NUFIN ALLAH! Part one story

NUFIN ALLAH! Chapter 11

by @ayshadansabo

📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻

 _*Arewabooks@ayshadansabo*_


 *Paid book:500* 


       *Chapter 11*


 _Free page_ 


Auwalu ya amsa sallamar Najma yana mai bata izinin shiga ɗakin.Ta shiga ta samu wajen zama bisa kujerar da ke nesa da shi,ta dubesa da murshi akan fuskarta ta ce, "Sannu da hutawa Yaya Auwalu, an barka kai kaɗai kana ta jira shiyasa na ce bari in zo in tayaka zama kafin su Baba Hakimi su gama magana da Kawu Kabeeru. Auwalu ya aza mata idanunsa da ke cike da zallar ƙaunarta yana faɗin, "Kin kyauta Najma, dama duk zaman ni kaɗai ya dameni." Daga haka ya fara janta da hira yana mai jin tsananin nishaɗi a zuciyarsa.


Daga can ɓangaren Gwaggon kaduna dasu Inna Mairo kuwa, Baba Hikimi ne kewa Alhaji Kabeeru Dukku nasiha mai ratsa zuciya. Yana mai tunasar dashi illar yanke zumunta da cin amanan ƴan uwantaka, domin tabbas sunci amanar zumunci da ƴan uwantaka akan yadda suka wofintar da Inna Mairo. Ya ɗaura laifin baki ɗaya akan Alhaji Kabeer yana mai sanar dashi cewa, "Amatsayinka na babban Yaya a garesu, kamata ya yi ace lokacin da ka kula cewa Mairo ta daina zuwa inda kuke wajen Gwaggo ka bincika da kanka ka gano miye matsalar, me kuma akai mata ko ke tayi da ta yanke hukuncin nisantarku da mahaifiyarku? Amma sai kayi biris ka cigaba da biyewa son zuciyan Iyayenmu mata, waɗanda dama sune ke assasa wutar irin waɗannan rashin jituwar da ke faruwa tsakanin ƴan uba.Domin kaso casa'in cikin ɗari na lalacewar zumunci a gidaje, Iyayenmu mata ne ke jagorantarsa, ba kuma sabida komi ba sai biye son zuciyoyinsu da mummunar kishin da ke rufe idanunsu. Idan ba anyi sa a da jajirtaccen uba mai sanya ido matuƙa da gaske ba, sai ka ga kafin kace kwabo sun raba kan ƴan uwa tare da jefa ƙiyayyar juna a zukatansu.Wanda wannan babban kuskure kuma babban zunubi, domin Ubangiji ya yi tir da bawan da ke yanke zumunta tsakanin ƴan uwan juna.Kana da laifi matuƙa da gaske wajen yin biris da lamuran Mairo, alhali kai ka fi girman hakkin kulawa da ita, sabida babban Yaya makwafin uba yake.Amma kai kayi watsi da amanar da Abbanku ya damƙa maka na riƙeta da amana ku kuma maye mata gurbinsa.....


