ALAKARMU (MUMMUNAR ALAKA)

Heart Touching...

by @mimsqueen



" Momy wai ya kuka kare kan batun Ramzia ne?" Kanwar Ramzia Islam tafada tana kallon momynsu dake kishingide kan taburmar, tana fifita saboda zafi daya korota tsakar gida ba wuta.


Tabe baki Momy tayi " uhm! Kedai bari Islam saura kadan yaya yau ta tado mana zaune tsaye Allah yataimaka dai Alhaji ya kau da zancen.


"Ni Walh haryanzu ya Ramzia haushi take bani fa!" Tafada tare da jan dan gutun tsaki.


" kul Islam karna karajin wannan zancen ba kinki Walh, koma me tayi 'yar uwarkice banaso".


" Amma Momy ita sai yaushe zatai hankaline dan Allah? Duba da kiga tarin dukiyar da ya Rasheed ya tara amma ita duk ta tara hankalinta kan ya Rayhan wanda haryanzu kwakwaran aiki bashi dashi, sai dai komai a mishi Kuma ae ya Rasheed yafi shi hankali" kallonta momynsu tayi tare tabe baki.


" uhm nidai nariga nafada mata ta kama mijin ta dan wannan yaron ba lallai ya iya rike ta ba koda iyayen sun yarda anmaida auren kanshi".


"Ahto ni bama wannan ba Momy itafa ko kwaso kudi ba tayi amata abu kiduba ya habiba har gida take dashi abunta Kuma tare akai aurensu amma ita ya Ramzia hmm" takarashe tana girgiza kanta cike da takaici.


" hmm Rahama ai kaf cikin ku Walh ita daban ce ba wayau, wannan yaushe ma take zuwa gidan inta zo mintuna nawa take ta tafi, kullum ita gata nan ne Allah dai ya ganar da ita".


Tsaki Islam taja " Kuma fa kawar ta Hindatu ba haka take ba walh!" Murmushi Momy tayi.


" tabdi kya hada Hindatu da Ramzia banda abunki itafa wannan Rahama ajebo ce, ita da yaran Ammi basu da banbanci basu San tanadi da rayuwa ba, tunda komai gani suke su samu koni da yaya bakiga muna da banbanci ba".


Dariya Islam ta sheke dashi " kai Momy! Ammi baiwar Allah da kin motsa zata turo Ki amshe sai business dinki kike banajin tana da abubuwan da kika mallaka a yanzu".dariya momyn nasu tayi.


" uhm! Baku bar Ramzia ba bare Ammi, kedai Islam baki da kunya walh". Tahir dake saurarensu tun tuni yana matsa waya yafada yana kallonta.


" Momy kinjishi yo meye nafada badai-daiba!".


" Allah yakawo ranar da itama ya Ramziar zata san halin ku tunda a gabanta kuyita damuwa da ita da Ammi da kunga bata sa.....".


Jifar da Momy ta mishi da takalmi yasa ya tashi da gudu " ai gaskiya nafada meye Ammi bata mana ita da ya Rasheed da ya Ramzia amma ku wannan gaskiya ba yi bane" Yafada lokacin daya fice.


" Au ni kake fada ma irin wannan maganar Tahir?". Momy tafada yana jinta Sarai yafi ce abunsa.


" kinji mun da Ko Allah yakyauta". Tafada suka cigaba d hirar su daga nan har labarin makwaftansu suka dasa wannan na daga cikin halayen Momy da Ramzia sam bata sani ba tunda tun tana shekara uku tabar gidan intaje Kuma Momy da 'yan uwan banda kulawa ba abunda suke nuna mata har ta koma bata Ko kwana wani sa'in hakan yasa bata wani zauna dasu ta sansu ba.


1week later....

Falon banda hayaniyar su Aleena dake kallon cartoon baka jin komai, kamar su kadai ne a falon amma abunda zai baka mamaki tana zaune falon.


Sai dai gaba daya tayi zurfi cikin tunanin rashin ganin Rayhan tun randa yadawo dasu daga gidan Ammi bata Kara ganin shi ba sai jakarta daya bayar aka kawo mata.


" Aunty! Aunty! Ruwan ya tafasa" yar yarinyar da bazata wuce 13yrs ba tafada da alama mai aiki ta ce Kuma sabuwace.


" Aunty!"


" shhhhhh! Kina ta mana ihu, bari namata magana". Aleena tafada lokacin data ja wayar Ramzia dake cikin hannunta dasauri Ramzia ta fusge.


" Ke! Meye haka!" Tafada da karfi Dariya Aleena take inda take taba Aaina.


" Kingani dama nace miki in kikai ma Momy magana bata jiba to kidau wayarta". Nan suka cigaba da dariya.


" Ni sa'ar wasanku ce!"


Tafada cikin bacin rai inda tayi kansu, nan take jikinsu yafara bari aikuwa nan tashiga bugunsu da wayar charger dinta nan gidan ya dauka banda kukansu ba abunda kakeji.


" dan Allah Momy ba zamu Kara ba please Momy".


" Rahama!"


Taji saukar muryar a kunnenta kamar dirar mashi cak ta tsaya dan ita kanta mai aikin nata tuni ta gudu kitchen saboda tsoro, da gudu yaran suka nufi bayan sa.


" please uncle kataimake mu kace mata bazamu karaba".


Runtse idannunta tayi cikin wani sabon bacin rai Ko kallonshi batai ba ta nufi inda suke tsaye bayansa ta daga wayar caf yarike hannunta.


" Don't you dare!" Yafada cikin tsawa batare da ta saurareshi ba cikin taurin kai irin nata tafara kokarin fusgar hannun nata.


Gam ya rike hannun tayi-tayi Jin bazata iyaba yasa tafara mai magana cikin bacin rai " leave my hand!".


Kin saki yayi idannunsa jazur saboda bacin rai " nace ka sakar mun hannuna malam!".


Wannan karon tafada tana kallon jajayen idannunshi wanda ke kallon nata " I will amma baki isa Ki sake taba suba!".


Yana kaiwa nan ya saki hannun nata bata bita kansu ba ta haye upstairs abunta cike da bacin ran, yadda yayi watsi da lamarinta harna sati yana gari bako waiwaye.


Ganin ta haura yasa ya rage tsayinsa zuwa gun su Aleena.


" why did you hurt your mother?!"


Nodding head dinta Aaina tayi tana shafa inda bulalar Ke cigaba da mata zafi.


" is not me is Aleena" tafada tana nuna yar uwarta dake fama da inda yake mata zafi itama.


" but kema kinyi dariya ko"


Nan suka shiga argument " ya isa! But let me tell you something Ko kunsan duk Wanda yabata ma momynsa rai meyake faruwa dashi?"


Kallonsa sukai cike da damuwa dakyar Aaina ta daga bakinta " Malama tace Allah yana fushi da duk Wanda maman sa Ke fushi dashi". Murmushi yayi tare da jan kumatunsu.


" wow malamarku is good gaskiya and she is correct kuna so Allah ya dunga fushi daku?!" Da sauri suka shiga girgiza mishi kai.


" No uncle!"


" to kudaina ma momynku laifi kunji Kudaina bata mata rai kunji, inma kunyi laifi kudunga bata hakuri kunji". Nan ma daga kai sukai alamun sunji.


" now go and continue watching your cartoons zanje naba momynku hakuri daga nan na kawo ointment ashafa agun owk and don't forget ku bata hakuri Kuma inta sauko!" Yafada lokacin daya dau hanyar upstairs din su Kuma suka koma suna share fuskokinsu.


Zaune take bakin gadon tayi kuka sosai kamar ita aka daka tunda take bata taba dukan yaran ta ba sai Yau sai dai ta musu nasiha, sai gashi yau ta musu mugun dukan da Ko ita ba taji Momy Ko Ammi sun taba mata shi.


A hankali ya murda kofar bedroom din inda yayi sa'ar samun kofar a bude da sauri tashiga share hawayenta ganinshi, maida kofar yayi ya datse tare da sa key abunda ya matukar tsorata ta tayi saurin tashi.


Jinginuwa yayi bakin kofar tare da harde hannayensa ya tsura mata idannunsa da haryanzu suke ja, ba alamun fara'a Ko walwala tare dashi tabbas ba karamun abu ke sashi hakan ba a tsorace take dashi gaba daya har jikinta yana wani irin kadawa.


" me....me....meka zo mun daki!" Tafada dakyar muryarta na rawa.


"So this are all what you are doing behind my back and also behind Rasheed backs!" Yakara she maganar cikin dan daga murya.


Cike da rashin gaskiya ta kalleshi " No! Yau ne kawai dan sun ba....".


" shut up!" Yafada lokacin daya nufe inda take tsaye gadan gadan tafara ja da baya har saida ta karasa jikin mirror din wanda hakan yasa wasu daga Kayan dake kai na make up suka samu damar kaiwa kasa, da sauri ta runtse idannunta da hawaye ke tsiyaya kamar ankunna Pampo.


Kallon kyakywar fuskar nata yayi a hankali yasa hannu yashiga shafawa inda lokaci guda taji ya matse mata baki da karfi dan Kara taso yi cikin sauri ya Kara zaro mata idannunsa " shhhhh".


