MUNƊO (Mai Hakuri)

Page 5

by @ayushermuhd

MUNƊO

(MAI HAKURI)


Na Zee Yabour 

 Da

Ayusher Muhd🤸🏻‍♂️


*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️




Dandano page 5.......


 Neman dafa gate yake cikin maye bai ankara ba yaji zai fad'i, yayi saurin mik'eqa yana d'ariya yace "Ah kai kaga wani gayu?" Yayi maganar yana dariya yana tangal tangal.


Gate aka bud'e da sauri Jairo mahaifinsa ya rike shi, ya jijjigashi yace "Yanzu Bilal bazaka ji fad'a ka daina wannan abin ba? Wuce muje ciki kafin yan unguwa su san abinda kake aikatawa ka ja mana surutu da baki."


Ya tuntsire da dariya yana kallanshi yace "Boss kaine? Ahhh ashe nazo gida."


Waigawa yayi yace "Ina motar da ka fita da ita?"


Kai ya girgiza yana dariya yace "Na bada aron ta..."


Ido ya zaro cikin tashin hankali ya jashi ciki, gudun maganar sa a wajen ta jawo hankalin mutanen unguwaa.


Tun a k'ofar shiga falo ya soma jijjigashi da cewa "Bakada hankali ne Bilal? Uban wa kaba motata?"


Bilal yana dariya yace "Kai kuma dadina dakai karanta, Ba nace na bada aro ba a yanda naje ɗin nan ba class na kasa arar da Toyota bayan nafi karfinta."


Baki ya bud'e cikin kunar rai ya d'aga hannu zai mare shi.


"Kul kar ka sake hannun ka ya kai kan fuskar sa wallahi."


Salame wacce hayaniyarsu ta sata fitowa ta fad'a tana karasowa cikin tsiya da masifa.


Jauro ya kalleta yace "kinaji me yake cewa?"


Ta zabgamai muguwar harara tace "Karya yayi? Karanta ce mana, motar ma har mota ce? Bayan duk ta tsufa, meyasa kake tunanin yana shaye-shayen? Duk ba kai kaja ba? Da ace hankalinsa a kwance yake ai bazaiyi ba, masifar talauci da babun da muke ciki kad'ai ta isa jefa shi wani hali."


Ta karasa tana kallan Bilal tace "D'an albarka wuce muje karka fad'i." Ta rik'osa tamkar k'aramin yaro.


Dariya yayi yace "Umma na takaina, meyasa duk kyanki baki auri mai hamshak'in mai kud'i ba kika tsaya anan?"


Murmushin takaici tayi tace "Shima da kudin sa ko ka manta?"


Ya jinjina kai yana neman fad'uwa yace "Ahh na tuna, Umma kice ya taimaka ya amso mana kudi a kauyen nan na tsani fita da Toyota din nan, sannan....." yasa dariya yace "Inasan iphone 14 irinta abokaina."


Jauro takaici yasa ya shige d'aki ba tare da ya sake cewa komai ba, ya zauna bakin gado yana kiran wayar Raheena wacce tana fara ringing ake katsewa.


****

RUGAR JIJJI



 Rik'e take da sandar kara tana tafe tana ɗan cila k'afa, wani irin dadi takeji wanda bazata taɓa iya tuna sanda taji irinshi ba.

Kallon Baffa tayi tace "Baffana in mukaje kauyen zaka siya mun burodi?"

Kai ya ɗaga yana dariya yace "Bayan burodi ma harda shayi zan siya miki kici ki koshi."


Tsalle ta sake yi cikin jin dadi ta matso kusa dashi kaɗan tace "kuma fa cinyewa zanyi kafin mu dawo."

Ya sake ɗaga kai yana dariya yace " Karki damu yau duk abinda kikeso zan siyan miki."

Da sauri tace "Baffa da gaske? Tab aradun Allah yau sai cikina ya zama katoto."

 Dariya yasa sosai suna tafe tanata janshi da hira wanda fin rabi shirmen ta ne dadi duk ya rufeshi yanda ya ganta ta saki ranta shi kanshi bai taba ganinta haka ba.

Sunyi tafiya ta sama da minti hamsin kafin suka isa kauyen.


Hada-hada ake tayi a cikin kauyen mutane sun cika sosai anata siye da siyarwa, ga motoci manya manya da suka shigo daga birnin ɗeban dabbobi.


 Baki ta saki galala tana kallon yanda ake ta ciniki, Baffa ya waiga ya sake waigawa bai ganta ba, juyawa yayi baya kawai ya ganta a tsaye ta saki baki tana bin mutane da kallo.

Dawowa yayi ya dan bugi saman kanta kaɗan ta kalleshi ta sake kifta ido tace "Baffa nan ne birnin da ake cewa?"

Dariya yasa yace "Kauye ma kin mai wannan kallon ya kenan idan kikaje birni?"

Ta murza idanun tace "Wai can yafi nan?"

"Nan fa kauyen kusa damu ne? Yan rugar mu ba wanda baya zuwa kece dai baki taɓa zuwa ba sai yau shiyasa kika ganshi daban amma ina zaki hada nan da birni."

Ta kalli inda mai siyar kalalaba take ta ruga a guje taje gun tanawa Baffa alama daya karaso.

Yana zuwa tace "Baffa zanci dan Allah."

Nan ya biya aka zuba mata taci, taci ɗan malele, alale tasha shayi da yaji madara, gyatsatayi ta kalleshi kamar zatayi kuka tace "Baffa aradun Allah ko yau na mutu......"

Mugun kallan daya sakar mata ne yasata yin shiru ba tare da ta karasa ba.

Ta haɗe labbanta alamar tayi shiru, yace "Tashi muje gun wanda xan gani."

Mikewa tayi suka nufi cikin kasuwar sosai, wurin masu siyar da dabbobi mai dabobin na ganinshi ya taho da sauri yana mai alamar karramasa yace "Maccido ose!"

Dariya yayi ya karasa suka gaisa fuskar kowa cikin farin ciki, mutumin yaba Munɗo gun zama sannan ya bata rake ta karba ta fara sha su kuma suka ja gefe suna magana.

Macciɗo ya kalleshi yace "Kana ganin za'a samu mai siyan?"

Da sauri yace "Kwarai kuwa, amma Macciɗo duka uban shanayenka zaka saida? Anya hakan ya dace?"

"Karka damu nasan me nakeyi, kai dai ka samomin mai siya sannan inda hali da daddare nakeso a kwashesu."

Shikam bai sake musawa ba tunda yasan zai samu kudi sosai, yace "Ai karka damu zan sanar da Alhajin goben nan ko jibi ma sai kaga yazo."

Cike da jin dadi yace "Nagode sosai."

Mutumin ya kalli Munɗo yace "Waccen ce yar taka da kake bani labari?"

Ya kalleta cike da tausayi yace "Itace."

"Ni ai da munyi hadin aure na bata yarona." Yayi maganar cike da bugar ciki dan yanda Maccido ke da arziki in dansa ya aureta ai sun more.

Kai Maccido ya girgiza yace "Kayi hakuri akwai inda xataje yanzu, in har daga baya ta dawo kaji kanawa ɗanka kamu har lokacin sai muyi hadin."

Ya shiga jijjiga kai yana dariya.....

Kusa da ita ya matso yace "Munɗo muje mu siya burodi."

Ta mike rike da rakenta suka je suka siya buridi da kunun gyada a leda. Nan suka zauna kasan bishiya suka ci har zasu wuce yace "Kinsan tsire? Gashi can ana gasawa."

Ido ta zaro tace "Baffa wanda kake kawomin a ɓoye?"

Ya ɗaga kai ta ruga a guje gun mai tsiren tana murna, binta yayi yana dariya a ransa, fatansa daga wannan lokaci ya zama babu wani abu da take sai murmushi da farin ciki.

Nan suka siya sai dataci tsinke shida sannan tace ta koshi.

Tare suka taho ganin duhu ya fara kawowa, tana tafe dadi duk ya hanata yin shiru tanatawa Baffa zuba shima sai biyeta yakeyi.

Ji tayi cikinta ya murɗa kallan Baffa tai tare da tsayawa ta ɗan durkusa tana ɗan matsa cikin, hankali a tashe ya dagota yace "Munɗo lafiya?"

Kasan leb'enta ta ciza tace "Baffa Cikina murɗawa yake."

Ajiyar zuciya ya saki yace "Dama ni nasan za'a rina tunda naga yanda kike ta ciye-ciye zo ki zauna a jikin bishiyar can na dubo ko ararrabi ne ki ɗan tauna kafin mu isa."

A hankali ta zauna a gefen bishiyar tana sake durkushewa, gashi sunada kusan minti ashirin kafin su isa kauyen.

Dajin ya ɗan shiga dayake duhu ya kawo kai yasa yake tabi yana dubawa sosai, itakam cikinta kawai take rikewa tanaji kamar zata zaga bayan gida.

Abinka da ruga su ba kunyar yin hidima a daji suke ba, dajin ta d'an fara shiga tana kiran sunan Baffa.

Ganin ba alamunsa yasa ta tsaya nan danan shakku da tsoro suka ɗan fara darsuwa a zuciyarta, karar da ta juyo ne yasa ta rikice wa "Aahhhhhhh!"

