Episode 38-39
💅SARKI SAMEER....💅
by❤xeemat.....love❤
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
﷽
Bismillah........ ✍
Episode38-39
""""""""""""""""""""""""""""""""""
Ahankali yadaga hannunsa ya dora akan nata amma kuma be janye shi daga kan bakin shiba da ta dora ganin hakan yasata qoqarin janye hannun ta amma sai yariqe kam tare da manna mata kiss akai da sauri ta fusge hannuta tana hararar sa wai kai dan Allah me ka medani me ka daukeni to wlh inka qara tabani ka taba wutar jahannama kuma Allah ya isa na taqara sa fada tana doka mishi harara shi abun natama dariya yabata dan haka ya dan dara sannan yace au hakama kikace to na yarda bari inqara tabawa yafada yana tunkarota da sauri tayi baya tana girgiza mishi kai da qyar ta iya bude bakinta tace dan Allah kayi hakuri wlh bazan qara fada ba yace kima qara aini imnai niyar abu sai na aikata bani kikeyiwa Allah ya isaba kuma idan na tabaki na tanba wuta ko to bari intaba wutar inji da zafi ko babu zata iya qona ni
cike da takaicin maganar sa tace ai ba ajikina zakaji zafin ba sai ka mutu Allah ze babbaka ka awutar jahannma kalidina fiha abada baza kavtaba fiyowa ba tunda burinka ka ringa taba matan da ba muharraman ka to wlh kaji tsoron Allah kadena halin da kakeyi tunkafin lokaci ya qure maka ka mutu a loda maka qasa tifa guda ko ma biyu sannan kasha azabar qabari daga nan kuma ranar tashin alqiyama ka shiga wuta kuma wlh..... Bata qarasa ba taji dal abakinta saurin sa hannu tayi ta dafe domi ba qaramin zafi taji ba saboda har saida kwalla ta tafito daga idon ta,
Kallonta ya shiga yi tundaga qasa har sama sannan yace ni kike cewa dan wuta ko to ai kema kinzama yar wutar tunda kema yanzu kika tabani kinga tare za asakamu awutar ?
tace ai ni iya bakinka nataba kuma ina da dalilin shiyasa yace ohhh daman baki ba ajinkin mutum yake ba kenan zakizo kinawa mutane maganar banza yen yen yen to saide ke kishiga amma baniba yaqara sa fada shima yana galla mata harara shiru tayi bata qara tanka mishiba dan tagaji da shi wlh so take kawai ta fita barinshi tayi awajen sannan ta nufi qofar dan budewa tayi ahankali ta leqa dan taga su saleem sun tafi ko suna nan aikwa tana lekawa tagano shi amma yajuya mata baya da sauri ta mayar da qofar ta rufeta ahankali tana juyawa tayi karo da mutum dagowa tayi tana kallon shi shima ita yake kallo sai kuma ta hade rai tare da cewa malam lafiya tafada tana bin ta gefenshi zata wuce har tayi gaba sai tajishi yana qoqarin bude qofara asukwane ta qarasa gurinsa tare da shiga gabansa tace me kake qoqarin yi har yanzu fa suna wajen dan Allah kar kafita kasama mana mafita yanda baza aganmu ba tunda tafara magana ya zuba mata manyan idanun shi yana kallon ta saida yaji tayi shiru sannan yace ya kikeso ayi nibanda wata mafita da ya wuce infita dan bazan tazama anan gurinba saboda ke ina da aikin yi marairai cewa tayi sannan tace dan Allah ka tsaya mune mi mafita wlh ina tsoron yaya saleem kuma sai yaje yagayawa mama taqarasa fada tamkar zata fashe da kuka tausayin tane yadan kamashi dan haka sai yadakata daga qoqrin bude qofar da yakeyi sannan yace to naji kinsan me za ayi yanzu ni zan fita ke kuma ki buya idan na fita zanja hankalin su gabadaya mu koma wani bangaren ke kuma sai kifito sannan kitana di qaryar da zakiyi ki kare kanki idan an tambayeki kingane ko kai ta jinjina mishi sannan tace to a ina zan buya yace can gurin ya nuna mata qarshen wata kusurwa idan kinga na dade da fita sai ki leko idan kinga ba kowa sai kifito kawai da to ta amsa masa sannan ta juya ta nufi inda yace mata din batace mishi komai ba shima be qara kulata ba ya bude qofar ya fita yana fita yaga ba kowa agurin ajiyar zuciya ya sauke tare da hamdalah saida yakalli ko ina ya tabbatar da ba kowa sannan tasake bude qofar ya dan daga murya tare da cewa kiyi sauri kifito ba kowa yana gama fada nata yayi saurin barin wajen ya nufi wata hanyar da ya tabbatar da baza su hadu da suba, """cikin tafiya sauri sauri gudu gudu har yaqarasa gaban office dinshi yana qoqarin budewa yaji ance sir cak ya tsaya tare da juyowa saleem ne yaqaraso gurinsa da sauri yana cewa sir tundazu nake zuwa wajenka bana samunka dan Allah ko ka ga qanwar nan tawa danazo da ita wlh tundazu nake nemanta duk inda nasan zata iya shiga naduba amma banganta ba
