NUFIN ALLAH! Chapter 7
📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_
*Paid book:500*
*Chapter 7*
_Free page_
Bayan sun idar da sallar la'asar ɗinne Najma ta sanya hijab ta nufi gidan Adama dillaliya. Ta taki sa a ta sameta a gida bata fita ba, don sam bata faye zaman gida ba sai yawon neman hajan saye da siyarwa. Najma na sanar da Adama maƙasudin zuwanta, tayi mata sallama ta kamo hanyar dawowa gida. Tafiya take yi cikin takunta mai cike da nutsuwa ta halitta, ko kaɗan bata kallon ko'ina sai inda ƙafafunta suke takawa. Kamar daga sama ta jiyo muryar Luban gidan Hakimi daga bayanta, sai tayi saurin waiwayawa fuskarta na haskawa da murmushi mai faɗi. Lubah ta ƙariso wajen da Najma ta ja tayi tsaye tana faɗin, "Hey! B beauty daga ina? Najma ta sake sakin murmushin da har fararen haƙoranta suka bayyana, sannan ta dubi Lubah tana bata amsa da faɗin, "Daga gidan Adama nake, wai ku kam ba za ku daina kirana da B beauty ɗinnan ba ko?" Lubah ta saki ƙaramar dariyar tana faɗin, "Yo ai sunan daidai da ke ne Najma, domin kowa ya yi miki kallo ɗaya zai shaida cewa ke ɗin black beauty ce ta gaske." Najma ta jefawa Lubah harara suna mai jerawa da juna suka cigaba da tafiya don komawa gida. Suna tafe suna hiran tuna baya na school ɗinsu da irin wuyar da suka daga farko farkon zuwansu makarantar kwanar. Najma ta dinga jin wani shauƙi da kwaɗayin son cigaban karatunta na kamata. Ta sani cewa a yanzu babu wannan halin, domin Baba Hakimi burinsa suyi aure ne ba karatu ba.Bashi da ra'ayin mace ta zurfafa karatu sai maza,hakan yasa ya bai wa su Lubah umurnin fiddo mazajen aure. Najma ce kaɗai bai matsawa ba don Inna ta sanar masa sam bata son ana mata maganar aure. Gashi akwaita da farin jinin samari, duk da cewa duk masu zuwa sai ta ce basu yi mata ba Sabida basu da wadatacciyar ilimi kamar yadda take da burin samun abokin rayuwar mai wayewa da ilimin addini dana zamani.Don haka sam bata sauraren dukkanin samarin ƙauyen giwa da ke nufota da ƙoƙon bararsu, don yawancinsu duk basu yi karatun kirki ba.Tun Inna na mata faɗa akan ta dinga sauraran masu zuwa gareta har ta gaji ta zuba mata ido, tana dai yi mata addu'a Allah ya yi musu zaɓi na gari, don komi lokacine ta sani idan lokacin auren yazo Allah xai kawo wanda zai sace zuciyar Najmar farat ɗaya har ta amince masa. Sannu a hankali suna tafe suna hira har suka iso ƙofar gidan Hakimi, wanda shi ne na farko kafin a yi can gaba sannan a isa gidansu Najma ɗin. Lubah ta dubi yadda Najma ta toge a tsaye alamun ba shiga gidan nasu zata yi ba,ta buɗe baki ta ce, "Najma yanzu muzo har ƙofar gida tare ba zaki shiga ku gaisa da Inna ba?" Najma ta ɗan saki murmushi tana narke fuska ta ce, "Afuwan my Lubcy! Sauri nake na je na sanar da Inna yadda muka yi da Adama, zan zo na musamman gobe na yini musha hira." Lubah ta harareta tana faɗin, "Allah ya kaimu goben, ki gaida min Inna Mairo ki sake mata sannu da jiki." Najma tayi gaba tana faɗin, "Zata ji In Sha Allah!" Daga haka ta cigaba da takawa har ta isa gida.A tsakar gida ta samu Inna Mairo ta shinfiɗa tabarma tana zaune tana lazumi da carbi riƙe a hannunta. Ta samu waje kusa da ita ta zauna tana faɗin, "Inna sannu da hutawa, na samu Adama ta ce zuwa da safe za ta zo ta ga girman katifar." Inna Mairo ta jinjina kai tana faɗin, "Allah ya kaimu Najma." ta ɗaura da cigaba da cewa, "Kina fita Babanku Hakimi ya aiko Ummaru da kayan abinci, gasu can an aje a madafi har da kuɗi dubu ɗaya ya haɗo dashi." Najma ta sauke nunfashi, girma da ƙaunar Hakimi na sake girma a zuciyarta. Cikin