Cikin sauri ta hadiye inda tashiga kokarin kwacewa daga rikon saboda zafin da takeji.


Murmushi yayi me sauti yana kallon cikin idannunta " that's it! Wannan croodile tears din naki which you always shed whenever you need sympathy ko".


Saketa yayi tare da kama kansa ya koma bakin bed din ya zauna inda ya rike ta tasa hannu saboda haryanzu tana Jin zafi a gun sosai, a hankali ta daura idannunta kansa wani irin faduwa gabanta yayi tunda take dashi duk fushi sa bata taba ganin sa a wannan yanayin ba.


Nan wata zuciyar Ke bata answer kan " koya san sirrin da take boye masane? To a ina zaiji?" Ganin bata da amsa yasa takasa magana tana kallonshi tunda yasa hannayensa akai idannunsa rufe suke sai wasu hawaye dake bin kuncinsa.


A hankali ta nufi inda yake zaune " Mr.Ray plea...."


" don't touch me Rahama! And don't call me that ever!".


A firgice tadan yi baya hankalinta a yanzu yakai kololuwar tashi Kara matsawa tayi gabanshi ta kai gwiwowinta kasa " dan Allah dan Annabi kafada mun laifin dana maka amma karka mun irin wannan horawar, na tabbatar wannan ba Mr.Ray dina bane wannan bana ganin So da Kaunata sam cikin idannunsa kayi ma Allah ka sanar dani indan yaran nan ne Ina neman gafararka please Rayhan".


Dariya ya sheke dashi yatashi wanda ya matukar bata mamaki "So? Kauna?! Duk a ina kika sansu na tabbatar da kin sansu ba Zaki mun wannan furucinba dan a dalilin Ki bana jin zan Kara yarda da wadan nan kalmomin!". Yafada cikin matukar zafin rai da fushi yayinda still hawayensa ke zuba.


" Rahamatu! Inbanyi wasa ba sonki zai zama ajalina!".


Da sauri a ta rungumeshi ta baya "please no! Dan Allah kadaina kiran wadan nan muna nan kalaman". Kokarin cire hannunta yake daga jikinsa amma sai kara rirrike shi take, sam tamanta komai burinta a yanzu bai wuce taga Mr.Ray dinta normal yadda yake ba.


" Kin kashe mai wannan sunan da hannun ki Kumanta kintaba sanina Kuma Kumanta kintaba ALAKA dani".


Nan Ramzia takara shiga wani Karin rudi " Walh bazan iya rayuwa ba idan kabarni Rayhan, please karka mun haka karka yi saurin datse ALAKARMU dan Allah!".


Murmushi yayi Wanda yafi kuka ciwo lokacin daya finciketa a jikinsa ya tura kan bed din " keda bakinki kin furta bamu da ALAKA dan haka kimanta da duka wata ALAKARMU!". Wani irin kuka Ramzia take me matukar cin zuciya share hawayen sa ya shiga yi.


Harya kai kofa ya juyo yana kallonta saboda ku kan da take me sauti ne sosai girgiza kai yayi " Rahama kinci Amanar So da Kauna da duk wani abu daya shafesu daga ranar da kika gayyaci HAYDAR cikin ALAKARMU kika tarwatsa komai!". Yana kaiwa nan yaja kofar yafita.


Cigaba tayi da juyi kan gadon tana wani irin kuka me matukar taba zuciya kamar wacce akaima mutuwa.


Yana sauka bai yarda su 'yan biyu sun san da fitarshi ba kai tsaye mota ya nufa saijin karar motarshi sukai, suna so su haura sama gunta amma suna tsoro haka suka cigaba da zaman su a falon suna kallonsu, abunka da yara kamar basu aka daka ba.


Sai da yayi nisa da gidan kafin yayi parking kamar karamun yaro haka ya sunkuyar dakai yana kuka yaci sa'a duhu yayi yana yi yana bugun starring wani irin kuka yake mecin zuciya.


" Rahama why? How could you? Meyasa zaki mun haka bayan na sakan-kance kin guji MUMMUNAR ALAKARMU saboda rashin tsabtarta da kyanta why?!". Nan yaci kukan sa ya Kara gaba.


A gida kuwa Ramzia takai tsawon 2hrs tana abu guda a hankali zancen shi na karshe yafara dawo mata. " A ina yasan Haydar?".


Wannan shine tambayar data kasa bama kanta answer gaba daya, duk tunanin ta bata gano komai ba kan kace me zazzabi ya rufeta sosai dakyar ta sauka gun yara inda tausayin junansu ya rufe su especially ganin yanayin jikin mahaifiyarsu.