SARKI SAMEER

Episode 30-31

by @azeemadahiru

💅SARKI SAMEER.....💅

       by❤xeemat.....love❤

   

        🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


       🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹

                ﷽


          Bismillah.........✍🏿

Episode 30-31


      '''"""""""""""""""""""""""""""""

__________________FULANI

Bayan fitar ba kuwar tata ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman zagaye falon take tana tunanin inde harda gasken wannan mutumin da wata manufa yazo me yasa hajiya sara zatace ta kore shi sai ta koreshi batare da ta dau matakiba ai ba inda zashi ya shigo kenan zata barshine anan ai ta azabtar da shi har sai yafadi wanda ya aiko sa sannan kuma akashe shi wannan shine hukuncin da yadace dashi sai kuma wani tunani ya fado mata to shugabansu yace mata bakin su daya ita kuma hajiya sara batace ahada da hamza ba ko kuma bata kalli idonsa bane dahaka zuciyar ta tayi na'am tabbas hajiya sara bata gashiba shiyasa itakadai de taringa saqa tana warware wa ta kulla wannan ta kulla wancan ta warware kuma jakadiya ta kira bayan tazo tace mata taje ta kira mata shugabansu da kuma me doruna tace suyi sauri suzo su sameta 

angama tafada sannan tatashi da hanzarinta tabar falon.....

Bajimawa suka shigo tare suna shigo wa fulani tace suje suyi ta dukan su har sai sunfadi wanda ya turo su kar su raga musu ko kadan kuma kar suyi abun da zasu kashe su batare da sunsan wanda ya aiko suba kawai suyi musu azabtar dasu musamman ma hamza tunda shi na lura yanaji dakanshi to ayi masa abun da sai yayi nadamar abun da yayi a ladaftar dashi abashi horo me tsananin gaske aitayi musu daga nan har waye war gari kuma kar abasu abinci ko abun sha, 

me doruna yace angama ranki yadade mu daman umarnin ki kawai muke jira yake uwar masarautar mu matar sarki uwar sarki kakar sarki yanzu zamu aiwatar da abun da kike so hannu ta daga mishi tare da yi musu nuni da hannu alamar ya isa suje suyi abun da ta Sakasu tagama haka kuma bata jira ficewar suba tashige ciki tabarsu agun suma fita sukayi 

suna fita basu wuce ko inaba sai dakin qasa inda suka ajiye su hamza kafin su shiga kuma saida suka qara kiran wani dogarin shima me duka ne sannan suka shiga ciki susu uku da qafa suka tura qofar dakin da hamza yake ciki saboda ba adaki daya suka ajiyesu ba suna shiga kuwa basuyi wani aune ba,  ba zato ba tsammani kawai suka ga hamza yayi tsalle kan shugabansu ya shaqeshi yana qoqarin rabashi da duniya da sauri sukayi Kansas suba qoqarin rabasu amma ina ko gezau beyiba sai faman huce yake fitar wa sai kace zaki yayi gudu da sarkin dogare yaga haka sai yadaga bulalar hannunsa ze da nufin yasauke ta akan hamza amma sai hamza yayi wani juyi aka sauke ta akan shugabansu a harzuke dayan ma yadaga tashi amma shima be samu nasarar samun hamza ba sai akan shugabansu ta sauka,


"Shide sugaba ya yaga takansa dan yakasa ihun ma da yakeso yayi sakamakon shaqar da hamza yayi masa sai maqyar maqyar yakeyi da ido idon shi yayi ja saboda qamshin mutuwar da yake ji,


Me do run a new yace kai wai kasa kwayane tare jansa yanaso ya rabasu amma shima sai yasamu tsarabar lafiyayen bugu da sai yakaishi faduwa qasa dayan ma kansa yayo shikuma ya buga mishi naushi da dayan hannushi saida bakin ya fashe saiga jini na fitowa ,

