The Twins part...
by @mimsqueen
8:34pm.....
"Uncle! Dady na kiranka a falo." Babban da Aunty Faty wanda zakai 15yrs Sudais yafada mishi, yana fada ya juya yabarshi gun.
Gaban Rayhan ne ya fadi jin mahaifinsu na neman shi tabbas yasan dama yana da laifuka sosai daya aikata mishi, ba abunda yafi damun shi irin facing din mahaifinsa a yanzu.
"Uncle!." Aleena tafada tana girgiza shi, kallonta yayi tare da shafa kumatunta.
" what do you want my beautiful?".
" Aleena tell him!."
Tabe face dinta Aleena tayi suka kalla juna ita da sister dinta "meya faru tell me".
" uhm nasan kaima zaka ce kana busy Ko like Dady?."? Shiru yayi yana nazarin yaran.
" No I can't be busy when my angels need me!"
" you see Aleena uncle ma yafi Dady son mu" ta karasa maganar a shagwabe kamar zatai mishi kuka.
Wani irin tausayi yaran suka bashi ya rungumo su duka, he can't believe cewan Rasheed will make this children feel this kamar marayu.
" Nima" ihsan wacce take sa'arsu tafada tare da rungumuwa a jikinsu duka. Wani irin emotion yake ji tare dasu na daban. "I won't let you feel this anymore Insha Allahu".
Yafada batare da yasan ya furta ba Aunty Faty ce ta leko ganin su yasa taji wani irin tausayinsu ya kamata, tayi sauri ta dake " kazo kai kadai ake jira a falon!."
Da sauri ya sakesu " inazuwa twins dina da ihsan dina ku kalla cartoons dinku but no fighting ok!."
" yes uncle!."
Suka fada suna nodding kansu da sauri ya fice yana ji Aaina nakara zancen yadda dadynsu bai sonsu, abun sosai ya mishi badadi ace har yara kanana suna fama da wannan dabi'ar tasa, bayajin zai iya barin Rasheed ya bata rayuwarsu duka.
Shiru ya tarar da falon duka 'yan uwansa ne da suke ciki daya haka ya tabbatar mishi saura suntafi, hakan yasa ya sauke ajiye zuciya a hankali ya karasa falon ya nema guri ya zauna kansa kasa.
" Inawuni Dady"
Murmushi Dadyn nasu yayi me sauti wanda har saida Rayhan din ya dago saboda mamaki kasancewarsa mai laifi.
" Lafiya kalau Abbana, ka gama fushin kadawo? Duk da bansan wanda yama laifi kaki koda lekomu bane har shekara biyar!."yakara sa cike da fara'a ba alamun bacin rai sam tattare dashi.
" Kayi hakuri dan Allah da...."
" No! Sam bana fushi dakai ai kana kira kana gaisheni nadai San bahaka nan bane amma bazan tambayeka ba inba kai ka fadamun ba, dan haka ya wuce". Sosai Rayhan yaji dadin kalamansa har sauran 'yan uwan nasa sunji dadi.
" Zancen tattauna wa kan batun Rahama da Rasheed, inaga Amina abar wannan zancen tunda ba wanda yakawo karar dan uwansa, Amma tabbas zankirashi namai magana Kuma inya dawo zamu zauna dashi danni kaina banyarda da tsarin iyalinsu shida Umar ba bashi kadai bane dukansu zan hada." Shiru yayi yana nazari.
" Amma a yanzu inaga zaman Rahama gida sai driver da maigadi bazai yuba tunda gidan da empty part why not shi Rayhan tunda yadawo ya dunga zuwa koda bazai koma ba sometimes suna ganin shi ae zaifi sauki especially Rahama dake makaranta ga yara." Dip falon yayi Ramzia kirjinta ne Ke bugawa kamar zai fito saboda tsoro.
Bangaren Rayhan shi kansa bayajin zai iya zama gida guda da ita a yanzu.
Inka leka bangaren Aunty Faty da Momy wacce bata wuce ba, da khairiyya dukansu basu support saboda ba yadda za'ayi ayi hakan duk da basu ganin zargin komai amma kodan zafin rashin junansu.
" Hakan ma yana da kyau kwarai Alhaji, kadai rigani furtawane amma zamanta hakan ae ba tsari duk da shima muna fata nan kusa amma kafin nan ya dunga kula dasu Ko nima hankalina zai kwanta." Dukansu ba Wanda yaso furucin Ammi.
