ALAKARMU (MUMMUNAR ALAKA)

Life Of Rayhan...

by @mimsqueen

Samir yana fita gefen kofar ya jingina tare da runtse fararen idannunsa da suka fara sauyawa, kusan hakan na faruwa dashi duk lokacin da Ashna takira Rayhan yaji yadda yake wulakanta ta.


Yau ma hakan ne ya kasan ce ji yake kamar ya bude zuciyar sa ya cire saboda wani irin mugun azababben kishi dake damun shi.


" Samir!"


Muryarta ta sauka cikin dodon kunnenshi, sake runtse idannunsa yayi dan gani yake kamar tsabar tunani ne yasa yake ganin hakan.


Nodding head dinta tayi tare da murmushi wanda yakara fito da kyauta sosai.


Ashna ba fara bace bakinta ba Kuma irin can sosai bane zamu iya kiran ta da chocolate colour sai dai tana da hanci ga manyan idannunta da kamar anzana , ga tsawo duk yadda zan kawata muku kyan Ashna bazaku fahimta ba.


Ganin haryanzu yana tsaye idannunsa na rufe yasa ta karasa tare dan ta bashi " Samir!".


A firgice yafarka daga duniyar daya shiga har yana dan hankadeta, saura kadan tayi kasa cikin zafin nama ya cafkota zuwa kirjinsa.


A dan tsorace ta zaro idannunta kan nasa, wanda tuni Samir ya manta duniyar da yake ya tafi cikin duniyar tunanin ta gaba daya. A hankali tayi kokarin dagowa daga rikon da sauri ya saita zuwa tsayuwa dai-dai lokacin da daya daga kannan Samir takaraso gun.


" what is really going on here? Tun daga nesa na hango wani scene saikace a film, guys....?".


" shut up! Wai Nadia yaushe nazama sa'anki a gidan nan!".


Dariya Ashna tashiga tuntsirewa tsayuwa Samir yayi kamar dolo ya kura mata ido, har tana kama cikin ta dan kusan Samir da Nadia koyaushe haka suke, basu jituwa kamar tom and Jerry Kuma ba ita Ke bi mishi bama amma kaga yadda suke zakace sakone.


Nadia nodding kanta tayi ganin yadda Samir ya kura ma Ashna ido, tana matukar tausaya ma dan uwanta gashi cousin din tasu sam bata ankara da hakan ba hankalinta nakan Amininsa na kud-da-kud.


A hankali tafara saita kanta " is h.....".


" dama do you have to ask ne bayan kinsan halin Rayhan mutum kullum yana daka kamar mace mtsw".


Harararta Ashna tayi ta kalla Samir da haryanzu ita yake kallo " let me see him!".


Kada mata head dinshi yayi alamun ta fito lafiya.


Tana shiga ya koma ya jingina da ginin kallonshi Nadia tayi cike da tausayawa " hmm! A dai juri zuwa rafi, dama dai so daya ake samun ta inta wuce hmm".


A zuciya ya dago zai mata magana sai dai tuni tashige falon, sanin me zai biyo baya idan ta tsaya agun " mtsw damn it!" Yafada yabar gun.


" surprise!"


Runtse idannunsa yayi tun kafin ya waigo ya kalleta sam baiyi tsanmanin ta a yanzu ba especially da sukai waya yanzu bata ce masa zata zo ba sam.


Karasa shigowa falon tayi kwance yake idannunsa na kallon sama sai dai a rufe suke, karasawa gefen kujerar tayi ta zauna.


" how do you like my Surprise baby!"


Tafada lokacin data kai hannunta kanshi tana shafawa, wani irin Karin bacin rai yaji ta dasa mishi da sauri ya tashi zaune.


" what brings you here?!"


Tabe face dinta tayi tare da cinno kyawawan lips dinta gaba " Are you not happy to see me? Haba baby!".


Dan sakin face dinshi dake hade yayi sanin halin ta " no! But ba muyi dake Zaki zo ba and yanzu muka gama waya so....?!"


" just kawai inaso nayi surprising dinka ne and kasan wani abu?"


Nodding head dinsa yayi cike da mamaki " how can I know idan baki sanar mun ba".


" she is here to stay!"


Nadia dake tsaye gefe tana takaicin su tafada da dan karfi.


Juyawa Ashna tayi cike da bacin rai " and who asked you that? And why did you follow me? Dallah malama kibamu guri kinzo kin wani batamun surprise dina dan iskanci get out!".


Cike da takaici Nadia tabar falon amma tadan ji dadi a ranta dan tasan tunda yasani it will be hard for him to stay for another day ma not days, murmushin Jin dadi tayi ta nufi part dinsu.