Hamzane yafara magana yace wlh duk wanda yaqara rabata sai na kashe shikamar yanda zan kashe wannan mufikin banzar me zuciyar shedan kwata kwata ba Allah aransa yajuya yana kallon shugabansu yace wlh ko kaje kafadi gaskiya ko kuma kabar duniya dan wlh wlh wlh sai na kashe ka idan baka fadi gaskiya ba yanzu ma abun da yasa zan sake ka kenan inaso ka koma yanzu ka gaya waccen banzar tsohowar me zubin saniya marar mutunci,kaje kace duk abun da kafada qarya kake in kuma kanason rasa ranka karkaje kasheka abune me sauki afareni yana gama fadar haka yayi wulli dashi jikake qato yafadi aqasa timm duk girmanshi hakan be hanasa saki qara ba sai haki yake yana goge gumin da ya tarar masa lokaci guda, juyawa hamza yayi ga sauran da suje jinyar jikinsu har yanzu basu dawo daidai ba harara ya watsa musu sannan yace kuma idan kunasan ranku da lafiyar ku kar kusake gigin tabani ko kuma kutaba baba to wlh sai na canza muku kamanni kar kuga kungir meni ba ruwana da girmanku ko wacce tasaku din zan iya lallasata agabanku inyaso a kore ni daga masarautar ko inga uban da ya isa ya kasheni lokacina beyi ba me doruna ne yasamu qarfin tashi yace kai qaramin dan isaka me kwana da wando duk abun da kake taqama dashi nafika ba za ayi yanda kake so dinba kai har ka isa kace mana ga yanda zamuyi bayan qasa da mu kake meye matsayin ka agidan nan to bari kagani hukunci ba fashi yanzu zan ladaftar da kai sai kayi nadamar tabani da kayi kayi babban kuskure wani shegen murmushi hamza yasaki me dauke da gargadi sannan yace ai gabi gaka ban hanaka ba dazu ma abun da yasa na tsaya ka dake ni dan agana waccan banzar ce amma kuma banaso inbata kunya agabanku shiyasa amma bawai tsoran ka nake jiba tunda nazo gidan nan ba tsoron kowa kuma bana ahiga harkar kowa yanda nataso nikadai nake rayuwa tun kafin zuwana nan haka nake rayuwa acikin gidan nan ko akwai wanda ze taba cewa gashi nayi mishi abu kodan kunganni shiru shiru to ni ba kawar lasa bace dan haka ka kiyayi kanka sa shiga harkata inba hakaba kuma hmmmm yafada yana cizon bakinsa irin zaka ci ubanka ne me dorina da yagama kaiwa qarshe duk tsoron sa da mutane sukeyi amma yau wannan mutumin zece wai baya tsoron sa aikwa ya ballowa kansa bala'i yana gama ayyana haka yadaga bulalar sa da iya qarfinsa ze sauke ta akansa aikwa caraf hamza ya ruqeta tare da fusgeta daga hannun sa be kalli kowaba ya nufi hanyar fita har dayan dogarin wanda aka fasawa baki yataso ze ruqosa sun dauka fita zeyi da mamakin su kuma sai suka ga yajawo qofar ya rufe tare da sa sakata sannan ya juyo yana kallonsu daya bayan daya fuskar nan tashi babu digon annuri akanta shugabansu dake jinyar maqogaron sa da yasha shaqa shi yafara mikewa yana neman hanyar buya dan yaga alamar wannan mutumin ba a hankalinsa yake ba kar yaje ya kashesu abanza sai yanzu yake da na sanin abun da ya aikata masa iya tsawan zaman da sukayi dashi besan haka halinsa yake ba yanda yake shiru shiru ya dauka ba abun da ze iya aikatawa ashe sumimu kasim ne be gama tunanin ba yaga ya tunkaro su dukan su bawanda be tsorata da ganin sa ba amma saboda qarfin hali bazaka ga hakan aka fuskar mutum biyun ba saide fuskar shugabansu ne kawai zaka ga zallar tsoro akai,

yana qarasowa gaban su ya shiga nade hannun rigarshi ya gyara ruqon dorinar sanna yafara sauke ta akan me doruna zuba mishi ita yake ta ko ina har kai saida ya kunce mishi abun da yanade kasa dashi sannan yaci gaba da zuba mishi ita da iya qarfinsa da Allah ya hore masa sude sauran bawanda yayi yunqurin dakatar dashi saboda kar suje yadawo kansu ,

