul bajima za su ɗanɗana kuɗarsu.  


 Tun da aka rantsar da shi ya hau karagar mulki ya yi kunnen uwar shegu da Malam Audu, ya ƙi cika masa alƙawarin da ya ɗauka, kullum yana cikin zirga-zirga zuwa gidansa da ofishinsa amma baya samun damar haɗuwa da shi.


 

 Daga ƙarshe ma Alhaji Matawalle Mainasara ya ba da umurnin a yi bincike game da Malaman makarantu saboda albashin da ake fitarwa ta ɓangaren ya yi yawa a yi tankaɗe da rairaya a rage wasu, a wannan tankaɗe da rairayan aka tankaɗe har da Malam Audu, albashin da bai taka ƙara ya karya ba wanda yake samu nan ma ya rasa, ya kai takardunsa makarantu ma su zaman kansu shiru babu inda aka neme shi.

 Alhaji Matawalle ba a iya makarantu kaɗai ya rage ma'aikata ba, duk wani ma'aikata da ke ƙarƙashin jihar sai da ya sa aka rage su, sannan aka zabtare duk wani kaso na albashi da ake ba su.

  Nan talakawa suka tsinci kansu cikin matsatsi da tsadar rayuwa. An zabtare maka albashinka a hakan kuma sai a ɗauki tsawon watanni ba a yi albashi ba, bisa dalilin haka ma’aikata da ke ƙarƙashin jihar suka dinga yawan tafiya yajin aiki.


 Uwa uba abin da ya fi addabar mutanen birni da ƙauyen da ke jihar matsalar tsaro, mutumin ƙauye na fargabar zuwa gona ko cin kasuwa don gudun abin da zai kai ya kawo, haka mazauna birnin ma kullum cikin firgici ba za a yi kwana biyu ba sai ka ji an kawo hari a wuri kaza ko kuma bomb ya tashi.


Harkar ilimi ma ya lalace, tattalin arziƙi ya yi dogon suma, al’umma sun shiga halin ha'ula'i. Komai ya yi tsada, daidai da gero da dawa mai ƙaramin ƙarfi sai ya yi da kyar, saboda rashin aikin yi da kuma sana’ar yi ya sanya wasu afkawa mugayen ɗabi'u.


 Yayin da zaɓe ya gabato ne gwamnati ta fara ƙoƙarin gyara wasu matsalolin domin samun ƙuri’un jama’a.



 Ƙasaitaccen mutum ne mai cikan haiba da sura. Ya sauke ajiyar zuciya da gyarar murya tare da cewa: “Masu kallonmu barkanmu da sake saduwa a wannan shirin namu mai farin jini mai taken ‘SIYASA RIGAR 'YANCI’ wanda muke gabatarwa a akwatin talabijin don gayyato muku 'yan takarkaru domin jin manufofinsu idan suka samu mulki. A yau filin namu ya yi babban kamu, inda muka gayyato gwamna mai ci kuma ɗan takarar gwamna a karo na biyu a inuwar jam’iyyar UCP.” Ya kai duba izuwa baƙon yana murmushi, “Mai girma gwamna, masu sauraro za su so jin me ya ja hankalinka na son ƙara zarcewa kan kujeraka, da manufofinka na ci gaba da za ka ci gaba da yi ma jihar taka a takaice.”

Ya sauke ajiyar zuciya tare da murmushi a fuskarsa. “Alhamdulillah, ina son na zarce ne saboda na ɗora akan kyawawar aiyuka da muka fara, jiharmu na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro muna iya bakin ƙoƙarin wajen inganta tsaro, amma ka san shi ɓarna za a yi shi nan take, amma kuma gyara sai a hankali. Na zanta da shugaban ƙasa akan matsalar tsaro da ya addabe mu, don shi ne abin da ya fi komai ci mini tuwo a kwarya, don ka san sai da zaman lafiya ake samun ci gaba. To shugaban ƙasa yayin mun wasu alƙawura wanda sirri ne tsakanina da shi ba zan furta su anan ba, amma za a gani a ƙasa. Talakawa ina muku albishirin matsalar tsaro ta zo ƙarshe duk wasu 'yan ta'adda sai mun daƙile su mun shafe su cikin kwanaki ƙalilan, don shirin da muka yi a wannan ƙaron ba irin wanda aka sani ba ne." Ya numfasa, sannan ya ci gaba, “Daga cikin manufofina na ci gaba da zan kawo wa jihata, akwai: bunƙasa ilimi, don kuwa ilimi shi ne gishirin rayuwa. Sannan farfaɗo da tattalin arzƙi, in sha Allah za a samu sauƙin rayuwa, then ina wa al'umma albishir duk wani ma'aikaci da muka dakatar mun dakatar ne saboda wasu bincike da muke kuma bincike ya kammala ƙarshen watan nan kowa zai koma kan aikinsa, tare da ƙarin albashi. Kuma a kowace ma'aikata za mu ɗauki aiki da zarar an sanar kana iya kai takardunka muddin kana da rabo za ka samu, don wajen ɗaukar aikin cancanta za a duba ba sani ba sabo."

Ɗan jarida murmushi ya yi, "Gaskiya ka yi mana daddaɗar albishir, na san masu sauraronmu zukatansu na cike da farin ciki na abin da ka ce. Daga ƙarshe wanne ƙira za ka yi ga al'ummar ka?"

 Ya shafa kasumbarsa, "Ƙira da zan yi gare su shi ne; daga sama har ƙasa su zaɓi jam'iyyar UCP, domin wannan jam'iyyar ita ce jam'iyya ɗaya da za ta jin ƙan talakawanta, ta kuma sauƙe haƙƙoƙi da suka rayata a wuyanta.”

Malam Audu zaune yake tare da abokinsa Malam Garba da ya zo duba jikinsa bayan an sallame shi a asibiti, suna kallon shirin da ake gabatarwa a akwatin talabiji, Malam Audu ya ce, “Maƙaryacin banza, mayaudari an yi walkiya mun gan ka, dube shi ko kunyar al'ummarsa baya ji ya zage yana suburbaɗa ƙarya. Babu wani abu da za ka ce ya yi tasiri wurin talakawa don mun ɗanɗana kuɗarmu a mulkinka."


 Ya kishingiɗa bisa pillow da yake kusa da shi ya ci gaba da cewa: " 'Yan siyasan ƙwarai nagartattu sun kwanta dama, 'yan siyasar wannan zamani ba don su kyautatawa talakawa suke neman mulki ba. Don haka na ci alwashin babu wani ɗan siyasa da zan ɓata lokacina akansa ballantana har na kai ga jefa kuri’a wanda na yi a baya ma yanzu ina nadama.”



