MUNƊO (Mai Hakuri)

Page 4

by @ayushermuhd

MUNƊO

(MAI HAKURI)



Na Zee Yabour 

 Da

Ayusher Muhd🤸🏻‍♂️



*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️



GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500

GUDA HUDU 1300

GUDA UKU 1000

GUDA BIYU 700

GUDA ƊAYA 400

_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)

_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour) 

_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)

_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)

_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)


ACCOUNT NUMBER 

2083371244

Zenith Bank

Aisha m salis




KATIN WAYA

***


Dandano page 4.......


 Maccid'o ya kalleta yace "Jeki canza kaya kizo muje wani guri, karki bari kowa ya ganki, kinji?"


Kai ta d'aga da sauri dadi duk ya hanata sukuni, da sauri ta nufi d'akinta,? Tunanin ta yadda zatayi wanka, sanyi take ji sosai, wanda ke ratsa k'asusuwan jikin ta, gidan babu mai bata ruwan d'umin da zata yi wanka, haka nan ta d'au bokiti ta d'ebo ruwa ta shiga wankan wanda ya d'auketa mintuna saboda sanyin ruwa, sai da dan' tsaya ta damtse ido kana take kwarawa jikinta ruwan, shiyasa sai tayi kwana biyu bata yi wanka saboda tsoron saka ruwan sanyin a jikinta da yadda baya shafa mata lafiya, yanzu sai mura ta mata mugun kamu kuma irin murar nan mai azaba da ke saukar mata ciwon kai.


 

Kayan da Danejo ta d'inka mata ta saka, ba kwalliya tayi ba dan ko mai bata shafa ba saboda batada shi, sai dai ta yi kyau dama (sabon kaya ko ba kwalliya akace....) tana fitowa taji ance "Dan iskanci sai nace kizo ki d'ebo ruwa b'angarena?" maganar Altine wato matar Baffa ce ta doki kunnuwan ta, da sauri ta russuna ta gaisheta tare da cewa "Kiyi hakuri wallahi ina tashi Dada ce ta sani gyaran turke."


"Wannan ba matsala ta bace, ki wuce ki d'ebo mana ruwa, banda rainin wayo ai ita Dadan baki manta da aikin da ta sakaki ba amma ni nawa da ya zama aikin ki kullum sai kinga dama kike yi." Ta jefa mata muguwara harara tare da cigaba "Uban me kike a tsaye kuma?"


Da sauri ta nufi b'angaren Abba ta d'auko bokiti zata fito taji kukan Gid'ad'o, sam ta manta an mata iyaka da shiga ciki, da sauri ta shiga ta tarar dashi a kasa da alama abu yaje d'aukowa ya fadi, da gudu ta karasa ta d'aga shi, Ta fara jijigashi tana cewa "Yi shiru an gidadon Baffa ina kaji ciwo?".


Saukar dundun da taji baya mai azabar zafi yasa tayi saurin kai k'asa, Altine ta fincike d'anta ta k'ara kai mata wani, wanda ya saka ta durk'ushewa gaba d'aya, tana jin tamkar an karya mata k'ashin baya, ta runtse idonta tsabar azaba, K'afa tasa ta hankad'eta tace "Shegiya muguwa, wato kinci yarinyar Laddo baki k'oshi ba shine zaki kama kaninki? Dama gaskiyar mutane da sukace in kika gama kama na waje cikin gida zaki dawo, to wallahi ko ciwon kai Gidado yayi sai kinga abinda zan miki a kauyen nan."


Da kyar Munɗo taja kafafunta zuwa waje, bokiti kawai ta d'auka ta fita tana share kwallar dake zubo mata.


"Ke da nake jiranki me kuma kike da bokiti?"


