You're Still In Love With Me....
by @mimsqueen
Not Edited So:
🅿️14
" Rahama kinkai ma dan uwan naki abinci kuwa?" Ammi ta tambaya tana kallon Rahama.
" zainab! Tashi kikai masa!" Momyn Rahama tayi maganar.
" A'a kibari sakonshi takai mishi ai anjima ba'a haduba" murmushin dole Momy tayi, cike da tausaya ma 'yar nata dan ta fahimci 'yar uwarta shakuwa take kallon abun gaba daya bata fahimci ya wuce nan ba.
Ramzia kallon momynta tayi, inda tama ta alamu da taje din, simi-simi Ramzia ta tashi ta nufi hanyar kitchen din.
" uhm bari na wanko hannu kan nafara taba Kayan dadin da zainab tayi" murmushin Jin dadi zainab tayi.
" Aikuwa saima kinci Momy hmm ai kaf duk nafisu iya snack" dariya Ammi ta sheke dashi.
" tab a ina lallai kindai fi khairiyya Ko?" Ammi tafada cikin zolaya ganin gaba daya hankalin khairiyya nakan waya, Aikuwa da sauri ta taso masu.
" Haba Ammi! Yanzu da yarinyar nan kike hadani akan batun girki, ae saiki sa ta rainani Walh" gwalo zainab tamata ta gudu tabarsu nan.
" Ammi have seeing what you have coursed?!" Murmushi Ammi tayi inda suka cigaba da hirar su lokacin da sauran bakin suke shigowa yaran kishiyarta jin dawowar Rayhan.
Ramzia tsayawa tayi jikin sink din tana tunanin yadda zata mika mishi abincin batare data ganshi ba.
" Rahama!"
Momy takira sunanta da sauri ta gyara tsayuwar ta, rufe kofar kitchen din tayi Wanda hakan ya tabbatar da tana son suyi sirri. Gaban tane taji yana mugun faduwa sosai.
" Rahama! Magana nake son fada miki kafin wani yazo dan haka kibude kunnuwanki dakyau kiji ni". Nodding kanta Ramzia tayi alamun tana saurararta.
" Amminku ta zo mun da wani zancen sai dai a yanzu bazan iya fada miki duka yadda mukai ba amma inaso dan Allah in antamabayeki batun auren ki nustu kibada amsa mai ma'ana, Karki nuna rashin Jin dadinki sam game da mijinki kodan albarkacin twins duk da nasan akwai matsaloli kici gaba da hakuri kinji!."
Shiru Ramzia tayi tare da runtse idannunta ta dago su kan mahaifiyarta " Insha Allahu Momy!".
" yauwa Allah ya miki albarka."
" Ameen."
Murda kan pampon tayi " yi maza kihada kikai mishi mana!" Momy tafada lokacin da take wanke hannu tana gama wa tafice.
Cikin kankanin lokaci Ramzia ta hada tray din ta wuce part dinsu dashi inda dakin shi dana Rasheed yake a gidan, ta kusa kaiwa kofar suka hadu da aunty Faty wacce take fitowa daga dakin, harararta tayi ta wuce batare da tanka mata ba hakan yasa Ramzia tadan ji saikin damuwar ta.
Tsayawa tayi bakin kofar jin yadd kirjinta ke mugun bugawa tare runtse idannunta gaba daya.
Rayhan dake zaune bakin gadon shi jin motsi yasa yayi shiru yana jiran yaji anmurda jin shirun yayi yawa yasa a hankali ya furta " Rahama!".
Dasauri ya tashi ya nufi kofar dai-dai lokacin da takai hannunta kan handle din kusan a tare suka murda saura kadan tayi kasa gun shigowa dakyar yayi nasarar tallafota sai dai baiyi nasarar, Hana tray din hannunta faduwa ba Wanda take kokari karsu fadi.
Jinta a jikinsa yasa tayi saurin kallonshi suka hada ido, wani irin abune ya ziyarce ta da sauri ta runtse idannunta, murmushi yayi me sauti wanda ke Kara ruruta mata wata irin wuta a zuciya ya dagota da sauri tashiga dai-daita kanta.
" I am ver...."
" sorry!."
Tafada da sauri lokacinda tayi kasa dan tattare Kayan da zube a kasa wanda any sa'a saboda flask ne basu zube ba Kuma carpet ya hana su plates din fashewa.
Nodding kansa yayi ganin yadda duk tabi ta rude tana dauka hannunta na rawa haka jikinta, duk abunda ta dauka sai ya fadi. Sunkuyawa yayi a hankali ya dau daya daga cikin plate din ya jawo hannunta yasa mata, kallonshi tayi suka hada ido, saikuma tayi sauri ta tashi ta juya mishi baya.