 Malam Garba ya dubi abokinsa ya ce, “Bayin Allah na kwarai nagartattu ba sa ƙare wa sai dai a ce sun yi ƙaranci, a yanzu haka ma a 'yan siyasar akwai na kwarai nagartattu masu ilimin addini da na zamani ba ma su ci da addini ba, ka ga Dakta Bashir Hadi  Umar Abdullahi na jam'iyyar NPC zaɓin talakawa ina masa kyakkyawar zato.” Ya dafa shi, “Abokina, ƙuri’arka shi ne ‘yancinka da ƙuri'arka za ka tunkuɗe azzalumai a karagar mulki ka maye gurbinsu da wanda kake wa kyakkyawar zato da fata, amma idan ka ƙi jefa wa ni ma na ƙi masu irin ra'ayinka ma suka ƙi, sai azzaluman su yi ta nasara suna cin zaɓe a ɓagas kuma su ci gaba da gasa mana aya a hannu, amma idan muka haɗa ƙarfi da ƙarfi muna tunkuɗe ire-irensu to ina tabbatar maka 'yan siyasa za su na jin tsoron talakawa suna yi musu abubuwan da ya kamata ko don kujerar su."

 Ya ja dogon numfashi, "Kai ai ko don butulcin da Matawalle ya yi maka ya dace ka yi zaɓe, saboda haka ka janye ra’ayinka na rashin yin zaɓe ka zaɓi wanda ya cancanta. Yanzu ne kake da damar yin ramuwar gayya, wanda aka ce ya fi ta gayya ciwo.”


Namir Alhasan da ke hira da mai girma gwamna ne ya kuma cewa, "Laifin daɗi ƙarewa anan zan ja linzamin shirinmu na 'SIYASA RIGAR 'YANCI' sai kuma wani mako idan Allah ya bar mu da numfashinmu za a kuma jin mu da wani baƙon."

 Ya juya kan mai girma gwamna, "Ranka ya daɗe muna godiya da samun damar da ka yi ka halacci shirinmu kuma ka amsa mana tambayoyinmu. Masu kallonmu a madadin Mai girma gwamna Alhaji Matawalle Mainasara, ni Namir Alhasan ke cewa mu kasance tare mako mai zuwa."



Washe gari da hantsi Malam Audu na zaune akan tabarma bayan ya kurɓi ruwan bunu da ke gabansa ya tuna da gwamna Matawalle da yadda ya sha wahala wajen yi masa kamfen da kuma yadda ya juya masa baya, ya kuma tuna da shawarar da abokinsa Garba ya ba shi a take ya yi na'am da shawarar kuma ya ce siyasar da zai yi a wannan karon sai ya fi na kowane lokaci don sai sun kifar da gwamnatin Matawalle ya ce, “Dole na koma marawa Dakta Bashir Hadi Umar baya. Bi iznillah sai mun kifar da wannan azzalumar gwamnatin da ta gaza tsinanawa talakawanta komai. NPC zaɓin talakawa wannan ƙaron ina tare da ke.”


Bayan Alhaji Matawalle ya koma gida suna zaune da abokinsa ya ce, "Ranka ya daɗe na ji hira da aka yi da kai a radio, amma ba ka tunanin abubuwan da ka ce za ka yi su lokaci bai kure ba, zaɓe fa shekara ɗaya fa ya rage."

 Murmushi ya yi, ya kurɓi ruwan roba da ke gabansa bayan ya sha ya ajiye sai ya ce,"Lokaci bai kure ba, cikin sauki zan saye zukatansu, ka san meye matsalar talaka?"


 "Sai ka faɗa ranka ya daɗe."

 "A ba shi kuɗi, yana samu tuni zai manta da azabar ya sha ta baya, to za mu ɗan tsaƙura a ɗan abin da muka tara mu ba su, idan muka ci mulƙi sai mu mayar da ninkin baninki abin da muka kashe musu. Ai talaka saurin mantuwa ne da shi ka azabtar da shi tsawon shekaru goma kana jiyar da shi daɗi na wata uku zai manta baya, duk ƙura-ƙuran da na yi a baya tsakanin shekara 1 ɗayan nan zan gyara kuma ina mai tabbatar maka zan lashe zaben, mulkin fa a hannunmu yake, tun daga sama har ƙasa."


 Alhaji Matawalle Mainasara kamar yadda ya alƙawarta ya cika alƙawarin duk wani ma'aikaci da ya dakatar ya koma bakin aikinsa har da su Malam Audu, kuma ya yi ƙarin albashi da ya faɗa, kafin wata ya ƙare ma'aikata ke ganin albashinsu aikin da ya ce zai ɗauka ma jama'a nata yunkurin kai takardunsu.

 Ɓangaren ruwa duk ya sa an gyare famfuna kowa ne layi idan ka ratsa za ka ga ruwa kamar zai fasa famfo.

 Harkar ilimi ma daga Jam'iar jiha har ya zuwa primary ana karatu babu fashi a kullum.

 Ɓangaren tsaro ma ana ta gwabzawa da masu tayar da ƙayar baya, kuma ana cin nasara a kansu.


 Fati ta zage dantse wajen yin sana'a don cimma burinta na karatun likitanci, duk wasu kyale-kyale ta mance da su duk da dama ita ba gwana ba ce a ɓangaren, ta shiga adashe tana ɗauka sai ta ji an fara sayar da Form ta je ta sayo ta cike. Mahaifiyarta ta ce, "Ke dai Fati kin dage sai kin yi karatun nan alhalin kin san ba ki da gata, ni dai na san da mahaifinki na raye zai yi duk wani faɗi-tashi don ganin kin cimma wannan burin naki, amma tun da baya raye ki haƙura, shi fa karatu ba farawa ba ce matsala ka samu ka gama shi ne matsala, ga fannin da kike da buri akwai kashe kuɗi, kin ga irin sana'ar da muke jalli joga yau fari gobe tsumma abin da za a sa baka ma wata rana yana gagara ballantana tsarabe-saraben karatu. Idan kin yarda da shawarata ki haƙura, idan wannan karatun likianci rabonki wata rana Allah zai nufe ki da yi ta hanyar da ba ki yi tsammani ba."


