Ramzia...
by @mimsqueen
"Rahmatu!"
Ammi takira sunan Ramzia da kanta ke kasa, yanzu su kadai ne suke zaune a karamun falon.
A hankali Ramzia ta iya amsa kiran Ammin tasu, sanin bakaramun abu bane zaisa Ammi ta nema ganin ta ita kadai harta baro gida batare da ta kirasu ba tazo.
"Rahama inaso karki boye mun damuwarki kifada mun kinajin dadin zama da dan uwanki!"
Tambayar sosai tazo ma Ramzia a bazata, shiru tayi batare da ta dago ba saboda rashin sanin amsar da zata bata.
"Ke! Karki kuskura kiboyemun wani abu inda matsala ki sanar dani".
Cikin sanyayyar muryarta Ramzia ta bude Baki " bakomai Ammi".
" kintabbatar bakomai? dan kinsan cikin ku banso naga daya yana cutuwar daya, dan haka indai yana miki wani abu kina takura kan tafiye-tafiyen nan nasa kifadamun!".
Girgiza kai Ramzia tayi "toshikenan my doughter na yarda tunda kince bakomai na yarda, Allah yamuku albarka"
"Ameen"
"but duk sanda ya miki abu don't hesitate kinji ko? Dan ke 'ya tace banso Ko kadan naganki cikin damuwa".
Sosai jikin Ramzia yakara sanyi sam tasan rashin jindadin dan Ammi bazai sa taji dadi ba, dakyar ta lalubo murmushi saboda kallon da Ammi Ke mata ta ce "to Ammi insha Allahu".
Sam a ran Ramzia Akwai damuwa, amma sam bata jin zata iya fitowa ta fada dan tasha fada ma mahaifiyarta complain din, Amma sam momynta taki yarda saboda yadda yarta keson 'yar tata da kuma yadda Rasheed yake dawainiya da gidan nasu.
Shirune ya ratsa falon ganin haka yasa Ammi katse shirun.
"kinyi shiru Rahama wai yaushe zaki koma school din? kinsan banson kina zama haka nan sam walh".
Murmushi Ramzia tayi "jibi zamu koma Insha Allahu".
"To Allah yakaimu gobe zan aiko akawo miki sako kinji, yanzu haka akwai kaya da aka shiga dasu kitchen Ki tabbatar kina sha da madara Kinji Ko dazu natura ma yan uwanki nasu, dan haka kul kukai wasa mazan zamani sai a hankali".
Sosai Ramzia taji kunya zancen Ammi, dan koyaushe ita ke basu ma ganin mata kuma wai harda ita surukarta, lamarin Ammi na matukar bata mamaki sosai.
" haba hajiya gunta kika zo kenan kinmanta dani".
Rasheed yafada lokacin daya shiga karamin falon da suke zaune dukansu dariya suka saka mishi.
"eh din gun diyata nazo dan tafika damuwa dani, kai yaushe nake saka a idona Abdul-Rasheed? Amma ita kam koyaushe bata gajiya da kirana da kuma duboni".
Shagwabe fuskarsa yayi gaba daya kamar ba shiba "kina fada gabanta sai ta rainani ae".
Yafada yana hararar Ramzia dake mishi dariya ita da Ammi, ganin yadda yadawo kamar karamun yaro.
"Aw abun dariya ma kuke mun"
Yafada lokacin daya dan jefi Ramzia da daya daga cikin throw pillows din kujerar irin na wasa, tashi tayi da sauri ta kwace, still tana dariyarta "Ammi zan duba abinci".
"jeki abunki yar albarka na"
Ammi tafada tana dariya ficewa Ramzia tayi cike da jin dadin uwa-surukar tata. Hakan yaba Rasheed damar komawa kusa da Amminsa inda ya daura kansa kan cinyarta.
"Ammina I miss you sosai"
"liar!"
Tafada tana dariya, dan dagowa yayi cike da shagwaba kamar karamun yaro "Allah Ammi ina missing dinki sosai, kinsan yanayin aikina ne".