Wani irin faduwa gaban Rayhan yayi, inda abunda ya tsana bai wuce ganin shi gida daya da Ashna ba yasan sam bazata barshi yasa ma sukuni ba tayita damunsa kenan.


" sorry baby, she just spoiled it for me"


Tafada lokacin data Kara matsawa gab dashi. Ganin hakan yasa Rayhan ya sake janyewa inda cikin rashin sa'a yaji shi jikin bangon.


" bakomai Karki damu. And dama inason fada miki ni gobe zan tafi Kd my mother just cal..." sa hannunta tayi kan lips dinshi lokacin data kara matsawa gab dashi, fuskar ta sam damuwa ce karara ciki ba annurin data shiga dashi Sam.


" shhhhhh! Please Rayhan Ko danni stay back kona 2days ne I left home nazo kawai just to be with you please!"


Kokarin tashi  yayi amma sai yajita gam a jikinsa, lokaci guda ta soma kokarin hada lips dinsu idannunsu na cikin na juna harta kusa, cikin wani irin yanayi ya kautar da face dinshi gefe.


Hakan bakaramun zafi ya mata ba ta sake shi ta tashi, binta yayi da idannun ganin sauyin yanayi ta lokaci guda.


" hmm!"  Tafada tare dan yin murmushi medan sauti.


" is about her again?"


" who?"


Yayi maganar cike da surprise " hmm Rayhan kenan! Duk da bansan meke damun kaba tun a London I try my best to make you mine but you always turn me down why?"


Murmushi ta Kuma lokacin data waigo saitin shi " zan amsa maka meyasa!"


" how? Mekike nufi Ashna!" Yafada cikin rashin fahimta.


" maza dayawa suna sona suna son kasancewa dani, Sam ban kasance mummunar mace ba Allah ya bani dukkan abubuwa da cikakkiyar mace Ke mallaka wacce Ko wani namiji zaiyi fatar kasancewa da ita, Rayhan!".


Tadan tsaya tana kallonshi a wannan lokacin fuskar ta ya ciko da alamar hawaye na shirin fara sintiri kan kyakywar fuskar tata.


Kallonta ya tsaya yana yi cike da tausayawa, shikansa abunda ke damun shi kenan ciwon so wanda haryau yakasa ma kansa magani, yana matukar tausayinta sai dai zuciyarsa taki bashi fili, yana son bata so Koda kadan ne amma zuciyar sa cike take da kewa da burin abunda bazai samu ba.


" Rayhan!"


Ta katse mishi tunani. " Baka kasance mazinaci mai bin mata ba sam, wannan hali da dabi'un naka suke Kara burge ni  sabanin wasu mazan wadanda suke da dukiya irinku Ko suka sama damar saka samu, najima Ina mamakin abunda yake hanaka Koda soyayya ne da mace sai daga baya nagane kayi nisa a soyayyar Rahama!".


Wani irin bugu zuciyar Rayhan tasoma kamar zata fito, tashi yayi batare da ya shirya ba yana kallonta a cikin wani irin yanayi me wuyar fassara.


" yes Rahama! Nasan zakai mamakin yadda nasan sirrin zuciyar ka, tabbas najima da sanin wannan rubutaccen sunan dake cikin ilahirin jikinka, zuciyar ka da ruhinka sai dai kash bansan WACECE Rahama da ALAKARKU ba sam wacce tayi ma ALAKARMU illa wacce najima inaso nagina sa...."


" Taya Ki kasan wannan sunan?"


Yakatse ta tare da tsareta da fararen idannunsa da suka rune a yanzu, kamar sojan da allurarsa ta tashi.


"Uhm!" Tana nodding head dinta tana murmushi me sauti Wanda cikin sa zaka fahimci akwai ciwo da zafi me tsanani a ran wanda Ke fiddashi.


" zaka iya tuna about 1 and half year ago wani zazzabi dakai?" Tafada tana kallonshi Wanda shima ita yake kallo yana kokarin tuna wani abu daya faru suna London.


Wata Rana.........

Yana zaune a gida shi daya yana rubuta wani project dinsa da aka bashi, a lokacin kansa yana masa wani irin matsanancin ciwo ga zazzabi.


Yayita kiran Samir da Musty da suka fita suka barshi shikadai shiru ya kwanta falon, saboda kamar every second ciwon nasa Ke karuwa. A wannan lokacin Ashna tazo gunsu itada kawarta Lana.