Da sauri ta goge idanunta tayi murmushi tace "Baffa kayi hakuri na manta ban zuba ruwa bangaren Altine ba" 


Idanunta da yanayinta ya tabbatar kawai abunda take b'oyewa, bai tambayeta ba sanin ko meye ba mai dad'i ba baya son jin abunda zai hargitsa masa tunani yanzu ya b'ata ransa, bashi da wata damuwa yanzu a duniya irin Mundo, yana fatan ranar da zata samu yanci ta fita daga zargin mutanen rugar tayi rayuwa kamar sauran mutanen, babban burinsa yanzu ya sama mata sauyi a rayuwarta, itama ta zama mutum kamar kowa tayi rayuwa mai cike da yanci kai, 


Kawar da tunanin yayi ya numfasa yace "Toh kiyi maza ki gama kizo muje, dan banasan rana ta fad'i bamuje mun dawo ba."


Da sauri ta d'aga kai alamar to sannan ta tafi.



Maccido yana tafe yana tunani tabbas abinda ya tsara shi zai aikata dole ya d'auke 'yarsa daga kauyen nan subar garin, ta haka zata samu yanci tayi rayuwa kamar kowane mutum, ta shaida itama tana da daraja da martaba dan' adam .




*******




KANO TA DABO.....



Had'adden gini ne na zamani, wanda sai wanda yaci ya tada kai da naira zai iya zama mallakin gidan, Tsaruwar wajen gidan kad'ai abun kallo ce, kama daga furanni da itatuwa da akayi wa bakin gidan ado dasu, kai hatta fitilun k'ofar gidan abun kallo ne, duk da unguwa ce ta masu hannu da shuni wato nasarawa gra, Gidan yana cikin gidajen da suka amsa suna a layin da unguwar ma baki d'aya, Tsadaddan mota ce kirar BMW X5 a bakin gate, sake horn yayi a karo na biyu, Fuskar sa na nuna alamar k'osawa da tsayuwar sa bakin gate d'in, Matashi ne wanda bai fii shekara talatin a duniya ba, ba fari bane sannan bai yi duhu can ba, hancinsa a tsaye yake, saje kad'an da ya kewayar fuska ya k'ara masa, labb'an sa kalar pink wanda suka k'ara k'awata fuskar tasa, Sanye yake da yadi fari mai shara-shara wanda kana hango singlet d'in jikinsa.



 A fusace ya zare belt dake zagaye k'ugun sa ya nufi kofar ya sa key ya bud'e yana k'ok'arin bud'e gate, Sautin kid'an dake tashi ya sa shi waigowa Mota ce k'irar Toyota ta wuce da gudun bala'i tamkar zata tashi sama, Kallo ɗaya yayi wa motar ya gane mallakin ta, Siririn tsaki yayi ya maida kansa kan gate ya sake kokarin buɗewa. Daga ciki aka buɗe wani dattijo ne yace "Tuba nake yallabai Arab Hassan wallahi na shiga ciki ne sam banji karar horn dinka ba." Yayi maganar muryarsa na d'an rawa wanda ke nuni ba k'aramin shakkar sa yake ba haka yana gudun yi masa laifi.


Kamar zai yi magana ya fasa, ba kasafai yake nuna fushin sa ba, balle ga mutumin da ya girme shi baya wata magana da zata zama tamkar rashin kunya ga wanda aka ma.



Juyawa yayi ya koma mota, Tare da danna kanta zuwa ciki, Yayi parking a wadataccen wurin da aka tanada dan parking motoci, Hannun sa ya kai kan mab'allun bud'e motar kamar wanda shocking yaja yayi saurin janyewa tare da komawa baya ya jingina da kujera ya d'an runtse idon sa tamkar mai jin rad'ad'in ciwo "DAN MACE" Kalmar da ta kasa barin k'wak'walwar sa tun d'azu, kalmar da duk sanda aka furta masa take wargaza tunani da farin cikin sa na ranar, ta saka masa b'acin rai da k'unci, a hankali ya dunkule hannunsa fuskarsa ta sake haɗewa.


Fitowa yayi daga mota ya ɗan furzar da iskar bakinsa kafin ya ɗau jakarsa, wayarsa dake kara ya ciro daga aljihu, sunan dake jiki ne yasa ya maida ita aljihun sa ba tare da ya ɗaga ba.