Murmushi tayi tare da girgiza kai " Haba Abbana! inda gaske kake missing dina meyasa baka zo kaduba niba bayan tun jiya ka dawo, kuma dasassafe Nasan kabar gida".
Murmushi yayi sanin ba yadda zaiyi ya mata karya bata gane shiba "I am very sorry Ammina".
Yafada lokacin daya Kara manna Kansa da cinyarta sa hannu tayi kan summansa kansa tana dan shafawa."Abdul-Rasheed!".
Jin yadda takira sunanshi yasa ya tashi da sauri, yana kallon ta ganin ba wasa fuskarta yasa yagyara zamansa, dan yabada muhimmanci sosai kan abunda zata fada masa, ya tabbatar abune me muhimmanci take dashi.
"yaushe yar uwarka zasu koma school?!"
Tambayar ta matukar zo mishi a bazata dan baiyi tunanin hakan ba, Kuma sam baisani ba shiru yayi ya sunkui da Kansa kasa yayi " hmm Nasan Baka sani ba, meyasa baka kulawa da yar uwarka yadda ya kamata ne?!".
Shiru yayi batare da ya bata amsa ba Sam "ka sauya halinka gaskiya, kullum abunda nake fada maka kenan ka kula da iyalanka dan Sam bana so nan gaba kazo kana regretting Abbana, shiyasa kaga ina yawan takura maka please karka yi nisa da iyalanka dayawa kaji".
Shiru yayi jikinsa duk yayi sanyi, yana saurarar ta harta kamalla ya mata godiya Aleena ce ta shigo da gudu. "Dady and granny food is readyyyyy and I am hungry, let's go and eat please".
Dariya Ammi ta mata "tabdi ba inda zamu Abbana, bamai cin abinci sai nan da 5hrs"
Zaro ido Aleena tayi "what? Like seriously! granny kana jinta Ko Dady?!"
Tafada tana kallon dadyn nata Dariya ya tuntsure dashi "Dady!"
Tafada da karfi tare da rike kugunta kai kace wata babbar macece saboda dariyar da yake mata.
"sorry my Angel but mom wish first"
Tabe fuska tayi Tana kallon Ammi " nikam I will eat alone, Kuma mamana zata tabi yarta!"
Harta juya zata tafi Ammi takira sunanta "Aleena! Ae kinyi mantuwa mamanki ma nice mamanta"
Aleena kallonta tayi ta kyalkyale da dariya "ae in Dady yabi maman shi momy ance yaran ta take bi koyaushe", haka suka cigaba da fama da surutun Aleena har suka kai baking dinning din inda suka tarar sai lokacin Zee da Ramzia ke jera abincin a dinning.
Kan kujera suka hango Aaina wacce ke kallon cartoon dinta hankalinta kwance. girgiza kai Ammi tayi " Aleena saita yo ka ita kuma tayo mamanta baiwar Allah ba ruwan ta da hayaniya" dariya su duka sukayi jin zancen Ammi.
Jin hakan yasa Aleena taji haushi ta tsuke fuskarta ta nufi inda Aaina ke kallo zungureta.
Kan sec sunfara rikici, salati Ammi tayi ta sanar da ubangiji kan ta karasa gun tuni mahaifinsu yakai gun.
"Aaina meyasa kike yawan son fada da yar uwarki ba dama ta miki wasa?!" Rasheed yafada yana kallon Aaina.
Cike da mamaki Ammi ta karasa gun "lallai yama kyau Abbana ae ita Aleena yakamata kai ma fada datazo ta sameta tana kallonta ta shiga tsokanarta".
"laaaaah ba tso......".
"Shut up Aleena!" Ramzia Tafada lokacin data karasa gun. "da Ammi Zaki yi musu?!".
" Ah bana so ana ma jikokina fada kul, wasa take itama karki mata haka" Ammi tafada tana jawo Aleena dake fusgewa.