tsananin nuna farin cikinta ta ce, "Ma Sha Allah! Allah dai ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.Gaskiya Inna babu abin zamuce da Baba Hakimi sai dai addu'ar gamawa da duniya da lafiya. Allah ya ƙara masa nisan kwana mai albarka, Allah kuma ya duba bayansa a lokacin da ƙasa zata rufe idanunsa." Inna Mairo ta amsa da cewa, "Ameen!" Najma ta miƙe ta nufi kicin ɗin don duba abinda aka aiko musu dashi tunda ita ce mai sarrafawa, domin tunda aka hana Inna yawan kusantar ɗumin wuta sai ya kasance ita ce mai yin girkin. Kamar dai yadda ya saba aiko musu wake da shinkafa ce sai gero da garin tuwo da ake niƙo masa sai dai kawai ayi ta ɗiba ana amfani dashi. Ta sake gode masa cikin zuciyarta tana tunanin abinda zasu sarrafa suci da dare. Tunaninta ya tsaya akan ta dafa musu shinkafar manja da alayyu kawai, tunda da rana kwaki suka ci da ƙuli. Koda ta sanar da Inna abinda take da niyyar dafawar, sai ta miƙa mata dubu ɗayan ta ce ta je tayo cefanan ɗari biyar ta dawo da ɗari biyar. Najma ta sake fita tayo cefanan ta dawo tana mai fara shirin ɗaura girkin. Inna tana daga zaune ta taimaketa da gyaran kayan miya da alayyahun, ita kuma Najma ta nufi kicin don kiciniyar rura gawayin da zata yi girkin da shi.
Washegari Adama dilalliya da safe ta zo ta duba katifar tayi masa kuɗi. Inna Mairo ta raina darajar da katifar tayi domin ta san cewa katiface mai nagarta irin ta da.Sai dai dagewa da Adama tayi akan cewa ba zata ƙara farashi daga yadda tayi masa kuɗi ba,sai kawai Inna tq amince domin a matse suke da son kuɗin. Zuwa yamma Adama ta zo da mai ɗaukar katifa ta biya kuɗi aka ɗauka, Inna Mairo sai da tayi ƙwalla lokacin da aka fita da katifar akan idanunta.
Najma ta damƙawa kuɗin bayan tafiyar Adama tana mai cewa , "Gasu Najma, sake irgasu mu gani." Najma ta amsa kuɗin ta sake irgawa tana sanar da Inna Mairo yawan kuɗin. Suka zauna suka lissafa kuɗin wake dana mai da za a siyo don cigaba da sana'arsu da ya karɓesu na tuyan ƙosai, wanda Najmar ce zata jagorancin cigaba da yi tunda Inna ba damar ta cigaba sabida kiyaye lafiyarta.
Ragowar kuɗin da ya ragu Inna ta amsa ta aje, da tunanin cewa washegari zata aika da kuɗin wajen Hakimi don a nemi ciko a sayo maganinta guda ɗaya da ba a samu saye ba sabida tsadarsa. Sai dai koda ta aika Najma da kuɗin Hakimi cewa ya yi a dawo mata da kuɗinta, yana sane da maganar da zaran ya samu hali za a sayo a kawo mata. Inna Mairo ta tasa kuɗin a gaba tayi zuru tana zurfafa tuni akan irin ɗawainiyar da Hakimi ke yi dasu, wanda ba kowani amini bane zai yiwa amininsa wannan halaccin da Hakimi ya gwadayi ba. Kuɗin sai ta sake rabashi biyu ta bai wa Najma rabi ta ce ta siyo musu mangyaɗa da manja na girki wanda zai jima musu, ragowar kuɗin kuma ta adana a hannunta don tsaran lalura.
Najma ta cigaba da suyan ƙosai kamar yadda suke yi, kuma ana samun ciniki mai yawa don sana'ar ta amshesu da gaske. Sabida yadda suke tsaftace sana'ar da kyau, suke kuma yinsa da arha matuƙa basa bin mugun riba mai yawa,don albarkan suke nema ba wai yawan kuɗin da za a zare albarkarsa ba. Tun ƙarfe bakwai idan ta kafa yin tuyan bata tashi a wajen sai ƙarfe goma, sosai Inna ke tausayinta tare da jinjinawa ƙoƙarin Najma sabida irin wahalar da take sha.Inna ke ɗan taimakawa da yin ayyukan gida irin su shara da gyaran ɗaki don ragewa Najma wasu wahalhalun. A haka suke cigaba da sana'arsu suna manejin rayuwa, da daɗi babu daɗi haka nan suke nuna godiyarsu ga Allah kullum.A hakan suke samun ƙarin wadatuwan zuci a koda yaushe,wanda shi ne kuma babban arziƙin bawa.
