NUFIN ALLAH! Part one story

NUFIN ALLAH! Chapter 12

by @ayshadansabo

📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻

 *Arewabooks@ayshadansabo*


 *Paid book:500*


     *Chapter 12*


 _Free page_


Gwaggo ta dubi fuskar Najma da har lokacin da alamun hawaye ta ce, "Kiyi haƙury Najma nan ma gida ne,kuma sannan ga Nasreen nan tsararki ce sai kuyi ta hidimarku ba zaki yi zaman kaɗaici da rashin abokin hira ba kinji ko?" Najma ta gyaɗawa Gwaggo kai fuskarta sam babu walwala ta ce, "Tuh!" Daga haka bata sake cewa komi ba, ta takure jikinta daga gefe guda tana sauraran hirar da Gwaggo ke jan Inna Mairo da shi.Gabaki ɗaya hankali da tunanin Najma na ga ƙauyen giwa ne, tana ayyana ko yasu Lubah zasu amshi zancen barowarsu garin giwa a rana tsaka? Wasu hawaye suka sake cika idanunta tana ƙoƙarin maidasu don bata so ran Inna ya ɓaci.


Gwaggo ko labarin bikinsu Adnan Dukku da Jiddah ta ke faman bai wa Inna Mairo, tana kuma sake bata haƙuri game da yadda ko bikin ba a sanar mata ba. Inna Mairo ta sanarwa da Gwaggo zancen zuwan Adamu drivernta da tarin abin arziƙin da Hajiya Zainab ta aika mata dashi. Gwaggon kaduna tayi shiru na wani lokaci,kafin ta dubi Inna Mairo da tsantsar mamakin da ke haskawa a saman fuskarta ta ce, "Yanzu dama zuwan da tayi ta ce in bata aronsa zata aikesa wani waje giwa ya tafi wajenki?" Inna Mairo ta gyaɗa kai cike da tabbatarwa ta ce, "Wajena ya je Gwaggo, kuma da tarin abin arziƙi babu abinda zance da irin ƙaunar da take nuna mini sai dai in yi mata fatan gamawa lafiya." Gwaggo ta jinjina kai ƙaunar surukarta na sake samum wajen zama a zuciyarta, sabida tabbas Momy mace ce ta gari da Alhaji Kabeer Dukku ya yi sa ar samu. Ta cigaba da kallon Inna Mairo tana faɗin, "Ai Zainab ta haifu Mairo, bani da abinda zan ce sai godia domin Kabeeru ya yi dace da macen ƙwarai mai ƙaunar dukkanin ahalinsa na birni da ƙauye.Don hatta mutanen Dukku hidimta musu take ba tare da gajiyawa ba.Shiyasa nake tsananin ƙaunarta a zuciyata,don tafi matar Ali sanin ya kamata, sannan ta fita son dangin miji da girmamasu." Inna dai jinjina kai tayi ta ce, "Allah sarki, gaskiya Yaya Kabeeru ya yi dace Gwaggo." Daga haka bata tofa akan irin yadda Gwaggo ke tsinan halayyar matar Yaya Alin ba, da alamu bata jin daɗinta sam! Ko kuma bata girmama Gwaggon irin yadda ita Momy ke mata. 


Sai dab da kiran sallar magriba Gwaggo ta yiwa Inna Mairo jagora zuwa ɗakin da ta ware musu ya zama mallakinsu. Bedroom ɗin na daga can ƙarshe ta wani corridor na daban bata cikin wanda ake shiga na ɗakin baccin Gwaggon ba, ta sanar da Inna Mairo cewa nan zasu ɗauka sabida yana da yalwa sosai.Inna Mairo ta dinga godia tamkar Gwaggo ta yi mata kyautar wani gagarumi. Ta shige daga cikin ɗakin tana ware idanu,tana kallon tsaruwar ɗakin da komi yake a tsare tsaf! Daddaɗan ƙamshi na tashi a cikin ɗakin don duk ranar duniya sai an gyare ɗakunan baccin duka an goge ko'ina. Najma sai daga baya tabi Inna Mairo zuwa ɗakin da aka ware musun, sosai ɗakin ya ƙayatar da ita amma ko a fuska bata nuna hakan ba. Ta samu saman sofa da ke ɗakin ta zauna ta mai zabga tagumi, don Inna Mairo ta shiga toilet ɗauro alwala lokacin da ta shigo. Koda Innar ta fito kallo ɗaya ta yiwa Najma tayi gaba zuwa wajen da ta shinfiɗa abin sallah.Ganin hakan ne ya sanya Najma tashi jiki a sake ta nufi toilet ɗin ita ma don ɗauro alwalar. 