" yes is good hakan Amina dan yanzu haka akwai gidana babba da nakeso shi Abdul-Rasheed da Rayhan su zauna tare da iyalansu, gidan katone part parts ba lallai ma su dunga haduwa ba saboda gate biyune kinga atleast sunajin motsin juna." Kowa yaji dadin wannan saboda zumunci amma komawar ne damuwar a yanzu ta Rayhan.
Ba wanda ya iya cewa komai dole kowa ya goyi bayan shawarar Dady da Ammi kodan zama da take da driver a gida suna kaita Ko'ina Ammi na ganin hakan bai dace ba gwanda inda dan uwansa kusa wasu abun ya musu kobai koma duka din ba.
Koda kowa zai tafi Ammi ta dage Rayhan yamaida su gida duk da tana ganin KB. Aunty Faty ba yadda batai kan Ammi tabar Rayhan ya huta ba amma sam taki, shima badan ya soba harda zasu sauke Momy ya yarda.
Tuni kowa ya hada iyalansa a mota suka dau hanya.
" uncle zaka zo muje park?" Aaina ta tambaya.
" yes my angel"
" will you also take us to school?."
Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba " yara sai surutu zai kaiku mana!."
" yessss! Dama munji su ya Sudais suna cewa wai Uncle zai dawo gidanmu." Aleena tafada cike da murna da jin dadi.
" dAgaske ne Uncle?" Yaran suka Kuma tambayarsa.
" Aleena shut up! Kundame mutane da surutu!" Tafada cikin bacin rai kamar zata dakesu.
Suna isa gidansu Momy tace tafito suyi magana, tasan me Momy keson fada mata sam bata son ji amma bayadda zatai.
" Look Rahama! Kinsan mezan fada miki koda Rayhan yadawo banso Ki shiga harkarshi iya ka cinki dashi abinci ina kwana please Karki bani kunya". Nan Momy tajima tana mata fada nasihu wanda agun Rahama suke Kamar bugun kusa take mata a kirjinta saboda zafin su.
" Uncle please come back to our house please! Please!."
Yaran suka cigaba da pleading dinshi murmushi ya musu na karfin hali " alright zandawo Insha Allahu"
" promise!"
" yes!" Tafada a hankali.
" Aleena zaa daina mana dariya muma muna da uncle yanzu, ranar Khadijah har dariya ta mana wai driver ke kaimu school basu taba ganin dadynmu Ko uncles ba, bamai kai mu park sai Momy kawai."
" rabu da ita Aaina muma ga uncle dinmu."
Sosai yaran suka bashi tausayi duka 10yrs but sunada wayo sosai harsun gano rashin kula da mahaifinsu ke musu, koba komai kodansu zai daure ya jure ya nesanta kansa da Rahama ya kula dasu, ta hanyar zama kamar Uba gunsu. Yayi alkawarin kiran Rasheed sosai kan zancen su dan bazai yarda ya bata rayuwar su duka kan Clark ba in yazama dole sai ya rayu da ita ya hada su harda Zarah ayi duk wacce za'ayi amma duk ya tsaida musu rayuwa gashi ga Rahama ga twins shi kansa Rasheed din no one is happy dole yasan yadda zasuyi.
Shigowarta motar ne ya katse mishi dogon tunanin da yake, twins Kuma nata faman surutun su harda fada suna argument tana shiga sukai tsit.
Tunda suka dau hanya ba Wanda ya tanka kowa, har suka je gida tsit tun tana jin zantukan yaran a hankali harta daina. Horn yayi gate man din yazo ya bude shiga yayi ciki yayi parking.
" come on girls, le...."
Tana waigawa taga sunyi bacci, sauka tayi ganin haka shima ya fito dan taimaka mata " Aleena! Aai....".
" shhhhh!."
Yamata tare da mata alamun karta tashesu, gate man dinne ya karaso zai gaishesa yamai alamun yayi shiru a hankali ya dau Aleena ya daura a kafada. Kallonsa tayi suka hada ido maida handbag dinta tayi gefe tadau Aaina itama a hankali tuni ya riga yakai bakin kofar amma sai yaja ya tsaya yana jiranta.
A hankali ta karasa bakin kofar ta bude tashiga yabi bayanta bata tsaya Ko inaba sai a dakinsu inda tasa Aaina kan bed dinta a hankali suna kallon juna ba abunda ke ran Ramzia sai yadda inda Rasheed ne ba ruwan shi sai dai ita ta tashesu da kansu su shigo da kafafunsu baruwansa.