Wata boyayyiyar ajiyar zuciya yasauke sannan yace ayya gsky bangan taba tunda kuka fita dinnan banqara ganinta amma gsky abun da mamaki kuma kunduba ko ina har dakuna kunduba saleem yace bamu duba ba gsky amma bari yanzu inje induba yafada yana qoqarin barin wajen sai yayi saurin dakatar dashi tare da cewa muje in taya ka amma inaji ajikina ba abun da yasame ta kuma tana cikin girin nan ba inda taje
Saleem yace to Allah yasa
tare suka jero suna qara duddu bawa dr.shettima ne yace saleem yanda zamufi sauri kai kabi tana nan hanyar ka duba na bangaren ni kuma bari in duba nan saleem kwa yaji dadin hakan da yace mishi koba komai yasan ya taimaka mishi dan haka godiya yayi masa sannan ya wuce dr.shettima saida yadan dara ganin harda yi masa godiya sannan ya nufi inda take kai tsaye yana zuwa yaga bata wajen sai kuma yafara tunani to ina ta shiga dan dube dube yara yi sannan sai ya hangota can nesa da gurin ta zauna aka kujera tare da yin tagumi tana jiran taga ta ina saleem ze bullo,qarasawa yayi wajen ta sannan yazauna akusa da ita dan neman magana kawai sai yadora kansa kan kafadar ta da sauri ta miqe dan ita tsoro ma yabata bataga zuwan shiba bare zaman shi kawai sai jin ankwanta mata akafada da tayi , dafe kanta tayi tare dacewa nikam yau naga takaina me kuma yadawo da kai wai baza ka rabu da rayuwata bane shima miqewa yayi yana kallon ta sai kuma ya hade rai kamar be taba dariya ba abun har mamaki yabata dan har ta fara tunanin kode aljanune dashi muryar shice ta katseta da cewa ke dalla can rufewa mutane baki dan kinsamu ma ina kulaki shine zakina wani yimin duk maganar da tazo bakinki,kasake tayi kamar sokuwa tana kallon sa dan magan ganunsa ba qaramin bata mamaki yayi ba tama kasa magana,
Dorawa yayi da cewa yanzu zankaiki gurin yayanki zance nasamoki a wani daki kina bacci dan haka sai ki canza mood dinki zuwa kamar wadda ta tashi daga bacci sannan kibiyo ni dan ba jiran shirmenki zan tsaya jiba yana kaiwa nan yayi gaba abunsa bushewa tayi awajen tabi bayansa da kallo takasa koda kiftawa har saida ya bacewa ganinta sannan ta dawo hayyacinta da gudu ta kwasa tabi bayanta saboda bata da mafita da ya wuce tayi yanda yace tayi sa'a kuwa tana beyi nisa ba dan har ta cimmasa yana tafiya tana binshi abaya har suka kai office dinshi budewa yayi yashiga itama ta shiga yana shiga ya dauki waya yakira saleem yana dagawa yace mishi gata kazo office dina yana gama fada ya kashe wayar tare da dauko wani file dake gabansa yafara dubawa ko kallon inda take beqara yiba kamar ma besan da ita a office din ba tayi mamakin wannan canjin da yayi lokaci daya bayan yagama tattabeta zezo yana wani ciccin magani saikace tayi mishi laifi bata san lokacin da tsaki ya subuce mata ba dagowa yayi yana kallon ta karaf suka hada ido da sauri ta rufe bakin ta tare da cewa ni ba da kai nake ba tafada tana turo baki har zeyi magana sai saleem ya turo qofar tare da sallama hakanne yasa shi yin shiru sai ya amsa sallamar sa sannan yace gata nan acan nasamo ta tana bacci ,
"Saleem yace haba auta kinga yanda kika daga min hankali kuwa daga cewa kijirani sai kitafi wani wajen ki kama bacci yafada yana kallon ta fuskar sa ba walwala dan har ga Allah yaji haushi yana nan yana ta faman nemanta amma ita tana can ta sharar bacci hankalin ta kwance...,
ahankali tace dan Allah yaya kayi hakuri wlh bansan baccin ze dauke ni gajiya nayi da tsayiwa kuma wajen ba kowa shiyasa kawai na shiga dakin kusa da wajen dan injiraka aciki sai kuma bacci ya daukeni sorry pls shiru yayi mata sannan yacewa dr..shettima
Sir nagode sosai Allah yabar zumunci bari kawai inje in dorata a napep ta tafi gida kar inje kuma ta qara jamin wata wahalar dr.shettima yace a'a karabu da ita kawai yau daya de naga ai ko gurin qawar tata ma bata shiga ba kuma zece ta koma gida hakan ai be dace ba kabarta yanzu muje dukan mu nima inaso inga marar lafiyar yafada tare da miqewa,
