The Desire...
by @mimsqueen
Slowly yayi kasa da kansa zuwa kyawawan lips dinta ya hadeshi da nata hakan yasa tayi saurin bude idannunta akanshi, dan a yanzu ta tabbatar ba mafarki bane Mr.Ray dinta ne da kansa a samanta.
Idannunsa rufe yake kokarin sarrafa bakin nata, ji dayayi a hakoran a hade ya tabbatar mishi da bata amsa gayyatar shiba, sake danna halcenshi yayi nan ma taki sai kokarin tashi data soma.
Dan hankadeshi tayi ta tashi ta juya mishi baya, idannunsa jawur da wata irin matsanancin bukatarta ya tashi ya nufeta a hankali zura hannayensa kan cikinta yayinda yake sa kansa cikin wuyanta.
Runtse idannunta tayi da karfi wannan karon saboda wani irin yarrrrr dataji ya ziyarceta, abunda tajima tana missing kenan ga kamshinsa dake Kara ratsata sosai.
Ganin hakan yabashi damar shigar da hannunsa cikin rigarta yayo sama yana kokarin taba Nonuwanta da sauri takai hannayenta duka biyu ta rike hannun nasa gam.
Dagowa yayi tare da runtse idannunsa yakara kokarin Kaiwa yakara jin karfin rikon data masa, tana matukar son Abunda yake so tajima tana so amma batajin zata sake yadda MUMMUNAR ALAKA tashiga tsakaninsu.
Sake matse idannunsa yayi tabbas ya fahimci me take nufi shikansa baya so Su cigaba da MUMMUNAR ALAKA kallonta yayi yayi murmushi me sauti wanda tana ji ta bude idannunta wanda suka Kai zuwa nasa ta cikin dressing mirror da suke facing.
Murmushi yake mata still dan lumshe idannunta tayi takara budewa dan kasa yayi dakansa saitin wuyanta, batasan lokacin datai mishi murmushi ba itama zuciyoyinsu ke wani irin bugu. " Tabbas dakai nadace!".
A zuciyarta ta furta batasan yafito fili ba nuna mata kansa yayi da ita yamata alamu da hannunsa, wanda yake nuna mata suna tare runtse idannunta tayi da sauri saboda wani abu dake fusgarta intana kallonshi.
" Baby bazan miki komai ba but let me have a little peace with you please" ya rada mata a kunne da sauri takara yin gaba tabarshi gun.
Cikin wani irin wahalallen yanayi da suke ciki ya koma kan gadon ya kwanta, tajima tsaye idannunta rufe zuciyarta da ruhinta gaba daya shi suke bukata a wannan lokacin.
A hankali takoma ta zauna bakin gadon murmushi yayi cikin wani irin yanayi ya dago zuwa zaune, ya mannata a jikinsa zazzafan hawayenta ne dake sauka kirjinsa saman rigarsa duminsu ya tabbatar masa da kuka take.
" I am sorry for leaving you all this while, please kiyafe mun baby". Yafad cikin cool voice dinshi.
" Koda yaushe tsawon shekarun nan kina rains ina matukar so naganki amma idan natuna abunda yafaru, da Rasheed sainaji na tsaneki na tasani kaina banson dawowa, I am very sorry baby". Yakara she cikin raunanniyar muryarsa wacce Ke rawa kamar karamun yaron da zaiyi kuka.
Kasa cigaba da jurewa tayi yana shirin magana tajuyo ta hade bakinsu gu guda cikin wani irin yanayi dukansu hawayene kan fuskarsu sunjima a haka, tuni kowannensu yamanta da wani zazzabi.
Sun dau lokaci sosai suna kissing din junansu yadda suke rungumar juna kamar zasu hadiye juna, jitake kamar taba shi kulata sosai anma wani abu na hanata shi kansa ji yake kamar yayi yaya amma inya tuna wani abun sai ya daure dakyar suka banbare junansu.
Ramzia kasa tayi daga kan gadon tana wani irin kuka tana matukar tausayin kanta dashi, Saboda haryanzu bata hango mafita kan abunda yake damunsu ba, ita duk tafi tausayin kanta ga Aure ga Kuma rashin kulawar miji Kuma ace tarasa wanda take so a fadin duniya sai brother dinshi uwa daya uba daya, jitake kamar ta kashe kanta ta huta a wannan wahalallen yanayin nata.
Shima Rayhan kukan da yake bai wuce kasancewarta mata gun dan uwansa ba uwa daya uba daya, ya rasa me zaiyi a duniya ya manta da ita, a dalilinta har kasar yabari tsawon shekaru amma haryanzu son yana nan kamar yanzu akafara.
Sun jima a hakan ba wanda iya rarrashin dan uwansa cikinsu daga karshe suka koma kallon juna kowa da abunda yake sakawa a ransa tsawon half hour yaga tayi bacci a jinginen da take shima Kuma baccin ke fusgarsa.