Ta sosa keyarta, "Umma, shi kenan na yi asarar kuɗin da na sayi form, ki sa a ranki Allah ne mai yi wa mutum, ni dai zan yi karatun nan, koda da ƙafa kullum zan dinga tafiya ina dawowa kuma sutura kwaya ɗaya zan dinga sanyawa, kai ni ko zan rasa abin da zan ci, duk abin da zan samu zai ƙare a karatun na ji na gani zan jure, ke dai kawai fata na gari nake buƙata daga gare ki."


 Fati, bayan ta samu admission, kuɗin da ke hannunta ba zai ishe ta yin registration ba, sai da mahaifiyarta ta sayar da ɗan taurenta kwaya ɗaya da take da shi ta ba ta ta haɗa ta je ta biya, Fati ta ji daɗi sosai ta dinga yi wa mahaifyar tata godiya. 


 Su Fati karatu ya kankama kullum cikin ziryar makaranta, ba a haɗa taura biyu a baki in ji masu magana, amma Fati ita kam ta haɗa tana sana'a duk da hakan na ba ta wahala, amma tana taɓawa kaɗan-kaɗan, saboda idan ta ajiye sana'ar kamar ta ajiye karatunta ne.


 Yayin da jarabawa ya kusa ta duƙufa da karatu babu dare ba rana, har ta rame ta rubuta jarabawarta cikin nasara.

Sai dai kuma da aka yi releasing na result sai ta ga ba ta daga cikin waɗanda suka haye ba ta tsallake ba, abin ya yi matuƙar zuwa mata da mamaki saboda yadda take answering questions tana da yaƙinin cikin kaso 100 za ta samu 70, amma sai ta gan ta cikin waɗanda suka faɗi. Waɗanda ba su mayar da hankalinsu ga karatu ba sai ta ga duk suna murna sun haye. Jikinta a take ya yi sanyi a zuciyarta ta ce, "Akwai lauje cikin naɗi."


 Ta yi kuka sosai na abin da ya faru da ita, mahaifiyarta ta ce da ita, "Duk wanda bai ji bari ba ya ji hoho. Sai da na hane ki da yin wannan karatun kika yi kunnen uwar shegu, ga shi yanzu kin yi biyu babu, ba kuɗinki ba ba kuma karatun ba. Ai Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce duk abin da babba ya hango yaro ko ya hau kan tudu ba zai hango ba, abin da na hango miki kenan ke ba ki fahimta ba. Yaushe za a bar ɗan talaka ya yi wannan karatun sai 'ya'yan masu akwai."


 Fati miƙewa ta yi don ƙwaƙwalwarta ba zai jure ɗaukar maganganun mahaifiyarta ba ta shiga ɗaki ta faɗa gado ta ci gaba da kuka. 

 Ranar yau a wurin Fati, ta yamutsa duniyarta daga mai taushi zuwa mai zafi, sai wani irin zufa ke karyo mata dalilin hali da ta tsinci kanta ciki. Hawaye masu zafi suka dinga tsere suna kwaranya a kumatunta.



 WASHE GARI.


 Malam Yahaya wanda yake a matsayin examination officer zaune yake a office ɗin sa bisa kujera mai juyawa yana waya yana kyalkyalewa da dariya bisa alamun yana jin daɗin hirar da yake, sai ya ce a wayar, "Ki zo hotel ɗin around 2 :30pm ki same ni a room da muka saba haɗuwa."

 Ya yi shiru kamar na 20 second, "My dear ɗumin jikinki daban yake da na kowane mace haka kuma daɗinki cikin miliyoyin mata ba za a samu tamkar ki ba."

 Jin ana nocking sai ya ce da ita, "I will call you later." Ya katse wayar kana ya ce, "Come in"

  Fati ce ta shigo sanye da hijabi ta rutsuna ta gaishe shi, yana washe ba ki ya amsa.

 

 Ta ɗan sosa keya ta ce, "Sir da ma...."

 Ya katse ta, "Have a sit, sai ki yi magana."


 Bayan ta zauna tana wasa da yatsun hannunta kanta a ƙasa ta zayyane masa damuwarta.


 Ya sauke gilashin da ke fuskarsa. Ya kafe ta da manya-manyan dara-daran idanunsa, kasancewar Fati ba ta saba da irin wannan kallon ba ta ji tsikar jikinta na tashi. Ya ɗan kanne mata ido ɗaya sai ya ce, "Faɗa mini I'D number ki da cikakken sunanki."

 Jikinta na rawa ta faɗa masa, ya dudduba sai ya ce da ita,

"Malama, ai idan mutum ya gama zana jarabawa sai yana bibiyar offices na malamai zai ga samaƙo mai kyau, ke kin yi hakan kuwa?"

Ta yi masa wani irin kallo na ba ta fahimci kalamansa ba ta ce, "Sir, bin offices kuma kamar yaya? Ban taɓa sanin ana haka ba."

Murmushi ya yi, "Na ga alamar rashin sanin kam a tattare da ke, don yadda kike zankaɗeɗiya da kin bi offices ko ba ki kashe kuɗi ba za ki haye. Wannan shi ne babban kuskuren da kika yi, idan kina so ki haye next year sai ki kuma yin registration kina kawo ziyara yadda kike ko babu abin hasafi zan hayar da ke. Fatan kin fahimta."



 Ta girgiza kai, "Ban fahimta ba sir, sai ka yi dalla-dalla."

 Murmushi ya yi yana kallon kwayar idon ta, "Idan kina son ki ci jarabawa sai kin ba ni kanki ina kusantarki, kin ga mafi akasarin 'yan mata haka suke, wasu za su ba da haɗin kan ma, amma idan muka fahimci mahaifinki manyan ɓaryayin gwamnati ne ko manyan 'yan kasuwa sai kin bayar da cin hanci ana releasing result sai ki ga kin yi passing kin fita da kyakkyawar. Maza kuma da babu ribar da za mu ci da su muna karɓar cin hanci mai tsoka kafin mu hayar da su. Amma ke yadda na gan ki talaka ce fitik, idan kika ba ni haɗin kai zan fito da ke duniya za ki manta da wannan talaucin kuma za ki yi karatu ki gama successfully."


 Wani irin firgici da tsoro da tashin hankali haɗe da mamaki suka dirarwa Fati lokaci guda sakamakon furucin examination officer, tabbas ta fahimci Malam tantirin mara kunya saboda yadda ya rufe ido yake faɗa mata maganganun da ya ga dama. Ta runtsa idanunta sai ta ji zuciyarta na tafarfasa haɗe da wani irin ɗaci da ta ji tun daga ƙirjinta har ya zuwa kan harshenta.