Saleem beyi masa musuba yace to sannan itama ta miqe suka fito a tare saida suka fara zuwa wajen dr jamil suka taho tare dashi sannan sukaje wajen Ameesha suka duba ta sannan suka fito Azeema sai faman matsar kwalla takeyi da ta tausayawa bestyn tata addu'a tayi mata Allah yabata lafiya office din shi sika qara komawa dukan su bayan shigarsu ne saleem yace sir bari inje kan aikina anajirana ke kuma saura ki qara yin wani wajen kiga yanda zanyi dake anan yana gama fadar haka ya fice daga ciki dan har yanzu haushinta yake ji,haka ta qari zaman ta shiru ba magana dan har yanzu be kulata ba ko kallonta ma beyi ba har aka kira sallah ya miqe yana niyar fita yace kishiga ciki akwai toilet aciki zamuje masallaci yana gama fada be jira amsar taba ya fice ajiyar zuciya ta sauke da daman duk atakure take dashi zaman da sukayi waje daya sai taji duk ta qosa tabar wajen amma ba dama,miqewa tayi taje tayo alwala bata tsaya duba sallaya ba ta curo dan kwalinta ta shimfida tayi tayar da sallah bayan tagama tayi addu'a ta nike ta koma inda take bata dade da zama ba suka shigo shi da saleem shiya fara shigowa yazauna a mazaunin sa sanna saleem ma yasamu kusa da ita ya zauna tare da mika mata ledar hannun sa da ya karbo mata abinci acikin hospital din takeaway ce aciki sai drink da water saida ya bude mata sannan ya miqa mata yana bata yace bari inkoma kici abincin sosai sannan idan da akwai wani abun da kike so saiki gaya wa yayanki ko kice yakirani yagaya min da ba yanzu zan dawo ba tace to nagode adawo lafiya yace Ameen sanna yajuya yace sir sai anjima, "ok" yace mishi kawai sannan yacigaba da abun da yakeyi shikuma ya fita,
da farko da kinci tayi amma ganin tana jin yunwa gashi kuma ba kallonta yake ba yasa tafara ci a hankali sai kace wacce akace sai taci ta dole har tagama kwa be kalle taba ahaka har aka qara kiran sallah yaje yayi ya dawo lokacin itama ta idar da tata,saleem ba dawo ba sai daf da magari ba yana shigowa yace ta taso su tafi sallama sukayiwa dr. Shettima sannan suka fita.......
*BOSSAY*
yau tunwajen la'asar ake neman dadda amma ba aganta ba hankalinsu duk yabi ya tashi ko ina sundu ba amma basu ganta ba abunde yafara basu tsoro dan yanzu sallar isha'i ake kira amma bata dawo ba haka kowa ya wuce dan gabatar da sallah kafin adorable daga inda aka tsaya bayan sun idar da sallah a masallaci bossay yafito yabiyo hanyar da wowa gida yana ta faman sauri yazo daf da gate din gidan sai yaga kamar gibtawar mutum ta gefen shi da har ya share ze tafi sai kuma yafasa yabi inda yaga anyi yana zuwa kwa yaga dadda ta rabe ajikin garu da mamaki ya tsaya yana kallon ta yama kasa magana ganin yaganta yasa ta harare sa sannan tace to uban sa ido ashe ka ganni ni wlh banason ganin ka shiyasa ma na buya inbari sai ka fara shiga sannan inshigo amma saida idon ka ya hango ni,
da qyar ya iya budar bakinsa yace I na kika je sai yanzu kika dawo duk kinbi kintayar wa mutane da hankali kallon sa tayi sannan tace to ubana shaqeni ingaya maka tunda kaine ka haifeni ko kuma mijina sukadai ne ne nasan zasuyi min irin wannan tambayar to bazan fada ba ta gama maganar tana ratsawa ta gefen shi zata wuce hannu yasa ya ruqota sannan yace dadda baki da gaskiya gashinan nagani a idonki kuma tunba yauba na fahimci baki da gaskiya akwai wani abun da kike boyewa dadda yau inason sanin ko ke wacece kuma a ina kika samo Ameesha daga gani ba jininki bace ita saboda ko kadan bakwa kama kigaya min gaskiyar wacece ke in bahakaba kuma wlh zandau mataki akanki ko in hadaki da 'yan sanda watakil su zaki gaya musu gaskiya idan nu baki gaya mana ba ya qasa fada tare da dawo wa gabanta yana qara cewa ke nake saurare yanzu nake sonji kuma dole kigaya min inba hakaba daga nan sai police station dan ko gidan nan bazaki shiga ba in kuma kina ganin qarya ne gwada kiga aiki da cika wa.............✍
*yauwa naji wasu suna ta tambayata wane group za sushiga a page din baya ai na fada nace duk wanda yake a facebook yayi searching din group din sarki SAMEER sannan yayi join anan zanringa yin posting....
Yan WhatsApp kuma suyi min magana ta number ta insaka su a group din whatsapp ****
Kar kumanta da comment ko like da share..