Ranar wata asabar da misalin ƙarfe sha biyu na rana, Najma ta fito daga wanka kenan tana shiryawa suka fara jiyo sallama daga bakin zauren shigowa gidan. Inna Mairo ta zari Hijab ta fice don ganin mai sallamar, duk da cewa kunnuwanta na jiyo mata murya kamar ta drivern Gwaggon kaduna ne. Tana fita kuwa tayi ido huɗu da Adamu driver,ta saki murmushi tana masa maraba da zuwa.A tsaye suka gaisa kafin ta juya zuwa cikin gida don ɗakko masa tabarma, ta shinfiɗa masa a nan zauren suna sake gaisawa cikin mutunci. Adamu ya dubi Inna Mairo cikin jin tausayin yadda duk ta lalace ya ce, "Hajiya Zainab ne ta aiko ni da saƙo, ta ce a gaidaki da kyau sannan idan na iso in kiraki zaku yi magana da ita ta wayata." Inna Mairo da ke sauraren saƙon Adamu driver, sai ta dubesa tana mamakin kalamansa. Ya cigaba da faɗin, "Bari a kwaso saƙon daga mota, in yaso sai na kirata kamar yadda muka rabu da ita akan ina isowa na kira kuyi magana." Inna Mairo ta jinjina kai tana faɗin, "To badamuwa Adamu, bari a kawo maka koda ruwan sha ne kafin a ɗaura sanwar rana ka ci." Adamu ya yi godia yana mai fita zuwa wajen ƙatuwar motar Hajiya Zainab Kaita da ya taho da ita. Inna Mairo kuma ta shiga cikin gida don kawo masa ruwan sha, tana mai sanar da Najma cewa drivern Gwaggo ne Adamu yazo. Ta cigaba da cewa, "Ya ce matar Yaya Kabeeru ce ta aikosa Najma, Allah dai yasa lafiya don ta ce idan ya bani saƙon ya kirata muyi magana. Naga dai ba azumi bane yanzu, ba kuma sallar layyane ya gabato ba bare ace saƙon da aka saba yo mini aike dasu ne suka iso." Inna ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya, hakan yasa Najma dubanta da kulawa ta ce, "Bakomi Inna,alkhairy ne In Sha Allah! Kai masa ruwan kiga abinda ya zo dashi, sannan kiji mai zata sanar miki ɗin." Inna ta jinjina kai tana gamsuma da kalaman Najma,ta juya ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da wani matsakaicin jug ɗin roba da ta ɗibarwa Adamu ruwan randarsu. Ta samu ya jibge manyan paper bags har guda uku daga gefe guda cikin zauren, ɗaya gefen kuma ya jingine buhun shinkafa da su taliya da kayan shayi. Ta ɗauke idanunta daga kan kayan tana mayarwa kan Adamu ta ce, "Adamu yanzu duk waɗannan kayan daga Hajiya Zainab suke? Kodai Gwaggo ce ta aiko ka ta ce ka ɓoye hakan?" Adamu ya yi murmushi, can ƙasan zuciyarsa yana sake jin tausayin Inna Mairo sabida yadda ƴan uwanta da Gwaggo basu damu da ita ba. Ga arziƙi can kamar yaci kansa, amma ita gata a cikin ƙauyen giwa da sam garin ya kula baya samun wani cigaba. Kullum yazo jiya iyau yake ganin garin, ba ya ganin wani sauyi na a zo a gani da garin ke samu. Ya sauke nunfashi yana faɗin, "Inna Hajiya ce ta aiko ni ba Gwaggo ba, don ita bata ma san nan nayo ba domin Hajiya Zainab cewa tayi ta ara mata ni zata aikeni wani waje. Don haka bata ma san cewa nan zan zo ba Inna, amma bari na kira Hajiyar kuyi magana." Daga haka ya zaro wayarsa daga gaban aljihun rigarsa yana mai danna kiran Hajiya Zee Kaita. Bugu biyu ana uku ta ɗaga wayar, Adamu ya shaida mata cewa ya iso, ta buƙaci ya sadata da Inna Mairon.Ya miƙawa Inna wayar ta amsa, hannunta na rawa ta kai wayar kunni bakinta ɗauke da sallama.Daga ɓangaren Hajiya Zainab ta amsa mata sallamar tana tambayarta lafiyarta dana ƴarta Najma. Inna ta bata amsa da cewa suna cikin ƙoshin lafiya. Hajiya Zainab sai ta tafi kai tsaye da tambayar Inna dalilinta na rashin zuwa wajen bikin manyan Yaranta biyu da aka yi wata ɗaya da ya wuce. Cike da kaɗuwa Inna Mairo ke duban Adamu tana sake damƙe wayar akan kunninta ta ce, "Yanzu kina nufin ki ce anyi auren Adnan da mai sunan Gwaggo banji labari ba?" Cike da tsantsar mamakin jin kalaman Inna Mairo ita ma Hajiya Zainab da bata tabbacin haka take nufi. Inna Mairo ta saki salati tana mai