Hakimi ya ɗan dakata domin bai wa Yaya Kabeeru damar magana.Yaya Kabeerun da ya yi shiru yana mai faɗawa duniyar tunani da nadama, sai ya ɗago manyan idanunsa ya ɗaura akan Inna Mairo yana faɗin, "Ki gafarceni Mairo tabbas mun yi kuskure, sai dai fatan kada Allah ya maimaita.Sannan kema kina da kaso mai yawa wajen aikata kuskure Maryam, don bai kamata ace ko wani irin abu Gwaggo ke miki zaki iya yin zuciya ki daina zuwa inda take ba, koda ace ita ce ta buƙaci hakan da kanta.Domin su Iyaye ba a fushi dasu sai dai ayi ta binsu ana rarrashi da kwantar da kai har su gano kuskuransu.Amma ke sai ki ka nuna cewa tabbas ba ita ce ta kawoki duniya ba, domin da Inna ce ke raye kome take miki ai ba zaki iya daina zuwa gareta ba.Don haka kema kinyi kuskure bana buƙatar a gaba ki sake aikata makamancin hakan. Ki yafe mana baki ɗayanmu kuskuren da muka aikata wajen wofintar dake, alhali munfi kowa kusanci dake kuma mu ya cancanta mu riƙe ragamar rayuwarki a lokacin da kika rasa miji da mahaifi, amma ba muyi hakan ba duk da cewa Allah ya bamu arziƙi da damar yin hakan. Ki yafe mana wannan babban kuskuren Maryam, In Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba.Zan yi amfani da bakina wajen roƙawa Ali gafararki shi ma, kafin ya zo ya roƙa da bakinsa idan yazo gari tunda a yanzu ya dawo ƙarsar yana can da Iyalinsa a garin Lagos." Inna Mairo ta jinjina kai tana sake share hawayen da ke zubo mata,wanda bana komi bane na farin ciki ne da Allah ya nuna mata wannan ranar da take zaune gaban Gwaggo da Yaya Kabeeru suna roƙon afuwa a gareta.Tabbas ta sake gasgata cewa mai haƙuri shi ke da nasara,sannan babu abinda ke dauwama a duniya walau jin daɗi ko akasin hakan. Baba Hakimi ya jima sosai yana nusar da Gwaggo da Alhaji Kabeer illar abinda suka aikata tare da sanar dasu lalurar da ta kama Mairo, duk kuma a sanadiyyar baƙin ciki da ƙuncin rayuwa ne da suka jefa zuciyarta a ciki. Don ba za a ce rashin ci ko sha ne ya sababba mata shiga ƙunci da yawan tunanin da har ya sanya ta kamu da cutar hawan jini ba, sabida iyakan ƙoƙari yana yi dasu wajen ganin basu nema abin ci ko abin sha da kuɗin cefane sun rasa ba. Illar ƙiyayyar Gwaggo gareta da kuma juya mata baya da suka yi ya janyo mata shiga halin ƙunci da yawan tunani. Jikinsu Gwaggo ya yi mugun sanyi, tausayin Mairo ya sake kamasu musamman Alhaji Kabeer da har wani ƙunci da kunyar Inna Mairo ya dinga ji. Ya sake bai wa Mairo haƙuri tare da yi mata albishir da cewa komi ya wuce a yanzu, don ba zasu sake barinta ba. Hasalima ta sanya a ranta ta dawo hannunsa kenan da zama ba za ta koma ƙauye ba ita da ƴarta, sai dai kawai su je suyi bankwana da mutanen garin su dawo.Inna Mairo ta dubi Yaya Kabeeru fuskarta na bayyana tsananin mamakin kalamansa, domin ba tayi zaton hakan ba cikin gaggawa. Kafin ta iya cewa komi ko Hakimi ya ce wani abu, Gwaggo ta rigasu da faɗin, "Tabbas Mairamu ba zaki koma ba kun zo kenan, muna godiya da tarin karamci da ƙaunar da Mai girma Hakimi da Iyalinsa suka nuna muku. Tabbas Hakimi ka cika amini na ƙwarai, kuma wanda yasan girman halacci a rayuwa. Mairo dawowarta garemu baki ɗaya shi yafi dacewa a yanzu, domin hakan ne kawai zai sake bamu damar kusanci da assasa ƙaunar juna a tsakaninmu." Mai girma Hakimi ya jinjina kai yana jin wani abu mai nauyi na son danne zuciyarsa. Cikin murya marar amo yake faɗin, "Alhamdulillah! Da wannan hukunci naku Hajiya Gwaggo, duk da cewa ni da dukkanin ahalina wannan hukunci ba zai mana daɗi ba. Amma a zahirin gaskiya hakan shi yafi dacewa, Mairo ta dawo ƙarƙashin kulawarku ko don ku kula da lafiyarta da samar mata magungunanta akan kari.Don a can ɗin wani lokacin kuɗin sayen magungunan kansa gagara yake. Zamu shiga alhini mai yawa idan ya kasance mun buɗe ido mun ga babu Iyalan Malam Mahmuda a kusa