A firgice ta fara kiran Baffa, hawaye tuni suka fara zirya a idanunta jin muryar Baffa ce tayi wannan karar.

Kuka take tana kiranshi, jin alamun ta kusa yin tuntube yasa ta kalli kasa, Baffa?

Jikinta ne ya hau rawa ta tsugunna tare da ɗagoshi, idanunshi sai lumshe wa suke yana kiran sunanta.

Kuka kawai take tana ihu tana fad'in "Baffa menene?Me ya sameka?"

Cikin wani irin yanayi da bata taba ganinshi ba yace "Munɗo maciji-ma......" kasa karasawa yayi, nan danan ta sake birkicewa ta kalli kafarsa duhun dare yasa bata iya gani ba, ihu kawai ta shiga yi tana cewa "Jama'a ku taimakemu, ku taimaka mana Baffana." Babu kowa babu alamun mutane a gun......

Su kuwa a can riga kowa ya cika yayi fal kowanensu da abinda yake jira yai wa Munɗo in ta dawo, ruwan gidajensu ba'a zuba ba, ba'a musu sirfe an daka garin tuwo ba, ba'ai dakan fura ba, ba'a zubawa dabobi ruwa da abinci ba. Yau har Maccido jira suke ya dawo suci zarafinsa. Itakam Danejo haka kawai ta dinga jin hankalinta yaki kwanciya, sau uku tana fita tana dubosu amma babu labarinsu. 


******

KANAWAN DABO.........


 Ummy tana zaune tana jan carbi a tangamemen d'akinta, wanda kamshin turare ne kawai ke tashi, sai ka kasa gane kamshin wani turaren ne, saboda dadinshi da sanyaya zuciya.

Sallamar dataji ne yasa ta saki fuskarta sosai wanda ta bayyanar da farinciki tsantsa, amsawa tayi idanunta na kanshi, macece fara mai dan jiki, kallo daya zaka mata kasan dadi da mayuka masu tsada ne sukasa fatarta canzawa da yin laushi.

 Shiga yayi ya zauna tare da lankwashe kafafunsa ya gaisheta, Ummy ta kalleshi fuskarta har yanzu a sake tace "Araab ya kukai da Kawun naka? Sun amince da auren?"

D'agowa yayi dayake ba mai fara'a bane shiyasa bazaka gane halin da yake ciki ba, ya dan kalli kwanukanta dake gefe yace "Ummy ban samu shiga ciki ba."

Ido ta bude tace "Bangane ba? Araab ba munyi dakai zakaje ka gaishesu ba tunda mun riga munyi magana da su Kawun naka?"

"Dana fita ne wani uzuri ya taso sannan ni Ummy banasan auran nan wlh yarinyar ke kanki kinsan ta fiya rawar kai."

Had'e rai tayi tace "Sai yaushe zakayi aure naga nima ka samu mai kula dakai? Araab haka zan ta zama sai dai ni kaita kula dani kai bamai baka kulawa? Sa'aninka duk sunyi aure sun haihu amma ace kai ko budurwa baka da ita, Meenal da Allah yasa ita take son ka ina tunanin zaka samu kulawa gunta itama shine kake ta gocewa?"

Sajensa ya shafa cikin girmamawa yace "Ummy ni bana bukatar wata ta kula dani, ku kadai nake bukata a rayuwata, in har kuna cikin farin ciki ni ya wadatar dani. Dan Allah Ummy karki sake kiran su Kawu, yar su ce banaso Allah ya bata wanda ya fini." Abinda yace kenan ya mike, sai daya kusa kofa idanunta na kansa tace "Sun fadi abu akaina ne?"

Waigowa yayi ya kalleta ba tare da ya tanka ba. Tayi murmushin takaici tace "Tunda har kamin alkawari zaka babu tantama kaje, na tabbatar abu akace a kaina wanda ya hanaka jurewa sai dai Araab ka sani ita rayuwa da kake ganinta babu wanda zaice ba'a zaginshi......."

"Ummy kiyi hakuri amma duk duniya babu wanda ya isa ya fadi magana akanki sannan na barshi, sai dai ki yafemun." Yayi maganar tare da saurin fita.

Ajiyar zuciya ta sauke har zuciyarta tayi sanyi ta d'auka za'a dace wannan karan.....

GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500

GUDA HUDU 1300

GUDA UKU 1000

GUDA BIYU 700

GUDA ƊAYA 400

_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)

_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour) 

_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)

_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)

_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)


ACCOUNT NUMBER 

2083371244

Zenith Bank

Aisha m salis




KATIN WAYA

***




Ayusher Ce🤸🏻‍♂️

Da Zee Yabour