Episode 26-27
💅SARKI SAMEER.....💅
by❤xeemat....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
﷽
Bismillah.........✍🏿
Episode 26&27
"""""""""""""""""""""
cigaba yayi da bubbuga ta yana kiran sunan ta amma shiru no response miqewa yayi yakoma gurin dadda dake kwance a qasa amma ita ga dukkan alamu babu wani ciwo ajikinta kamar ma suma tayi yana zuwa gabanta yatabbatar da ranta kwasa yayi aguje yafita waje ruwa yadebo yadawo duk yabi ya rikice ya fita hayyacin sa yanazuwa ya yayyafawa dadda aikwa tasauke wani dogon numfashi tunda yaga haka be bi takanta ba yaqara komawa kan Ameesha yana qara kiranta amma ina dadda da tadawo daga doguwar suman datayi ahankali tafara bude ido amma bata gani radau sai dishi dishi jin kamar ihun mutum adakin kuma kamar muryar namiji yasata qara rife idon tare da dan murzashi sai ta qara budewa sosai yanzu tagani sai yanzu kuma abun da yafaru dasu yashiga dawomata a brain asukwane ta mike kamar wacce aka tsikara bossay nagani ta miqe yayo wajenta yace dadda me yafaru daku waye yaayi muku haka ankashe ta fa Ameesha ta mutu sai nakashe duk wanda yakashe ta saina kasheshi da hannuna yafada yana nunawa dadda hannu dadda datayi mutuwar tsaye jin abun da bossayn kecemata sai kuma tashiga girgiza kai hawaye na rigerigen fitowa daga idanunta muraya na rawa tace bata mutuba bata mutuba kar kaqara cewa ta mutu ni jikata bata mutuba nasan bazata mutu tabarni ba tafada tana qaraswa inda Ameeshan take akwance itama jijjigatan tayi amma abun da bossay yaji yagani itama haka tagani qamewa tayi awajen ta kasa koda daga hannuta ko motsi takasayi bossay dake bayan ta shima ya qame din sai kuma can daga bisani yazabura yayo wajenta yace tare da daga ta yasakata akafada yace dadda muje asibiti shi sai yanzuma ya tuna da asibitin rudewa tasa duk yama manta da wani asibiti said yanzu be jira cewar dadda ba yafice da sauri dadda ma ai da sauri tabiyo bayansa ko mayafi bata daka ba bare tayi tunani saka takalmi atare suka qaraso gurin motar back seat yabude yasaka ta dadda ma tashiga bayan shikuma yakoma gaba da sauri yatashi motar yajata a tsiyace da gudu idonsa ya rufe kawai gudu yake kwararawa akan titi dan alokacin da wata motar zatasha gabansa inajin baze tsaya ba dan ze iya bi takanta tunkan yazo waje yake dokawa mutane horn wanda yake son ransa kwa ya matsa ya basa hanya duk wanda yaga irin gudun da yakeyi kamar a filin tsere sai ya jinjina masa ko tsoro ma bayayi yaje yadaki wani gurin wasu suce Allah yakiyaye wasu kuma suce Allah yasa ya bugu da wani abun saboda wannan gudun da yakeyi yayi yawa bekamata yaringayi ba kowade da abun da yake cewa akansa duk inda yazo wucewa
Oho shi bema san sunayiba shide kawai tafiya yake ahaka de har yaqarso batate da wata matsala tasame suba sunzo lafiya lafiya yana zuwa yabuga wa gate man din horn shima da wuri akabude shikma yadanna cikin hospital din da yabari dazu saigashi yanzu ya dawo ko parking be gama daidai tawaba yafito ya bude baya yayi saurin bide baya ya cuccubota daman ba nauyi garetaba yana fito da ita yayi ciki da ita dadda nabinshi abaya yanashiga da ita nurses din dake gurin sukai saurin zuwa aka dakko gado aka dorata akayi emergency da ita sukuma ka tsayar dasu