Page:1
by @maidambu41
SANIN GAIBU...!!
_Sai Allah_
ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023
*Mai_Dambu*
Page:01
Sadaukarwa ga Sa'adatu Ambassador, Maman Rumaisah, Shafin gabaki daya ta ce , Na gode da karamcin ki tare da gudummawar da kika bawa labarin nan Allah ya saka da alkhairi 😍🌹
_Shimfida_
"Ummina ki min addu'a!" Ya fada cikin matsanancin azaba, hawaye na zuba mata ta ce mishi. "Abu Turab naga gawar Abubakar ban yi kuka ba, na ga gawar Umar ban yi kuka ba, Abu turab me yasa nake kuka akan ka? Me yasa nake kuka???" Mother tears.......!
Emir of ilorin palace.
𝗔𝘀𝗮𝗹𝗶𝗻𝘀𝘂
Wadanda suka fara zama a Ilorin su ne Baruba wadanda suka zauna a can tsawon shekaru kuma suka dauki yankin nasu ne; sun tafi ba tare da sanin dalili ba. Sai kuma Ojo Isekuse, wani basaraken Yarabawa, wanda ya zauna kusa da dutsen kaifi inda mafarauta suka taru suna wasa da kayayyakinsu. An yi wa Ilorin suna ne bayan da dutsen kaifi da har yanzu yake wanzuwa. Ana zargin Ojo Isekuse ya fita ne bayan ya yi lalata da ‘yarsa, kuma wani dangi mai suna Asaju ya sauka a kusa da dutsen da ake yankan. Bayan Asaju ne mutane da dama suka zauna a kauyuka masu zaman kansu daban-daban da ke kewayen yankin da ake kira Ilorin a yau.
A farkon karni na 19, Ilorin yana arewa maso gabashin daular Oyo, yana da yawan Yarabawa, Hausawa da Fulani. Ya zama hedikwatar wani Janar na Oyo, Afonja, wanda ya kasance sarkin yakin da kujerar Ilorin ce kuma wanda daga baya ya gudu don guje wa yakin kunar bakin wake da aka tura shi ya kashe shi bisa ga umarnin Alaafin na Oyo. Shi kuma wani malamin addinin Islama mai suna Shehu Alimi, wanda ya gudu daga Oyo saboda muzgunawa kungiyar asiri ta Ogboni.
Shehu Alimi da Afonja sun kulla kawance domin yakar sojojin Oyo da ke gaba sannan suka fatattaki sojojin Oyo a yakin farko. Alaafin ya yanke shawarar tura wata babbar rundunar da ta tabbata za ta kashe Afonja tawaye tare da kawar da malamin, Shehu Alimi, wanda ya ba da tallafin soji ta hanyar gayyatar Jama’a. Dakarun Jama’a da na Afonja sun kai wani harin ba-ta-kashi a Oyo-Ile, hedkwatar tsohuwar Daular Oyo, inda suka kona ta.
Ilorin ya zama babbar siyasa da soja bayan faduwar tsohuwar Oyo. Ba tare da sunan shugaba ba, Afonja da Alimi sun ba da jagoranci ga mutanen da ke zaune a yankin. Afonja da Salih Janta, wanda kuma ake kira Shehu Alimi, sun samu kyakkyawar alaka har zuwa lokacin da Alimi ya rasu a lokacin tsufa.
Bayan rasuwar Shehu Alimi, an yi takun-saka da sarautar Ilorin, gari ne mai tasowa. Alfas sun so kafa Halifancin Musulunci bisa ilimi, yayin da Afonja ke shirin sake kafa cikakken mulkinsa, amma Abdulsalam ya fito da taimakon mayakansa. Suna da kwakkwaran iko da Jama'a wanda shi ne mafi yawan sojoji a Ilorin. An kashe Afonja ne a lokacin mulkin Abdulsalam, a lokacin da wata hatsaniya ta barke tsakanin sojojin Yarbawa da Jama’a, wanda ya haifar da matsi na Afonja. An dakatar da addinin Yarbawa da Egungun a Ilorin saboda wannan lamarin. Ilorin ta zama masarautar Khalifancin Sakkwato.[1]
Na wani lokaci, Ilorin ta kasance babbar cibiyar cinikin bayi. A da, an fi tura bayi zuwa arewa ta hamadar sahara, amma yanzu ana tura su kudu ta kasashen Yarabawa zuwa bakin teku don samar da bukatu daga Amurka, Indiyawan Yamma, da Brazil. An kwashe bayi daga kasashen Ibo zuwa gabas da kuma garuruwan Yarabawa da aka ci da yaki, da kuma daga yankunan da ke gaba zuwa arewa, ana cinikin tufafi da sauran kayayyaki.
