๐๐๐LAILAH๐๐๐
Chapter 15&16
๐๐๐LAILAH๐๐๐
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF
GIMBIYA AUSHU๐๐๐
ELEGANT ONLINE WRITERS๐
PAGE 15-16
__________________Bayan ruwan ya tafaso ta dauriye jug ta juye a ciki ta kai dining ta dawo ta dauriye three cups ta bude cabinet,gwangwanin sugar ta dauko ta fito,zuba ma kowa tayi tasa ma nata dana Husna sugar sannan tace"Mama na sa miki sugar",a amman kadan,"toh Mama",dauka tayi ta kai musu parlor,mika ma Mama ta farayi Sannan ta mika ma Husna,"thank you sweet Anty na",Allah ya kawo miji nagari".
Daka mata dundun tayi abaya,ihu Husna tayi tace wayyo bayana,juyawa Lailah tayi tabar wurin ta koma dining ta zauna,plate ta dauka ta bude cooler ta sa abinci dai-dai cikin ta,lipton din ta fara siping a hankali,sai data sha kusan rabi kafin ta fara cin abincin,bayan ta gama takai plate din kitchen ta dauriye,"parlor ta dawo ta zauna kusa da Mama suka sata tsakiya,Mama tace"baza kije kiyi karatu ba?".
"Zanyi Mama amman sai nayi sallan magriba".
"Toh Allah bada sa'a".
"Tunda ba yanzu za kiyi karatun ba kimana girki mana".
"Toh Mama".
"Tashi ki bita"
.
"Mikewa Husna tayi tana turo baki har ta shige kitchen".
Lailah na ganin ta tace"an koroki Kenan",ta fada tana dariya,turo baki Husna tayi tace"sai in koma yanzu".
"ni Ina ruwana ki koma mana,kin dai san sauran jeki",turo baki tayi tace " mai zan miki yanzu".
Blending,ki dibi timatirin na gani.
"Toh Anty"bayan ta dibo ta nuna mata.
Ya isa,ki gyara su da kyau,in kin ga dama kisa hannu a ido.
Turo baki Husna tayi kaman za tayi kuka tace" i ba da bane,i yanzu bana haka",gyra kayan miyar tayi ta zuba a blender ta nike su,bayan ta gama,ta dauriye tunkunya ta zuba a ciki da daura kan gas ta kunna.
Freezer ta bude ta dauko nama ta wanke ta zuba a tukunya tasa kaya ta daura a gas ta kunna.
Lailah dake ta kallan duk abin da take ne tace"ashe dai kin iya aiki saura aure".
Bubbuga kafa Husna ta fara yi a kasa tace"ni wlh ban kai ba",ta fada tana kunkuni.
"Dariya Lailah tayi har da rike ciki sabida yanda Husna tayi.
6:45 suga gama komai har wanke-wanke,jera coolers din suka yi a dining,gwanin ban sha'awa.
Daki duk suka nufa dan yin sallah.
Bayan Lailah ta idar tayi Azkar,ta yi karantun Al-Qura'an,sai da aka yi isha'i ta kulle ta mai da shi,mikewa tayi ta tada sallah ta tayar,bayan ta idar tayi shafa'i da wutiri,bayan ta gama ta sauko dan lokacin cin abinci yayi,tana shiga parlor Daddy ya shigo, gaida shi tayi tana mai sannu da zuwa
"Mamana ykk,ya exams".
"Lfy lau Daddy,exams kam Alhmd Masha Allah".
"Ubangiji Allah ya bada sa'a ya taimaka".
"Ameen Ameen Daddy nagode".
Dining suka nufa ta ja ma Daddy kujera.
"Thank you My daughter Allah ya miki Albarka",ya karasa maganar shi yana zama kan kujeran.
Kujera ta ja ta zauna kusa da Daddyn ta Mama tayi serving din su,bayan sun gama,Lailah bata tsaya parlor ba tayi musu sai da safe ta wuce dakin ta.
Handout ta dauko,ta fara karatu, ba ita ta kwanta ba sai 2:38am bayan tayi nafiloli.
Washe gari morning paper suke da shi, bayan ta gama shiri tayi wa Mama sallam.
Adddu'a Mama tayi mata tare da fatan Alkhairi.
karfe tara suka fara paper suka gama sha daya,bayan sun gama ta zauna ta cigaba da karatun next paper.
Biyu dai-dai suka shiga wani paper.
Malan sa'ad na shiga ya ce kowa ta fito da bag din shi da phones, and Don't make any attempt of exam malpractice, yana daga kai ya hango Lailah a baya, yace"hey come back hear".
