MUNƊO (Mai Hakuri)

Munɗo Page 2

by @ayushermuhd

*MUNƊO*

*(MAI HAKURI)*

Na Zee Yabour 

 Da

Ayusher Muhd🤸🏻‍♂️



Page 2





Zuciyarsa ce ta karaya cikin rauni ya kalleta yace "Kiyi hak'uri Munɗo In Shaa Allah watarana komai zaizo karshe." 

Hawaye suka sake zubowa tace "Baffa sai yaushe? ."

Tausayinta ya sake kamashi ya rasa me zai ce mata. Shiru tayi itama bata ce komai ba, ita dai zata so ya nisanta ta da k'auyen nan.


Ganin duhu ya fara kawo kai yasa yace "Munɗo tashi muje gida?" Kai ta gyad'a masa ta mik'e dan batasan yimai musu.



Tunda aka hango su kan hanya, wasu da gudu suka sanar da Laddo, cikin k'ank'anin lokaci suka biyo hanya wasu da itace wasu ashana suna fad'in "Yau sai sun k'ona tsinanniya kowa ya huta."



Maccido tsayawa yayi a hanyar shiga gari bayan ya aiki wani yaro ya kira Mahaifinsu.




Munɗo ihu da karajin su da ta jiyo ne ya sake firgita ta, ta kama Maccido ta rik'e, "Ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru." Ya fad'a yana k'ok'arin kwantar mata da hankali, sake kankameshi tayi jikin ta na kyarma.


Su Laddo tuni suka had'a itacen, cikin hargagi yace "Wallahi Maccido karka bari na irga biyar baka ajiye yarinyar nan ba, gashi can Sahi tace in har ban ɗau mataki ba yarinyata da aka kashe ba, sai ta tafi gidan su, da rashin jaririyata zanji ko matata? wannan annobar ai gwara mu kasheta kowa ya huta."


Wani ya matso yasa takardu ya kunna ashana, tuni wuta ta kama balbal gashi dama lokacin hunturu da wuta ke saurin ci, Maccido shi kansa tsoro ya fara shigar sa, na fargabar ganin suna neman kashe masa 'ya tamkar zasu kashe wata kaza. 


Laddo cikin zafin nama ya nufo su yana neman fincikar Munɗo, cikin tsawa dashi kanshi bai san ya iya ba saboda tsabar hakurin sa yace "Wallahi Laddo in baka matsa daga gun yarinyar nan ba zakaga yanda ake k'unar bak'in wake, na gaji da takurar da kuke ma munɗo, shin da wane dalili ma zaku d'aura mata maita, aradun Allah yau ni da ku ne?"


Laddo cikin zafin rai yace "Wallahi sai na zubar da jinin 'yar ka tunda na rasa tawa, kasha k'arya ta cinye mun yarinya ta zauna lafiya." Ya karasa maganar yana neman kara kai hannu gun Munɗo, banda kuka itakam ba abinda take.




Gyaran muryar da suka jiyo ne yasa kowa juyawa, mahaifinsu ne wanda kowa ke shakka, Ardo suke ce mishi, shine Babba a rugar, duk yaran yayye da kanne ne a rugar ma'ana jini d'aya, anan suka girma suka haifi nasu yaran, har sukai yawa haka. Kakansu ya rasu shekara biyar da ta wuce shine aka nad'a mahaifinsu Maccido a matsayin Ardo wato shugaba.


Cikin girmamawa kowa ya gaisheshi, ya kalli saurayin dake hada wuta yace "Kashe ku biyoni dukanku."

Suka d'unguna suka bi bayanshi suna kunkuni akan koma menene sai sun zubar da jinin Aljanar mayu.



Gaban bukkar sa suka isa inda yake zama nan kowa ya sauke gwiwowinsa a kasa, Munɗo na gefe Maccido ta takure wuri d'aya haryanzu jikinta kyarma yake.



Gyaran murya yai yace "Laddo na dauka na sanar da kai yarinyar ka bata yi kalar kamun mayu ba?"


"Wallahi Ardo yarinyata mayyar can ta kama ta?"

 Maccido cikin zafin rai yace "Akan me zaka dage itace?"

Laddo ya mike yana neman yin dambe, gyaran murya Ardo yai hakan yasa ya koma ya zauna cikin ladabi.

Maccido ya kalleshi yace "Ardo na gaji da abinda ke faruwa, shi yasa na nemi ka shiga maganar nan, tunda kowa ya gaji da zaman mu a rigar nan, zan d'auki yarinyata mu bar garin nan."


Nan danan guri yai tsit, sukai tsuru-tsuru kowa na kallan dan uwansa, shi kanshi Ardo sai da idanunsa suka firfito waje, dan duk abinda zai faru bazasu tab'a gangancin barin Munɗo da Maccido subar garin nan ba. 


Maccido ya cigaba "Ardo ina neman izininka zan koma birni gun Gidado shi kad'ai garini na tabbatar zai zauna damu."


Ai cikin sauri Ardo yace "Babu inda za ka je, ko so kake ka nuna mana iyakarmu? To ahir dinka, aradun Allah in na sake jin kalamai irin wannan ranka sai ya b'aci."


Kasa yai da kansa dan shikam baiga amfanin zaman ta a garin ba dan haka dauketa zaiyi ya gaji da rayuwa cikin fargaba.


Ardo cikin ɓacin rai ya kalli su Laddo yace "Kai kuma kada na sake jin maganarnan ta wuce yarinya dai ta mutu sai a kaita a birni Allah zai baku wata."