Ai kuwa kamar ya san me Fati take rayawa a zuciyarta ya fashe da dariya tare da cewa: "Daga yau daga yanzu ma idan har kin amince za ki iya fara toshe matsalolin da ke addabar rayuwarki a tare da ni."

 Ta miƙe cike da ɓacin rai, "Allah ya tsare ni idan har wannan hanyar shi ne hanya da zan bi tukun na cimma burina har na koma ga Allah to kar na cimma. Kai kake ganin ina da matsaloli, kai ne kake cikin babbar matsala mai halakarwa. Ina maka nasiha da ka sauko daga kan tsani da ka hau mai halakarwa tun lokaci bai kure maka ba, kar ka bari tsanin ita da kanta ta jefar da kai, don idan ta yasar da kai da kanta ka gama wulakanta. Ka tuba ka koma ga Allah tun kafin lokaci ya kure maka. KOWA YA YI DA KYAU zai ga da kyau haka ma wanda ya yi akasin haka. Shi da ma ɗan'adam a rayuwarsa na da zaɓi biyu shiriya ko ɓata duk wanda ka zaɓa yana da saƙamako tun a duniya kyakkyawa ko mummuna. Daga ƙarshe ina son ka sani wannan turba da kake idan ba ka yi gaggawar bari ba akwai ranar nadama da-na-sani da za su zo wanda ba za su yi amfani ba."

 Ta ja dogon tsaki ba tare da ta duba shi ba ta fice. Ya kyalkyale da dariya tare da cewa: "Ke ce da asara. Muddin ina kan kujerar nan kuma a makarantar nan za ki yi karatu ko ke ce huda-huda ba za ki tsallaka ba, muddin ba za ki ba da haɗin kai ba." Ya ci gaba da duba file da ke gabansa.

 Tana cikin adaidata ta ce, "Mutum kamar kamili nagartacce ashe saɓanin haka ne ya Allah ka yi mini katanga da ire-iren su."


 Dakta Bashir Hadi Umar Dattijo ne da yake da matakin PhD yana ɗaya daga cikin lectures na Jami'ar jihar, yayi aiyuka a ma'aikatu daban-daban duk wanda ya yi aiki da su suna yaba ƙwazonsa da riƙon gaskiyarsa da amanarsa. Bai taɓa riƙe muƙamin da ya shafi siyasa ba amma  halin ha’ula’i da jihar take ciki ya sa ya fito takara domin ceton al’umma. Duk da yake jam’iyyar da ya fito a cikinta ba ta yi shuhura ba, amma ya yi ƙoƙari matuƙa wajen wayar da kan al’umma musamman a lokacin da yake yawon kamfe yana faɗakar da jama’a muhimmanci zaɓen nagartaccen shugaba wayayye mai ilimin addini da na zamani wanda ya cancanta shi zai kawo wa jiha ci gaba kar a yi duba da jam’iya ko kuɗi.

 Malam Audu na Matawalle ya canja sunansa zuwa gadan-gadan ɗan gani kashen Malam Bashir, wasu idan suka gansa sukan ce da shi gadan-gadan sai ya ƙarasa da da ɗan gani kashen Malam, haka a social media wannan sunan ke yawo.


 Kullum ba shi da aiki sai tallata ɗan takararsa a kafafen sada zumunta a wani sa'ilin kuma yakan ɗora hoton Matawalle tare da zayyano yadda ya kassara musu jiha, da kuma abubuwan da yake yi a yanzu na yaudara. Alhaji Matawalle da ya fuskanci abubuwan da Malam Audu da yake yi na tasirantuwa ga jama'a zai iya kawo masa matsala a tafiyarsa take ya sa aka nemo masa shi.



Alhaji Matawalle da Malam Audu zaune suke a guest room nasa, an ajiye masa abubuwan tanɗe-tanɗe da lashe-lashe a gabansa, lamarin ya zo wa Malam Audu da mamaki wai shi ne yau ake mutuntawa haka, da walakin goro a miya.


 Ajiyar zuciya ya sauke, yayin da yawaltaccen murmushi ya bayyana a fuskarsa ya dubi Malam Audu tare da cewa, "Saboda ba ni da enough time ba zan yi dogon surutu ba, kai tsaye zan faɗi dalilin da ya sa na gayyato ka."

 Ya gyara zama ya ɗan numfasa kaɗan ya ce, "Audu na Matawalle, kar ka yi tunanin na manta da gwagwarmaya da ka yi mini a baya, ina sane da kai kawai wasu abubuwa ne suka sha mini kai sai isa ban waiwaye ka ba, amma ka sani na yi maka tanadi da lokaci ne kawai zai nuna haka, Malam Audu ina so ka bar tafiyar matsiyaci, me ƙwaryar sama ta ci ballantana ta ba wa ta ƙasa. Ka dawo tafiyata ka ci arziƙi, ina mai tabbatar maka kana daga cikin list na waɗanda zan ba su commissioner idan na zarce."

Ya sauke ajiyar zuciya ya dubi PA nasa ya ce, "Miƙo mini jakar can." Ya amsa da "To, Ranka ya daɗe."


 Ya dubi Malam Audu, "Na ba ka kwana biyu ka je ka yi shawara akan batu da na zo da shi, ga waɗannan kuɗaɗen na ba ka su ne a matsayin somin taɓi, idan ka yarda za ka yi tafiya da ni, za ka yi faɗi-tashi kamar yadda ka yi a baya zan ba ka ninki ba ninkinsu, haɗe da ba ka kujerar commissioner.." Yana gama faɗa masa ya fice PA shi ya mara masa baya.


 Malam Audu ya juya ya ga muƙarraban Alhaji Matawalle ɗaya bayan ɗaya bai waiwayi kuɗin ba, ballantana ya kai ga ɗauka ya ja dogon tsaki kawai ya fice.

 'Yan maulan Alhaji Matawalle suka fara kallon junansu ɗaya daga cikin ya ce, "Asararre kai ko a lahira ina ga ba ka daga cikin masu rabo."

 Ɗaya daga cikin ya ce, "Kai dai bari abokina, a ba ni wannan makudan kuɗaɗen ai ko ubana ne idan ba zan samu irin wannan a wurin sa ba, zan bar tafiyarsa ballantana wani can banza."