Bayan Inna Mairo da Najma sun idar da sallar isha'i da suka jira aka yi, sai suka fito zuwa falon zuciyar Najma cike da jin haushin yadda zasu kwana basu da ko kayan canji, tunda bada shirin kwana suka zo ba bare har a riƙesu ace sun taho kenan. Gwaggo bata fito daga ɗakinta ba sai wajen takwas da rabi, suka haɗu suka ci abin dare tare da su Inna Mairo.Abinci kala biyu na sashin Gwaggo da Tabawa ce mai yin girkin, sai kuma wanda Momy Hajiya Zainaba ta aiko daga part ɗinta don karrama su Inna Mairon. Sun ci sun yi ƙat! Tare da yin godiya ga Allah, don ba ƙaramin sakin jiki Inna Mairo tayi ta kwashi farfesun kazar da aka yiwa wani irin haɗi na musamman.Najma ma da yake mai son naman kaza ce, ta ci abin ta sosai bata ƙwari kanta ba, sabida Gwaggo basu waje tayi bayan ta ci abu ba mai yawa ba don abinci kaɗan take iya ci ita.


Hira sosai suka dasa tsakanin Gwaggo da Inna Mairo. Gaba ɗaya Inna Mairo sai take ganin komi kamar almara, don abu ne bata tayi sabo dashi ba tun ƙuruciya har girma, a ce wai Gwaggo ta zauna cikin raha da sakin fuska tana hira da ita,wannan abu ne da bai taɓa faruwa ba. Suna tsaka da hiran nasu suka jiyo sallamar Nasreen da Momyn ta, Gwaggo ta amsa sallamar tana basu izinin shigowa. Nasreen ce a gaba hannunta riƙe da wani babban bag, sai Momy na biye da ita hannunta ita ma ɗauke da wani ƙaramin paper bag.Suka samu waje suna gaida Gwaggo tare da sake gaisawa da Inna Mairo cikin fara'a. Najma ta sake gaida Momynsu Nasreen tana duban ɓangaren da Nasreen ɗin ta zauna tana sakin mata murmushi. Momy ta amsa da kulawa idanunta akan Najma take tsokanarta da faɗin, "Mai kuka har kin share hawayen? Banda abinki Najma nan ma ai gida ne." Gwaggo tayi karaf ta ce, "Kema dai kya faɗi Zainab, ni gani nayi sam bata farin ciki da zancen dawowarsu nan ɗin." Najma tayi saurin duban Gwaggo tana mai ɗauke ido daga gareta ta mayar kan Inna Mairo, wacce ta zubawa Najma idanu tana jifanta da harara. Najma ita kaɗai ta ankare da irin hararar da Inna Mairo ke jifanta dashi,don haka sai tayi saurin maida dubanta ga Gwaggo tana faɗin, "Ba haka bane Gwaggo,ina tunanin ƴan uwana su Hanne ne, domin zasu ji babu daɗi idan aka ce zamu dawo nan ɗin." Gwaggo ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Karki damu zasu saba da rashinku kamar yadda kuma zaku saba, sannan zaku dinga zuwa kai musu ziyara ba wai za a rabaku da zuwa inda suke bane kin ji ko?" Najma ta gyaɗa kai cike da gamsuwa tana faɗin, "To Gwaggo mun gode!" Momy Hajiya Zainab kallon Najma kawai take yi tana jin ƙaunarta har cikin zuciyarta. Komi na Najmar birgeta yake yi, musamman nutsuwar da take gani tattare da ita.Nasreen da ke kallon Najma ita ma murmushi tayi tana faɗin, "Ai Gwaggo ni rarrashi ma nake mata ɗazu amma ko kallo ban ishe ta ba." Nasreen tayi maganar da wani irin salo na shagwaɓa, hakan yasa Najma zuba mata ido tana mamakin taɓararta ta ce, "Kiyi haƙuri gaba ɗaya hankalina ne ya tashi a ɗazu ɗin." Nasreen ta watsa hannuwa tana faɗin, "Alright! Sis ya wuce, but ni dai i like u, kuma ina so ki sake jiki damu mu zama tamkar twins ko Momy?" Momy ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Gaskiya kam da kun gama birgeni idan kuka haɗe kanku daughters ɗina." Tayi maganar da tsantsar nuna ƙaunarta ga Najma da ƴarta Nasreen. Gwaggo da Inna Mairo suka haɗa ido suka saki murmushi, kowanne cikinsu na sake jin ƙaunar Hajiya Zainab na sake yawa a zuciyoyinsu.


Hajiya Zainab ta tura bag ɗin dake gabanta wajen Inna Mairo tana faɗin, "Innar Najma ga kayanan kala 2 mun siyo, kafin zuwa gobe ayi fita na musamman don samo muku kayan sawa da sauran abin buƙatu." Inna Mairo ta janyo bag ɗin tana nunawa Gwaggo ta ke cewa, "An gode da ɗawainiya Momyn Nasreen." Nasreen ma bag ɗin da ta shigo dashi ta miƙawa Najma tana faɗin, "Sister ga naki kema kafin mu fita shopping gobe." Najma ta amsa tayi godiya mai yawa tana mai nuna wa Gwaggo ta ce ta taya ta godia.Gwaggon kaduna ta dubi Momy ta ce, "An gode ƙwarai Zainabu, Allah dai ya saka miki da aljanna.Irin yadda ki ke hidimta wa ahalin Kabeeru da zuciya ɗaya, Allah ne kaɗai zai biya ki.Allah ya yi miki albarka na gode ƙwarai." Momy tayi ƙasa da kai tana cewa, "Bakomi Gwaggo ai an riga an zama ɗaya, Allah dai ya bamu ikon cigaba da yi muku biyayya." Inna mairo tayi saurin amsawa da cewa, "Ameen." Najma ta miƙe ta nufi ɗakin da aka saukesu da bag ɗin kayan,zuciyarta na cika da jin daɗin yadda Nasreen da Momy ke nuna musu kulawa. Koda ta buɗe bag ɗin kayan bacci ne ta gani kala biyu, sai wasu haɗaɗɗun ready made boubous na material masu shegen kyau suma kala biyu. Akwai undies da bra ma kala biyu,sai perfumes masu sanyi da daɗin ƙamshi guda uku. Abu na ƙarshe da ta ciro sune kayan wanka da su brush da toopaste masu kyau. Ta dinga jinjinawa Nasreen a ranta tana mamakin yadda tayi ƙarfin halin zaɓo mata har da bra, alhali gani ɗaya tayi mata a yau ɗin. Ta ɗago bra ɗin tana juyasu a hannu, tana kuma kisima cewa tabbas zasu yi mata daidai. Toilet ta shiga ta cire kayan jikinta ta gwada bra ɗin,sai gashi ya yi mata daidai har yaso ma ya ɗan matseta kaɗan.Amma ta san da zaran an wanke sau ɗaya zai iya ɗan saki,yadda zai mata normal ba takura. Rigar baccin da ta shiga dashi kalan milk ta sanya, ya yi mata kyau matuƙa tsayin rigar ya tsaya iya guiwarta ne. Ƙirjinta da babu bra ya fito sosai, hakan ya sanya tana futowa ta ɗauki hijab ɗin da tayi sallah ta zura. Falon ta sake fita daidai lokacin da su Momy suka miƙe suna wa Gwaggo sai da safe, ta ƙarisa tana duban Nasreen ta ga irin yadda take dubanta daga sama har ƙasa.Ta saki murmushi lokacin da Nasreen ta ƙariso wajenta tana yin ƙasa da murya ta ce, "Sis kin gwada bra ɗin?" Najma kunya ya rufeta ,ta ɗan lumshe manyan idanunta tana gyaɗa ta ce, "Sunyi Sis, na gode." Nasreen ta saki smile ta ce, "Thank god! Sai tomorrow zamu fita ki darji kaya masu kyau sosai, don so nake wannan black beauty skin ɗin naki su sama product masu kyau na body wash dana shafa,ta yadda fatarki zata yi sulɓi black skin ɗin ya fiddo da asalin kalarsa."Najma ta saki murmushi ba tare da ta ce komi ba.Momy ta tayi gaba tana faɗin, "Najma gud night, ko zaki taho mu je ki kwana tare da Sis ɗin naki?" Najma tayi saurin girgiza kai alamun a'a, hakan ya sanya Nasreen tsuke fuska tana magana cike da narkewa take faɗin, "Please! Muje Najma." Inna Mairo da idanunta ke kan Najma sai tayi mata alama da ido akan ta bisu ɗin. Sai Najma ta sakarwa Nasreen murmushi tana cewa, "To muje, amma da yin safe xan dawo wajen Innata." Duka suka saki dariyar yadda Najma tayi maganar cikin ƴar shagwaɓa.Nasreen ta ja hannun Najma suka fice bayan sun yiwa su Gwaggo sai da safe.Momy ta rigasu yin gaba zuwa part ɗin nasu,su Najma suna tafe tafiya ne a hankali Nasreen na mata hira har suka isa cikin haɗaɗɗan part ɗin nasu. Lokacin da suka dangana ga ɗakin baccin Nasreen ɗin, sake baki Najma tayi tana kallon tsaruwar ɗakin.Komi na ciki white ne babu surkin kowani kala, don ita white is her favourite colour. Komi a tsare yake a ɗakin,banda sassanyan ƙamshi da sanyin air condition babu abin ke tashi a ɗakin.Ta samu saman sofa ta zauna, idanunta akan Nasreen da ke amsa call ɗin da ya shigo mata. Najma sai ta ɗauke kai daga dubanta ta mayar kan ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta na sake yaba kyawun komi na cikinsa. Daga yanayin yadda Nasreen ɗin ke wayar ta gane cewa da ƙanwarta Nabeelah ce, don ta ambaci sunanta sannan ta ji tana sanar da ita zuwansu har da koɗawa Nabeelah kyawunta. Ta sauke wayar a kunni tana blushing ta dubi Najma ta ce, "Nabeey na gaidaki, gobe ko jibi zata dawo.Ta je gidan wata friend ɗin Momy ne, age mate ɗinta tayi birthday yau." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Ina amsawa." Nasreen ta sake sakin mata murmushi ta ce, "Ki cire hijab ɗin mana Sis, kamar wata matar liman." Najma ta yi murmushi tana jin nauyin yadda za ta cire hijab ɗin Nasreen ta ga yadda rigar ta fiddo asirin cikar ƙirjinta da ƙasanta. Gane hakan da Nasreen tayi ne ya sanya ta faɗin, "Ni dai ai ƴar uwarki ce, kuma tare zamu rayu in ma baki cire yau na ganki da rigar bacci ba, watarana ma a gabana zaki sanya.So gara kawai ki fara yin komi kai tsaye,ke naga alama kunya tayi miki yawa Najma." Najma ta ɗan saki dariya tana kai hannu ta zare hijab ɗin jikinta. Nasreen ta kafeta da ido tana sake gano asalin kyawun da Allah ya yiwa Najma.Duk da kasancewarta baƙa sosai, Allah ya yi mata baiwar kyawu mai fisgar hankali da cikar halitta. Ta sauke numfashi a hankali tana faɗin, "Sis u are very black beautiful! Gaskiya na jima banga baƙar fatar da ta birgeni irinki ba. Najma tayi ƴar dariya tana ma rasa abin faɗi,don ba yau ne ta saba jin ana koɗa kyawunta ba duk da kasancewarta baƙace sosai. A karon farko Najma ta samu kanta da kwanciya akan gado da shinfiɗa na alfarma, wanda laushin katifar kawai aka bar bawa dashi ni'imace. Tunda tayi juyin farko bata kuma ba sai da kiran sallar asuba ya shiga cikin kumnuwarta.Don sosai ake jin kiran sallar da ake kwaɗashi daga cikin masallacin gidan Alhaji Kabeer Dukku dake daga waje. Ta tashi zaune tana mai karanto addu'ar tashi daga bacci, ta sauka daga gadon ta nufi tsararren toilet Nasreen da ya gaji da haɗuwa.Alwala ta ɗauro ta fito sannan ta tada Nasreen ɗin ita ma.Sai dai tana buɗe ta ɗaura akan Najma sai ta sake gyara kwanciya tana faɗin, "Ina period Sis,yi naki sallar ki dawo mu cigaba da bacci." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Ok to!" Daga haka ta nufi wajen sallar da aka saita shi ya kalli gabas, ta ɗauki hijab akan sofa ta saka ta tada sallar.


Sai da ta gama yin azkar ɗinta gaba ɗaya sannan ta koma gado don sake kwanciya,amma abinka da rashin sabo duk yadda taso bacci ya sake ɗaukanta abin ya gagara. Ta riga ta saba aikin bauta a giwa, sam bata san wani zancen a koma baccin safe bayan anyi sallah ba. Haka ta dinga juyi tana tuno giwa da ayyukan da take gabatarwa a lokuta irin wannan. Wani abu ya tokare ƙirjinta, tana ji kamar ta buɗe ido ta ganta tana suyan ƙosanta ana mata layi ana saye. Wajen ƙarfe bakwai da rabi ta sakko daga kan gadon, don ta san babu wani bacci da zai ɗauketa don bata saba da hakan ba. Falo ta fito ta zauna tayi shiru tana faman tunanin mai zata yi ne? Ta miƙe tsaye tana nufan hanyar da taga mai aikin Momy jiya ta fito daga wajen, ta cigaba da takawa har ta shige cikin corridor ɗin. Daga can ciki ta fara jin karakainan masu aikin, sai ta kutsa kai ciki bakinta ɗauke da sallama. Rabi da Laure masu aikin Momy suka amsa sallamar suna duban Najma cike da mamaki.Ta samu waje tayi tsaye tana gaida su,don Rabi dattijiyace Laure ce kawai matashiya da bazata gaza shekaru ashirin da biyar zuwa da shida ba.

Tambayarsu Najma tayi akan ko akwai aikin da zata iya kama musu? Rabi ta dubeta da kulawa tana faɗin, "Baiwar Allah da dai kin koma kin yi kwanciyarki kada Hajiya ta tuhumemu da sanya ki aiki." Najma tayi saurin girgiza kai tana sanar dasu cewa, kwanciyarce ba za ta iya ba don bata saba da ita ba, gara dai su bata wani abin ta kama musu matuƙar hakan ba laifi bane. Ganin ta dage sai Rabi ta bata ƙullun ƙosai da suka niƙa a blander ta ce ta buga, sabida Alhaji Kabeer Dukku mutum ne mai son yin karin safe da kayan gargajiya bai damu dasu chips ba. Don shi ake yin ƙosai da su waina duk safiya, matuƙar yana gari ba ya koma Abuja ko ya bar ƙasar bane.Ga tsananin mamakin Rabi gani tayi Najma har ta fita ƙwarewa wajen iya sakin ƙosai a mai,sannan yanayin yadda ta ƙarawa kullum ruwa ta ce zai cushe a yadda suka barsa. Sai suka ga tabbas hakan ne kuwa, domin kwasan farko da soya suaa ga irin taushin da ya yi.Kafin suce kwabo ta kammala soya lafiyayyan ƙosan da ya yi taushi matuƙa, ta juye shi a ƙawataccen kular da ake zubawa Daddy Kabeer Dukku a ciki. Ta wanke komi tas da tayi amfani ta dashi, ta kife a wajen adana kayan da aka wanke.Ta koma gefe guda tana kallon yadda suke yin soye-soyen su chips da haɗin lafiyayyen sauce irin na ƴan gayu. Take ƙaunarta da son girki ya motsa, ta dinga ayyanawa a ranta dolema ta riƙa zuwa tana taya su aiki, don ita ma ta koyi abubuwan da bata iya ba.Wajen ƙarfe takwas da rabi suka kwashi warmas ɗin da aka zuba komi ciki suna kai wa dining suna aje wa, na ɓangaren Daddy sun shirya shi a babban tray an aje daga gefe guda.Sabida basa shiga ɓangarensa, Momy ce da kanta ke zuwa ta ɗauka, wasu lokutan ma da kanta take tashi tayi masa girkin. Shi ne yake hanata tashin safen a wasu lokutan da yawa, sai ya zamana tafi amsar ragamar girka masa luch ko dinner.