Dariya su duka sukai lokacin da Ramzia tajawo ma Ammi kujerar baya ta zauna "bisimillah Allah!" Ammi tafada lokacin data karashe zama akan kujerar.
"Aaina!"
Ammi ta kwala mata Kira "Na'am!" Ta amsa ta taho inda take nuna mata kujera kusa da ita ta zauna, Ammi tayi tazauna kai Aleena banda tabe fuska ba abunda take momyn su na harararta tashi tayi ta koma kusa da Dadynta daya cigaba da lallaba ta, cike da annushuwa su Kai dinner suna hirarraki su Ammi basu bar gidan ba sai kusan 9pm.
Cike da jin dadi sukai musu rakiya hargun mota inda suna shiga, Ramzia ta kalla yan twins din nata "oya time for......"
Tayi shiru Tana kallonsu " sleep!"
Aaina Tafada da karfi tare da dago hannunta alamun su tafa da maman nata, mika mata tafin hannunta itama Ramzia tayi suka tafa banda Aleena dake ta faman bata rae.
Cike da jin dadi Ramzia ta mika ma Aleena hannu, Amma sai ta basar ta nufi Dadynta dake kallonsu, cike da jin dadi kallon juna Rasheed da Ramzia suka kalla juna tare da sakar ma kansu murmushi.
" oya girls let's go"
Tafada nan sukai ma Rasheed sallama suka haura sama cike da jin dadi ya koma cikin lallausar kujerarsa ya bude wayarsa.
Messages yagani na wata no daya sa "HT"messages ne kusan guda 11 dan zaro ido yayi "seriously!".Tare da shiga ciki.
"Hi Babyna😍"
"ya kake?"
" ina kashiga shiru ba reply😔"
"Rasheed I miss you so much nan koshi ba we need to meet soon".
Murmushi yayi "hmm mata kenan!".
"ina kishiyata❓😒"
Dariya sosai abun ya basa, waigawa dan ya tabbatar shi daya ne aiko yayi sa'a shi daya me gun ya dake ya maida Kansa wayar.
"Nasan kana nan kana cin amanata jin shirun nan naka hmmm😭"
Dan cute smile yayi "lol" Yafada a zahiri.
"And.....I need cash, uhm nasan tafada maka zamu koma school jibi dusar kawar tawa".
Dan zaro ido yayi jin abunda tafada girgiza kai yayi.
"yauwa jibril yazo mun da wani batu we need to meet sorry😣"
Tsaki yaja tare da dan girgiza kai cike da jin haushi wannan karon.
"Hmm ina matukar Jin haushin rashin Ka kusa dani Rasheed walh i really luv you my baby💋".
Dauke kansa yayi daga wayar jin motsin Ramzia da sauri yagyara zamansa.
Cike da murmushin jin dadi ta gangaro tazo ta zauna dan nesa dashi ganin idonsa nakan Tv din yasa bata damu ba tashi tayi "inazuwa".
Sama ta kuma Hauwa tabarshi gun zaune inda yamaida fuskarshi kan wayar ya cigaba da chat dinshi, hindatu kan yadda ta matsu su hadu Koda ya duba Faith offline yagani hakan ba karamun takaici ya samishi ba.
Tana hawa wayarta taja dake kan gado sosai taga taga messages a wayar tata budewa tayi da sauri tabude tare da juya idannunta.
"like seriously!"
Tafada tana bin messages din da idanu Tana scrolling hannunta up tana duba sunayen groups da mutanen da suka mata messages takai kan nashi kamar bazata buda ba.
Har saida gabanta ya fadi a hankali ta viewing text din nasa.
"Assalamu Alaikum! My Queen inafata kina nan cikin koshin lafiya ya twins dina❓"murmushi tayi jin yana tambayarta yara cigaba tayi da karantawa.
" inafata duk kuna nan Lafiya haba Rahama ! what did I do so wrong da kika daina receiving call dina haka, is it dan about what happened between us last time❓ then I am very sorry insha Allahu bazan kuma bari hakan ya faru ba tun da bakiso, but inkin shigo school Monday talk to me please abar gabar nan wahala yake bani please dear".