Ilorin ya ci gaba da fadada kudu har sai da aka duba shi a cikin 1830s ta ikon girma na Ibadan, jihar Oyo. Sojojin dawakan Ilorin ba su da wani tasiri a cikin dajin da ke kudu, kuma a cikin shekarun 1850 Ibadan ta sami damar samun bindigogi daga ’yan kasuwar Turawa a bakin teku.[1] Kamfanin Royal Niger ne ya mamaye babban birnin kasar a shekarar 1897, sannan kuma aka shigar da filayensa cikin yankin Arewacin Najeriya da Ingila ta yi wa mulkin mallaka a shekarar 1900, duk da cewa masarautar ta ci gaba da gudanar.
𝗗'𝗮𝗸𝘂𝗻𝗮 𝘂𝗸𝘂 𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝗴𝗮𝗷𝗶 𝘀𝗮𝗿𝗮𝘂𝘁𝗮𝗿.
Saboda irin tarihin da ya ke da shi na musamman na Ilorin, na farko a matsayin Yarbawa daga cikin Daular Oyo, sannan a matsayinta na fulani mai mulkin Halifancin Sakkwato, tana da al’adar yin sarauta wadda ta kasance gauraya da al’adun gargajiya da aka samo daga bangarorin biyu. Duk lokacin da sarautar Masarautar (wadda ke hannun Fulani zuriyar Shehu Alimi) ta kasance babu kowa, wakilin kowace kwata a masarautar wato; Balogun Gambari (Hausa), Balogun Ajikobi (Yarabawa), Balogun Fulani (Fulani) da Balogun Alanamu (Yoruba) - tare da shugaban gidan sarautar Afonja, Mogaji Aare, da kuma babban hakiminsa mai suna Baba. Isale na Ilorin - a taru domin zabar sabon sarki tare da nada sabon sarki, bisa amincewar gwamnan jihar Kwara. Sannan an ba wa Balogun mafi dadewa sarautar Balogun hudu sarautar Balogun Agba, wanda hakan ya sa ya zama na biyu a kan Sarkin Ilorin. Dukkan Balogun na da gundumomi da suke gudanarwa a madadin sarki.
Akwai kuma sarakunan gargajiya da kowanne ake kiransa Daudu (ko Hakimin Lardi). Suna aiki ne a matsayin hakimai masu wakiltar sarki a garuruwan dake fadin masarautar Ilorin kamar su Afon, Bode Saadu, Ipaye da Malete, da dai sauransu.
Lakabi masu daraja a cikin.
𝗦𝗮𝗿𝗮𝗸𝘂𝗻𝗮𝗻 𝗠𝗮𝘀𝗮𝗿𝗮𝘂𝘁𝗮𝗿
Masu mulki
Gyara
Sarakunan Masarautar Ilorin:[3]
Fara Ƙarshen Mulki
1824 1842 Abdusalami dan Salih Alimi
1842 1860 Shita dan Salih Alimi
1860 1868 Zubayro dan Abdusalami
1868 1891 Shita Aliyu dan Shittu
1891 1896 Moma dan Zubayru
1896 14 Janairu 1914 Sulaymanu dan Aliyu
1915 Nuwamba 1919 Shuaybu Bawa dan Zubayru
17 Fabrairu 1920 Yuni 1959 Abdulkadir dan Shuaybu Bawa
30 Yuni 1959 1992 Zulkarnayni Gambari dan Muhammadu Laofe Dan Bawa "Aiyelabowo V"
1992 Agusta 1995[4] Mallam Aliyu dan Abdulkadir
1995 Zuwa Yau Ibrahim Sulu- Gambari
𝗠𝗮𝘀𝘂 𝗠𝗮𝗸𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗺𝗮𝘀𝗮𝗿𝗮𝘂𝘁𝗮𝗿
Masarautar dai ta shaidi irin karramawa ga fitattun ‘ya’yan Masarautar da Sarki na yanzu ya yi. Wadannan sunaye ne da aka ba su;[5]
Waziri of Ilorin Emirate
Turaki of Ilorin Emirate
Zanan of Ilorin Emirate
Dan Iyan of Ilorin Emirate
Grand Mufti na Masarautar Ilorin
Madawaki of Ilorin
Malami Ubandoma of Ilorin Emirate
Tafida of Ilorin Emirate
Shettima of Ilorin Emirate
Mutawali of Ilorin Emirate.