 Malam Audu zaune yake a dandamalin kofar gidansa ya ce a fili, "Alhaji Matawalle ashe daman ka san ina da rana? Ai ko duniyar nan gaba ɗaya za ka ba ni ba zan yi tafiyarka ba."

 Malam Garba ne ya zo, bayan ya zauna sun gaisa, Malam Audu ya zayyane ma abokinsa abin da ya waƙana tsakaninsa da Alhaji Matawalle Mainasara.

"Haba abokina, amma ka yi wautanci, me ya sa kaki karɓa, yasin idan ni ne karɓewa zan yi idan zaɓe ya zo na juya baya na zaɓi wanda ya dace."

 Ya girgiza kai, "Hakan da muke yi shi ya sa 'yan siyasar ke yi mana abin da suka ga dama, suna ganin kuɗinsu zai sa su samu kanmu cikin sauki duk rashin kyautatawa da suka yi mana. To ka sani ni ba na daga cikin waɗanda za a yaudara da kuɗi, na samu arziƙin siyasa a baya yau ina yake ɓeran masallaci ya fi ni, to haka idan na kuma karɓa ma babu tasirin da zai yi, saboda haka ka sani na fifita 'yancina sama da abin duniya."

 


 Alhaji Matawalle Mainasara yayi mamakin abin da Malam Audu ya yi masa, amma jiga-jigan manyan 'yan siyasa sun nuna masa ya kwantar da hankalinsa suna nan suna saye ƙuri'un jama'a ba makawa shi zai lashe zaɓe.


 Ranar zaɓe jama'a sun fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu suka zaɓi waɗanda suka cancanta. Cancanta ta fi kuɗi. Ko da naka, ka so na kwarai. Yayin da mutanen Dakta Bashir Hadi suka kasa suka tsare babu damar a yi musu maguɗi komai a idonsu ke waƙana.

 Talakwar jihar sun ba da abin mamaki, sun gaza mance wahalhalu da suka sha a baya, duk da gyare-gyaren da Matawalle ya yi hakan bai sa ya samu ƙuri'ursu Dakta suka dinga jefawa ƙuri'arsu.

 Jama'ar Matawalle Mainasara da suka ga alamun maigidansu zai iya shan kayi, saboda Dakta Bashir shi ke jan ragamar mafi kaso cikin ƙananan hukomomi hankalinsu ya tashi suka fara tayar da tarzoma suka nuna dole a ƙara zaɓe saboda akwai inconclusive.

 Shugaban zaɓe ya ce ina wannan zaɓe ingantacciya ce saboda haka babu wani abu da za a dakata.



  Matawalle yana zaune a falonsa tare da muƙarrabansa suna sauraron sakamakon zaɓe da ake faɗi a talabijin, da ya fahimci Dakta Bashir shi ne akan gaba da ƙuri'u masu rinjaye na kananan hukumomi jihar, sai ya shiga tashin hankali zufa ya fara yanko masa ba ƙaƙƙautawa.

Zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa, sa'ilin da aka sanar da Dakta Bashir Hadi na jam'iyyar NPC a matsayin wanda ya lashe zaɓe shi ne zaɓaɓɓen gwamnar jihar ya miƙe ya fara kai wa da komowa ya bugi teburin da ke kusa da shi, “Kamar ni Matawalle za a ce na faɗi a zaɓe. Mutumin da na ɗauke shi a matsayin ɗan kuikuyo da nake biyansa albashi shi ne wai zai jefar da ni? Duk irin mahaukacin kuɗi da na ɓarnatar, amma talakawa suka ɓige da zaɓan matsiyaci. Tabbas ba sahihin zaɓe a ka yi ba, sai na kai ƙara kotu.”Ya goge zufan da ke tsatssafo masa a saman goshi da kyalle, “Lallai abokin hamayya baya kaɗan. Ko a mafarki ban yi tunanin wannan matsiyacin zai yi nasara a kaina ba.”

 Ɗaya daga cikin muƙarrabansa ya ce, “Ranka ya daɗe, kwantar da hankalinka kotu za ta ba ka kujerarka, ai wannan zaɓen daga gani an saye shugaban zaɓen, tun lokacin da jama'ar mu su ka ce inconclusive shugaban zaɓe ya ki nasan hakan ne za ta biyo baya.” 

Alhaji Matawalle ya ciji laɓɓansa ya girgiza kai ya ƙara sautin talabijin ya ƙura idanu sai ya hango Malam Audu ne da ya yi gwagwarmaya a baya a kansa yake gabatar da jawabin murnar lashe zaɓe da Dakta ya yi da cewa, “Kamar yadda kowa ya sani sunana Malam Audu labaran, wanda ake wa iƙirarin gadan-gadan ɗan gani kashen Dakta Bashir. Muna yi wa Allah godiya da ya ba mu nagartaccen gwamna. Mu yanzu talakawa mun farka daga dogon suma da muka yi a baya, mun fahimci me ake nufi da siyasa da kuma wa ya cancanta a zaɓa. Shi da ma rayuwa duk wanda YA Yi DA KYAU zai ga da kyau, haka ma wanda ya yi akasin haka zai ga saƙamakonsa. Muna fata za mu ga da kyau a wurin Dakta. Ina ƙira ga talakawa da ke faɗin duniya idan za su yi zaɓe su duba waɗanda suka cancanta ta hanyar nagartar ɗan takara da wayewarsa da kuma iliminsa. Haka shi…” Matawalle ya kashe talabijin saboda takaici ba tare da ya bari ya gama sauraron maganganun Malam Audu ba.



  Wayewar Litinin ta kasance safiya mai ɗumbin tarihi ga dukkan jama’ar da ke jihar, domin duk inda ka zaga za ka ga suna fara’a suna jin daɗin wanda suke fata ya lashe zaɓe, tsiraru ne fuska a murtuke kamar damammen koko wato waɗanda suke goyon bayan Matawalle.


 A mako mai zuwa ne aka kuma yin zaɓen shugaban ƙasa, a nan ma party NPP ce ta yi nasara ta kayar da shugaban da ke kan mulkin na jam'iyyar UCP.


 A ranar da aka rantsar da Dakta Bashir Hadi, Matawalle Mainasara ya shiga tashin hankali kamar ya zauce haka ya kasance ya fara sambatun magana sai wani wuri daban aka nema aka killace shi matarsa kaɗai ke tare da shi. Gaskiya giyar mulki bala'i ce.


