SANIN GAIBU....

Page:2

by @maidambu41

SANIN GAIBU...!!

   _Sai Allah_

ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023

     *Mai_Dambu*

Dedicated to Handicapped ❣️😓


```Ina mata yan kamshi matan yan yayi TOH ga turaren mu nan.

Ga turaren orientica kuzo kusiya arha kwasha kwasha 1700```

Page:02

Gari ne mai cike da albarka, lokacin da suka zo garin tana amarya kusan shekaru arba'in kenan. Tana da yara shida da Malam Aminu, uku maza maza uku mata. Haka abokiyar zaman ta, Larai tana da yara biyar. Ƴaran Inna Laminde sune manya akwai Zakari ya'u, suna kiran shi Ya'u sai Yusuf suna kiran shi Dabo,sai Ibrahim suna kiran shi Iro, sai Alaweeyah suna kiran Addah Weeyah sai Shamsiyah tana kiran Maman Sailuba, sai Auta wacce haihuwar yazo mata a bazata domin a tunanin su tun kan Shamsiyah don sai da ta girma sosai domin takai shekaru goma aka haifi Auta Sa'ade. Ya'u yana zaune a Sokoto shi da iyalin shi, domin da taimakon Allah da samun jajjurtaciyar Uwa Ya'u ya samu ilimin boko, na Addini kan dama suna yi. Na bokon ne Malam Aminu yaki cire kwandalar shi su amfana da shi. Fadin irin wahalar da Inna Laminde ta sha akan Yaran ta sai Allah, domin har surfe sai da tayi ita burinta Yaranta su samu ilimin. Alhamdulillahi Ubangiji ya dafa mata domin bayan Ya'u ya samu diploma akan aikin jarida, wata gidan Radio a sokoto ta dauke shi aiki, dama Yusuf yana na shi karatun domin shi jami'an danfodiyo ya samu, inda yake bangaren kimiyya kere-kere. Iro kuwa kasuwanci ya faɗa, domin yaki bokon tunda ya gama secondary ya ajiye boko, sai Allah ya saka mishi albarka shi kan yana garin Binji a can yake kasuwancin shi. Wani ikon Allah yaran duk sun san wahalar da Uwar su ta sha, haka yasa basu da wacce suka sani sai ita. Ɗakinta kuwa da ita kanta da suturan da take sakawa wallahi zaka dauka wata hamshakiya ce, nan kuwa ba kowa bace. Duk karshen wata suna hanyar me kulki dukkan su kuwa. Haka yana mugun yiwa Malam Aminu ciwo duk da ya hana su, moran shi amma Yaran basu mishi kugunta ba. A kome sukawa Mahaifiyar su zasu mishi, shima albarkacinta yake ci. Ba karamin al'amari ba ne domin lokacin da suka ce su boko zasu yi ba zasu yi kiwo ba, cewa yayi sai dai tana fita mishi da kiwo. Haka ta amince dake tana da wata kawa matar mai gari ita ta bata Shawaran ta saka Yaranta a makarantar boko, babu amfanin barin su suna yawo a daji da sunan kiwo. Ita kuwa ta amince. Shine fa aka fara samun matsala da Malam Aminu. Har aka haifi Sa'ade yarinyar ta taso cikin kulawa da soyayyar yan uwanta. Musamman Addah Weeyah da ta kusan aure. Domin itama tayi karatu har zuwa aji uku na secondary su, kafin Uban ya daka tsalle ya ce bai iya ji ba, duk da kiri-kiri yake fifita yaran Larai akan Yaran Inna Laminde. Yaran Larai sun, Yakubu, sai Jamilu, Ikilima tana aure, sai Harirah da Rabi. Ikilima tana aure a Binji gidan Sarkin Fulani. Domin Larai Mahaifiyar ta yar gidan ce, Malam Aminu kyakyawan gaske ne, idan ka gan shi ba zaka tab'a yarda shi ya tara Yara har goma sha daya haka ba. Haka itama Innna Laminde tana da kyau na asalin Fulanin Somalia. Laluran Sa'ade ya faru ne sakamakon cutar bakon dauro da aka yi, wanda kowa yasan yadda ciwon yake,. Shi ya tab'a mata wuyarta da kunnen ta daya. Bata ji da kunne daya sannan bata magana. Domin tana da shekaru biyar ciwon ya same ta, da farko har an fasa kukan ta mutu, sai da aka zo mata wanka sai a ka ga tana da sauran numfashi. Haka ta sha jinya kafin Allah ya bata lafiya. Sai dai fa bata hmm-bata humm- haka laluran ya same ta. Yayunta har asibitin Udut suka kawo ta, amma ba baki ba ido a lokacin karfi imani ne kawai yasa Inna Laminde bata mata fatan ta mutu kowa ya huta ba. Gashi a lokacin bata isa ta fita wasa ba, idan yara suka mata magana suka ga bata amsa ba, sai su watse su barta. Idan