August -12- 2009
*10:30pm*
_Hawaye ne ya zubo mata, sakamakon hango shi da tayi yana wucewa duk da kasancewar dare ne amma hasken da ya haska harabar gidan ya hasko mata shi, yana tafiya cikin ruwa dauke da lema, da alamu ita yake nima. Tirjewa tayi mutumin da ya shake wuyarta ya kuma matseta, tare da jin wani bakon al'amari yana ratsa jikinta, cikin tsannanin azaba da masifar da bata tab'a haduwa da shi ba. Wani irin ajiyar zuciya take saukewa, tana jin kamar ta mutu ta huta. Haka ya gama keta alfarmarta sannan ya tashi a kanta, duk da bata ga fuskar shi ba, sai dai kamshin turaren shi ya tabbatar mata da waye a tare da ita. A hankali ta yunkura zata mike suka sake mai da ita, haka su hudu nan suka keta alfarmarta. Kafin daga bisani suka shake ta, sai da suka ga bata motsi sannan suka kyale ta_
******************************************
Sokoto State... Binji LG
Maikulki
Rabewa gefe tayi, ta dauki kokonta ta koma can jikin bango ta tsuguna tana sha hawaye na zuba mata. D'ago fararren idanunta tayi tana kallon Mahaifin su da ya shigo. Yana kallon tsakar gidan, "wallahi duk lokacin da na kalli Sa'adatu sai naji kunya ta kama ni, musamman idan ta fita cikin mutane ana nuna mu. Duk sai naji na muzanta. Shi yasa bana kaunar tana fita da shegen idanunta a wurin." Ya fada yana tsaki. "Larai zuba min abin karyawan nan, kuma ki tabbatar sun shirya su tafi makarantar idan Allah ya jarabce ka da haihuwar bakar ƙaddara babu yadda ka iya, yanzu don Allah taya zata fahimci karatu." Tab'e baki yayi yana kallon matar da ta fito daga madafin. Duban inda yarinyar take tayi na dan lokaci kafin ta ce mishi. "Bawa baya tab'a kaucewa ƙaddaran sa, Malam itama ba sayawa kanta tayi ba, duk da haka ba zai saka mu tsane ta." Ta fada tana wuce shi. Tsaki yayi yana faɗin."haka kawai an tashi an haifa min nakasashiya a cikin Yarana." "Sai ka gayawa Ubangijin da ya baka ita ka ji" ta bashi amsa, daukar ƙara yayi nufi Yarinyar.
Ganin shi dauke da kara yasa ta sake kofin kunun hannunta, ta mike zare mata idanu yayi cikin masifa ya kira Yan uwanta. "Harirah, Rabi" fitowa suka yi sanye da Uniform, fari da hijab din su iya cinya. "Na'am Baffa" "ku bata kayanta itama ta biku tunda abin na munafunci ne ta tafi tunda na san ba gane kome zata tab'a yi ba." "Wai Malam meye Sa'a ta maka ne? Makarantar nan dai wallahi ko kana so ko baka so dole ta je" "Assalamu alaikum, iyyi lafiya?" "Yaya wa'alaikumunsalam sallama, Alhamdulillahi gara da kika dawo wallahi na rasa yadda zan yi da Malam akan Sa'a " kallon shi matar tayi,.kana ganin fuskarta kasan ranta yayi azababben ba'ci." Gyada kai tayi sannan ta nufi wurin Yarinyar me suna Sa'adatu" "Tashi ki shirya yanzu na saka hansiya ta dinka miki kayan ki." Murmushi tayi tana share hawayen ta." "Innah laminde zamu makara fa" "kuje zan kawo ta" "ba da yawuna ba zaki fita na dai gaya miki" Malam ya fada yana kad'a babban rigar shi. Juyawa tayi ta ce mishi, idan kaga ban fita ba, tow bana numfashi shi ne fita ya zama wajibi ne" ta riko hannun Sa'a ta kaita banɗaki ta wanke mata jiki, zasu fita ta riko hannunta. Ta kanne mata ido daya, tare da mata alamar ta mata wanka kawai don Allah. Murmushi tayi tana faɗin."Sa'ade zaki makara dai" hakan ta kuma dibo ruwa ta mata wanka tass. Sannan ta fito da ita shirya ta tayi, ta dauko mayafinta tana faɗin. "Larai bari na kai Sa'a makarantar." "Tow Yaya sai kin dawo" bata ga malam a cikin gidan ba, alamar yana kofar gida, koda ta fita ta same shi tare da mazan makotar su.