  Zaɓaɓɓen gwamna ya shiga office ɗin sa, ya duƙufa yin aiki gadan-gadan ba ji ba gani, yana iya ƙoƙarinsa ganin ya faranta zuƙatan talakawarsa, daidai da aiki idan ya bayar sai ya bibiya an yi aikin yadda ya kamata ko kuma ana sa ha'inci a ciki, cikin ƙanƙanin lokaci ya kawo gyara a jihar ya kuma yi aiyukan da tsawon shekaru goma ba a yi su ba.

 Gwamna Matawalle Mainasara ya miƙa ƙara ƙotu bisa zaɓen da aka yi, sai dai kuma kash ya gaza cimma nasara dole ya haƙura ya dangana a dole.

  

 Mai girma gwamna ya ba da sanarwa zai ɗauki nauyin karatun 'ya'ya mata 50 a faɗin jihar waɗanda za su karanci fannin likitanci, amma sai an shirya jarabawa wanda ya ci ne zai amfana da wannan garaɓasar.


 Fati na jin haka ta shiga cikin jerin masu yin jarabawar, bayan ta yi ta duƙufa da addu'a babu dare ba rana ta yawaita nafilfili musamman da sulusin dare da azumi bisa Allah ya ba ta nasara akan abin da ta sa a gaba.

Allah ma ji roƙon bayinsa ana sake jarabawar Fati da ta je ta duba sai ta ga tana daga cikin waɗanda suka yi qualifying. Ta dinga hamdala ga Allah subhanahu wata'ala domin shi ya nufa, zuciyarta cike da farin ciki ta nufi gida ta yi wa Ummanta daddaɗar albishir.

 Examination officer Malam Yahaya kuwa, wata daga cikin ɗalibansa ce da ya ci amanarta ya dinga badala da ita da zummar zai aure ta ya munafurce ta ya je ya auri wata da ta ga haka da shike gogaggiyar 'yar duniya ce ba ta da mu da abin kunya ba, ta sake hotuna har da video na iskanci da suke a social media.


 Aure a sirrance ya yi bai taɓa tunanin Zara za ta sani ba, amma maganar duniya ko a ƙarƙashin ƙasa ka binne sai ta fito an ji.

 Zaune yake a saitin mirrow cikin gajeren wando da singlet yana taje sumar ƙansa amarya ta turo kofa babu ko sallama tana huci ta miƙa masa wayarta.

"Ungo." ta ce da shi, "Honey lafiya kin haɗa rai me ya faru?"

 Ta dalla masa muguwar harara "Na ce ka karɓi wayar ba kuma ka ga abin da ke cikin wayar, za ka karɓa ne ko ba za ka karɓa." Ta faɗi hakan cikin ɗaga murya.


"Calm down dear zan karɓa mana."

 Ya karɓa yana dubawa sai ya ga hotonsa tsirara shi da Zara, ya zaro ido, "What? Wallahi wannan haɗawa aka yi ban ma san yarinyar ba, aikin maƙiya da mahassada ne suna son ganin bayana Allah ya fi su."

  Zara ce ta bankaɗo ta shigo, kanta ɗaure da attachment ta sanya matsatssun kaya, kallo ɗaya idan ka yi mata za ka gane gogaggiyar'yar duniya ce.


 Yahaya na ganinta ya rikice ya ce, "Me ya kawo ki ta ya ya kika san nan ne gidana?"


Ta kyalkyale da dariya tare da yin tafi, "Ka mance da waye Zara ina ga shi ne za ka yi wannan tambayoyin, amma idan da kana sane da waye ita, ai ka san wannan ƙaramin abu ne cikin aiyukanta. Ni za ka yaudara ka ci amanata ka wanye lafiya ƙarya kake wallahi."

Mahfuza ta shiga mamaki tabbas hotunan badala da ta ga na mijinta da wannan yarinyar da ke tsaye gabansu ne.

 Ya nuna ta da yatsa, "Ki fita daga gidan nan tun muna sheda juna. Idan kuma ba haka ba sai na karairaya ki wallahi. Wa zai auri karya, ai ko mata sun ƙare a duniya ba zan aure ki ba, ballagaza shashasha."


 Mahfuza ta cukume mijinta, "Wallahi sai ka sake ni saki uku, ba zan taɓa zaman aure da mazinaci ba, na yi nadamar auranka da na yi. Duk rashin bincike ne da iyayena ba su yi akanka ba ya jawo mini haka, ni ma da kwaɗayin kawai na gan ni gidan miji duk ƙawayena sun yi aure sun bar ni na ƙi yin duba da nazari da bincike akan nagartarka kawai na yi duba da ɓarin kuɗi da kake yi mini na yarda da auranka. Na yi nadama amma kuma na godewa Allah da ya tona asirinka ban ɗauki tsawon lokaci ina rayuwa da mazinaci ba."

Zara ta yi wani murmushin mugunta, "Haba sister yaushe aka yi aure za ki zaɓi zawarci. Ki karɓi ƙaddara kawai. Ni da ma na zo na yi muku fata na alheri ne, kuma na san yana gigin amarci da kyar ya hau social media ya ga abubuwan da na ɗora shi ne na zo na yi masa tuni ya hanzarta hawa ya gane ma idonsa kar a ba shi labari. Ashe tuni amarya ta gani ta kyalkyale da dariya."


 Malam Yahaya kamar ya nutse a ƙasa saboda kunya ya jiƙe sharkab da zufa kamar wanda aka watsawa ruwa.

 Ta kyalkyale da dariya, "Ango ka sha ƙamshi. Happy marriage life."

 Tura kofa aka yi sai ya ga uwargidansa da yaransa samari maza biyu, da police da wani babban soja sanye da uniform kana da ɗalibarsa Fa'iza sanye da hijabi tana nuna shi "Daddy shi ne wannan." Ta fashe da kuka.

 Mujahid da ya ga Zara ya nuna ta da yatsa, "Mummy wannan ba ita ba ce yarinyar da hotonta da Daddynmu yake ta trending a social media ba."

 Mahfuza ta zaro ido a zuciyarta ta ce, "Daddy, Mummy me hakan ke nufi? Alhaji fa ce mini ya yi matarsa ta mutu kuma ba ta taɓa haihuwa ba."

 Zara ta tauna cingam da ke bakinta ta hura kana ta ce, "Kwarai ba karya ni ce, kuma dai kun gani ashe? Abu ya yi kyau gaskiya."