Me dorina tun yana daurewa yana rurrufe jikinshi da hannu har yafara hawaye yana cewa dan Allah kayi hakuri wlh bazan sake dukan ka ba hamza yace kama sake mana ai so nake kaji ta ajikinka da kyau kaji yanda mutane suke ji idan ka dakesu kai har dadi kake ji ana tsoronka ana cemaka me doruna to yau ga me doruna yazama me karbar doruna😂  

Hamza be qyale shiba sai da yatabbatar ya hada masa jikinsa waje guda saida yaga yafara dena motsi da magiyar da yakeyi sannan ya rabu dashi ya juyo kan sauran tuni suka fara bashi hakuri da magiya amma ina shibesan meye magiya ba a wannan lokacin takan dayan dogarin yafara shima saida ya tabbayar da ya daku sannan yarabudashi yadawo kan shugabansu,    shugabansu na ganinshi yafara roqonsa shima murmushi hamza yasaki sannan yace kai ko kunya ma baka jiba inyi hakuri fa kace kai kozan hakurama ai bazan hakura akanka saboda kaine ummul aba isin faruwar komai badan kaiba sukansu baza su dake niba kaine kaja musu arayuwata babban abun da nafi tsana kenan ayimun sharri afadi abun da banyiaba sannan aci zarafina akan abun da banda laifi kai kuma duk ka aikata hakan kaga kwa naka ai sai yafi nakowa yana gama fadar haka shima ya rufar masa da duka wani qarfine yake qara zuwan masa sakamakon wani haushi da yake qara tasowa da cikin zuciyar sa dan daga qarshi ma da yaga dorunar bazata gamsar dashiba jefar da ita yayi sannan yasa hannun sa yarinfa dukansa kamar zarrare haka yake dukansa ta ko ina har saida shugabansu yade na motsi amma be dakata ba saida yagaji dan kansa sannan ya rabu dashi yazauna yana sauke numfashi yana kallonsu da kowa yake a kwance yakasa tashi ga shatin bulala rudu rudu ajikin su kara kallon shugabansu yayi sai kuma ya faahe da dariya yana nuna sa yace ashe duk kurin banza ne ai nazata kana da qarfi ashe baza ka iya kwatar kanka ba yanzu gaka agabana a kwance asume kuma ba abun da zaka iya yana gama dariyar yace musu akwai ruwa acikin gurinnan da sauri suka bashi amsa da babu saide yan dan fita da ga waje ze ga wata bambu akwai ruwa aciki bece musu komai ba ya miqe tare da cire sakatar yabude ya fita yana fita yashiga dakin kusa dashi inda baba yake yana kusa da qofa duk yana jin abun da yake faruwa kuma yaji dadin hakan yasan ko ba komai zasu dan samu sauqi,

Bude shi yayi sannan yace baba fito mukoma nawa dakin sannan kaga yanda nayi da wadan can shedanun murmushi baba yayi yace ai duk inajinku amma na jinjinawa qarfin halinka yanzu baka tsoron wani abun yabiyo baya yace baba kar kadamu koma me ze faru ya faru a shirye nake yana fadar haka yayi gaba yace baba shiga bari indebo ruwa awaje,


to Kasai baba have amma baya tunanin ze iya shiga ciki shikadai dan haryanzu a tsorace yake dasu dan haka sai yaja burki abakin qofa yana jiran dawowar sa sai sushiga tare amma shikam bada shiba baze shiga ba suje su huce akansa yana gurin Hamza ya dawo gurin da ruwa a hannun sa yace baba yanaga ka tsaya anan baka shiga baba yayi murmushi yace yaro kai naked jira mushiga dan bazan iya shiga ba nikadai saboda tsaro shiyasa najira ka 

Shima hamza murmushi yayi kawai yace to mushiga aranshi kuma yace Allah sarki baba tsoro yake ji kenan suna shiga hamza ya nufi inda shugabansu yake memakon ya yayyafa masa ruwan kawai sai ya juye masa duka akan fuskar sa arazane shugabansu ya tashi sauke ajiyar zuciya tare da cewa dan Allah kayi hakuri wlh zanje infada mata gaskiya kaimin rai kar ka kasheni dan Allah na roqe ka baba saura qiris ya yi dariya amma sa ya hadiye abarsa wai mutumin da yake daka musu tsawa yana musu fada da fadar abun da duk yaga dama amma shine yanzu yake magiya da roqon ayi hakuri to duk ina cika bakin 

Hamza be yace yaza ayi da inkashe ka saide idan kamin taurin kai to shine zan aika ka barzahu dan haka yanzu zan kafa maka sharadai idan kabi mu zauna lafiya idan kuma kayimin tarin kai kasan sauran gyada kai shugabansu yayi sannan yace na yarda koma me kake so zanyi maka shi kafada kawai girgiza kai hamza yayi sannan yace good man haka make son ji ashe zamuje da kai abun da nake so dakai shina na farko zakaje ka warware abun da ka kulla sannan zaka bamu hakuri agaban mutane zaka durqusa ka nemi yafiyar mu agaban kowa da kowa sannan daga yau duk inda kaga baba ka gaidashi kar kasake yimishi kallon banza ko ka hantare shi ko tsawa duk ranar da hakan tafaru sai nayi tsiranka kai bama mukadai ba daga yau banaso na qara jin wani yace kayi mishi sharri akan abun da be aikata ba kace yayi wlh inna kamaka da hakan bawanda zesan lokacin da zan dauke ka incanza maka kamanni abun na qarshe kuma ko da wasa kar kai gigin gayawa wani abun da naimaka yanzu zamu zauna tare daku anan harsai kowa yaji sauke sannan zaku fita kuma gaba dayanku kuma banyarda wani yanuna alamar anmasa wani abun ba kufita kucigaba da yanda kuke ina fatana kowa yaji abun da nace yafada yana jiyawa yana kallon sauran da sauri suka amsa masa da eh munji kuma zamu kiyaye ya karkada kai tare dacewa good haka akeso dayan dogarinne ya kalli shugabansu yace amma ka cuce mu wlh sai na rama akanka daman kasan duk wannan abun da ka fada qarya kake 

me dorina ne ya dora dacewa nima abun da nake so nace kenan wlh ka kuka da kanka idan kowa yasan qarya kake sharri kayi musu ba zakaji dadi ba dan har uwar masarauta ma da take goya maka baya yanzu sai ka karbi hukunci idan ni kwa akasa in hukunta ka to kasani sai sauke duk dukan da kasa akai min banjiba bangani ba dayan ma yace ai tare zamuyi daman nima haushin shi nake ji tun ba yauba ni banma san me yasa akabashi shugaban muba me dorina yace yana zuwa yana kai qarya da gaskiya yana neman gindin zama ba dole yasamu fada ba awajenta mana abashi shugaba alhalin be cancanta ba

shide shugabansu be kula kowannen suba shi babba tashin hanakalin sa shine ta yanda ze tunkari fukani da zence qara ne maganr da yagaya mata sharri yayi musu besan ta inda ze fara ba inbe fada ba kuma wannan me qarfin dokin yace ze kashe shi to yazeyi inde yana son ransa dole yayi masa abun da yake so in kuma bayaso yaqi fada shikwa yaza ayi yazabi mutuwa akan ya fada da haka ze fada saide yasan kashinsa ya bushe qarshen sa yazo kowa yanzu ze dena yarda dashi sannan uwar masarauta baza ta qara yarda ya rabeta bama bare yafada mata wata magana tayarda ,