damu, amma hakan ba zai hana mu taya Mairo farin ciki ba domin wannan shi ne irin gatan da ya dace ta samu daga gareku. Allah ya haɗa kanku ya baku ladar zumunci,ke kuma Mairo ina fata barinki garin giwa ba zai zamo silar lalacewar zumunci da ƙaunar da ke tsakaninmu da juna ba ni da ahalina baki ɗaya?" Hakimi ya kai ƙarshen maganar fuskarsa na bayyana zallar alhini da irin kewar su Inna da zasu yi. Don sabo shegen abu ne, musamman su da suka riƙi juna tamkar ƴan uwa.Inna Mairo ta share hawaye tana duban Hakimi a karon farko ta ji wani irin abu na dukan zuciyarta game dashi, ta lumshe idanunta tare da sake buɗe shi akansa ta ce, "Har abada hakan ba zai taɓa faruwa Baban Hanne, domin ku ɗin kun zama wani ɓangare na rayuwarmu ni da Najma. Ba zamu taɓa manta halaccinku da ƙaunar da kuka nuna mana ba,domin kun tallafemu a lokacin da muka rasa dukkan gata.Kun riƙe mu tamkar jininku ba tare da nuna gazawa ko gajiya damu ba, wannan kaɗai ya isa ya sanya mu dauwama muna yi muku addu'ar gamawa lafiya tare da damƙe igiyar zumunta tsakaninmu da juna. Zamu yi kewar da zai wuce yadda zaku yi namu Hakimi, domin daku muka yi sabon da ku kaɗai ku ke sanin farin ciki ko damuwarmu. Ku kaɗai ke fara kawo mana ɗauki a dukkanin abinda ya taso mana, mai daɗi ne ko marar daɗi. Kune cin mu ku ne shan mu tare da suturarmu,taya zamu manta dukkanin wannan alkhairyn har mu kasa cigaba da sadar da zumunta tsakanin mu da juna? Hakan ba zai taɓa faruwa ba Hakimi, ina sake godiya tare da fatan alkhairy ga rayuwarka da ta Iyalinka baki ɗaya." Inna Mairo ta tsaida maganar hawayen tsananin kewar da zasu yi na baro garin giwa su dawo nan ɗin na wanke fuskarta. Gwaggo da Yaya Kabeeru ne suka cigaba da tataunawa akan Hakimi zasu tafi su bar Najma da Inna Mairo a nan ɗin. In yaso nan zuwa kwanaki uku shi da Gwaggo da su Inna Mairon zasu yi mota guda su yiwa Inna Mairo rakiya zuwa giwa, don su yo bankwana da Iyalan Hakimi su kuma ɗakko abinda suke so. Inna Mairo ta dinga sharan hawaye tana tuno fuskar Uwargidan Hakimi Inna Karima, tana ayyana irin kewar juna da zasu yi.Daga ƙarshe Yaya Kabeeru ya janye Hakimi zuwa ɓangarensa, ya yi masa masauki a ƙawataccen falonsa na ƙasa inda yake ganawa da baƙinsa. Sun tattauna muhimman lamura akan abinda ya shafi rayuwar Inna Mairo da ƴarta Najma. Hakimi ya yi masa dukkanin bayanin da ya shafi yadda hawan jinin Inna ke yawan tashi, ya kuma sanar dashi abinda likita ya faɗi na cewa zuciyarta na barazanar kamuwa. Alhaji Kabeer Dukku ya dinga yiwa Hakimi godia tare da jin ƙaunar dattijon na ratsa shi, don Hakimi ya fara zama dattijo don ya haura shekaru hamsin da takwas, kaɗan ya rage ya kai shekaru sittin a duniya.Suka yi sallama da Alhaji Kabeer bayan ya jaddadawa Hakimi cewa suna nan tafe nan da kwanaki uku. Daga shi har Iyalinsa duka zasu rako Inna Mairo garin giwa don tayi sallama da abokanan arziƙinta, shi kuma suyi godiya ga Iyalan Hakimin. Daga Inna Mairo har Gwaggo da Hajiya Zainab, dukkaninsu suka rako su Hakimi har bakin mota lokacin da zasu tafi. Najma na wani irin kuka mara sauti don ita ko kaɗan hukuncin cewa ba zasu koma garin giwa ba bai mata daɗi ba, domin da mutanan garin ta saba,sannan su ta taso ta sani a matsayin komi nata.Don haka a yanzu farat ɗaya ace za a rabota da ƴan uwanta su Hanne tana ganin tamkar rashin adalci ne da datse mata farin cikinta.Auwalu kansa kallon Najma ya dinga yi zuciyarsa na masa wani irin suya, hakanan yake jin bai ji daɗin yadda za a ce ba za su koma giwa ba. Ya dinga mita a zuciyarsa yana faɗin da can mai yasa suka yi watsi da lamuransu, sai a yanzu ne suka san da cewa Inna Mairo ba za ta cigaba da zaman karkara ba? Har Hakimi ya shiga mota Auwalu mita yake a zuciyarsa yana ji tamkar ya sanar da Najma sirrin zuciyarsa a kanta,ya haɗe fuska tamau