Adnan ya sharara mata mari, " 'Yar iska karuwa kin san hotunan nan ɓata mana suna da ya yi, abin da kika yi shi yake ta trending a social media, abokaina da suka san mahaifina sai ƙirana suke a waya."

Ta kyalkyale da dariya, "Marin da ka yi mini ba zai sa raɗaɗin abin da ya faru da kai ya goge ba, zafin da kake ji a rai ya fi zafin marin da ni nake ji. 'Yar iska da karuwa da ka ce da ni kuwa ubanka shi ne ubangidana a harkar, shi ya kamata ka fara cin zarafi. Ku sunanku ne kawai ya ɓaci na kuma rayuwata ya lalata. Lastly i am warning you idan hannunka ya kuma taɓa jikina you will regret stupid."


Police ɗin ne ya yi tsawa ya ce, "Ku dakata mu mu yi abin da ya kawo mu."

Ya dubi Malam Yahaya, "Hope ka san yarinyar nan da ta nuna ka da yatsa ta fashe da kuka."

Kansa a ƙasa ya ce, "Eh, na san ta sir."

"To za mu tafi office da kai za ka amsa wasu tambayoyi."

Zara cikin fari da ido ta ce, "Sir a fasa kwan mana a nan ba sai an kai ga office ba ahalinsa su ji."

Ya dube ta, "Ki shiga taitayinki ba a yi wa aikinmu katsalandar."

Babban sojan ne ya ce, "'Yata za ka ci wa 'zarafi ko? To wallahi sai ka shiga gidan yari."

 Zara ta zo kusa da Yahaya ta kalle shi sama da ƙasa a wulakance ta ce, "Kaɗan ka gani."

A ka ingiza Malam Yahaya aka tafi da shi.


Bayan ta yi kyas kyas da cingam da ke bakinta ta dube su ta ce, "Shekara 2 muke shaƙe aya da Alhaji da zummar zai aure ni, kawai sai labari ya riske ni ya yi aure har mata tare a lokacin da na ji sai da hanjin cikina ya kaɗa, ya yi mini alƙawarin zai aure ni bisa dalilin haka na watsar da duk mazan da muke lalata na tsaya a iya shi. Na shiga damuwa da ɗimuwa sanadiyyar samun labarin aurensa, na zaɓi wannan hanyar na yaɗa hotunanmu da video ma duniya don ya tozartu ya kunyata bisa abin da ya yi mini. Ya ɗanɗana zafin da ni ma nake ji"

 Ta girgiza ƙafaɗa, "Ni abu na rashin kunya ba sabo ba ne gare ni, shi ɗin ne dai na sani dole ya shiga tasku, babu wani namijin da duk iskancinsa zai so abin zai taɓa martabar iyalansa."


 Adanan ne ya yi kanta zai mangaɗe ta, mahaifiyarsa ta shiga tsakani ya ce cikin zafin rai, "Wa ya buƙaci jin labari fice mana daga gida."

 Ta juya dara-daran idanunta, "Zan fita, amma ka bari na isar da saƙona na ƙarshe zai amfane ka zai amfani iyayenka."


 Zara ta dubi matan da 'ya'yan ta yi guntuwar dariya, "Ko kun fahimci maganar laftanal inda ta dosa? Ina kyautata zaton wannan kamilar yarinya ciki Yahaya ya yi mata, ni fa ba cikin ba ne damuwata cuta mai karya garkuwar jiki da ya harba mata, amarya kema na san an ci amarci da shi a gaggauta yin gwaji, ke kuma uwargida, ina ga da kamar wuya idan an harba miki, don da bakinsa ya ce da ni ya fi shekara uku bai kusance ki ba ba ki da maraba da dutse, amma kuma idan kina tunanin akwai lokacin da jaraba ya addabe ki kika yi wasu 'yan siddabaru ya kusance ki, to a tuntuɓi likita, don samun nutsuwa. 'yan samari Babanku na da cuta mai karya garkuwar jiki don tare muke shan magani. Kaɗan ya gani sauran bala'i na nan tafe."


 Adnan ya yi kukan kura zai yi mata duka ta kauce, "Ka taɓa ni yanzu sai na ƙira maka police a jefa ka a inda tafin hannunka ba za ka iya gani ba saboda tsananin duhu, kuma sai na ba da umurni kafin a fito da kai."

 Mahaifiyarsu Adnan ne ta ja hannunta, "Don Allah ki tafi, mun gode."

"Ban buƙatar godiya, tafiya kuma ko ba ki faɗa ba zan tafi."

 Tana tauna cingam tana kwarkwasa ta fice. Mujahid wuri ya nema ya zauna ya tafka tagumi, amarya barin wajen ta yi cikin sheshshekar kuka.

Yayin da Adnan sarkin zuciya ya dinga gwara kansa a bango yana cewa, "Ya Allah me ya sa ka tsawaita rayuwata na ga wannan baƙar rana. Na yi nadamar zuwa cikin wannan duniya, na yi nadamar kasancewata tsatso na wannan baƙar zuriya."

 Mahaifiyarsa ce ta jawo shi, "Ya isa haka! Zantukanka saɓo ne babba wurin mahallici."



Mahfuza ta faɗa gado ta kwanta rigingine hawayena na malala a ƙuncinta ta ce, "Ya Allah na gode maka, tun da na shigo gidan nan ina off babu wani abu da ya shiga tsakanina da wannan macucin. Idan na harbu da wannan cuta ina zan saka raina, ya iyayena za su ji a ransu. Yau nake tunanin samun tsarki sai kuma ga abin da ya faru, ya Allah na gode maka da ka ƙare ni."

 Ta miƙe ta fara haɗa komatsan kayanta a akwati, tana fitowa abokiyar zaman nata da ta ganta ta miƙe ta tare ta, "Ina za ki tafi?"

 Ta share hawaye, "Gidan iyayena, aurena da Alhaji ya ƙare. Ko shi ne autan maza aurena da shi ya ƙare, maƙaryaci ya ce da ni matarsa ta mutu bai da 'ya'ya sai ga shi na gani. Ga abu mafi muni mazinaci ne yaushe mutum zai haɗa iri da shi."


"Ki yi haƙuri ƙanwata, ki koma ɗakinki komai zai daidaita. Ai Alhaji ba iya waɗannan ba ne 'ya'yansa akwai mata uku ma again."

 Ta ja jakarta, Mujahid ya ce, "Umma, bar ta, abin da ta yi shi ne daidai ko kema zama da Abbanmu ya ƙare ku miƙe mu tafi."


