ALAKARMU (MUMMUNAR ALAKA)

Back To The Academy...

by @mimsqueen

Tashi tayi haryanzu jikin nata bai daina kadawa ba meta tuna da sauri ta koma kan bed din ta dau wayar tata buda text din tayi.


Hi Rahama,

Inafata kina nan lafiya ya yarana it has being long Ko dan waya kinyi blocking duk inda zan same ki why? Meyasa kike son bata mana ''Alakarmu' anyway nasan kinji zancen dawowata but not the day don't worry I just want to surprise you, nasan kintsorata da ganin message dina har yar da phone din kikai don't be scared I am all yours Rahama see you soon.


"Ha!"


Sound din daya fito bakinta kenan da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tana kallon message din.


Rahama why are you so Quite?


Wani message din ya Kara shigowa wayar, kokarin kashe datar ta soma inda takarajin shigowar wani.


Karki kashe!


Tsura ma screen din wayar manyan idannunta tayi tana kallo, ta rasa me Rayhan yake nufi da ita sam a rayuwarta.


Send me your pic I wanna see that beautiful face of yours please?!


" mtsw"


Taja tsaki tare da kashe datar komawa tayi kan bed din ta kwanta tare da runtse idannunta.


Tsaye take lokacin da taji hannayensa biyu ya shigo jikinta zuwa dan cikinta inda tsoro yabi ya dubibiyeta jin yadda yake Shafa ilahirin jikin nata. Inda lokaci guda salon ya sauya inda ya shiga wasa da kan nipples dinta dake cikin Riga tare da sako kansa zuwa wuyanta yana bi cikin wani irin yanayi, wani irin nishi ta sauke tare da matse idannunta duk da a tsorace take dashi din tana matukar Jin dadin abunda yake mata.


Sosai Ramzia ke Kara mimmikewa a kan bed din gaba daya ilahirin jikinta amsa mata yake " Ramzia!".


Aka Kira sunanta a wannan lokacin hakan yayi dai-dai da budewar idannunta ganin yanayin da tashiga tuna abunda yafaru baya nan take hankalinta yatashi.


" No! No!! Banson sake tunawa A'uzubillahi yes , is forbidden I can't have such thought innalillahi subhanallah".


Duk wannan surutun ita kadai take yinsu inda ta tashi ta nufi toilet ta dauro Alwala tashiga nafilfilu bata rintsa ba sai kusan 3am na dare shima barawon bacci ne yayi awon gaba da ita.


Tun kiran sallar farko Ramzia ta tashi tashiga wanka tare da alwala saida tayi nafilfilu kafin tayi sallah bayan ta idar ne ta nufi dakin gogan Wanda Ko juyin farko baiyi ba.


Da sallama tabude kofar dakin sanyi karara kamar kankara sanadiyar uban A/C daya cika shi kansa ya nannade gaba daya cikin blanket din.


Nodding head dinta tayi ta nufeshi dan kai hannu tayi ta tabashi " tashi asubha tayi already"


Sake Kara gyara kwanciya yayi haka tacigaba da trying dakyar ya tashi ya shiga wanka a cewarsa flight dinsa 7am.


Sai da ta tabbatar yashiga ta nufi bedroom din twins ga mamakinta dukansu sun tashi Aaina tayi wanka Tana shiri Aleena Ke cikin toilet itama Tana wanka hakan ba karamun dadi yamata ba.


" come here"


Ta Kira Aaina alamun bata so Aleena taji.


" did you wake your sis?"


Girgiza kai Aaina tayi kamar radi tabude baki " Nima ita ta tasheni".


Dan zaro ido Ramzia tayi " are you sure cutie?"


" I can hear you!"


Aleena Tafada daga cikin toilet din da karfi dukansu tuntsire wa sukai da Dariya sai da sukai mai idar su suka tsagaita.


" I am proud of you girls Allah yamuku albarka let me go and prepare you girls something special".


Cike da jin dadi tabarsu dakin ta nufi kitchen kamar yadda ta saba.


" Aaina meyasa kikai ma Momy karya?"