Tun daga harabar gidan zakaga tsaruwar gidan, ga fitilu da suke haske gidan, ciki ya shiga kai tsaye.


Daga cikin gidan kuwa da gudu yan matan suka sauko kasa masu kama ɗaya da alama 'yan biyu ne.


Wacce ke gaba ta ɓoye abin hannunta tace "Dan Allah ki kyaleni na gama ba nace zan baki ba?"


"Kinsan Allah bani ai ni Ummy taba ba ke ba."


Kofar da aka buɗene yasa suka koma sama da gudu ɗayar har tana neman faɗuwa.


Wata muguwar harara ya maka musu, ya wuce ciki kai tsaye.


 Da gudu suka fad'a ɗaki suna haki, kallon juna sukayi ta gaban tace "Ikram duk ke kika ja mana wlh kinfi kowa sanin Ya Araab ya tsani faɗan nan namu, yanzu ina zaman-zamana kija a mun faɗa ko rank'washin sa mai masifar zafi".


Cikin tsiwa wacce ta kira da Ikram tace "Dama nasan haka zakice, banda dama kinso masifar kawai dan na ɗau wayar Ummy sai ki biyoni? Taki ce?"


"Ko ba tawa bace ai dai ni taba ko?"


"Ko ma dai menene kece kikaja kuma Allah Yaya ya rank'washeni sai na rama a kanki." Ikram ta faɗa tare da fitowa daga ɗakin cikin sanda.




*****


 Cikin sauri ya shigo gida har kafafunsa na harɗewa tun kafin ya karasa shiga ya hau masifa yana kiran "Salame! Salame! Ke Salamatu?"


Fitowa tayi daure da zani ɗaure a kirjin ta tana hamma tace "Nifa na tsani ka dinga kirana haka kamar wacce naci bashi ha'a! Nace sunana Salmah akan me zaka dinga kirana wata Salame sai kace a ruga? Kai duk yanda akai dakai sai ka nuna asalinka." Ta karasa tana haɗe fuska.


 "Yaran nan ne ya fita yanzu a mota ko?"


Ta sake yin hamma tace "Shine mana menene? Kai wai kullum nikam abin fad'a kake nema?"




"Haka kika ce? Yaran nan akansa kowa zagin mu yake, kinaji jiya Ina masa faɗa akan kar ya fita in har dole ne sai ya fita kada ya ɗaukar mun mota sanin ta'asa da jawo mana magana da yake, ko cika yan' unguwa da yake da kid'a an sha kawo mun k'orafi, amma ke ko a jikin ki wani sa'ili ma ke kika d'auko masa mukullin motar, wacce irin banzar tarbiya ce wannan".


Wata muguwar harara ta mishi tace "Silar wa muka kasance a haka ne? Kabi ka karar da duka dukiyar mu, gidan da muka siya ka siyar, ka kawo mu nan gida kamar akurkin kaza a hakan kake so a hana shi shakatawa? da me kake so yaji dadin rayuwa bayan ga abokan sa duk suna shanawa?"


Baki ya bud'e yana kallanta yace "Mene? Na cinye ko d'anki ya cinye? Ko ni nabashi takardun siyar da gidan?"


D'ankwalin gaban kanta ta sake turawa gaba cikin takaici tace "Da ubansa ya wadatar dashi ai bazai d'auki abinka ya siyar ba, in ka yi zuciya kaje ka amso kudi a kauyenku ai kunada ragowar shanaye da in ka tattaro a kalla zamu samu mu bar zaman dan gidan nan." Ta karasa tana jan dogon tsaki. (Duk wannan cikin hausar su da bata gama fita ba suke yi)


"Ita kuma Fad'ima tana ina?" Takaici yasa ta sake yi mai tsaki ta wuce ciki ba tare da ta amsa mai ba.