Sauka yayi ya dauke ta daura ta kan bed din yaja mata blanket ya dau pillow ya kashe mata light yaja kofa, falo ya koma inda yadauketa dazu yakara pillow din yakwanta agun, yadan jima kafin bacci ya daukeshi.
Ba wand ya farka cikinsu sai Assalatu ya farka yadaura Alwala har yayi sallah tana bacci inda ya zauna kan sallayar yacigaba da addu'oinsa.
Tashi tayi a dan tsorace ganinta akan gadon wayam taga ba alamunshi murmushi tayi, ta fada toilet tayi wanka da alawala kamar yadda ta saba, saida tayi sallah ta bude kofar tafito tunda ta isa stairs din ta hangoshi zaune gun sallah yana rike da carbi yana Azkar dinsa.
Murmushin Jin dadin ganin sa tayi, gabanta ne yayi saurin faduwa lokacin da zuciyarta tace mata " inama Rasheed ne yake haka!".
Wanda sam Rasheed baida Ibada duniya da neman kudi yasa a gaba Wanda hakan yake Kara matukar banbantasu.
Jin alamunta yasa yadaga kai murmushi yamata ya cigaba da abunda yake ita Kuma ta nufi dakinsu Aleena tun kafin takarasa take jin muryoyinsu da alama fada suke.
" Aleena is mine!".
" no is not!".
" Aleena!".
" Aaina!".
" Shut up! Kuma zance ma dady da Momy a daina saya mana abu iri daya inkin bata naki Ko kin batar saiki dau nawa ki kwace!". Dariya Aleena ta kyalkyale dashi.
" Whatever but bazan bayar ba din". Aleena tafada tana dan gudu.
" Aleena give it back!". Nan itama Aaina tabita inda tayi nasarar cafketa sai kokawa.
Ramzia dat bude kofar tsayawa tayi tana kallonsu batare da tace musu komai ba suma Kuma ba wanda yasan da shigowarta.
Dariyar da sukaji ne yasa dukansu suka waiga har Ramzia tsayawa sukai suna kallonshi Su duka, ganin yadda suke kallonsa yasa ya kallesu. " carry on guys" ya musu alamu da hannunsa.
" oh haka ma zakace? Kaga suna wannan shirmen kace sucigaba?!" Tafada tana kallonshi.
" yes mana! I just remember you and khairriya isn't this the way you guys always do?". Nan yaran suka sauko gunsa dan son jin labarin momynsu wacce Ke harararshi sosai.
" guys! guys! Come on Uniform first then Story on dinning ok". Yafada yana kallonsu.
" owk uncle". Kallonsu yayi cike da mamaki, suma kallon sa suke yadda yake tsura musu ido strangely.
" I didn't hear you shout a little bit!". Yafada da karfi lokacin daya bar kofar ihu sukai cikin hadin baki.
" owk uncle!".
Rufe kunnuwanta Ramzia tayi tare da runtse idannunta " Shut up! Your dad is......". Shiru tayi takasa karasawa.
kallonta suke suna Dariya " Momy is not dad but uncle!".
" yes! yes! But tell me something". Tafada tare da dan sunkuyowa.
" what Momy! we are getting late". Aaina tafada cike da kosawa.
" kunyi sallah?".
" yes!". Suka bata amasa a tare.
" Thank you girls now finish up and meet me downstairs ok?".
" owk".
Tafada lokacin da taja musu kofa tashiga kiran some aikinta wacce ta amsa mata daga kitchen.
Harta sauko wayam nan tayi tunanin ya fita amma ga mamakinta tana shiga kitchen ta ganshi, yana aikace-aikace tsayawa tayi sororo, gefe me aikinta ce dake fere Arish.
" And now what is Mr.Ray doing?". Ta tambaya tana kallonshi.
" Ina kwana Aunty?". Me aikinta ta fada da sauri.
" Lafiya!". Ta bata amsa a takaice.
" I am working, so go you are not needed here". Dariya ta sheke dashi.
" like seriously?"
"Yes baby serious!".
Kallon yarinyar tayi da sauri saboda sunan da ya kirata tuna bata Jin turanci yasa hankalinta yadan kwanta.
" kinyi sallah?". Ta tambaya yarinyar.
" nayi Aunty". Tabata amsa.
Kokarin zama Ramzia tayi da sauri ya juyo " please kije falo nace kina hanani aiki fa". Yafada cikin yanayin fushi.
" alright sorry".
Da sauri tafita zuwa dinning koda Su twins suka fito mamakine ya rufesu dan dadynsu is not that type of person sam.
" Momy Uncle ke mana breakfast!". Aaina tafada tana kallonta tana murmushi, daga mata kai tayi alamun eh.
"Aleena you see I told you uncle yafi dady kirki sosai". Harararta Aleena tayi.
