ASHRAF: beauty meets ugly

Chapter 03

by @azizat


03




Da Asuba kamar kullum Dad ne ya fara tashi daga bacci. Ya shiga banɗaki yai alwala ya fito. Yana fitowa ya ga Mom ta tashi zaune tana mammatsa wuyanta gashinta yayi buzu-buzu.


Tura kekensa yai zuwa gefen gado yai mata sallama. Hannunsa ta kama ta kissing sannan ta gaida shi. Duk da dai kusan gaba ɗaya rayuwarta tayi shi ne a Nigeria, har yanzu akwai al'adunsu na Larabawan Lebanon da bata dena ba saboda ya riga ya bi mata jiki.



"Ki je ki taso Ashraf ya same ni a falo"


Kafin ya gama maganar ma ta miƙe. Ta ɗauki robe ɗin rigan baccinta ta fita, a staircase ta ƙarisa ɗaura robe ɗin yayinda take ƙoƙarin ɗaure dogon gashinta mai tsantsi.


A hankali ta buɗe ɗakin Ashraf ta shiga. Kamar kullum bata tsammanci zai tashi daga barci da wuri haka ba sai kuma ta ga gadonsa wayam ba kowa.


"Ashraf Dad ɗinka yana jiranka a ƙasa" ta furta da ɗan ƙarfi.


Har zata fita ta lura ba fa alamar motsi a banɗaki. Ta je bakin banɗakin ta ƙwanƙwasa.


"Ashraf" "Ashraf" amma shiru.


Ta gwada buɗe ƙofar banɗakin taji shi a buɗe.

 Idanunta ta waro waje ganin Ashraf baya banɗakin. 

To ina Ashraf ya shiga? ta tambayi kanta.


Tabbas bayan abinda ya faru jiya idan Dad ya gane Ashraf bai kwana a gida ba wani tashin hankalin za a kuma shiga yau a gidan nan.


Ta sauko ƙasa gwiwarta a sace ba tareda ta san ƙaryar da za ta faɗawa Dad ba.


Dad yana zaune a kekensa yana jan carbi duk da ba duka wutan falon aka kunna ba kana iya ganin baƙin carbin daya ke ja.



"Erm, Sayyidi, inaga Ashraf..."


Ɗaga mata hannu yai dan ya riga ya san kwanan zancen tunda ba yau Ashraf ke ƙin kwana a gida ba.


Ya ɗan juyar da kekensa yace " na tafi masallaci"


Mom ta zo da sauri ta buɗe masa ƙofa ya fita.

Yana fita ta sauke ajiyar zuciya. Tabbas idan Ashraf bai nutsu ba kwanan nan hawan jini ne zai kasheta. Ita kanta ta gaji da kare shi a wajen mahaifinsa.


Tana shiga ɗaki numbar wayarsa ta fara kira amma duka numbobinsa uku a kashe suke. Hatta special numbarsa da Dad bai san da shi ba ta kira amma switch off.


Ya Allah! Ta faɗa tana zama bakin gado.



Dad bai dawo daga masallaci ba sai ƙarfe shida da rabi.


Yana zuwa Mom ta haɗa masa ruwan zafi ta taimaka masa yai wanka. Lokacin da suka fito yace wa Mom a shirya masa abin karyawa da wuri zai je office.


Mom ta kalle shi cikin rashin fahimta. Baya zuwa office sai Monday na farkon wata da kuma Friday na ƙarshen wata. In dai yaje ba a waɗannan kwanaki ba to wata matsala ne ta taso ko kuma dai wani taro ne aka shirya na musamman.


Mutane uku ke da ragamar tafiyar masa da Kamfani. Ashraf, Umar da kuma Tahir mijin Zulfa.



"Akwai board meeting ne yau?" Ta tambaya cike da fargaban hasashen da take a zuciyarta.



"Zan sauke Ashraf a matsayinsa"


"What!"


"Uyuuni Dan Allah kada ka yiwa Ashraf haka. Zan masa magana, he'll change, i promise"



"Sarah" ya kira sunanta cikin sanyin murya.


"Idan Ashraf ya cigaba da tafiya a haka ba rayuwarmu zai cutar ba, rayuwarsa zai cutar. Ba zamu cigaba da zama da shi har abada ba. Idan har a shekaru talatin da ɗaya bai yi hankali ba ban san yaushe zai yi ba."


"Ina roƙon ƙi Sarah, kada ki shiga cikin hukuncin da zan masa"


Ta sauke numfashi. Idan Dad yai magana irin wannan to da wuya ya chanja ra'ayinsa.


"Sayyidi wa zaka bawa kamfanin kenan? Umar?" Ta faɗi sunan ranta na ƙuna dan ba ƙaramin ƙasƙanci bane a ce an cire Ashraf an bawa ɗan direba shugabancin kamfani.


"Idan fa ka cigaba da nunawa Ashraf cewa Umar ya fi shi ba zai taɓa maka biyayya ba.