Hamza be ya katsesu da cewa kunga ni kuncikani da surutu daya yaje ya debo ruwa kuzo ku wanwanke fuskar ku sannan kowa yamaida abun kansa ya nada sannan kugoge quarar jikin ku da ruwa ku saita fuskar ku yanda de ba wanda ze ganku yace wani abun yafaru da ku kungane ko dukansu sukace eh mungane yace to daya yaje saura kuma yabata min lokaci inyi maganin sa da sauri me dorina ya mike yafita da sauri yadauki boket din da hamza ya ajiye bayan ya watsawa shugabansu 

be dauki lokaciba yadawo ahakanma kuma saida ya fara tsayawa ya shirya kansa tsab kamar ba abun da yafaru dashi saboda acewar sa ai daman ko bece musu kar sunnuna wani abuba daman baza sununa ba saboda duk wanda yaji ai saiyayi musu dariya ace kamarsu suka tsaya akayi musu wannan dukan dan haka saida ya tabbatar yayi need need sannan yadawo yana zuwa ya ajiye musu kowa yatashi shide shugansu da qyar ya iya mikewa saboda ko wace gaba ta jikinshi ciwo suke mishi ahaka yafara shrya wa shina tare da maida madaurin sa sannan suka goge kayansu sa suka baci da qasa saboda ba falasta a qasan dakin bayan sungama hamza yabisu da kallo daya bayan daya ya tabbatar da ba me ganewa wani abun yafa ru dasu sannan yacewa su me dorina sujashi sukaishi hargaban tsohuwar nan danshifa baze iya kiranta da kowane suna ba inba tsohuwa ba ko tsohuwar banza haka yake cemata daman tun ba yau ba saboda daman jininsu be haduba tunfarkon zuwanshi gidan yaji batai mishi ba sam 


Yace kusahsi agaba kuje sannan kuce yafada mata abun da kukaji yana cewa bayan kungama dukanmu munsuma kunje debo ruwa kuka dawo kukaji yana cewa shi ai duk yanda zesa adaki mutum yasani saida ya gargade mu amma mukaqi ji yanzu gashinan ya mana sharrin da ba mu isa nucire kanmu aciki ba watakil na akshe mu da kukaji haka sai kuka tambaye shi maganar da kukaji yanayi gaskyace ko qaraya yaqar tabbatar muku da qarya yake sai kukaga hakan be dace ba shiyasa kukawo shi domin ayanke mishi hukuncin qaryar dayayi kuma kuce munsuma ko ruwan ma baku watsa mana ba muna can asume Allah yasama bamu mutuba,

kungane me naked nufide kuyi duk yanda zakuyi ku nuna mata ku kuka jishi da kunnen ku ba wani yafada mukuba inkukayi haka shikenan bani ba ku dukan su amsawa sukayi da angama inde wannan ne baka da matsala da hakan yace zaku iya tafiya ruqeshi sukayi daya yaruqe gefen sa dayan ma ya ruqe gefe haka saka sakashi a tsakiya suka fita dashi zasukaishi wajen uwar masarauta.........✍🏿


Yau kunsamu update da wuri kuma ina fatan inde ba wani uzirine ya taso min ba in Allah ya yarda zan qara yi muku wani zuwa anjima da daddare in Allah ya yarda 


*ina qara tunatar daku zandena posting nan da wani lokaci akwane group sai group biyu nafa da muku jiya dan haka ku hanzarta shiga wanda kuke so*


Follow me all👇


Facebook @Azeema dahiru(xeemat)

Arewabooks@azeemadahiru

WhatsApp @~~~~writer~~~~~

Wattpad@xeemat

My WhatsApp number ***


#comment

 #share

  #likes

   #vote

   

      """""""""""""""""""""""""""""""