ALAKARMU (MUMMUNAR ALAKA)

Rayhan's Back...

by @mimsqueen

           9am....

Motar su Ammi tayi parking cikin gidansu Ramzia, karar motar yasa yaran suka shiga tsalle suna murna.


" Ammi! Ammi! Ammi is here".


Kan Ramzia tace kobo sunyi waje da gudu, bin bayan su tayi amma saita ga sun shiga mota already.


" Ammi tace kidauko mayafi mutafi" zainab tafada lokacin data zuro kanta waje.


Da sauri Ramzia taje ta sako mayafinta tafito, inda tashiga mota driver yaja. Har wannan lokacin kirjin Ramzia bai daina bugu ba saboda matsanancin tsoro daya addabeta.


Basu tsaya Ko inaba sai taga su nufi Airport, duk da tadan tsorata amma ganin Ammi na dariya yasa hankalin ta ya kwanta tabbas yanzu ta fahimci Rayhan ne yadawo, nan wani sabon fargabar yasame ta yadda zata fuskan ceshi wannan yana faruwa duk sanda zasu hadu.


Haka har suka isa ciki inda musa driver yayi parking. Kb shima yayi perking murmushi Ammi tayi me sauti.


" Munzo now Aleena zata canki what we are here for" zainab tafada tana dariya.


Girgiza head dinta Aleena tayi " no Aunt zee please tell us!" Aaina tafada cikin shagwababbiyar muryarta.


" Oya muje!". Ammi tafada tana musu dariya sosai.


Ramzia ce a farkon gefen kofar hakan yasa tabude kofar jin Ammi tace su  sauka nan bugin kirjinta ya Kara tsananin ninkuwa.


Kai hannu tayi ta bude caraf kuwa ta hangoshi tsaye suna facing din juna cikin shigarsa ta kana nan kaya daya saba formal blue shirt ce jikinsa, sai wandonsa cream colour abunka da farin mutum yayi matukar yin kyau, sai black sunglass dinsa dake manne idannunsa, rataye yake da dark jacket dinshi yayinda daya hannunsa ke cikin pocket dinshi, gefenshi Kuma trolley-sleeve bag dinshi ne me kyau da daukar ido.


Tunda suka hada ido ya tsinci kansa cikin wani irin tashin hankali, saboda bugun da zuciyar sa take kamar zata fito. Dukansu biyu kallon juna suke sun kasa dauke idannunsu ga junansu.


" is Uncle Rayhan! Yeeee! Please Momy kibude muje gunsa". Ihun yaran ya fargar da ita duniyar data lula gaba daya.


Ammi shiru tayi tana mamakin abunda yafaru girgiza kanta tayi, sai dai tafi Alakanta hakan da haduwar jini da shakuwarsu, da wannan ta cire tunanin.


Tuni twins suka isa inda yake inda suka cika shi da surutu da ife-ife "Rahama muje mana!".


" Na'am!". Tafada dan sam hankalinta baya kan su Ammi sam, hankalinta yatafi gun Rayhan dake wasa da yara gaba daya.


" muje"


Zainab ta maimaita mata dan tuni Ammi ta karasa gun " kai! Kai! Kuyi a hankali karku ballamun da". Dariya su duka sukai.


" Ammi yarana nefa sunjima basu ganni ba, let them enjoy".


" to me 'ya 'ya saika wuce muje, idan munje gida saiku karata". Tafada lokacin data riko hannun Aaina.


" bro kaga yadda kakara haske kamar bature wow!". Nodding kansa yayi yadan saci kallon Ramzia dake tsaye tana kallon kasa.


"Uwar magana Zaki fara ko?!"


Tabe yan lips dinta tayi " ae gaskiya nafada Ko ya Rahama dan Allah bai kara kyauba kalleshi fa kiga?" Tafada tana jawo hannunta wanda badan taso ba ta dago suka hada ido, tayi saurin dauke idonta saboda yanayin data ji.


" zainab! Kuzo muje gida haka kwa karasa acan" da sauri zainab tabi bayan Ammi, dama kayansa already driver ya kwashe yasa a booth.


Yaran da gudu suka nufi inda KB driver yake dan sun dage motar daya shiga nan zasu shiga, ganin haka Ammi ta leko.


" Rahama to kibisu a motar ku kawai ku rigamu dan zan tsaya nadauka Momynki dama tafito mu take jira!".


Gaban Ramzia ne yayi wani irin mugun faduwa runtse idannunta tayi, tuni su Ammi suka bar gun zuwa yayi zai wuce ta gefenta cikin rashin sani hannunsu ya gogi ba juna sake runtse idannunta tayi ga kamshin perfumes dinsa data gama haddacewa gaba daya, shi kansa da yayi gaba saida yadan tsaya tare da runtse nasa idon. Yau gashi ga Rahama gabansa ne yaji ya fadi lokaci guda ya bude idannunsa yabar gun ya isa mota.


Still tayi agun, tana tuna wasu abubuwa da suka Ki barin zuciyarta " Momy! Momy! Ke muke jira" Aleena ta kwala mata kira.


Bude idannunta tayi da sauri ta karasa ta bude ganin yaran ne a tsakiya yasa taji sauki, haka Kb yatada mota tunda suka fara tafiya bata ce komai sai shi da yara da suke surutunsu.


Kallon inda hannunsa ya shafi nata yayi, Wanda ya haifar mata da shiga duniyar tunani.


Long time ago.....

" why kake son koyaushe kaji hannuna cikin naka? Why do you love me so much Rayhan?".


Murmushi yayi me sauti tare da sake matsawa gab da ita, inda ta manne da jikin bangon har suna iya jin bugun zuciyoyin juna.


Sa hannunsa yayi kan fuskarta tana kallonshi cikin wani irin yanayi, yake mata murmushi a hankali yake kara shige ta, hakan tasa tafara jinta cikin wani yanayi runtse idannunta tayi tana sauke wani irin ajiyar zuciya.


Jikinta banda rawa ba abunda yake a wannan lokacin, gani take kamar kissing dinta zaiyi amma ga mamakinta sai taji ya daura hannunsa kan lips dinta ya rufe, a hankali ta bude rinannun idannunta a kansa idannunsa cikin nata.


Murmushi yayi tare da nodding din kansa yaja da baya ya juya da sauri tafara kokarin saita kanta.


Ya juyo yana kallonta har lokacin ya lura da alamun tsoro tattare da ita.


" Rahama! Rahama! Rahama!"


Yafada tare da kura mata ido " I can't live without you! I cannot imagine my life without you!" Yafada a sanyaye yana kallonta.


Cike da damuwa ta kalleshi dan sam itama tana jin yadda yake ji a ransa " but what if I di...." da sauri yakaraso kanta karasa yasa hannu ya rufe mata baki.


" shhhhhh! No such things will happen Allah bazai mana haka ba, so pleas.....".


" Ramzia! Ramzia! Ramzia" muryar khairiyya ce ta karade ilahirin gun.


" Na'a...."


Bata karashe ba taji ya hade bakinsu kokarin ture shi ta shiga yi amma Ina duk yadda taso hakan bai samu ba saima ji da tayi jikinta ya sake.


Cigaban labari.....


" Momy! Momy! Bacci kikai kiketa murmushi?".


Aaina ta tambyeta da sauri ta gyara zamanta dan idonta rufe tashiga wannan duniyar, satar kallonshi tayi cike da jin kunya, taga yana danna wayarsa ajiyar zuciya tayi dai-dai lokacin da Kb yayi parking cikin harabar gidan.


Dai-dai nan taji shigar messages, tana dubawa taga nashi ne.


Hi Rahama! You didn't  change at all.....I miss home.


Abunda ya rubuta kenan tana daga ido taga sunfi ce anata ihun Uncle Rayhan yaran 'yan uwa.


" me zan gani!" Aunty Faty tafada lokacin data fito daga falo. Wanda hakan yakara haifar ma Ramzia wani irin mugun bugun kirji.


" Rayhan amma baka da kirki shine da mukai waya jiya you didn't inform me?!".


Karasawa yayi ya hugging dinta saboda murna, har wasu hawaye taji yafara zubowa idannunta shima hakan ne a bangarensa 5yrs kenan rabon shi da gida Nigeria.


Sauran ma haka suka baibayesu cike da murna. Ramzia kuwa ganin Aunty Faty yasa gaba daya ta hargitse da damuwa especially ga Rayhan.


Kokarin sulalewa tafara yi ganin duka hankalin su nakanshi caraf kuwa idannunsu ya hadu dana Aunty Faty wacce ta saki Rayhan da sauri.


" tare da yarinyar nan kuke?"


Girgiza kai yayi sanin yadda ta tsani Rahamarsa " yes da.....".


" aw kenan ita kafada ma zuwanka suka dauko ka?".


Shigowar motar su Ammi ne ya tsaida zancen.


" me like a waje haka duka?" Ammi tafada hakan yasa Aunty Faty ta daka ma Ramzia harara taja hannun Rayhan zuwa ciki.


Bayan sun shiga ciki ake gaggaisawa " oya Rahama jeku hado dan abun motsa baki mana" Ammi tafada inda suke 'yan hirarraki da Momy.


Tashi Ramzia tayi ta nufi hanyar kitchen " uhm bari naje muyi tare" zainab tafada.


" yi zamanki zamu hado tare" jin haka yasa Rayhan yayi saurin kallonta, sanin ba alkairi zatabi Rahama dashi ba yasan ta sarai ji yayi kirjinsa na mai wani irin bugu me zafi.


" Ke! Naga jikinki yana wani rawa harda zuwa dauko shi to Walh karna kuskura naganki kusa dashi, kina jina?!"daga mata kai Ramzia tayi alamun taji dan tun suna yara take matukar tsoron Aunty Faty Wanda kusan dashi ta girma.


