ALAKARMU (MUMMUNAR ALAKA)

Ramzia Getting Worse ...

by @mimsqueen

Tashi tayi haryanzu jikin nata bai daina kadawa ba meta tuna da sauri ta koma kan bed din ta dau wayar tata buda text din tayi.


Hi Rahama,

Inafata kina nan lafiya ya yarana it has being long Ko dan waya kinyi blocking duk inda zan same ki why? Meyasa kike son bata mana ''Alakarmu' anyway nasan kinji zancen dawowata but not the day don't worry I just want to surprise you, nasan kintsorata da ganin message dina har yar da phone din kikai don't be scared I am all yours Rahama see you soon.


Free pages👇🏼


🅿️09


'Food Chemistry and brewing'


Abunda na iya tuna ganin lecturer din ya rubuta kan board din kenan lokacin da naji alamun text a phone dina.


Please Rahama meet me outside your class, please dan Allah.


Tsaki Ramzia taja Wanda hakan ya jawo hankalin student da lecturer gaba daya kanta, Sam bata lura ba maida wayar cikin handbag dinta tana yatsina fuska.


Kallonta Hindatu tayi tare da tabota, dagowa tayi suka hada ido, saida tayi mata alamu ta Kallah board din hakan yabata damar ganin yadda ajin yayi shiru aka tsura mata uban idanu.


" sorry sir!"


Tafada a hankali tare da dan Jan last word din alamun she really meant it.


" Rahama leave my class!"


Yafada cikin Jin haushi dan inda abunda Mr. James yatsana bai wuce yana lecture a dunga interrupting dinshi ba.


Sake lankwasa muryar Ramzia tayi alamun rarrashi " please sir!"


" no just leave or I will leave"


" no!" Student suka fara ihun bazai fita ba yayinda wasu dama baso suke ayi lecture din ba.


Ganin haka yasa ta dau shirginta tabar class din amma ranta yayi koluwar baci ran haidar saboda shiya yajawo mata,wanda inda abunda Rahama tayi hating tayi missing lectures dinta tana sakai kuwa ta hangoshi zaune can gun bishiyun dake can gefe.


Nodding kanta tayi saboda tsabar takaici, gogan banda murmushi ba abunda yake mata yana mata alamu da hannu da tazo.


Kamar bazata ba saikuma ta nufi inda yake Ko tunanin me tayi oho.


" bisimillah!"


Yafada tare da nuna mata gefenshi wani irin takaicinshi ne ya rufeta ganin gab dashi yake nuna mata.


" haba Queen dina bafa fada muke ba please sit!"


Yakara she cikin muryar tarairaya hakan yasa taje can dan nesa dashi ta zauna. Rakata yayi da kallo da mayukan idannunshi yana murmushi me kashe zuciyar me kallo irin nasu na kyawawan samari.


" yauwa kokef.."


" look haydar I am not here to waste my time with you, so cut all the long thing and tell me, why you are constantly bothering my life now for what offense? Why?" Tafada tana kallonshi cike da bacin rai, ganin sun hada ido yasa tayi saurin dauke kanta daga kallon shi.


Shiru yayi ya tsura mata manyan idannunsa tare da wani irin murmushi me wuyar fassara da dan sauti fassararshi, jin hucin murmushin nasa yasa ta dago da sauri caraf idannunsu ya shige cikin na juna.


Wani iri tsuma taji jikinta ya soma mata, batare da ta dauke idannunta cikin nasa ba " wannan wani irin mayene why is he.....".


" why is he....what?!"


Ya maida mata tambayar nan take tayi saurin dauke idannunta cikin nasa ta juya " look haydar indai kan abunda yafaru ne last time I am very sorry is unlike me Walh ba haka nake ba ban.....".


" I know! I know! Tabbas nasan ba halinki bane abunda yafaru, kawai kaddarar muce nima Kuma haka ba tsinci kaina Wanda sam ba halina bane, so is just that I can't take you out of my head and mind that it's! Kuma inaso kema Ki yarda ALAKARMU rubuttacene da sai ya faru!".


Nodding kanta tayi batare da ta kalleshi ba " you really have to dan ni matar Aurece nafada maka dan Allah kafita a harkata, please haydar kayi ma Allah bazan iya cin Amanar mijina da sunnah ba nayi MUMMUNAR ALAKA DAKAI, Sam ALAKARMU bazaiyuva!" takara she tare da facing dinshi kallonta yake still wannan karon ma murmushi yake.


Jin yayi mata shiru yasa ta tashi tsaye " And please is my last warning delete my contact banson ka sake kulani else....hmmm!" Tana kaiwa karshe ta soma tafiya.


Still yana zaune kamar Wanda aka daddaure agun " else what!"


Wai gashi tayi bata ce mishi komai ba tajuya tacigaba da tafiya.


Kallonta yake duk yadda take motsa structure dinta dake burgeshi take tana shiga ranshi sosai " Kai Ina I can't leave you Rahama kinhada komai da nakeso gun mace" Yafada a ranshi.


Harta kusa kaiwa gun kofar yakira sunan ta.


" Rahama!"


Cak ta tsaya batare da ta waiga shi ta kalleshi ba.


Tashi yayi cikin taku na Isa ya karasa bayanta " Rahama nafada miki gaskiya I will not leave you Walh kome za'ayi I am ready to go to any lenght to have you as mine Walh".


Mamaki sosai kalamunsa yabata ta juya " Anything fa kace?"


" yes of course anything!"


Murmushin takaici tayi " Haydar Ina mamakin maza irinka Walh masu bibiyar matan wasu baka tsoron kayi aure wataran wani yabi matarka?!".


Shirune ya ratsa tsakaninsu na 'Yan second hakan yasa tayi murmushi Jin bai iya ce mata komai ba.


"Well you see Baka da amsa Kai kanka"


Girgiza kai tayi harta daga kafa taji yana murmushi hakan yasa ta waiga batare da ta motsa ba.


" bana Jin Akwai wata mace da zanyi kishinta a duniya inbake ba!"


Yadanyi shiru tare da gyara tsayuwarsa ya zura duka hannayensa cikin aljihunsa, binsa kawai take da kallon mamakin karfin hali irin nasa take sosai.


" hmm! Rahama bazan taba kishin wata mace a duniya bayan Ke ba, kamar yadda bana Jin zan iya Alaka da wata macen bayan Ke shiyasa ALAKARMU keda matukar muhimmanci a rayuwata yadda baki tunani Kuma Insha Allahu saina maida kalmar MUMMUNAR ALAKA zuwa KYAKYAWAR ALAKARMU!".


Dan tsaki taja mara sauti sai lips dinta daya dan motsa zai tabbatar maka da abunda tayi, haydar kuwa ganin yadda ta motsa lips din ya matukar burgeshi ya shirga wata duniyar inda yake tuno abunda yafaru tsakaninsu.


Ganin yadda yake kallonta yasa tashiga kallon kanta ganin bata ga komai ba kallo ba yasa ta juya " uhm tirrrr da irin wannan Alakar banda Alaka dakai Kuma bazan taba ba dan haka kadaina kiranta da ALAKARMU ka kirata da Alakarka Kai kadan ka mtsw" taja tsaki tabarshi tsaye kamar wani dolo.


Sam bai ankara da ta tafi ba saida ta bace mishi sam baisan kwanar da tayiba, ya dudduba baiga alamunta ba hakan yasa yayi tunanin takoma class yajuya yabar gun.


Ramzia kwanar bayan class dinsu ta nufa bayan wata katuwar mango tree inda abubuwan dake faruwa cikin life dinta ke damunta sosai, kuka ta fashe dashi lokacin da take tuno abunda yafi damunta.


Wata Ranar Friday


Ranar Ramzia sunfi to school su uku driver dinta baizo ba tajira shiru inda karshe takira shi yake shaida mata motar ta lalace.


" Ramzy what is the problem?"


Sakura tafada tana kallonta, dan ciza lebe Ramzia tayi " nothing Walh Yau kb bazai sama zuwa ba".


" what?!"


Hindatu tafada " yes hindu yace yafito motar talalace yanzu haka yana garage" takarasa cike da damuwa tuna Rasheed Sam ya hanata hawa keke naphep Ko machine sam.


" so now me zamuyi?"


" kamar ya me zamuyi hindatu? Yawuce tahau keke naphep?" Takara she tana kallonsu suma zuba mata idanu sukai.


" what?!"


Tafada ganin kallon da suke mata " to nida Ke hindatu ae naphep muke hawa mai zai cita dan Yau kawai tahau?".


Girgiza kai hindatu tayi " hmm Rasheed is the problem" hindatu Tafada tana kallon Ramzia dake kallonta Jin yadda takira sunan mijin nata gatsal.


" yes eh mana Nasan ya hanaki but ae baya kasar and in fact inbaki hau ba a kafa Zaki tafine?" Nan dai suka tursasata kan tabiyosu inyaso Su sauketa.


Ramzia Jin haka yasa ta amince, Kai tsaye suka nufi gate din dai-dai lokacin Haydar Ke danno musu horn ta baya.


Juyawa hindatu tayi cike da jaraba ganin haydar ta saki murmushi tare da daga mishi hannu " guys kunga wa muka samu?".


"Wa?!"


Samira tafada dukansu suka juya can gefe yaje yayi parking.


"Muje!"


Hindatu tafada tare da fusgar hannun Ramzia sanin bazata yarda ba indai tabi tata.


" sakeni bazaniba"


Ramzia Tafada tana kokarin cire hannunta amma sam hakan baisa hindatu ta sake taba saida takarasa da ita gaban window din haydar.


"Barka da fitowa"


Yafada yana kallon Ramzia suna hada ido ta dalla mishi harara hakan yasa yayi saurin dauke idannunshi kanta yamaida kan hindatu.


" barkanmu dai zakace tunda kaima gashi kafito yanzu" hindatu tafada tare da murmushi.


" Aikuwa dai" samira tabata amsa.


" aa yanaga harda gimbiyat...."


" ba'azo daukarta ba motar ta lalace!"


Hindatu ta katse shi tare da bashi amsa,mintsininta Ramzia tayi "ouch!" tafada saboda taji zafi.


" to ku shigo na sauke muku hanya"


Jan hannunta Ramzia tayi alamun tace aa Amma sai hindatu tace bakomai.


Ramzia ba yadda batai bazata shiga ba Amma dole suka tirsasata gidan gaba sukaita surutu, a hakan ma sai da suka San yadda zasuyi suka rigata sauka.


Tunda suka sauka zuciyar Ramzia Ke dukan uku-uku saboda tsoro duk da motar da tintet, sunyi tafiya me nisa caraf taji ya riko hannunta " Ramzia why?".


Bata ce mishi komai ba sai kokarin cire hannunta datake cikin nasa " please talk to me mana"


Nan ma shiru tayi banda motsi da alamun numfashi ta kan kokarin cire hannunta bakajin komai.


Gefen titi ya koma yayi parking yayi locking kofar " please let me go haydar!".


Tafada da karfi cike da fushi, sake hannun nata yayi jikinta na wani irin rawa, murmushi yayi ganin yadda take kokarin bude kofar duk ta rikice mishi.


" dan Allah dan Annabi kabari nafita".


" indai kin yarda Zaki yi abunda nasaki zanbarki" runtse idannunta tayi dan Sam bata fahimci me yake nufi da ita ba gashi yamma tayi sosai kasancewar last paper dinsu ne yau a school basu fito dawuri ba, ga yawon kai su hindatu dayayi baza'a jima ba zaa kira magrib.


" mekenan"


Tafada tare da waigawa kallonta yake yana murmushi.


" I want hold you just wannan dayan kawai dagashi Zaki iya tafi...."


" Bazan taba aikata hakan ba Walh Kuma dole kabarni natafi".


Nodding kansa yayi tare da dan murmushi me sauti ya tada motar inda yashiga yawo da ita yafita nan ya shiga nan, karshe har aka Kira magrib inda kb suka shiga kiran wayarta Wanda su Aleena kenemanta anjita shiru hakan bakaramun Kara tada mata hankali yayiba.


" dan Allah Haydar kayima Allah kabarni".


Bai amsa ta ba tacigaba da tafiya suna karade gari, ganin dagaske yake tafara tunanin amincewa tana saka Tana warwarewa.


" wait!"


Tafada dan kallonta yayi hakan yasa ta runtse idannunta duhu yayi sosai sai dai akwai hasken futilu da motoci.


" zanyi!"


Zancen yazo mishi a bazata " really?"


" yes I will".


Gu ya nema gefen titi yayi parking motar yagyara zama ya maida dubansa gareta.


Kai hannunsa yayi zuwa nata yariko duk da tana Jin wani iri haka ta hakura batare data hanasa ba runtse idannunta tayi sosai kirjinta na bugawa.


Tabbas abunda yake damunsa itama yana damunta sosai, Wanda tunda ta fahimci zai zama matsala ta janye mishi tadaina hulda dashi Sam Ko a bangaren karatune duk da yakasance suna karatu tare a cikin makaranta lokaci guda tadaina ta janye mishi sakamakon wannan mugun yanayin da zuciyoyinsu Ke bijiro musu.


Shiru yayi yana kallonta duk da ba sosai yake iya ganinta ba, yana Jin wani irin yanayi duk sanda ya kasance da Rahama yarasa why.


Sun jima yana wasa da hannayenta yana kallonta yayinda idannunta Ke rufe, wani irin feelings take ji ajikinta tundaga kanta har zuwa kafafunta jikinta rawa yake.


A hankali yasoma matsawa gab da ita har suna iya Jin numfashi junansu bata ankaraba taji ya hade lips dinsu gu daya, tare da rungometa sosai.


Kokarin cire bakinta da jikinta tasoma tana dan tureshi, inda a hankali tafara sakin jikinta saboda yanayin da tashiga mai wuyar fassara, itada kanta ta soma maida mishi martani sosai, ganin haka yabashi damar sa hannayen sa cikin jikinta inda yacigaba da yawo dasu jikinta especially breast dinta.


Sun dau mins sosai a haka sun manta Sam a ina suke sosai suke tsotse bakin junansu kamar zasu cinye juna kusan dukansu a bukace suke.


Ringing din wayarta ne ya fargar da ita da sauri ta janye shima ya koma mazauninsa inda yashiga maida numfashi.


" please ka...."


Kasa magana yayi ya bude lock din motar itama cikin wani wahalallen yanayi take mishi magana.


Da sauri ta bude murfin motar tafita ta rufe jikinta na bari tahau kan titin taci Sa'a tasama naphep tashige.


Wannan rana dakyar taje gida kusan ta jima rabon data jita cikin irin wannan mawuyacin yanayin, haka ta shiga gida komai daurewa take tana ma 'ya 'Yanta da dare yayi tashiga wanka Tasha kuka sosai, dakyar take iya kallon kanta ga wani irin yanayi da zuciyarta ke Kara bijiro mata kansa wannan Ke matukar damun Ramzia.........