Yahaya ya ɓoye wa matarsa lamarin aurensa a jita-jita ta ji a hakan ma a ranar auren, kuma tun da amarya ta zo ya tare a can bai waiwaye ta ba.

 Hajiya Karima zaman haƙuri zaman 'ya'yanta take da Alhaji, babu wani haƙƙin aure da yake sauke mata, kasancewar tana aiki sai take ɗawainiyar gida da albashi da take samu.

 'Ya'ya mazan ma da shike suna sana'a sai suke tallafawa mahaifiyarta su.

 Hajiya Karima idan ba ita ta fito ta faɗa maka matsalar da take ciki ba, sai ka rantse ka ce tana cikin jerin mata masu jin daɗin rayuwar aure, don duk rashin mutuncin da Alhaji zai mata ba ta tanka masa kuma ba ta sa abin a ranta ballantana ya dame ta, tana godewa Allah da ya nufa tana aiki kuma tana sana'a tana rufawa kanta asiri da 'ya'yanta.

'Yan'uwa mata a riƙi sana'a duk ƙanƙantarsa yana da albarka, kar a dogara da miji ko wani, ki dogara da kanki ki tsaya da ƙafafunki za ki ga nasara a rayuwarki, kuma kin huce takaici.

Hajiya Karima da ba ta aiki da sana'a wanne irin hali kuke tunanin za ta shiga.

 Mijinki ko Ɗangote ne ki kama sana'a. 


 Kasancewar Malam Audu na da masters ya samu lecturing a College of education na jihar, kuma Dakta Bashir ya naɗa shi adviser. Suna rayuwarsu da matarsa Mairo cikin so da ƙauna da kwanciyar hankali.


 Malam Yahaya, an miƙa shi kotu kan zargin yi wa Lawisa Umar Tanko ciki ɗalibarsa, 'ya ga laftanal Umar ya kuma amsa laifinsa, kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 2.


 Bayan ya fito daga zaman kaso, hukumar makarantar da yake aiki a ƙarƙashinsa ta kore sa a aiki bisa manyar laifuka da ta kamasa da shi.

 Saura lectures masu ɗabi'u irin nasa ma tuni suka canja gudun kar su sun ci kansu a irin halin da Malam Yahaya ya tsinci kansa ciki. Bahaushe ya ce idan ka ga gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta, to ka shafawa naka ruwa.


Amarya da Hajiya Karima kuwa tun ana ziryar kotu suka tilasta mijinsu ya sake su ba a son ransa ba ya sake su.


 Malam Yahaya tun da ya fito a gidan yarin ya ji duniyar ta yi masa zafi, mata da 'ya'ya sun guje shi ga aikin da yake na rufin asiri ma ya rasa, ga cuta mai karya garkuwar jiki da yake da shi. Maganganun Fati ne da ta taɓa yi masa office suka dinga yawo a ƙwaƙwalwarsa.

 Mahfuza tana gama idda da wata biyu Allah ya mata gyaɗan dogo ta samu miji ta yi aure.

 Alhaji Yahaya har durƙusawa Hajiya Karima ya yi yana ba ta haƙuri bisa abubuwan da ya yi mata ta yafe masa, sannan ko don albarkacin 'ya'ya da ke tsakaninsu ta koma ɗakinta. Kullum yana sintirin zuwa gidansu biko

 Na ji daɗi shi ne gari ba wai na sha wahala ba. Hajiya Karima fafur ta ƙi, ai ko ka lau yake ba shi da cuta ta gama aure da shi ballantana yana da cuta.

 'Ya'yansa kuwa kullum tana yi musu nasiha kar su guji mahaifinsu ko ya yake uba uba ne, takan tilasta su zuwa gaishe shi da yi masa ihsani.


 

 Kamar yadda ya saba yau ma Malam Yahaya tsaye yake a bakin kofar gidan su Karima ya aiki ɗan almajiri da a yi sallama da ita.


 Bayan ta fito sun gaisa ta ce, "Abban Mujahid yanzu ina da banbanci da baya, tsawon magana da kai haramun ne saboda akwai igiyar wani a kaina kana iya faɗan abin da ya kawo a hanzarce, na ɗaura aure kuma nan da sati zan tare a Saudiyya zan zauna."

"Wannan tatsuniya ce ki ɗaura aure ban sani ba, ke dai kawai idan yawan zuwa na ne ba ki so sai mu daidaita ta waya."

Ta watsa masa invitation card na aurenta tare da cewa, "Waye kai da zan ɗaura aure har ka sani, kai lokacin da ka yi naka ba a jita-jita na ji ba. Wallahi gwamma na karashe rayuwata ba tare da na yi aure ba da na auri irin ka."

 Ta ja dogon tsaki ta bar shi tsaye. Da ya duba katin ɗaurin auren sai da gabansa ya faɗi, don mijin da ta auran shahararren mutum ne da duniya ta san shi ɗan ƙasar Nijeriya ne amma hulɗa da kasuwanci ya sanya ya koma da zama a Saudi Arabia.

A fili ya ce, "To a ina ya gan ta ko in ce a ina ta gan shi har suka kai ga yin aure."

 Karima ba ta kusa ballantana ta ba ka amsa amma na ari bakinta na ci mata albasa zan ba ka amsar tambayarka. Allah ne ya haɗa su fakat!


 Malam Yahaya da ya koma saboda yadda abin ya kaɗa shi take ya ji zazzaɓi ya rufe shi haka ya kwana bai runtsa ba.


Fati, ta zama cikakkiyar Nurse, ɗaya daga cikin lectures na su ne ya yi duba da ƙoƙarinta da hazaƙarta, ya kuma lura da kamun kanta ya miƙa mata kokon bararsa ta soyayya, kasancewar ita ma tun da take makaranta ta lura da shi mutum ne mai nutsuwa da jan aji tuni ta amshi soyayyar.

 Soyayya ta yi ƙarfi abin har magabata suka shigo ciki aka sanya ranar bikinta da shi.

 Bayan ta tare a gidansa ne ta samu aiki a specialist hospital, bayan nan ta nuna wa mijinta ita fa tana da buƙatar kara zurfafa karatu ta zama professor a fannin cututtukan da ya shafi mata, ya nuna mata yana tare da ita zai ba ta duk wani gudummawa muddin bai fi ƙarfinsa ba.

 Fati zamanta da mijinta abin sha'awa mahaifiyarta da ƙannenta ma tana kula da ɗawainiyarsu.


Alhamdulillah


Ƙarshe.