Tashi tayi sim-sim kamar wata tsohuwar munafuka ta dawo gaba ta zauna.
Karfe hudu suka gama aka amsa papers din su,da zai fita ya mika wa Lailah papers din sannan yace"ta biyo shi da su".
Lailah najin haka ta yi salati a zuciyar ta,jikin ta har rawa yake dan tsoro,ya rigaga isa,knocking tayi amman shiru bai amsa ba,ta jira sawon minti uku kafin ta kara wani,sai da yayi minti daya kafin yace"waye?".
"Is Khadija sir".
"Okh come in".
Tura kofad tayi ta shiga bakin ta dauke da sallama.
"Amsa sallamar yayi ciki ciki",
Tsayawa tayi a tsakiyar office din tace"here are the papers sir".
Da hannu ya mata nuni alamun ta ajiye shi.
Bayan ta ajiye ta juya da niyyan barin office din ta ji yace"come back here",tsaura kadan ta kife tsabar tsoro da rashin sabo".
Murya a tsanyaye yace"Sweep my office".
Dagowa tayi ta kalle shi hawaye ya taru a idon ta,juyawa tayi ta kalli office din taga babu alamun datti ko kadan illa tashin kamshin da office din yake kaman anyi barin tulare.
" baki ji bane,ya fada kaman wani mai whispering".
Wurin da aka ajiye sweeping stick ta nufa ta dauka ta fara sharan kamar yanda yace.
Jingina yayi da kujera ya kulle ido yana kallan duk abinda take ta kasan ido, baza ka taba sanin idon shi biyu ba.
Bayan ta gama tace"am done sir".
Bude idon shi daya yayi yace"gud".
Muryar ta a tsanyaye kamar wata mai koyon magana tace"can i go sir".
Gyara zaman shi yayi yace"No" ba tare da ya kalle ta ba.
Shagwabe fuska tayi tacena tace"my driver will be waiting for me outside".
"That is non of my business".
Hawaye ne ya gangaro kuncin ta tasa hannu ta share.
Murmushi yayi yace"my crying baby",wani bangare na zuciyar shi yace"ko dai ka fara son ta ne?",nooo! ba san ta nake ba,kawai dai tana birge ni ne kuma tana da kokari da hankali, bazan taba soyayya ba,"love is fake"
Katse mishi tunani tayi da fadin"pls sir can I go,i don't want my mum to get worried".
Shiru yayi kaman bai ji ba ya cigaba da abinda yake.
Wuri ta naima ta zauna ta dau waya dan ta kira driver,yace ta ajiye shi,sir zan ce mishi ya wuce ne.
"Okh"
Driver ta kira tace ya wuce.
Sai karfe shida suka bar makaranta,in hankalinta yayi dubu toh ya tashi,dan taga miss calls din mama amma ta kasa dagawa dan batasan abin da zata ce ba,suna fita ko kallan shi bata yi ba tayi hanyyan gate,murya a causashe yace"keh",a tsorace ta juyo,yace dawo nan.
Dawowa tayi ta tsaya ajikin motar tana hawaye,a zuciyar shi yace"abu kadan kuka sai kace baby girl mtsww",shiga na ajiyeki ba mutsu ta shiga shima ya shiga ya tada motar, babu mai magana har ya kaita gida ta fita ta kulle kofar, har ta juya ta fara tafiya taji yace"baki iya godiya bako".
"Juyowa tayi tace"nagode".
"Inkin shiga ciki kice mata an muku extra lecture ne sabida paper da kuke dashi gobe Lecturer bai yi covering ba".
Juyowa tayi tana kallan shi da alamun mamaki taga hankalin shima baya kanta yana kan wayar shi,tsayawa tayi tana kallan shi,muryar shi taji yace"bar kallona and do what I said in ba hakaba ke ce a ciki",ya fada tare da barin layin,bin shi tayi da ido har ya bace wa ganin ta,juyawa tayi ta shige gida,ta na shiga ta tadda Mama tana tsintiri a parlor,kafin tayi wani magana taji Mama tace"daga ina kike Lailah", tsoro ne ya kama ta,amman tana tuna abin da yace mata sai taji wani jarumta ya shige ta,nan ta gayawa Mama.
Mai yasa baki kira ni ba?,
"Na kira but not reachable".
"Okh dana kira mai yasa baki daga ba",
"Ban ji ba Mama wayar na silent ne shi yasa........................
COMMENT
VOTE
AND
SHARE.
GIMBIYA AYSHU๐๐๐.