Bai iya musu magana ba Wanda hakan ya matukar tada ma Ashna hankali har suka Kira doctor dake kusa yazo ya dubashi a wannan lokacin sam bazai tuna abubuwan da suka faru ba tunda Doctor din yazo harya tafi sai dai Koda ya farka yatadda Musty zaune inda ya shaida mishi, Ashna kwana tayi tana kula dashi har suka dawo da Asubha sai da gari ya waye ta tafi.


Cigaba.....

Dago idannunsa yayi suka hada ido dan iya abunda ya tuna kenan.


Murmushi Ashna ta mishi tare da share hawayen dake tsiyaya idannunta " yes! I did take of you the whole night duk zafin ciwo da juyi a lips dinka ba abunda nake iya ji sai wannan sunan a hankali" ta karasa kamar zatai kuka.


" wannan daren shattered all my dream about us a nan na fahimci kayi nisa sosai Rayhan, haka yasa nama Samir magana wanda shima yaki bani information kanta I decide to continue Ko wata rana zanyi riba, Amma a yanzu nafara sarewa, kullum abun nafin karfina Rayhan ina matukar sonka I can't live without yo....".


Tausayin kanta da nasa yasa ya rungumeta shi kansa ji yake kamar zaiyi ihu, tabbas so guba ne ji yake kamar ya cire zuciyarsa ya cire Rahama yasa ta amma Ina abun yafi karfinsa.


Sunjima a haka motsin shigowar Samir yasa sukai saurin rabewa amma ina idannunsa ya ruga yakai, da sauri ya juya yabar dakin goge hawayenta tayi bata jira komai ba itama tabar falon, komawa kan kujera Rayhan yayi yarasa abunda ke masa dadi sam. Bangaren Samir shima damuwar ce kusan a Abuja a yau love triangle din is hot irin yayi zafi totally din nan.


Komawa kan kujerar Rayhan yayi yana tunano abubuwan da suka faru a rayuwarsa dake matukar Kara mishi wahala wajen manta Rahama.


Zaune suke suna kallo cikin 'yan uwansu duka-duka Rayhan bazai wuce 12yrs ba a wannan lokacin kallon yarinyar dake gefenshi yayi ya mata murmushi wacce bazata wuce 10yrs ba. Sam ba wanda ya lura da hakan bayan su kuwa hannayensu ne sarke jikin bangon cikin na juna wanda kusan koyaushe basu rabuwa da yin hakan.


Lokaci guda Nepha suka dauke wuta Wanda hakan yana duhu damar mamaye ilahirin falon.


" A kunna gen!"


Muryar wata daga ciki naji yayinda sauran suka fara fita kokarin neman abun haskawa.


Tashi da sauri tayi ta cire hannunta cikin nasa " Rahama! Rahama! Inazaki a duhu".


Muryarsa ce ta karade duhun tashi yayi yana lallube cikin ikon Allah yasamu ya fusgota lokaci guda sukai kasa tafada kansa.


Jinta jikinsa ya saukar ma dan yaron da wani irin dadi wanda baisan na meye ba baisan komai ba. Haka kawai yaji baiso ta tashi daga jikinsa saka hannayensa gaba daya ya mamaye ya rike ta yadda bazata iya tashi ba, yayi ganin tana kokarin tashi Jin ana kiran sunanta can daga daya falon.


" Karki tashi!"


Yafada a hankali dai-dai lokacin da haske ya haska Ko Ina na falon idannun babbar yar su ce takai kansu Aunty Faty wacce Ke zaune ita daya a falon, Sam bata san suna falon ba a tunanin ta sun bi sauran ne.


Tashi tayi da sauri ta nufesu ganinta yasa suka  soma kokarin tashi kafin kace me tuni taba Rahama azababben maruka biyu, yar yarinyar da batasan komai ba. nan take ta fashe da Kuma shima Rayhan din kuka yasa mata duk da bata tabashi ba.


" Ke! Wannan irin iskacin da ake gidanku da yaran makofta kikeso kizo kina mana a gida Ko? Mtsw Ammi da kwashe-kwashe yaushe zata hada yaran geto da nan yaran da tun suna kanana suke iya iskanci, tafi kibanguri!".


" Rayhan!"


Tashi yayi lokacin da Samir ya katse mishi tunani a zuciye.


" wai mekake shirin aikatawa da Ashna bayan nida kai munsan baka sonta!".


Samir Yafada cikin daga murya da bacin rai. Nan Rayhan ya shaida mishi abunda ya faru da batun tafiyarsa Kd gobe. Samir yaji dadin Jin tafiyar sosai koba komai baiso Rayhan na nisa dasu Ammi dakyar yadawo ma daga London din kunsan shiya dawo dashi.









                  Sai mun hadu a Next Page......👌