Aleena tafada lokacin data fito toilet din da dan towel dinta.


Dariya Aaina tayi mata " banaso tace Ke baki tashi bane".


" but Aaina lying is a bad habit bakiji me malam a tafada bane bad kids lie not good ones".


Tabe face Aaina tayi " sorry sis next time zan kiyaye" murmushi sukai ma juna inda suka cigaba da shiri.


Tana cikin hada break fast suka fito " good morning"


" morning my sweet princesses how are you today?"


Tafada lokacin da take dan kallonsu Tana musu dariya.


" fine Momy mekika dafa mana?"


bude musu soyayyan chips din tayi, tamaida murdin inda ta bude musu ferfesun cat fish din datayi gefe Kuma soyayyan plantain ne.


" no Momy niban son chips corn flask kawai zansha ya isheni" Aaina tafafa Tana tabe face dinta.


" why is that so my angel?"


" Momy!"


Tadan fada cikin shagwababbiyar murya sanin momyn tasan bata cin Arish and she hate bread.


" gues what?"


Aaina ta juya Tana kallon momyn nasu bude daya kwanon tayi inda eyes din Aaina yakai kan soyayyun Samosa da spring rolls tashi tayi da sauri ta nufi momyn nata, duk wannan abun Aleena na kallonsu ba abunda take so irin taga dadynta kusan duk hankalinta ya karkata can fannin.


Jin Aleena shiru yasa uwar ta kalleta ganin idonta nakan upstairs din yasa tayi murmushi dan indai yana gidan Aleena ba abunda take so irin ganinsa kusa da mahaifin nata.


" Aleena baby eat up! Zamuyi late kinga Momy ma takoma school Yau".


Murmushi tayi tashiga caccakar dankalin kamar bazata ciba Jin alamun saukowarsa yasa tayi saurin juya cike da fara'a Amma ganin sa da dan travelling bag din yasa murnarta ta koma ciki.


" hi darlings!"


Yafada cikin murmushi lokacin daya karaso gun Su.


" dady har zaka tafi?"


" yanzu Aleena Ko gaida dadyn bakiyiba ba harkin fara mai suru..." daga ma Ramzia hannu yayi ganin yadda maganarta ke Kara bata ma Aleena rae.


Rungumota jikinsa yayi " haba my cute princess a gun aiki ana neman Dady so Dady has to go owk"


Tabe lips dinta tayi alamun Tana shirin sa mishi kuka " no cute princesses don't cry" tuni dan tears din dake face dinta yasa ma ikon gangarowa.


Sa hannu yayi yana goge mata " I am very sorry amma nikaina dole ne naje princes dina or do you want our business to go down all my had work?".


Girgiza mishi Kai tayi tashiga share hawayenta " wow that more like my angel"


Yafada tare dan Jan kumatun ta " duk abunda kuke so ask your mom or give me a call and I will make sure you get it".


Murmushi Aleena tayi " what if is big?"


" no cutie nothing is too big for Dady to buy"


Dariya suka kyalkyale dashi " nace Momy ta saimun irin bag dinta wai yayi girma" nodding kansa yayi sanin inya biye ma Aleena dukansu sai sun makara tashi yayi daga sunkuyon dayayi jikin kujerar tata.


" let's eat Ramzia kisaya mata irinta duk girman ta tunda tanaso" zatai magana yasa mata hannu, irin wannan al'adar tasa Tana matukar bata mata rae Amma ba yadda zatai dashi.


Sai a lokacin ya kalla Aaina wacce tunda ya fito bata bi takansa ba illa abincinta, Sam Yafada meyasa ita bata damu da lamuransa ba dan ya lura Ko magana bata cika mishi ba inba dole takama ba sai yar uwar.


Kallon Ramzia dake gefen sa Tana cin abincinta yayi batare da yace mata komai, kusan yana ganin kamar Tana tura ma Aaina tsanarshine sam ba halinsu daya da yar uwarta ba as young as she is sai bad hali.


Nan suka kammala breakfast like a happy family sukai sallama saida ta tabbatar driver ya daukesu shima gogan ya tafi tadawo gida dai2 lokacin mai'aikinta tashigo nan tabar mata aikin ta haura sama.