Haka ta wuce su, bata mishi magana ba. "Aminu idan Sa'ade ta kara girma ka aurar da ita mana tunda kaga ita Uwarta bata san harkan arziki ba." Kallon mutumin yayi kafin ya ce. "Ilya babu me auren Sa'adatu, duk da ni kaina nasan duk cikin Yarana babu me kyanta kuma ba za a kuma samu ba, sai dai ina jin takaicin haihuwar ta da aka yi a gidana babban kuskure na, shine gaya mata Yarinyar zata tafi kurmi niman kudi gashi abin haushi daya yadda Uwar lamaran ta kwadaita min arzikin da suke samu. " Shiru suka yi kafin Malam Musa ya ce mishi. "Kuma kaga kuma Laminde bata kyauta ba, ai bai dace ta kai ka gidan me gari ba domin dai nasan idan kuka samu arzikin nan tare zaku ci shi,ba kai daya ba waye ya sani ko har da Hajji zaku tafi." Kwafa. Malam Aminu yayi yana faɗin"Yo shima me garin ai bakin munafiki ne, ina cewa kin min magana yayi sai ganin dogarai kawai bisa kaina, wai daga gidan Hakimin Binji" kwafa ya kuma yana kallon hanyar da suka bi, yana tuna irin cin zarafin da aka mishi, anan yaji wani yana cewa za a kara musu malaman makaranta. "Tass mai gari ya ci zarafina, da goyan bayan hakimi, duk amanar da yake tsakanin mu na tsawon shekaru wai don Laminde ta kai ƙarata akan nakasassshiyar yarta ya zauna ya tsefe ni kamar ya samu kitso har da cewa bani da imani. Waye zai yarda a haifa mishi nakasashe kuma abin takaici nifa ban hanata kome ba, Bara kawai zata tayi mu samu kayan alatu amma uwar ta hana mu na dai san da ace ta tafi meye ba zamu samu ba? ?" "kai Malam Aminu ka ji tsoron Allah bayan haihuwar ta tasamu ciwon ba haifarta kuka yi da shi ba." "Eh meye maraban dambe da fada? Gaya min meye bambancin? An haife ta da shi ko ta samu ai duk daya ne, babu abin da ya min ciwo kamar kashe kudina da nayi na bin hawa, sannan itama Laminde aka saka ni na biya mata, Allah ya isa min" ya fada kamar zai yi kuka.
.... Inna Laminde har kofar aji ta raka Sa'ade. Sannan ta leka ajin, "Malam ayi hakuri ta makara " "Ba kome innah " "mun gode sosai" sannan ta nuna mata cikin ajin, rike yar jakar buhun simintin ta tayi me littafi kwaya uku. Zama tayi Innar ta leke ta, tare da d'aga mata hannu. Bata fuska tayi kamar zata yi kuka. Domin rashin yarda irin na Sa'ade. Murmushi Inna tayi ta bar makarantar.
A hankali taji hawaye ya zubo mata, tausayin rayuwar Sa'a take, tayi kankanta da fuskarta al'amari me girma haka. Sai dai kamar yadda Uwani matar me gari ta gaya mata dole ita zata tsayawa Sa'a..
Asalin su yan garin Maikulki ne, ko nace mazauna garin. Fulani ne da suka fito daga yankin sahara, domin yanayin su ya fi kamancecceniya da bororoji. Sai dai su fararren ne, ba bakaken fulani ba. Duk da suna yawo ne da dabobbi kafin su zauna a garin Maikulki na karamar hukumar Binji, Garin...