Runtse idannunta tayi saboda yadda take ji, cikin sauri tayi kokarin daga kafa dan barin dakin.
" Rahama!."
Muryarsa ta sauka cikin dodon kunnenta wanda yasa ta Kara daskarewa agun, tare da Kara runtse idannunta.
" why are you doing this to us?."
Yafada yana kallon bayanta sam yarasa meyasa? Meye damuwar ta?. A hankali ya karasa gabanta.
" bude idannunki!" Yafada da dan karfi hakan yasa tayi saurin bude idannunta a kanshi, dan tasan hali yana iyayin komai a yadda yayi sounding.
Cute smile dinshi ya mata wanda yasa tayi saurin lumshe idannunta Kamar tana mafarki.
" you are still in love with me ko?."
Gabanta ne ya fadi jin furucinsa da sauri tadan yi taku ta karka ta yadda bata kallonshi.
" No I am not!"
" then why are you like this?" Murmushi tayi wanda hausawa kankira da yafi kuka ciwo.
" kawai!"
Sa hannunsa yayi yana kokarin juyo da ita ta ture shi tare " karka manta ni matsayin matar wa nake gunka koda ina kanwarka ada!".
Sosai kalamanta suka daki zuciyar sa har saida ya manne da jikin kofar ya runtse idannunshi.
Itama ji tayi gaba daya zuciyarta namata zafi saboda sam zuciyarta taki yarda da furucin nata, runtse idannunta tayi ji kamar ta bude taciro zuciyarta Ko zata huta. Shirune ya ratsa dakin na wasu seconds.
" Rahama!"
Yakara kiran sunanta a kasalance saboda wutar dake ruruwa a zuciyarsa.
" Ki kalla idona kice bakya sona, hakane kadai zai tabbatar da bakyayi".
Shiru tayi saikuma ta juyo tafara kokarin bude kofar da yake jiki " na riga nafada maka tun 5yrs ago remember? And you also accept and left then why do you want to bring it up Rayhan?!" Takara she kamar zatai kuka.
" saboda inason tabbatar da hakan!"
Matsawa tayi da baya tana kallonshi " Rayhan wake up! Ka tausaya mun ka Kuma tausaya ma kanka a yanzu ba wata ALAKA tsakanina dakai data wuce ta kai dan uwana ne na jini Kuma karar wanka dan uwanka."
Murmushi yayi tare da sauke wani irin huci " ba maganar ALAKARMU na baya nake miki magana ba inaso kawai kikara tabbatar mun you are happy with him or not, duk da last 5yrs Ammi tabaki zabi na in baki farin ciki a rabaku in baki manta ba munyi dake you will choose to leave him dan muyi aure we love each other more than anything, Amma to my surprise you choose to stay with him meyasa?!" Yakara sa maganar da karfi, da sauri ta dago suka hada ido.
" what is forcing you? Waya saki dole bayan kinsan baya sonki kema baki sonshi inaso nasan abunda kika boyemun last 5yrs din nan!." Runtse idannunta tayi saboda sam bata jin zata iya bashi amsa.
Knocking din d akayi a kofar yasa yayi saurin shigewa toilet ita Kuma tashiga kokarin saita kanta, Khairiyyace ta shigo hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya.
" uhm! Act of guilt!."
" me kenan how?"
Murmurshi Khairiyya tayi " bro come out is just me!" Takara she tana dariya.
" kyaji dashi" Ramzia tafada lokacin data fara kwasar Kayan dake kasa wanda ya zuba, da sauri-sauri take kwasa jikinta na rawa.
Nodding head dinta khairiyya tayi ta sunkuya kije Hindatu tazo tana falo zan kwas...". Bata karasa saurarata ba tayi sauri ta fita daga dakin, binta da kallo khairiyya tayi.
Fitowa Rayhan yayi " yaushe kika karaso?"
Ya tambayeta murmushi ta mishi " Dama yaushe zaka sani tunda ka gudu kabar mu a kasar kana can kana hutawarka."
Murmushi yayi " still the same Allah ya shirya ki."
Dariya ta mishi " but bro hope kasan yau Ammi tace zata kuma magana kan zaman Bro da Rahama!."
Girgiza mata kai yayi cike da mamaki " kamarya what is happening?!."
" hmm bro nothing has change walh sai yayi spending month baizo ba idan yazo ma baya iya week tare dasu kaga dole ayi magana."
Mtsw yaja dogon tsaki.
" but is not his fault but Rahama I can recall antaba haka she still choose to be with him Ko so let her deal with it!".
Kallonsa tayi cike da mamakin kalamansa na I don't care.
" do you really meant it?!"
" yes of course mana!."