lokacin da Gwaggo ke masa fatan su isa lafiya. Alhaji Kabeer Dukku kuwa matsawa ya yi daga jikin motar ya miƙawa Auwalu wata ƙaramar envilop, mai ɗauke da damin kuɗin ya ce su sha mai dashi. Auwalu ya amsa ya yi godiya fuskarsa sam babu walwala, sai ma ƙarin baƙin ciki da alhinin daina sanya Najma da zai dinga yi a idanunsa ke sake kassara zuciyarsa. Inna Mairo ta matsa har jikin motar tana sake yiwa Hakimi godiya tare da yi musu addu'ar Allah kiyaye hanya.Ita kam Najma ta kasa isa jikin motar  sai tsayawa tayi daga nesa tana cigaba da kuka mai cin rai. Nasreen da ke tsaye daga bayanta ne ke faman rarrashinta akan tayi shiru, amma ko duban Nasreen ɗin ta kasa yi bare ta saurari rarrashinta da take yi. Dukkanin zuciyarta na ga su Hanne da Lubah, waɗanda ta san yau kwanan kuka zasuyi idan suka ji labarin za a rabasu da garin giwa su dawo nan ita da Innarta. Ita ko kaɗan hakan bai yi mata daɗi ba don duk yadda Gwaggo ke wani nuna nadamarta ba birgeta take yi ba, sai ma sake jin zafinta da take yi a cikin zuciyarta idan tana tuna irin yadda Inna ke kuka da idanunta na irin baƙin ciki da ƙiyayyar da Gwaggon ta nuna mata. Hannunta Inna Mairo ta kama lokacin da motar su Hakimi ta bar wajen,ta yi ƙasa da murya tana cewa da Najma, "Ki yi shiru ki tsaida wannan kukan Najma, nan ma gida ne kamar can kinji ko?" Najma ta ja ajiyar zuciya tana cewa, "Amma Inna meyasa zasu ce ba zamu koma can ba alhali ni nafi son can, duk talaucin da muke ciki a can wallahi nafi son can da nan ɗi....." Hannu Inna ta sanya ta rufe bakin Najma tana jifanta da wani kallo mai cike da gargaɗi ta ce, "Karna kuma jin kina faɗin hakan Najma, Gwaggo  da Yaya Kabeeru sun yanke hukuncin mu dawo nan ɗin. Kuma hakan shi ne daidai domin sune tilashina ba Hakimi ba, shi halacci yake nuna mana amma ba don nauyin kulawa damu ya rataya a wuyarsa ba. Lokaci ya yi da za a barshi da Iyalansa ya hidimta musu, don koda kuɗin maganina aka cigaba da barinsa tabbas ana shiga rayuwarsa. Ki sani yau da gobe sai Allah Najma,sannan duk yadda zaki yi kewar su Hanne da Lubah bai kai yadda ni zanyi kewar baro garin giwa ba. Domin gari ne da tarihin rayuwar da nayi aciki da mahaifinki ba zai taɓa gogewa a zuciyata ba, sannan ban taɓa sha'awar baro garin ba koda wasa.Don haka ki daina faɗin komi da zuciyarsu ba zai so ba idan sun ji, shi komi NUFIN ALLAH ne Najma. Haka ALLAH Ya NUFA cewa lokaci ya yi ne da zamu baro garin giwa ba don mun gaji da garin ko mun daina son jama'ar cikinsa ba, sai don haka ALLAH Ya so Ya kuma yi NUFIN zai kansance." Inna Mairo ta kai ƙarshen maganar tana duban yadda hawaye ke gudu akan black beauty face ɗin Najmarta. Tuni su Gwaggo sun rigasu yin gaba don su suna takawa ne a hankali Inna na rarrashin Najmar, hakan ya sanya babu wanda ya ji dukkanin kalamai da rarrashin da Innar kewa Najma. Najma ta jinjina kai cikin sanyin muryarta ta ce, "Shikenan Inna, ba zan kuma magana ba amma ki sani zan jima ina kewar su Lubah." Inna Mairo ta gyaɗa kai tana sakin ƙaramin murmushi ta ce, "Na san hakan zai faru Najmata, amma a hankali zaki rage jin kewarsu idan ki ka saba da zaman nan ɗin. Ki yi addu'a ne kawai akan Allah yasa dawowarmu nan ɗin ya zame mana alkhairy kinji ko?" Najma ta jinjina kai ba tare da ta iya cewa Inna komi ba. A haka suka isa part ɗin Gwaggon kaduna, suka sameta zaune a falo alamun jiran shigiwarsu take yi...........✍🏻




*Pay 500 in to this account number👇🏻* 

 *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:**** 

   


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* 

 *MTN* 

 *GLO* 

 *AIRTEL* 

 *9MOBILE* 

 *MONTHLY VADILITY 💃🏻*


 *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA *** DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻




#Lovestory#

#Najma#

#Aysha Ɗansabo Lemu🥰