Yana ajiye ta yana kokarin tashi Aleena ta riko hannun shi tare da rungumeshi " please Dady karka barni."
Tafada a hankali tare da Kara gyara kwanciya, tsura mata ido yayi tare da danyin murmushinsa wanda ke Kara bayyana kyawunsa, a hankali yakai hannunsa kanta yana shafawa inda yake matukar tausayin yaran a ransa yana ji kamar karya tafi yabar su amma ba hali wani irin abune da baitaba jiba yakeji.
Dagowa yayi suka hada ido, dan tun dazu shi take kallo cike da tausaya musu da kanta. Da sauri ta kauda kanta daga kallonshi ta nufi hanyar fita yana binta da ido har tabar dakin.
Kokarin cire hannunsa yayi jikin na Aleena amma sake kokarin rungume hannun take, hango dan teddy dinta yayi da dabara ya cire hannunsa ya sa mata teddy din yatashi, har yakai kofa zai switching musu light yadawo kamar ya tuna wani abu nan bisu daya bayan daya ya musu addu'a, wani iri yake ji kan yaran tare da zafi wanda yarasa kona meye.
Duk da yana da kusanci sosai da Zarah baitaba Jin hakan kanta ba, nodding kansa yayi lokacin da zuciyarsa Ke basa answer " dole kaso su ciwon su yazama naka kodan Rahama."
Murmushi yayi medan sauti wanda ya karashe da wani irin huci wanda zaka fahimci baya cikin farin ciki sam a wannan lokacin, harya kai kofa yakara waigowa yana kallon yaran, zuciyar sa na kwadaita masa abubuwa da dama " inama da sun kasan ce nawa nida Rahama da ba abunda zaku nema a duniya ku rasa, babu abunda ba zanyi kanku ba amma a yanzu ma zanyi iya kokarina kanku."
Yafada a ransa yana murmushi yatashi yana kallonsu.
Ramzia dake makale tana jin wani irin abu a wannan lokacin itama kusan abunda zuciyar ta ke kwadaita mata bawani abune mai banbanci da nasa ba, wasu irin zafafan hawaye ne taji a kumatunta daya nabin daya, jin motsin yasa tayi sauri tabar gun.
Fitowa yayi ya hango ta yadda take sauri-sauri, bai bi ta kanta ba saboda ya tabbatar ya tunkareta bazaiyi dadi ba, da sauri ya sauka yafita yafada motar yamata key, gate man na budewa yayi ma motar wani irin ja aguje yabar harabar gidan.
Tunda taji karar yadda yama motar key tayi sauri ta nufi downstairs dan yima sa magana ta tabbatar tukin ganganci zaiyi amma ina tana bude falon yana ficewa gidan, jikinta na bari tashiga neman inda tasa wayarta nan ta tuna a motar tabarshi, gabanta ne ya cigaba da matukar faduwa komawa tayi dakin ta ta nade kamar wata marainiya tarasa ya zatai da masifar da suke ciki a yanzu.
****
" wai meyasa kake damun kanka ne da zancen Ramzia Ko yaushe?!". Hindatu tafada a fusace kamar tana ganin sa.
" na riga nafada maka Ramzia zaka same ta nan bada jimawa ba kodan gogan da yadawo yanzu, cikin ruwan sanyi zan cigaba da lallaba maka ita dan ina da target". Shiru tayi da alama tana saurarar abunda yake fada mata.
" oh my God Haydar dadina dakai baka yarda da magana ta tunda nace zaka sameta ae angama magana bai kamata ace haryanzu kana wadan nan zantukan ba cool down mana haba!".
Jin motsin mijin ta yasa tayi kasa-kasa da murya " kaga malam gobe a cikin makaranta zamu karasa tattaunawa". Tana dadin haka ta kashe wayar.
" bari namata ma text kafin wannan nanataccen yazo yatasani gaba, kamar wani mayun wacin zaki na dai san yanzu takoma gida".
Nan ta shiga compose message ta lalubo no din Ramzia tashiga rubuta message, tana gamawa kuwa taji sa jikinta Yau kam itama tana cikin bukata dan yau batai harka ba haka tasake jiki suka cigaba da sha'aninsu gogan kuwa ji yake kamar Yau sallah dan yayi watanni rabonsa da samun wannan damar gunta.