Tashi tayi rike da tray din har ta kai kofa ta juyo ta kalleshi kansa sunkuye kallo daya zaka mishi kasan yana da damuwa.
" I think kana da dama haryanzu kai da ita amma inkukai wasa akwai regret babba, I don't see why zaku cigaba da boye halin da kuke ciki tunda Allah yabamu uwa me fahimta na tabbatar Ko yau tasan kana son Ramzia walh saita hadaku". Tana kaiwa nan yafita tabarshi cike da tunanin zantukan ta.
" please kikiramun Aaina da Aleena!" Yafada da karfi dan taji, duk dan ya nuna baya cikin damuwa murmushi kawai tayi.
Haka kurum yake masifar son yaran a rayuwarsa cikin yaran 'yan uwansa ba wadanda suka kwanta mishi kamarsu, Ko yaushe yana son kasancewa dasu Wanda yana alakanta hakan da sonda yake ma mahaifiyarsu.
" Ah! Ah! Ashe kina hanya harna cire rai". Ramzia Tafada lokacin da sukai hugging juna ita da hindatu.
" where is he?"
Hindatu ta tambaya a kunnenta a hankali yadda mutanen gidan bazasu jiba, murmushi Rahama tayi ta sake ta batare da ta bata amsa ba.
" Nazo gida umma Ke fada mun Rayhan yadawo nace bari na shigo Ina zuwa a kace kina nan". Nan ta zauna falon banda hira ba abunda ake ga hayaniyar yara Ko ina.
Kallon Ramzia Hindatu tayi " kizo muje ku gaisa da umma tace ta jima bata ganki ba".
" Amm....."
" tashi kuje mana Rahama ku gaida mun hajiyan!" Sam basu San tana jinsu ba sunzata hankalinta nakan yar uwarta.
Tashi sukai Rahama ta karba hijab din zainab, Aunty Faty banda harara ba abunda take mata Amma sauran yan uwansu da wadanda suke uba daya kowa da fara'a yake kulata.
Suna fita kuwa a filin gidan suka tadda su Aaina dake wasa da yara 'yan uwansu cike da jin dadi, suna ganin ta suka yo gunta.
" Momy zanbiki" nan sauran yaran ma suka yo kanta da wayo da dabara ta samu ta musu wayo suka fito.
" so now what?"
" kamarya kenan hindatu?" Murmushi hindatu tayi.
" he is back!."
Tabe fuska Rahama tayi " to saime inya dawo?"
" Hmm! Baki tsoron yasan gaskiyar abunda kike boyewa?."
Da sauri Ramzia ta kalleta " ba yadda za'ayi ya sani, bayan Ke a duniya bana jin akwai wanda yasani kema inaso Karki Kara tada mun zancen" shiru hindatu tayi.
" you can't hide the truth from him forever Rahama, but yanzu ya zakiyi?" Shiru Ramzia tayi tare da sauke ajiyar zuciya.
" shiyasa nazaba yin nesa dashi ba wata MUMMUNAR ALAKA da zata Kara shiga tsakanina dashi Insha Allahu."
" Allah yasa kam but!".
Tayi shiru kallonta Ramzia tayi " but me? Kinsan you can tell me anything Ko?".
"Uhm tunda kince" Tafada tana murmushi.
" you need Haydar to get ride up Rayh....".
" No bazan iya aikata hakan ba Insha Allahu I won't commit myself into such Forbidden relations Insha Allahu!."
" hope so!"
Hindatu tafada tare da harararta tana kitsa abunda zatai mata a nan gaba kan wannan hidden secret din, wanda tajima tana jiran samun dama gun Rayhan kodan ta rushe Auren Rasheed da Rahama, and tana ganin wannan shine damar ta na rushe komai tunda yadawo angama!.
Tafada a ranta. Kai tsaye gidansu hindatu dake gaba da gidan Ammi wanda bai wuce gida biyar tsakani ba suka shiga.
Cike da ladabi Ramzia tagaida ummansu Rahama wacce banda sa musu albarka ba abunda take, kana kallonta zaka fahimci dattijuwar Arziki ce sosai sam batai kamada irin iyayen nan ba, sosai ta kwanta ran Ramzia shiyasa musamman take mata sakon kaya da abubuwa kota kawo mata duk sanda ta sama lokaci.
Shiyasa hajiya Umma Ke matukar sonta kamar Hindatun ta ta dauketa Kuma dalilin Ramzia Ammi ta biya mata hajji kusan sau biyu, kusan gidajen da mutanen ciki suna matukar mutunci da zumunci da juna haryau ba wanda yasan halin da hindatu Ke ciki especially ana ganin amuntarsu da Ramzia wacce kowa ya shaida dabi'unta.
Mu hadu a Next Page........ Don't forget to comment, share and also votes.