"Sayyidi ni ina ganin a bawa Ashraf wani damar. Allah zai gyara. Zai yi aiki yadda ya dace. Ashraf shine ɗan da muka haifa. Ba zai yiwu mu so ɗan wasu sama da namu ba"


Dad ya girgiza kai. Mace kenan. Shi abinda yake hangowa daban ita abinda take gani daban.


Ashraf ɗansa ne, amma a irin halin Ashraf ya ƙwammace ya bawa bare ragamar dukiyarsa.



Mom dai ta fita tana ƙuƙƙuni. 

Abin ya dameta ta ɗau waya ta kira Hajiya Halima ƙanwar Dad ta labarta mata abinda yayanta ke shirin yiwa ɗansu.



Da Mom da Hajiya Halima duk kusan halinsu ɗaya ne. Shiyasa ma a cikin 'yan'uwan Dad babu wanda suka shaƙu da Mom sama da Hajiya Haliman.


Ta wani fannin ma har gara Mom dan ita ba laifi zuciyarta akwai ɗan tausayi amma Hajiya Halima sam idan kai ba nata bane to kallon walaƙantacce zata maka, sahalewarka ɗaya ka zamto kana da kuɗi ko kuma ka fito daga tsatson kuɗi.



Hajiya Halima ta bawa Mom haƙuri akan zata yiwa Dad magana. Bai isa ya saka ɗan Driver a matsayin shugaban kamfaninsa ba.



Da haka suka rabu.


Koda ta serving Dad breakfast kasa cin komai tayi. Ita gashi bata san ina Ashraf yake ba ga kuma maganar da Dad ya ɗauko wai zai cire Ashraf ɗinta a matsayin CEO na kamfaninsa.


Dad kam ko a jikinsa a nitse yake cin abincinsa duk da kuwa zuciyarsa cike take da baƙin cikin Ashraf, amma yana ƙoƙarin mamaye baƙin cikinsa da yiwa Ashraf ɗin addu'a a koda yaushe.


Gashi dai 'ya'ya uku kawai Allah ya bashi, amma guda ɗaya yana bashi ciwon kan da ko mai 'ya'ya talatin ba shi da shi.


Da Su'ad namiji ce da ya yi sa'ar samun ɗa na gari sai kuma tazo a mace. Gashi aure ya cillata har ƙasar Germany. 



Ita kuwa Zulfa. To! sai dai hamdala kawai.


Ga Ashraf kuma daya kamata ya zamo masa sanyin idaniyarsa, ya zamo sanadin kukansa.

Kullum ya ɗaura goshinsa a ƙasa cikin sujuda kaso hamsin na addu'o'insa akan Ashraf yake ƙarewa.



Ƙarfe bakwai da minti arba'in na safe Dad ya fita a gida zuciyarsa cike da yaƙinin hukuncin daya yanke shine dai dai.




***




Da sauri Ashraf ya fito daga hotel ɗin zuciyarsa na tararradin mi zai faru idan Dad ya gane bai kwana a gida ba.

Sai daya shiga motarsa tukunna ya kunna wayarsa. Ganin ƙarfe takwas na safe ya sake shiga ruɗani. Yanzu kam Dad ya sani sai dai kawai ya nemi ƙaryar da zai kare kansa.


Ganin idan yace zai koma gida lokaci zai wuce kuma zai iya haɗuwa da Dad a gida sai kawai ya wuce office direct.


 Idan Dad ya ritsa shi cewa zai yi da sassafe ya fita saboda anyiwa wani abokinsa rasuwa. Koma dai wani ƙarya ne zai yi dan ya goge laifinsa a wajen Dad. In har ba Kamfani ta farfaɗo daga asarar da aka tafka a investment na ƙarya da yai ba shi da Dad zaman mage da ɓera zasu dinga yi.


Yana shigar da motarsa parking space na kamfanin ya ga motar Dad a wajen.

Ya duba screen ɗin wayarsa.

Yau dai ba farkon wata bane. Mi Dad ya zo yi?



Jiki a sanyaye ya fito daga mota. Ba tareda wani confidence ba ya shige cikin kamfanin, kwata-kwata yau babu flirty smile daya saba yiwa ma'aikata, fiskarsa a ɗaure take cike da wasu-wasi.




Yana haurawa sama ya haɗu da Mr Solomon wanda yace masa Dad yana board meeting.


Da sauri Ashraf ya ƙarisa ɗakin taron. Ba dai wani abun Dad ya shirya masa ba.


Yana buɗe ƙofar ɗakin idon kowa ya yo kansa. 

In dai kaga taro irin wannan to ba ƙaramin major decision za a ɗauka ba.


Suna haɗa ido da Dad yai saurin saukar da kansa ya wuce da sauri ya je ya zauna kusa da Umar yana faɗin "sorry i'm late"


Tunda Ashraf ya zauna sai wajen yai tsit aka kasa cigaba da magana.


Dama wani mai suna Mr Wasiu ke maganar kafin Ashraf ɗin ya shigo.



"Mr Wasiu ka cigaba da bayaninka" Dad ya faɗa


Mr Wasiu yai gyaran murya yace "kamar yadda nake faɗa inaga Mr Tahir Sambo shi ya dace da acting CEO zuwa lokacin da za a naɗa sabon CEO.