Ɗakin Nasreen Najma ta koma ta tadda Nasreen ɗin ta shiga wanka. Ta samu waje bisa sofa ta zauna tana ƙarewa ɗakin kallo a hasken safiya da ya haske ɗakin, domin windows ɗin a buɗe suke. 


"Sis ina kika shiga na tashi na ga baki a ɗakin?" Nasreen ta wurgawa Najma tambayar lokacin da ta fito daga bathroom. Najma ta saki ƙaramin murmushi ta ce, "Ina kitchen wajen masu aiki, na je taya su wani abin.Kinsan mu ƴan karkara ba muyi sabo da komawa baccin safe ba sai ku ƴan gayun birni." Yadda Najma tayi maganar bilhaƙƙi sai ta bai wa Nasreen tausayi. Ta narke fuska tana duban Najma ta ce, "Amma ai yanzu dole ki saba tunda kin dawo nan ɗin." Najma ta sake yin mirmushi tana cewa, "Bari in shiga wankan nima, idan yaso ina fitowa sai na tafi wajen Innata tunda kayan da zansa na can." Bata jira cewar Nasreen ba ta zare hijab ɗin jikinta ta nufi toilet.


Nasreen bata barta komawa part ɗin Gwaggo ba, sai ta bata wata rigarta ta saka na wani haɗaɗɗan batik kalar red and green.Ɗinkin free boubou akai ma rigar hakan ya sanya ya yiwa Najma daidai, sabida tafi Nasreen cikar jiki sosai. Tare suka nufi falo sukai breakfast a dining, bayan sun kammala Nasreen ta ja hannunta suka nufi side ɗin Daddynsu. Cikin sakin fuska da fara'a yake amsa gaisuwar Najma tare da miƙa mata hannu alamun ta isa garesa,ta isa ta zauna kusa da shi yana tambayarta yadda suka tashi. Najma ta gaida Momy Hajiya Zainab cikin ladabi,tana mai yaba kyawun da Momyn tayi cikin atamfar jullious holland da ke jikinta.


Basu jima a wajen Daddy ba suka fice zuwa part ɗin Gwaggo.Sun samu Inna Mairo tare da Gwaggo sun kammala karyawa kenan, suna zaune suna hira cikin annushuwa.Har ƙasa Najma ta tsuguna ta gaida Gwaggon kaduna, Gwaggo ta amsa da sakin fuska tana tambayarta ya baƙunta? Najma ta yi murmushi tana ƙin cewa komi. Inna Mairo ko kallon Najma take yi tana yaba kyawun da kayan Nasreen suka yi a jikinta. Nasreen ta gaidasu Gwaggo ita ma cikin ladabi, tana mai duban Gwaggo ta sanar da ita fitan da zasu yi da Najma zuwa yin shopping zuwa ɗan anjima kaɗan.