Dakin Su Aleena tafara shiga ta kintsa har toilet din saboda zafin namanta cikin mins kalilan ta kamala tafito inda ta nufi dakin gogan.


Tashiga gyara Kayan laundry dinsa ta hada gu guda inda tadunga sa hannu pocket tana tunanin koyayi mantuwa kanta bayar wanki inda a nan tayi kicibis da latter dinda Faith tayi mishi.


Harta daga zata karanta komai ta tuna saikuma ta mayar ta ajiye mai cikin wardrobe din bedside dinshi.


9am take da lectures haka ta dage ta kamalla shirinta tsab kafin lokaci tabar gida, saboda sam bata so tayi late kotayi missing tunda farkon komawarsu hutu semester ne wannan shine farkon second semester dinsu a second year dinsu na HND inda take karantar Science laboratory Technology gabanta har faruwa yake tsabar anjima suna hutu.


Kb driver dinsu ne yakaita har cikin makaranta tana sauka kuwa ta hango Su hindatu suna tahowa ita da wata kawarsu.


" uhm gafa mutuniyarki nan"


Tayi maganar Tana tabe fuska lokacin data hango Ramzia.


" wakenan?"


" kalla can" Tafada tana nuna mata direction din da Ramzia take daga musu hannu.


" kice uwar shirme dai"


" hahahaha Kai Amma hindatu Sam baki da mutunci kawarki ce fa"


" A'a to saime dan kawata ce sai bazan fada aibunta ba kome kike nufi?".


Ajiyar zuciya ya sauke " ahhh jarabatu Allah yabaki hakuri gani nayi ance tare kuka girma tun kuna yara Amma wane ni!"


Tafada tare da dan Jan karshen dai2 lokacin da Ramzia ta karaso inda suke tsaye.


" tab lallai Yau babbar rana ce wai hindatu tadawo school first day of resuming Kuma to add to it ma Ko late bakiyiba harma kin rigani zuwa" Ramzia Tafada tana kama baki.


" Ramzia kenan banda abunki ae da zafi-zafi ake dukan karfe" hindatu Tafada tana murmushi.


Murmushi Ramzia tayi me sauti " Allah yasa wannan karfen na kirkine bana tsiyaba"


"Uhm kema da wani zance yo inkin ji hindatu zatai kame aikin sa bata taba na Alkairi sai addu'a"


Dariya dukansu suka kyalkyale dashi dai2 lokacin da yafito daga motarsa hada ido sukai da sauri Ramzia taja hannun hindatu batare da ta lura ba " muje kafin mutumin nan ya rigamu shiga".


Tayi Ko nasara dan Sam hindatu bata lura da Haidar ba da sai sun tsaya dinta zuba ita a yanzu ba abunda yake sonyi irin ta kaurace ma ganinsa gaba daya.


Dan da Akwai yadda zatai Ko a school kar ta Kara hango shi da tsab zatai saboda yadda take jinsa.


Wayar hindatu ce tayi Kara alamun message.


"Ya nashigo fa!"


Mtsw a ranta wani irin takaicin sa taji kamar bazata mishi reply ba.


"Kaga malam kadan saurara mun sanin kanka ne bazan iya hadaku yanzu ba in zaka jira mufito in bazaka iyaba karike kudinka Ka Kara gaba dama sunmin kadan".


Take ta sending mishi " wai mekike naga kamar hankalinki baya nan gaba daya ma".


" nothing kawai na duba sakone a whatsapp dina"


Din takara Jin saukar shigowar wani text din.


"Karki damu indai kudine zaa Kara kawai dan Allah inason ganinta ko a capterial ne please hindatu".


Nodding kanta tayi "Angama!".


Abunda ta tura mishi kenan suka cigaba da hirar su Sam, Ramzia bata ankara ba dan jama'ar class dinsu sunhadu anata gaishe2 yaushe rabo da kawayen Arziki.


Sunjima suna hira basu fara lectures ba sai kusan pass 10am saboda farkon dawowa hutune.