 "Mr Tahir has being working for this company for over 15yrs now. Wannan kaɗai ya dace a bashi wannan dama"


Ashraf ya tashi a hargitse.


"Dad mi kake shirin yi? Dad are you firing me?" "You can't do this to me Dad."'

" Dad?" " Dad?"




"Mr Ashraf ka zauna" Dad ya faɗa ba tareda ya birkita da yadda Ashraf yake a rikice ba.



"Dad i'm your son. Dad ka riga kayi min alƙawari idan na dawo Nigeria zaka bani kamfaninka. Dad you made me quit my music career. Dad..."



"Mr Ashraf!" Dad ya daka masa tsawa.


Ashraf ya haɗiyi sauran kalamansa ya ɗau wayansa dake kan table ya tura kujerarsa da ƙarfi ya fice daga ɗakin taron.


Dad ba zai masa haka ba. Not after alƙawarin da ya masa na cewa zai sake masa komai idan ya bar yin waƙa ya dawo Nigeria.


Ba zai yarda da wannan ba. Idan aka saka Tahir ko Umar a CEO ba ƙaramin cin fuska bane a wajensa.

Taya ma zai fuskanci abokanansa daya jima yana taka musu ƙafa saboda yana da matsayi sama da su.


Yana shiga mota ya naushi steering zuciyarsa zafi kaman an cinna mata wuta.


Tun kafin ya bar haraban wajen ya shiga kiran numbar Mom ko da saninta ake shirin ci masa fuska.




***



Yau tun da safe suke aiki amma har yanzu basu gama ba. Sabbin littattafai aka kawo musu basu gama sorting ɗinsu ba.

Dan ma dai Baba na nan dan haka kowa aiki yake tuƙuru saboda a tabbatar an kammala komai an shigar da komai cikin computer.


Qayyisah na zaune tana shigar da record cikin computer wani coursemate ɗinta ya kirata.


Tana ɗaukan kiran yace " Zee Qayyisah kina da labarin an buɗe portal jiya kuwa. Yanzu na gama cika nawa"


"Ina da labari amma ban cika ba tukunna inaga sai gobe"


"Ki samu ki cika kwana huɗu fa kawai suka bayar"


"Zan cika, nagode"



Tana ajiye wayar Baba ya shigo office ɗin. Jikinsa ya jiƙe da gumi, fiskarsa kamar wanda yai alwala.



"Sannu da aiki Baba"


"Yawwa sannu Zainab. Mi ake cikawa ne?"


"Wai registration na tafiya service ne"


"Ya abin yai sauri haka yaushe kika karɓo result"


"Baba bai yi sauri ba fa. Wannan strike ɗin ne ai ya maida komai baya"


" ina kike son cikawa ne?.


"Ko Bauchi zaki cika saboda ki dawo kusa da gida?"


Qayyisah ta amsa da uhum. Ba zata iya buɗewa Baba inda take so ba dan ta san ba zai taɓa yarda ba. Tana furta sunan Abuja zai ce mata a'a.


Da dare kowa ya zubawa Qayyisah ido lokacin da take ƙoƙarin cika form a NYSC portal.



"Allah yasa a kaiki Maiduguri" Aliyu ya faɗa yana dariya. Zaidu ya talli kansa yace "baka da kai"


Anty dake kallo tace " ai Zainab sai Abuja, Abuja kopa wee"


Baba yace "ku yi mata addu'ar alkhairi. Allah ya fimu sanin inda alkhairinta yake"


"Baban Zainab ai akwai alkhairi a Abuja. Abuja ai kaman gida ne, gidan kawunka ai kaman gidan Ubanka ne"


Da gayya tayi maganar tunda ta san irin gabar dake tsakanin Baba da Alhaji Sani Muƙaddas wan matarsa.


Baba yai shiru da maganar ya adjusting reading glass ɗinsa ya cigaba da karanta littafin dake hannunsa.


Qayyisah ta kalli Anty Fa'iza sannan ta maida kallonta ga Baba wanda ta sani saboda kawaicin akwai yara a wajen yasa shi yin shiru da maganar da Anty Fa'iza ta faɗa.


Har yau tana mamakin irin soyayyar iyayenta.


Soyayyarsu typical example ne na abinda ake cewa 'idan ba shi ba sai rijiya' 


Hawwah Muƙaddas ta jefar da duk wani gata da jin daɗi da take da shi saboda soyayya. Wannan yasa har ta koma ga Allah babu shirin kirki tsakaninta da 'yan'uwanta musamman ma da yake akwai wanda ake so ta aura a gida amma tayi biris tace Aminu Mailittafi take so.


Sai da Allah yai mata rasuwa ne ma suka sake nuna tsanarsu ga Baba ta hanyar ce masa shi ya kashe musu 'yar'uwa.


Bata son tuno labarin rasuwan Ummanta dan yanzu zata fara hawaye.

Ta sauke ajiyar zuciya tareda maida hankali kan abinda take yi.


Koma ina aka turata ma Allah yasa nan ne alkhairinta. 

Maganan yin service a Abuja kam babu shi in dai ana son zaman lafiya....




©AzizatHamza2023