awaje da wuri nurses din sukayi saurin rufawa kanta suna bata taimakon gaggawa dan ganin tadawo hayacinta yayi da awaje kuma bossay yake ta faman zarya yakasa zaune yakasa tsaye sai kuma can yadauko wayar sa yakira Ammi ya sanar da ita cewa suna hospital Ameesha ba lafiya dagana kuma yakshe beyi mata kwakwaron bayani ba wata nurse ce tafito daga cikin dakin dasauri dukan su sukayi kanta suna cewa ta farfado girgiza musu kai tayi tace A'a haryanzu ba wani sauyi zamuje musanar da doctors suzo su dubata saboda munkasa taimaka mata tana kaiwa nan tayi gaba dadda ta dora hannu aka tana kuka tana cewa shikenan sunkasheta sun huta suncuce ni bossay ne yayi qarfin hali yace dadda dan Allah kidena wannan maganar in Allah ya yarda bata mutuba zata dawo muci gaba da rayuwa tare sannan yakamota yazaunar da ita akan kujerun tare da ruqo hannun ta sannan yace dadda suwaye sukayi muku haka suwaye suke qoqrin rabaku da duniya kigaya min dadda shiru dadda tayi takasa bashi amsa qara tambayarta yayi nanma shiru tayi tana tunanin mezatace mishi ya yarda dan bazata iya gaya masa gaskiyar abun da yafaru dasuba saboda ba hurimun sabane abun su ya shafa ba shiba dan haka bazata sakashi aciki ba saida ta yanke shawarar abun da zatace Mishi sannan tafara cewa wasune suka shigo fuskarsu duk a rufe suka shigo suka jata zasu fita da ita nikuma natashi na ruqeta ina roqonsu ina riqeta sai wani ya makama min abu tare da jafar dani tundaga nan kuma banqara sanin meke faruwa ba saida kazo tagama bashi labarin tana Matsar hawaye yayi mamki da jin hakan yace dadda kuma bakisasu ba to ku a ina suka sanku tace nima bansani ba nide kuma nasan ba harkar kowa nake shiga ba bare wani yace namishi ba dede ba yace dadda dan Allah wai ku suwaye kuma daga ina kuke baku da dangine ya qarasa maganar yana qare mata kallo yana jiran yaji me zatace amma kawai sai ta juya masa baya batace mishi komai ba ganin hakan yasashi qara juyowa inda tajuya din yace dadda baki ce komai ba hade rai tayi sannan tace wai da tambayar ka zanji koda halin da jikata take ciki tana fadar haka ta mike ta bar masa wajen ta canza guri tazauna tare da tafka tagumi
shide kawai binta yayi da ido yana kallonta da mamaki shibega wani abun jin haushi ba anan daga tambaya kawai shima zama yayi be qara yunqurin binta ba suna ahaka doctors din da suka shiga tun dazu basuga shigar suba sune suka fito yanzu suna fitowa sai bossay yatashi da sauri ya qarasa girin su yana tambayar yajikin nata doctor yace ina iyayenta dadda ce tayi saurin qarasowa gurin tace gani doctor yakalleta tundaga sama har qasa yaga ko takalmi babu gata ba mayafi ajikin tsofe tsofe da ita zata wani ce itace mahaifiyar yarinyar kai yagirgiza bece komai ba yajuya yakalli bossay yace kaifa wanene dinta sai yace yayan tane yace to kai kasame ni a office yana fada ya wuce gaba shikuma ya bishi abaya suna shiga yayi yazauna sannan yanuna mishi kujera yace have a seat zama yayi yana fuskantar shi saida yadanyi jim sannan yafara magana yace agaskiyar magana yarinyar ku tana cikin mawuya cin hali garin ya akai haka tafaru kukayi sake hartaji wannan babban ciwon haka bossay yace wlh nima bansan me akai mata ba ina shigwa gidan natarar da ita awannan halin