Murmushin takaici tayi bayan ta karasa "uhm wannan iskanci badani ba bazan taba yiba Insha Allahu".
Ji tayi bazata iya cigaba da chat din ba sanadiyar tunanin abunda yafaru daya farmata lokaci daya tare da faduwar gaba tuna dole zata ganshi jibi "nashiga uku!"ta furta a hankali tare da closing eyes dinta.
Take tafara hasko kyawawan lips dinshi da kyakywar fuskarshi jin feelings dinsa ne ke taso mata sanadiyar abunda yafaru ranar da suka kamalla exams "subhanallahi!"
Tafada cikin raunanniyar voice dinta tare da bude idannunta da tuni suka rune zuwa ja saboda matsanancin sha'awar da takeji tashi tayi a hankali cikin kasala ta nufi toilet din, shiga tayi ta tara ruwan dumi cikin dan bucket din tsaki taja ganin zai bata mata lokaci hakan yasa ta sakar ma kanta shower, sosai yake jin dadin yin hakan har lumshe ido take saboda Tana cikin matukar sha'awa a wannan lokacin jin ruwan a jikinta yadda Ke sa mata jin dadin jikinta sosai.
Ta jima a toilet din kafin ta sama natsuwa, a hankali ta motsa yan kyawawan lips dinta "ya Allah karka jarabceni da irin wannan rayuwar" ta furta a gaban mirror din ganin still fuskarshi take Kara gani runtse eyes dinta tayi sosai tafito toilet din.
inda tashiga ta zabo yar sleeping gown dinta me kyau da bayyana surarta tasa kan kace me Ko Ina ajikinta kamshi yake turaren Ramzia karshe ne a cikin turaruka da muke dasu.
Sai da ta tabbatar ma kanta tayi kyau ga gashin nan nata daya sha gyara ta zubo su ta gefen wuyanta tagaba tafito zuwa falon taku take cike da kasaita, A hankali take sauke kafafunta kamar batason sauka, Amma sai dai kash gogan nata idonshi nakan phone dinsa Sam baisan ma tana saukowar ba.
Sosai taji ranta na kuma baci da I don't care habit din da yake nuna mata, Amma ta daure ta dake ta karasa kusa dashi ta zauna gab dashi.
Baiko kulata ba yadan kautar da wayarsa yadda bazata iya ganin abunda yake a wayarba, sam Ramzia bata lura da hakan ba a wannan lokacin sam bata da buri irin na Rasheed ya kasance da ita a bed.
A hankali takai hannunta jikinsa a dan tsawace batare da ya kalleta ba yaja tsaki "Haba Rahama what is it again now".
Duk da bata ji dadin ba haka ta sake langwabe kanta cikin shagwa tace "cewa nayi bari nazo nayi hira da mijina nakaina dan na lura aikin nan yana mungun so ya dunga shiga lokacina gaba daya" a shagwabe ta karasa maganar.
Murmushi Rasheed yayi me sauti " banda abun ki ae da aikin kike samun bukatun yauda give me kuma kike bukatar ke kuwa".
Tabe dan lips dinta tayi tare da kokarin da kanta kan cinyarsa kanta na karasa samun ma sauki kuwa ya dan tureta ya tashi "Haba! Mekike so ne I am busy to Ina tattauna important business ne tunda Yau Amma ta hanani".
Bai saurareta ba haye sama ya barta a gun wani irin damuwa da bacin raine suka sauka mata Wanda inda sabo yakamata ace ta saba a yanzu dan mostly itake fara neman Rasheed kuma kusan Ko yaushe he always end up disappointing her koya accepting suyi making luv karshe baya ending yadda take so sam batajin dadin auratayya dashi Sam a bed in suna sex bata Jin komai sai wahala mostly hakan yasa in taji hindatu na labarin sex da friends dinsu abun yake bata mamaki.