tana jin wuyan haka zata zauna tayi ta kallon uwar hawaye na zuba mata, sai taga kwano zata dauka tana budewa. Akwai lokacin da Inna Laminde ta tafi zaman bikin Ikilima da ta haihu, Yarinyar nan ta sha wahala domin ba kowa ke gane abin da take so ba, dama idan Innarta tana nan kwanciya take a jikinta ta hakan take fahimtar bata da lafiya. Sai kuma idan tana jin yunwa zata yi ta buɗe kwanika tana kuka. Tow tunda uwar ta tafi dake tana da kulafuci, don ta Uwar ce tare zasu tafi malam ya hana wai zata ja mishi magana a ce gidan shi a kwai kurma. Haka ta tafi tabarta cikin jinya domin bata da lafiya sosai, ita kuwa Inna Larai bata sani ba, sai da ta kwana bata ga tazo taci abinci ba, shi ne da safe ta leka dakin nan ta ganta a gadon bunun Innarta, yadda ta d'aga labulen dakin ta bude idanunta da suka yi jajjur, tana kallon ta kafin hawaye ya zubo mata. "Ni Maimunari yarinyar nan Allah yasa ba wani abu ke damunki ba" ta shiga ta tab'a kanta, jin yadda ya dauki zafi yasa ta fitowa ya cewa Malam da yake zaune a tsakar gida. "Malam taimaka ka bani cafeno yarinyar nan bata da lafiya, jikinta yayi zafi sosai." "Ke Larai bana son munafunci, ta mutu mana ko an gaya miki ina mara ba ita ne gara ta mutu kowa ya huta." Shiga ɗakinta tayi ta bankade zanin gadonta ta dauki kudi, ta fita yana mata magana amma ta bawa banza ajiyar shi yaji haushi kuwa, haka ya shiga dakin da tsumagiya ya shiga zane Sa'ade. Ga ciwo ga duka, Allah ya gani ya tseneta kamar ya kashe ta, yana cikin dukarta Inna Larai ta shigo gidan. Dakin ta nufa da ta ga takalmin shi. Ganin yadda yake dukar ta yasa fasa ihu, don ta suma. Fada sosai suka yi da Malam ta maida Sa'ade ɗakinta domin Rabi da Harirah sun bi Inna Laminde sunan Ikilima. Fadar irin kiyayyar da Malam yake nunawa Sa'ade sai ya baka mamaki. Haka ta taso da mugun tsoron shi, tana ganin yadda yake dariya da farincikin da yan uwanta amma ban da ita.

  Lokacin da ta cika shekaru tara Ya'u da Yusuf sun tsayar da shawarar su tafi da ita wurin su, amma bawan Allah nan fir yaki kuma ya hana a sakata a makarantar. Haka suka hakura itama bata son nisa da Innarta. Ana haka wata mata da take zuwa sayan madara a gidan ta jima bata zo ba. Dama bata da aiki sai daukar yara tana kaisu birni aikatu, masu laluran kuma tana kai su irin su Abuja da Lagos bara. Haka yasa ta wannan zuwan da zata koma an bata sakon madara zata saya shi ne ta ga Sa'ade, shi ne ta tuna akwai wani me kudi a can Lagos da ya ce ta nima mishi kurma mace ko namiji zai dauki nauyin a mishi jinya. Ganin Sa'ade yasa abin da take hangowa zata samu ya kara rikita mata lissafi, tasan Malam Aminta da mugun son abin duniya, don haka tana gama amsar madaran ta dauki kuɗi me yawa ta bashi kudin madaran sannan ta bawa Sa'ade kudi me yawa tana faɗin. "Malam Aminu ga arzikn a cikin gidan ka, amma ka kasa amfana da shi, gaskiya ya kamata ka san darajar haka." Ta fada tana kallon Sa'ade. "Kina nufi wannan abin Arziki ne? Hhhhh" ya fashe da dariya, yana nuna Sa'ade da take zare idanu. Domin tasan duk lokacin da Baffan su ya nuna ta yana magana tow ba abin dadi yake fada akan ta ba. Mikewa tayi daga bawa dan ragon ta madara a fidinbotul,ta koma dakin Innar su. Da take kallon kofar dakin. Kallon juna suka yi ta koma bayan Inna Laminde ta kifa kanta tana sauke ajiyar zuciya, hawaye ne masu zafi suka zubo mata, tana matukar tausayin yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Malam Aminu suka fita da Tabawa, anan ta tsara shi da kudin da zai samu, akan Sa'ade, ta mishi alkawarin wani sati zata zo in sha Allah. Bai fadawa Inna Laminde ba, kawai yayi gaban kan shi. Sati na zagayowa kuwa sai gata da uban kudi dama tun ana gobe zata zo, ya ke cewa Inna Laminde ta shirya Sa'ade gobe tabawa zata zo ta tafi da ita. Aikuwa tace bata san