amma yanzu dr. meye abunyi metake bukata dr. Jamil ya nufasa yace munsha wahala gurin gano ina matsalar take sai da qyar muka iya ganowa amma de mutabbatar bata mutuba ahalin yanzu da sauran numfashin ta saide kuma tana tsaka me wuya dan da qyar ne inzata tashi saboda sai anyi mata aikin kwakwalwa wanda yake da riski wala mutum ya tashi wala kuma yarasa ransa kuma koda yatashin ma ze iya mantawa da komansa da kowa ina akaci sa'a kuma zata tashi lfy qalau saide wataran za ana kasa gane kanta idan abun yajuya mata bade yanda bata yiyuwa bossay ne da yaji gaba daya duniyar tamishi zafi yace sir amma me yasamu kwakwalwar tata yace mishi jini ne ya shiga ciki dan haka dole sai an fidda shi
Ya salam bossay yace sannan yaqara cewa to ba matsala yanzu aikin zekai yaushe da fara shi da gama shi doctor yace mishi a kwana daya ma za a gamashi to amma babbar matsalar itace wanda ze mata aikin baya nan yayi tafiya shine babban likitan amma da sauqi naji ance nan da two weeks ze dawo inyaso mu sai muyi mata allurai da zatai ta bacci harzuwa lokacin da ze dawo hakan ba matsala bane saboda mu bamu da ikon akan bangaren wannan aikin saide mujira da wowarsa yanzu zamu cigaba da bata kulawa anan har zuwa yadawo sannan yace ze iya tafiya ko kuma zasu iya tafiya gaba dayan su saboda bawanda ze samu damar ganinta daga nan har zuwa lokacin da za ayi mata aikin dan haka ba buqatar suyi tazama anan hakannan duk halin da ake ciki za ana sanar dasu......
Jinjina kai bossay yayi sannan yayi masa godiya tare da miqewa jiki asanyaye babu kwari yabar office din yana fitowa ya nufi inda dadda take yana zuwa kuma sai yaci karo da su Ammi ita da faruq da yakawo ta suna ahigo kuma sukayi qoqarin kiranshi danjin a inda suke sai kwai sukai karo da dadda anan Ammi tayi mata magana sai take gaya musu yaje wajen dr. sai suka zauna suma suna jiran fitowar tashi yana qarasowa gabansu duk suka dago suna kallonsa ganin jikinshi duk amace yasa dadda cewa ta mutu ko dannan sun kasheta ko sun rabani da ita takarasa fada tana qara sakin wani marayan kukan Ammi ce tace haba dadda kiyi hakuri mana ki tsaya musaurari me zece bata mutuba in Allah ya yarda ki kwantar da hankalinki sannan ta juya tana kallon bossay tace Aliyu me yake faruwane munga jikinka duk amace me dr. Yace maka huci yadan furzar daga bakin sa sannan yace dadda ba mutuwa tayi ba amma de dr. yace dayan biyu ko tarayu ko ta mutu tasamu accident din brain and blood dole sai anyi mata aiki kuma doctor din dazeyi mata ba yanan sai nan da two weeks zedawo sannan za ayi mata sai yan dakata sannan yadora da cewa yanzu sunce zamu iya tafiya ba wanda ze samu damar ganinta sai angama yimata aiki dadda ce takatse mishi maganar dacewa na shiga uku na lalace yanzu haka za abarta har sainanda sati biyu tana kwance so ake akashe min yarinya lokacinta beyiba to wlh banyarda ba kaf girman asibitin nan ace ba wanda ze iya duba ta sai wani yadawo daga wani waje gskiya wannan maganar da sake inde ba kasheta zasuyiba faruq ne da yau yafara ganin ta maganar ta taso tabashi dariya amma sai yaruqe yace dadda kamar yanda yaji suna kiranta dashi sannan yace bafa zasu kashe ta ba tunda kikaji sunce haka to sunsan me suke yi wannan asibitin