" Ke banda rashin hankali irin naki da iskanci ya zaki hada wa da kani Ke daya? Yaro duk yakasa sukewa saboda ke inma asiri ne walh wannan karon saina karya....." " mekuke hada mana!" Khairiyya ta katse Aunty Faty lokacin data shigo.


Da sauri ta nufi Rahama tayi hugging dinta " Walh tunda nataho nake ta addu'ar na tarar dake kiranki ne kawai banyi ba" Tafada cike da jin dadin ganin yar uwarta.


" shin kin makance ne Khairat Ko kuwa tsabar iskanci ne".


Tabe fuska Khairat tayi " kai aunty kinfa san in naga twinny dina walh sai a slow sorry" Khairat ta karasa tana kallon Aunty Faty cike da murmushi me wuyar fassara.


Tsaki Aunty Faty tayi ta nufi kofar fita " ina kwana Aunty Faty" tsaki Aunty Faty taja bata waigo ba haka bata amsa mata ba.


Kallon Ramzia tayi tana dariya ta mika mata hannu suka tafa " kinga nayi miki maganinta tunda naji kuna tare nasan da matsala especially dana ga ya Rayhan nasan bazata raga miki ba." Murmushi Ramzia tayi.


" Amma ni banaso kina mata koba komai she is our big sister fa!" Ramzia takara she maganar cikin sanyin murya.


" wannan Kuma bata shafeki ba malama baki san yadda kuke ban haushi bane, keda ya Rayhan bama me Kara ban haushi irin ya Rasheed. Hmm nifa banki ya sake......"


" please khairy kibar wannan zancen kar aji kinsan gidan cike yake" Ramzia tafada lokacin data rufe bakin Khairat da hannunta.


" alright then! Saikuyi tayi tunda rayuwar kunci kuka zabar ma kanku ku ukun, nidai nafada nawa." Nan suka cigaba da shirya tray din suka sauya hira.


Koda suka fita falo basu iske shiba dama can shi ba maison hayaniya bane dakin shi ya koma cike da damuwar da yakasa sabawa dashi.


Kamshin da yaji dakin nayi yasa yayi murmushi sanin bakowa zai gyara mishi daki haka ba sai auta zee, mika yayi tare da sauke dogon ajiyar zuciya ya fada kan lallausan gadon nashi " there is no place like home".


Yafada yana kallon POP din wasu irin hawaye ne yaji suna sauka kan face dinshi masu zafi, fiddo wayarshi yayi cikin pocket dinshi kai tsaye gallery yashiga ya viewing vedio dinta.


Idannunta rufe suke tana murmushi me daukar hankali, a hankali lips dinta ke motsawa tana sake fadadashi, wannan sabon vedio ne daya mata a hanya batare da ta sani ba.


Murmushi yayi me ya tuna sai yayi wurgi da wayar nan take yanayinsa ya sauya, zuwa damuwa da bacin rai sa daya hannunsa yayi aka.


Yana tunanin taya zai cigaba da rayuwa inda zai dunga ganin matsayin matar dan uwansa, dan bugun kirjinsa yayi " why can't I get her out of my head? Why Rahama how could you do this to me?!" Yafada da dan karfi jin motsi a corridor dinshi yasa yayi wuf yashige toilet din.


Share hawayen dake kan fuskarta tayi ta tura kofar " My Little brother kana ciki?" Aunty Faty tafada da dan karfi sake goge face dinta tayi ta nema gefen bed din ta zauna, wayarsa daya Ke gefe ta dauka inda taga abunda ke kai vedio din Ramzia ne, runtse idannunta tayi saboda abunda take ji dan tsaki taja a hankali.


Yana murda kofar tayi saurin maida wayar, da murmushi kan face dinshi ya fito " my sweet sister, naji muryar Ki nashiga toilet ne. Nagaji dan ma na kwana biyu a Abuja." Yakara sa yana kallonta tare da riko hannayenta yana murmushi.


" eh nashigo nakara ganin kanina haba! 5yrs ba wasa ba fa!" Ta janye hannunta tare da dan tabe fuska, ganin ya yi kasa dakai yasa tayi murmushi taci gaba da magana.


"sai dai naji muryarka a waya sai chat yau gani gaka a zahiri kaga kuwa, bazan barka ba kona 5mins gaskiya". Dariya dukansu suka sheke dashi sosai shima yake jin dadin ganin ta dan yana jin ya Faty kamar Uwa ta bangarori da dama dan tana bashi kulawa a koda yaushe a rayuwar sa kaf 'yan uwansa yafi shakuwa da sabo da ita.








                  Na matsu naji Asalin labarin wannan zazzafar soyayya ta Mr.Ray da Ramzy....I know Kuma you are all curious about it keep following Alakarmu very soon it will unveil....👌