Laddo ji yake kamar zuciyarsa zata fashe sai dai ba yanda zaiyi, da barinsu Munɗo da Maccido gwara yai hakuri.


Ardo yana kaiwa nan ya mike a fusace yai ciki, Maccido ya kalli su Laddo kafin ya kama hannunta su kabar gun zuwa tasu bokar.


Suna shiga ta share hawayemta tace "Baffa baza'a barmu ba."

Yai kalleta tare da murmushi. Zama yai a gefen gado ta zauna a kasa zaiyi magana cikinta yai karar yunwa ji kake kululu.... Dariya yai itama dariyar tai kafin yace "Munɗo kinci abincin rana?"


Ta girgiza kai alamar a'a tace "Yau ba Danejo bace da girki."


Zuciyarsa ta sake kuna wai in ba mamansa bace da girki bamai bata abinci sai dai shi a nashi ya deba mata ko suci tare? Yarinyar da ake amsawa tai surfe ta bakace ta maida gari amma in an girka bamai bata.

Mikewa yai zai fita da sauri ta mike tace "Baffa fita zakai?"


Yake yai yace "Yanzu zan dawo, abincina zan amso, kinji?"


A hankali ta daga kai sannan tace "To!"


Kallan ta yai bayasan a sake hantararta ne shiyasa bayasan zuwa da ita can.


Bangaren matarshi ya nufa wacce take yarinyar kanwar mahaifinsa da aka aura mishi ita.


Tana zaune tanacin tuwon dawa miyar kubewa ɗanya yasha manshanu, macece da batafi shekara ashirin ba, gefe kuma radio ne takeji ga madarar shanunta a kwarya, daurin kirji ne a jikinta, tayi kitso irin manyan nan, daga damanta kuma ɗanta ne dan shekara uku yana zaune yanacin nashi tuwon shima, gefe kuma wuta ce da suka hada saboda sanyin gari.


Tsayawa yai daga ɗan nesa dasu kaɗan yana kallan ikon Allah zuciyarsa na sake kuna. Yanzu duk abin nan dake faruwa ko lekawa batai ba balle ma ta taimaki yarinyar sa? Tunowa yai da yanda tace bazata bari ta zauna da yarinyar nan a bukar ta ba dole sai inda suke tara abinci aka kwashe yasa gado yarinyar ke kwana a can da tana karama, bayan takai shekara tara ya barta take kwana ita kadai.


Gyaran murya yai ta waigo ta kalleshi kafin ta mike cikin girmawa da kunya tana mai sannu da zuwa, Giɗaɗo wato ɗanshj ya kalla wanda ya taso da gudu ya faɗo kanshi.


Hannunsa ya rike kafin ya ɗaga shi sama yace "Malam Giɗaɗo b'ata ni ake sanyi ne da miya?"


Dariya yaran ya shiga yi ganin yanda Baban kemai wasa, a hankali ya saukeshi sannan ya kalleta yace "Kinba Munɗo abinci?"


Nan danan yanayinta ya canza tace "Nima nawa aka aikomin da naka, bansan komai akai ba."


Yawun bakinsa ya hadiya yace"Yanzu shikenan ke sai kisa ɗanki a gaba ita ko taci ko kar taci babu abinda ya dameki? Ace babu mai tausayin bata abinci kaf rugar nan? In ɗanki ne akewa......"


Katseshi tai da cewa"Macciɗo kar ka sake haɗa min ɗana da mayyar ƴar ka, banasan cin mutunci, sannan tun kafin ai aure na faɗa maka bazan kula da ita ba dan haka yanzu kar kuzo min da abinda bazan iya ba."


Ta sungumi ɗanta da kwanan abincinta ta shiga ciki, saman kansa ya rike kawai ya ɗau langar abincinsa ya fita.


Ɗakin da take ya nufa tana jin motsinsa ta ruga a guje ta kankameshi, saman kanta ya shafa yace "Muje muci abinci, yau kinsan me aka dafa?"


Kai ta girgiza tana kallan kwanan kafin tace "Me aka dafa Baaba?"


Ya kalleta yana karasawa ciki yace "Canka zakiyi in ba haka ba yau ba hirar dare."


Dariya tasa tace "Baffa nifa na sirfa dawar nasan tuwon dawa ne miyar ce dai bansan wace akai ba."


Yace"Tunda kin faɗi zo na baki hukunci."


Dariya tasa ya mika mata kwanan, amsa tai ta jawo roba a kasan gado ta gutsiri kadan ta tura ragowar gabanshi.

Fuska ya tsuke yana kallanta, sake karawa tai kadan tana neman turawa gabanshi ya amsa ya zuba mata sama da rabi sannan ya tura gabanta, kamar zatai magana ta fasa dan batasan bacin ran Baffa.


Kan kace me sun cinye abinci yo dama abincin mutum daya ina zai isa mutum biyu.

Kallanta kawai yake cike da tausayi, yarinya ko wasa da kawaye batasan yanda ake ba, kowa ya tsangwameta duk inda taje sai kya ra.

Gyatsa yaji mai y'ar kara wacce ta dawo dashi daga tunaninsa, kallanta yai kawai suka sa dariya, ya kalli kwanan wanda ta lasheshi tas kai kace wanke wa akai.


Dariya ya sakeyi itama tai dariya........



Zee Yabour

Da Ayusher Muhd🤸🏻‍♂️