bakamar kowane asibitin yake ba inde kinga mutum ya rasu anan to daman Allah yayi anan ze mutu kwananshi yaqare amma suna aiki da kwakwalwa basa wasa da marar sa lfy kuma zasu kula da ita fiye da yanda kike tunani bossay ne yadora mata dacewa dadda aikin ne ba kowa yake yiba saboda riskinshi sai wanda ya kware a harkar sosai inba hakaba za a iya rasa ranta gaba daya ma dan haka ki kwantar da hankalinki babu abun da ze sameta in sha Allah shiru tayi bawai dan ta yarda dazan censu saidan ba yarda zatayi idan tace zata daga murya akai ina zatakaita dole ta hakura ta bi duk abun da sukace Ammi ce ta ruqota ta zaunar da ita tare da qara tabbatar mata ba abun daze faru da ita saboda tasan asibitin basa wasa da aikin su bare harsuzama barin wani duniya saide idan Allah ne yakarbi abunsa kuma wannan daman ba wanda ya isa yahana idan Allah yaso karba dole ayi hakuri hakade taita kwantar mata da hankali har ta fahimce su Ammi tace to yaje ya karbo number dr. din inyaso sai suringa kira suna jin halin da take ciki da to ya amsa mata sannan ya juya ya ya koma office din be dade ba yadawo yace musu ya karbo su tafi miqewa sukayi gaba dayansu kowa jiki ba kuzari suka fito daga asibitin dadda tace itade amaida ta gida Ammi tace a'a tayi hakuri su wace tare ai bazataji dadin zaman gidan ba ita kadai dadda tace taji su maidata da kwai abun da zatayi sukace to su wuce gidan tare tayi abun da zatayi ta dauki duk abun da zata dauka tunda daman sungama shirya wa sai suje tare sujirata tagama
nanma haka tace musu bata yarda ba kawai suje ita ta zatahau motar haya Ammi tace dadda bafa inda zamu bari kije ke kadai bossay ya dora dacewa daman kuma ga abun da yafaru wai wasune sukaje fa gidan sukayi musu haka kuma take so ta qara komawa haba dadda sai kace ba kyason ranki bekamata ki komaba kar kije suqara dawowa suyi miki wani abun kawai ki muje ni karma kikoma gidan kwata kwata kibar musu komai
Dadda jin batun nasu kowa da abun da yake cewa dole ta hakura amma ita tana da dalilin ta nason komawa to amma kar tadage akan komawar har sufara zargin wani abun dan haka tayanke shawarar kawai ta bisun inyaso daga baya ta saci hanya ta koma gidan (tofa dadda me kika ajiye agidan nifa nafara zargin wannan yar tsohuwar nan 🤔dana kasa fahimtar inda ta dosa har yanzu)jin shirun nata yasa Ammi ta cewa faruq yashiga mota yata fi shikadai ita kuma zasu hau motar bossay ita da dadda har yajuya ze shiga motar Ammi tace kai naga har wani sauri kake to wlh kayi gudun haukannan sai na saba maka kama jira mu fara tafiya kaikuma kabi bayan mu saura inga ka wuce mu tana gama fadar haka ta budewa dadda baya tace dadda shiga ba musu dadda tasa kai ta shiga ita kuma ta rufe tasake bude gaba ta shiga tundazu daman bossay ya shiga dan haka kawai tayar da motar yayi tare da yin rivers yadanna hancin motar yana tafiya kamar bayaso yayin da faruq kuma yake binsu abaya cike da takaicin umarnin da Ammi ta bashi gashi kuma yaga alamar yayan nasu kamar ma yana sane yake irin wannan tafiyar oho
shikam bossay bema san yanai ba dan yama manta da shi abayansa ahaka suka fita daga asibitin kowa zuciyar sa ba dadi ...........
#comment
#share
#likes
#vote
Story and writing.......✍🏿
by
❤xeemat....love❤