" yes amma nafi son dady nidai". Tafada tana tabe baki.
" Uncle nidai nafiso yanzu dan yana sonmu sos...".
" shut up Aaina dady is dady uncle is uncle!". Aleena tafada cikin Jin haushin yar uwarta, tafara jin haushin Rayhan saboda yadda Aaina ke nuna tafi sonshi akan dadynsu.
Sam Ramzia hankalinta baya kansu tana tuna abubuwan dasuka faru tsakaninta da Rayhan, murmushi tayi tare da rufe face dinta, gaba daya hankalinta baya kansu har Rayhan yafito da foodflask zaiyi magana Aleena tamai alamu da momynsu yayi shiru.
Dukansu shiru sukai suka tsura mata ido tayi matukar yin kyau yadda take tunanin tare da murmushi har tana nodding head dinta tare da ciza lips, a hankali takara shigewa kujerar ta rufe ido ganin zata shiga sabon yanayi yasa Rayhan yayi saurin katse ta.
" Tantaran!". Yafada da dan karfi wanda ya farkar da ita a zabure takoma ta zauna cike da jin kunya.
" uncle ka bata mana show, Momy is so happy". Aaina tafada suna Dariya.
" I think Momy is thinking about Dady or maybe he is coming back". Maganar yarinyar dukansu ya tabasu.
" Aleena Ina kika koyo irin wannan surutun?". Ramzia Tafada cike da son ji dan zancen yarinyar ya mata girma.
Kallonta Aleena tayi wacce tuni idannunta suka raina na mujiya " ahm da....".
" forget about it, ba lokaci let's eat saina sauke ku nadawo nakai momyn ku Ko". Cike da jin dadi da murna suka sa mishi ihu suna murna Yau uncle dinsu ne zai kaisu.
Sai dai bangaren Ramzia taki yarda Su hada ido duk yadda yaso sai dai har ranshi yake Jin dadin farin cikin daya saka Su.
Nan gun yayi shiru inda sukai breakfast yaran suka tashi sai da ta musu addu'a kafin suka shiga mota, hakan ya matukar burge Rayhan saida yashiga mota suka hada ido killer smile dinsa yamata da sauri ta juya ta koma ciki tana dariya kirjinta wani irin bugu yake na farin ciki, jinta take kamar a sama saboda tsananin farin cikin da take ciki.
" Aunty!".
Yarinyar takira sunanta da dan karfi kasancewar kiran na biyu kenan ta lura Auntyn nata tayi nisa.
" Na'am Lazima, ki hada wanke-wanke kiyi kinji, sannan banda fita Ko gun maigadi iya kacinki cikin gida so ki haura dakinsu twins kigyara kinji kar Wanda yazo kila bude". Gyada mata kai yarinyar tayi ita Kuma ta haye sama.
Cikin kankanin lokaci tashirya bai jima ba shima ya shigo gidan ya tarar da ita cikin shirinta, KB yayi mamaki d yaga tashiga motar Rayhan inda ta shaida mishi zata kirashi idan ta kusa gama lectures, suka fice.
A motar ba Wanda yace ma kowa komai shi Rayhan Burinsa a yanzu bai wuce yasan waye Haydar ba, sannan ya Kuma yima hindatu warning sosai dan ya jima da fahimtar ba mutuniyar arziki bace.
Kai hannunsa yayi ya riko nata lumshe idannunta tayi. " Nasan kina cikin matsi da damuwa Rahama kisani bake daya bace nima Ina ciki me tsanani walh, na kuma san duk abunda yake faruwa tsakaninmu bakyau is Forbidden ace muna irin wannan relationship din but I will try my best not to cross my limit Insha Allahu duk da still I am crossing but bazan yi crossing yafi haka ba, I just want you and the girls to be happy always". Yakara she cikin sanyin muryarsa.
Tabbas maganar sa gaskiya ce ita kanta bataso Su koma cikin wannan MUMMUNAR ALAKAR a yanzu burinta koda zasu kasan ce tare Su sama junansu ta hanya me kyau bata haramci ba " we are here Rahama!".
Ya katse mata tunani lokacin dayayi parking " zanje gida but I will come and pick you let me know inkin....".
" no karka damu k.....".
" nace call me!". Yafada cikin hade ransa dake firgitata Kai ta daga mishi alamun to ta wuce yana komawa motar ya janyo wayarshi yayi dialing wata no, nan take akai picking " Hello!". Aka fada daga daya bangaren muryar namiji ne.
" hope kaga message dina!".
" yes nagani sir!".
" alright then, inaso a binciko munshi da duk wani information kansa". Yafada cikin hade rai, makala sunglass dinsa yayi yatada motar waigowa tayi suka hada ido lokacin daya ja motar.
" Insha Allahu sir!". Ana fada ya kashe wayar..................