Inna Mairo a part ɗin Momy suka yi lunch, don tunda ta je gaida Yaya Kabeeru Momy ta hanata komawa part ɗin Gwaggo,suka zauna suna hiransu cikin nishaɗi. Labarin auren su Jiddah da Adnan Momy ke bai wa Inna, tana sanar da ita cewa Jiddar wani ɗan majalisa ta aura suna zama a Abuja.Amma yanzu haka ma bata ƙasar sun tafi yawon honey mun da mijinta, Shi kuma Adnan yana port harcourt da matarsa,a can yake aiki da ma'aikatan man fetur na ƙasa wato (refinery). 

Misalin biyu na rana Nasreen ta kwashi su Momy da Inna Mairo da Najma cikin ƙamar motarta KIA suka fita yiwa su Innar shopping,tunda ya kasance basu zo da kaya ba dole a nema musu kayan sawa da sauran kayayyaki na buƙata. Suna tafe Najma da ke zaune a front seat ta yane kanta da ƙaramin veil da Nasreen ta bata, tana faman kallon yadda Nasreen ɗin ke tuƙa motar cike da ƙwarewa.


Siyayyan kayan sawa masu uban yawa dasu kayan shafa,zuwa su underwears kaɗai sun lashe kuɗi masu yawa. Daga Najma har Inna Mairo mamakin irin kaya masu tsada da ake ɗibar musu sukai tayi, bama kamar Najma da Nasreen ke jidarwa komi na gayu da ta ga zai dace da ita. Hatta body wash na wanka wasu irin product masu tsada na african black queens ta ɗaukar mata, waɗanda zasu gyara fatarta su fiddo asalin kyawun black skin ɗinta. Basu koma gida ba sai can yamma, domin sun biya gidan wata ƙawar Momy da ke saida ɗinkakkun kayan sawa na mata,aka zaɓarwa Inna Mairo wasu dogayen riguna masu kyau da tsada.


A gajiye suka shigo gidan suka nufi ɓangaren Gwaggo gaba ɗayansu, don nuna mata siyayar da aka yo ɗin.Sabida Momy ta gama sanin halin surukartata, ta kuma karanceta tare da bida ita duk ta yadda take so. Gwaggo ta yaba da siyayyar har ma da cewa ba a siyawa Inna Mairo kaya masu yawan da tayi zato ba,don haka zuwa in an kwana biyu ita ce da kanta zasu shiga kasuwa da Inna Mairo ta zaɓi wasu kayan a bada ɗinki.Momy ta dinga dariya tana sanar da Gwaggo cewa ai dama wannan somin taɓi ne aka yi siyayyar, za a sake fita idan sun sake natsawa an je giwa an dawo. Inna Mairo da Najma suka dinga zubawa su Gwaggo godia tamkar ba zasu daina ba, har sai da Gwaggo ta dakatar dasu ta ce godiyar ya yi yawa ai abinda ya dace ne aka yi. Nasreen da Momy suka nufi part ɗinsu yayinda Najma ta maƙale wajen Inna Mairo, duk yadda Nasreen taso su wuce tare ƙi tayi sai ta ce mata sai zuwa dare zata je mata hira............✍🏻




*Pay 500 in to this account number👇🏻* 

 *0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank*

*OR* 

 *PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻

 *8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM* 

 *ACCOUNT NAME:OPAY*



 *Evidence of payment to this number:**** 

   


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻* 

 *MTN* 

 *GLO* 

 *AIRTEL* 

 *9MOBILE* 

 *MONTHLY VADILITY 💃🏻*


 *DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA *** DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻





#Lovestory#

#Najma#

#Aysha Ɗansabo Lemu🥰