jin zuciyarta na matsewa da wani irin ɓacin rai mara misaltuwa. Mamakin halayyar Gwaggo da irin ƙiyayyar da take mata na sake tayar da hankalinta, domin bata taɓa tunanin hakan zai iya faruwa ba koda wasa. A ce wai anyi auren manyan Yaran Yaya Kabeeru ƴan gaban goshin Gwaggo, amma bata aiko an sanar mata ta halarci bikin ba sabida kawai Gwaggon ta nuna mata cewa har yanzu zuciyarta bata risina akan nuna mata ƙiyayyah da rashin son ta raɓi inda suke ba. Wasu hawaye masu zafi wanda bata shirya fitowarsu ba suka gangaro daga fuskarta, ta sanya hannu tana sharesu tana cigaba da sauraren kalamai na rarrashi daga bakin Hajiya Zainab ɗin. Wacce zuwa lokacin da suke wayar da Inna ta gama gane duk wani laifi na wuyar surukarta Hajiya Gwaggo, wacce ita ce bata son Inna ta raɓi ƴan uwanta bare har ta amfana da ni'imar da Ubangiji ya yi musu na tarin arziƙi. Domin zuwa yanzu arziƙinsu kullum sake bunƙasa yake, sun samu ɗaukaka a rayuwa matuƙa da gaske. Musamman mai gidanta Alhaji Kabeer Dukku,wanda ya gama zama babba sosai a wajen aikinsa, sannan ya zama ɗan siyarsa ɓoye dake ci da gwamnati.Yana samun manyan kwagiloli daga gwamnatin tarayya, sanadiyyar amininsu dake kusa da shugaban ƙasa sosai. Inna Mairo ta dinga sauraren maganganun Hajiya Zainab da irin ban bakin da take mata na cewa ta daure ta cigaba da kai musu ziyara,karta cigaba da biye Gwaggo ta zo don sadar da zumunci tsakaninta da ƴan uwanta ne. Ita dai Inna tana jin Hajiya Zainab ne kawai, amma zuwa lokacin zuciyarta ta riga ta kulle da tsananin baƙin cikin wannan tozarci da nuna mata iyakarta da Gwaggo tayi. Don bata yi zaton duk lalacewarta da yadda Gwaggon bata sonta zata iya bari ayi auren Ƴaƴan ɗan uwanta uba ɗaya amma ace wai bata sani ba. Tabbas dole zuciyarta ta girgiza, ranta kuma ya sosu domin iyakan tozarci da rashin ƙauna har ma da ƙyama duk an nuna mata. Ta danne zuciyarta har zuwa lokacin da suka kammala yin magana da Hajiya Zainab ɗin,sannan tayi mata godiya mai tarin yawa akan abin arziƙin da ta aiko mata da shi. Ta miƙawa Adamu wayarsa tana mai jin ƙaunar matar Yayan nata na mamaye zuciyarta, babu abinda zata ce mata sai godiya don ta fiye mata ƴan uwanta da Gwaggon.Tunda har ita taji ciwon rashin zuwanta bikin, ta kuma aiko takanas don a ga lafiyarta a kuma ji dalilinta na rashin halartan bikin. Bata bar ta haka ba kuma sai da ta aiko mata da tarin abin arziƙi, wanda take kyautata zaton kayan biki ne a waɗancan jakunan takardan.Sabida sai a yanzu take ganin tambarin sunan Yaran da aka aurar ɗin a jikin paper bags ɗin.Cikin wani irin sanyin murya ta dubi Adamu driver tana mai miƙa masa wayarsa ta ce, "Adamu ga wayar taka na gode, ka yi haƙuri ka jira Najma ta kammala abinci sai kaci ka yi sallah kafin ka juya." Adamu ya dubeta cike da sake jin zallar tausayin yadda yaga ɓacin rai kwance a idanunta ya ce, "Kiyi haƙuri Inna, komi na rayuwa mai wucewa ne." Inna Mairo ta jinjina kai tana kai wa matuƙa wajen sake danne damuwa da ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ta ce, "Bakomi Adamu, tabbas komi mai wucewa ne. Allah dai ya bamu ikon cin jarabawarmu ta rayuwa, domin kowa akwai ta inda ake jarabtarsa." Adamu ya jinjina kai yana sake kwantar da hankalinta da kalamai masu daɗi, don ya hango ɓacin rai mai yawa kwance a idanunta. Shi ya shigar mata da kayan abincin zuwa ciki, ita kuma ta ɗauki jakunan duka ta nufi cikin gidan, tana nufan ɗakinsu dashi zuciyarta na mata wani irin nauyi da zugi.......✍🏻
*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:****
🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*
*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA *** DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻
#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