Da kallo ya bita ranshi ya kara b'aci, wayarsa ya d'auko ya sake kiran Bilal sai dai har ta katse bai d'auka ba, komawa yayi waje ya zauna tare da dafa kansa, haka zai cigaba da rayuwa? Yaransa duk babu mai jin maganarsa? Ita Fad'ima yayi kwanaki bai saka ta ido ba, in yayi magana Salame ta fara masifa akan ya kawo kudi, shi kuma Bilal duk wani arzikinsu ya k'arar a shaye-shaye da bin mata, babban gidansu ma ya siyar sai wannan suka samu suka siya, anya haka zai cigaba da rayuwa? Ko dai ya koma kauye ya roki Danejo ne akan ta taimakesu da kudi? Kila in ya samo kudi sosai Salame ta rik'a jin maganarsa ya samu ta sa bakin wurin ganin ya daidaita rayuwar yaran sa, su natsu wuri d'aya tamkar sauran nagartattun yara. 




*********

BLUES CLUB


Kid'a ke tashi ta ko'ina wanda ke ratsa har cikin dodom kunne, Ko na kusa da kai baka jin maganar sa idan ba yayi da k'arfin gaske ba, Yan' mata da maza ne cakud'e a wuri, da yawa daga ciki rawa suke cikin bad'ala suna rungumar juna, mazan daga ciki na kama k'ugun mata suna juya d'uwawu, Yayin da wasu kwalbar giya a hannun su suna kwankwad'a, Wasu kuma mazan na gefen rungume da mata suna lalubar juna, har masu shan shisha, wiwi da sigari duka akwai wurin. 'Wa'iyazubillahi'


 Matashin saurayi ne mata sun kewaye shi yana taka rawa tamkar zararre, kwalbar giyar hannun sa, ya d'aga kai ya kwankwad'e sauran ya cilar a kasa, rigarsa ya zare ya cilar a kasa yabar vest ya na rawa, Matan suka hau ihu da tafi, Yana sake jin kansa sama yana juyi, 


Baya yaji an ja shi da k'arfi, a fusace ya juyo ya kwashe wanda ya jawo shi da mari ba tare da ya tsaya jin dalili(kunsan yan' shaye shaye zuciyar su a wuya take) Saurayin da ya ja shi a fusace shima ya kai masa naushi, Fad'a ya kaure a tsakanin, gefen kwalbar daya fasa ya d'auka a kasa yana neman kaiwa d'ayan bugu.


Da sauri aka rik'e hannunsa, wani ya jijigashi yace "Bilal bakada hankali ne? Kisa kake son yi?"


Fizge jikinshi yayi cikin maye yace "Ku bar ni na masa tabon da har abada ba zai sake shiga gona ta ba".


Jan shi yayi suka fita waje yace "So kake a kulle ka? Kai wai meyasa duk sanda muka zo nan sai ka ja mana matsala? Yanzu sai ka kawo wani abin mu basu dan suyi hakuri su barmu mu sake zuwa."


Kai ya girgiza yana layi yace "Banda komai wallahi kaima ka sani. Ni yanzu ba wannan ba, Beb d'in ka nake so mu d'an...."


"To kace bakada komai ta ina zata bi ka?"


Hannu yasa ya ciro mukullin mota yace "Ga d'ani ka tabbatar ka dawo da ita gobe ba tawa bace ta tsoho ne kasan da ita yake neman kudi."


Cikin sauri ya amsa yace "Ai karka damu goben nan zan dawo da ita, in na dawo da ita sai na kawo ma Beb d'in."


Kai ya jinjina cikin maye yace "Yanzu ajiyeni a gida sai ka wuce da ita."


Tare suka shiga motar, dadi duk ya kama abokin, suna tafiya yace "To amma ya maganar takardun mota? Kaga dai kar yan' road safety su kamani su tambayi takardun mota."


Ya ba je akan kujera yana sauke numfashi yace "Ba motata bace, nima banda su wannan tsohon da kake gani wayo gareshi."


Harararsa abokin yayi, suka isa layin yana saukeshi ko jiransa baiyi ba ya ja motar a guje....



Ayusher Ce🤸🏻‍♂️

Da Zee Yabour