zancen ba, duk abin da za ayi sai ayi. Yarinya shekara tara ya hana a saka a makaranta sannan ya ce za a kaita wani wuri. Haka suka kwana suna rigima, washi gari sai ga Tabawa ta zo, ganin da gaske rabata zasu yi da Yarta. Don haka bata yi kasa a gwiwa ba, ta dauki yarinyar suka nufi gidan Mai gari, tun safe ake babu ɗaya shi kuwa ya kafe sai an tafi da Sa'ade, Mai gari ganin al'amarin yafi karfin shi yasa su a gaba har zuwa gidan Hakimi. Anan aka yi ta ta kare, har yake barazanar sake ta, dake suna shiga garin Binji ta samu wani Yaro a gidan Hakimi ta tura shi ya kira mata Ibrahim, can sai gashi a gaban shi aka yi Shari'ar inda Hakimi yasa a bincika mishi Makarantar Maikulki ko akwai malamai, nan me gari ya gaya mishi babu wasu malamai ba sai an kai da bincike ba, a duba kodan rayuwar Sa'ade. "Zan yi magana da shugaban karamar hukumar Binji zai yi magana Baturen ilimi in sha Allah za a kawo ma'aikata da yarda Allah, ita kuma Sa'adatu Mai gari idanun ka ya tsaya akan ta, sannan duk abin da yake tafiya zan na tuntubar ka." "In sha Allah zan saka Idanu " "kai kuma wallahi naji labarin wani abu ya kuma faruwa sai na tura sakon zuwa shugaban ƙaramar ƙungiyar kare hakkin dan Adam sun daure ka. Kuma itama Tabawa a gaya mata ta bar kasar Binji kafin na same ta." Da wannan aka kashe zancen, Allah da ikon shi ya hadata da matan me gari, tayi ta bata shawara. Yadda zata kula da Sa'ade. Koda suka dawo gidan ma tashin hankali da masifa, dama shi Ibrahim tun a can ya bawa Babar su hakuri domin yasan halin Baban su, ba zai iya rigima ba. Haka ya tasata a gaba da bakar magana kamar zai doke ta. Laminde ke nan, a yayinda takwarorinta suke kurmi da kudu niman abin Arziki shi ne zaki tozarta ni ta hanyar kai kara na, gidan Anamimin can wato ki jindadin ayi min dariya tow na gode tunda a iya gidan hakimin Binji kika tsaya na zata zaki wuce har lahira ne da ni. Karewar Gidan hakimi, tow wallahi na rantse da Allah babu hannuna a kan Yarki ku nima mata wani Uban ba ni ba." Haka gefe guda Abokan shi zuga shi suke akan Laminde tafi ƙarfin shi ashe kuri yake da karyan yafi karfin gidan shi. Ita kan Inna Larai babu ruwanta domin har ita bai kyale ba, shi yasa bat shiga cikin hayaniyar su.

  --- a dawo labari.

Federal Ministry of education

Sokoto State

Kamar yadda Hakimi ya tura sakon shi, haka Shugaban karamar hukumar Binji ya tura zuwa ga Commissioner ilimi. Dr Sharif Hamidu. Kasancewar yau satin shi biyu da dawowa daga Umra. Ya kuma yi daidai da kwanakin da ya ɗauka na Hutu. "Yallabai akwai takardun da aka turo da kuma na aiki, daya daga karamar hukumar Binji. Kwantomar Binji da kan shi ya kawo yana bukatar a baka sakon" kallon sakataren shi yayi kafin ya ce. "Ok na ga ni" mika mishi takardan yayi, ya duba kafin ya zuba mishi idanu. "Suna bukatar malaman makaranta ne." "Tow ko za a tura wurin me girma Gwamna ne" girgiza kai yayi sannan ya ce. "A tura musu yan bautar kasan da za su yi service makarantun mu, sannan zan tuntubi me girma Gwamna da maganar." "In sha Allah za ayi haka." "Allah ya sa" ya furta,

 Fita sakataren yayi shi kuma ya fara aikin shi da ya bari. Yana nazarin maganar da shugaban karamar hukumar ya turo mishi. Akwai yara masu yawan gaske da suke buƙatar kulawar Malami da gwamnati, a halin da ake ciki har an fara diban yaran nan zuwa birane domin niman kudi wasu Bara, da sauran su. Babban abin damuwar yarinyar da ake son a fita da ita bata ji bata magana kuma a haka za a fita da ita birni ba a san inda za a tsaya da ita ba. Cire glass din shi yayi yana mamakin wannan al'amarin. Me ya dace su? Dole a tura musu malaman, wayar shi ya janyo ya gwada kiran me girma Gwamna...

ASHRAF, SANIN GAIBU,TSINTUWA is not free, Pay N400 ONE, TWO N800, THREE 1K to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza