Page:5
by @maidambu41
SANIN GAIBU...!!
_Sai Allah_
ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023
*Mai_Dambu*
Page:05
Ganin ita ɗaya ne yasa take mugun jin kanta, ta kafawa kanta giggiwa da wani irin izza, bata san kome ba sai niman kudi. Domin bayan dawowarsu amsar kamfanonin ta tayi ta cigaba da kula da su, koda wasa Dr Sharif bai saka kan shi cikin duniyar ta ba, gudun kar a samu matsalar reni. Hajiya Dawlah ta rena talaka, ba a bakin kome yake a wurinta, shi yasa Yaranta suka taso da bakin kiyayyar talaka, idan ka cire Abdul babu ruwan shi, a duniyar Hajiya Dawlah kudi yafi kome daraja, shi ya sa bata harka da kananun mutane, sannan duk tsiyar mutum be tab'a zuwa inda take. Akwai gayen da ya nime auren Yarta Sadikkah, duk da suna son juna be hana da Hajiya Dawlah tasan bai da kumba susa ta mishi fata-fata ba. Idan kana Niman me kin jinin talaka toh wallahi tana sawun gaba. Duk da tarin dukiyar da Allah ya bar mata, akwai abu daya da tayi akan Abdul shi ne tura shi jami'an A.B.U zaria anan yayi degree din shi na farko, duk da a lokacin masu kudin da suke tura Yaran su, kasashen waje, ita bata tura shi ba koda mahaifin yayi magana cewa tayi. "Su makarantun can koyarwar suke da practice anan kuwa koyarwar su theory ne. Duk dalibin da ya samu tarkada daga makarantun nan guda, A.B.U, A.T.B.U, B.U.K, Udut. babu inda zai shiga ba a nime rike shi ba, domin jami'o'in sun san me suke kuma suna da good stander." Ba yadda ya iya da ita, haka ya hakura ya zuba mata idanu, domin yanzu yana fara magana zata ce kome sai shi yake da iko yayi. Kowanni Uba yana da burin ya tsaya akan Yaran shi amma Dawlah taki barin shi ya tsaya a kan yaran shi, sam bai san soyayyar mace ba, har sai da Allah ya haɗa shi da wata yar katsina me suna Fareedah, sun je wani aiki ya hadu da ita, kuma cikin ikon Allah sai aka yi dace itama daga babban gida ta fito. Auren shi da Fareedah shi ya janyo rigima wanda har Hajiya Dawlah ta bar mishi gidan ta koma gidan mahaifin shi, shi kuma ya zuba mata ido, don babu mahaifin ta ba zai iya wulakantata ba, shi yasa ya bar ta da halin ta, ana cewa kowacce mace da Arzikin ta a lokacin faduwar shi da Fareedah, ya samu manyan mukamai masu ban mamaki, domin sai da ya rike daraktan a majalisar dinkin duniya, uniter Nation. Allah sai ya nunawa Dawlah duk abin da take ji da shi yana ji dashi, dukiya ilimi, suna da daukaka. Amma a kullum cewa take da bazatarta yake rawa. Allah ya albarkaci Fareedah da yara uku, biyu maza mace daya. Fareedah tana da kirki hakuri da kawaici uwa Uba, biyayya da sanin kan namiji. Sai Allah ya haɗa jinin su da Abdul wanda shine yake rike da kamfanin simintin Mahaifiyar shi, ta tsani taji Abdul yana magana da Fareedah, tayi ta fada kenan Abdul baya kaunarta yafi kaunar mahaifin shi da matar shi. Daga ita har Yaran ta sauran babu ruwan su da Dr Sharif sai Abdul shima Abdul don babu yadda ta iya da shi ne. Domin yana gama degree din shi Mahaifin shi ya tura shi Canada ya tafi yayi masters din shi. Duk da bai da lafiya, amma yana da kokari.
Wannan shi ne kaɗan daga Abdul Hakim Sharif Hamidu.
•°°°
Fadar Sarkin Kwara.
5:30pm.
Mace ce dattijuwa, tana sanye da atamfar super neuver. Tasha ruwa da jin jiki saboda yadda tayi haske, wai ma don zanin babba ce yasa bata yagalgyale ba, yadda suke tafiya zaka rantse da Allah gidan zasu bari. "Iya kina ganin fadar gaskiya zai kubutar da ni? Iya ina matukar jin tsoro" juyawa tayi tana kallon shi, jikanta ne wanda iyayen shi suka rasu suka bar mata shi. Yazo da alamari me girma, taya zata yi shiru. "Kabiru taya zamu yi shiru bayan masu laifi suna raye baka gan su ba ne." Rintsa idanun shi yayi. "Iyah mu hakura don Allah, mu bar masarautar nan" "ko daya haka ba zai faru ba" ta cigaba da tafiyar ta, kamar zata kifa. Tana isa sashin Sultanah Badi'atul Noor, wacce ake mata lakabi da Sultanah karama. Suka jan tunga suka tsaya, "Gajiyah me ya kawo ki bangaren Sultanah karama?" Sarkin kofa ya tambaye ta, kasancewar an bashi umarnin tsaya a kofar sashin Sultanah tun faruwar al'amarin kisan Ummul Mansurah da ake zargin D'anta da yi, Sultan Abdulrahman Dan Aliyu Sulu Gambari ya hana kowa shiga wurinta, kuma kar a bari ta fita sai da dalili. "Sarkin kofa, alfarma nazo nima ina son ganin Sultanah" kallonta yayi Gajiyah mutuniyar kirki ce, ba zai iya hana ta shiga ba, don haka ya ce mata. "Kin san dokar hana shiga da fita da aka kafa, don Allah kar ki jima a cikin sashin domin Sultan zai iya zuwa kowani lokaci " gyada mishi kai tayi cikin farin ciki" In sha Allah ba zan wuce yadda kake tunani ba." Bude mata kofar sashin aka yi, ita da jikanta suka shiga cikin sashin. Zubewa bayi suke suna gaishe ta. Domin ita din jakadiya ce ta Sultanah Babba. "Gajiyah kece yau a bangaren Sultanah karama?" "Eh wallahi nice Zuwairah ina uwar dakin take?" "Tana lazumi ne" shiru suka yi kafin tace. "Don Allah ki nima min iso alamarin ujula ce" shiru tayi kafin ta ce mata. "Shi kenan bari na mata magana" wucewa tayi cikin babban falon, can ta wuce hanyar upstairs din, hango Iyatuh tayi dauke da kayan wanki. Murmushi tayi mata ta ce mata. "Sannu da kokari Yar nan?" "Yawwa Mama Zuwairah." Ta wuce dakin Sultanah Badi'atul Noor, ta bude a hankali, Aljannan duniya kenan. Duk inda ake niman kayan alatu na rayuwa ya samu a falon, katon hoto ne ita da Yaranta biyar. Maza uku mata biyu. Fuskartar ce juya ta jimami, wucewa tayi har bakin kofar ta buga. Gyaran murya aka yi, bude kofar tayi bakinta dauke da sallama. "Assalamu alaikum " ajiye Alqur'anin hannunta tayi tare da zare glass din idanunta ya zubawa Zuwairah ido" zubewa tayi a kasa tana mata kirara. "Barka da warhaka, uwar dakina baya giya marayu, me uban ma kin goye shi, Uwargidan Sultan Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari, takawarki lafiya Giwa me tafiyar kasaita, Barkan ki da hutawa uwar zakuna uku, Babar Didih da Addah, Mamar Hamma Bubah, Uwar Sanda Babuga. Makiyan ki fadawar ki. Allah ya dawo miki da farincikin ki" zuba mata ido tayi, kafin ta ce mata. "Zuwairah da na jinki" gyara zama tayi sannan ta ce mata. "Ranki shi dade Gajiyah tana son ganin ki" "ki je idan aikota aka yi ta sako ne ta baki" "ranki shi dade, bana tunanin sako ne kamar ita da kanta tazo domin ta ce min ujula ce." "Tow ki mata iso" ta cigaba da karatunta, "na barki lafiya " ta juya ta fita, ajiyar zuciya ta sauke tana me jin kwalla na cika mata idanu. Duk Yaranta basu tare da ita, Zakiyyah da Rumaisah kawai take jin sauki daga gare su, Autan ma sun taso shi a gaba. Lumshe idanunta tayi tana tasbihi ga Ubangiji wanda ya cancanci girmamawa da bautawa. Tana zaune a wurin Gajiyah da jikanta suka shigo dakin, zama suka yi ta zuba musu idanu. "Barka da hutawa, akawala baki musaya, hankaka meda dan wani nata, alfadari kike me ado da zinari, maliya me ruwan alkhairi, Uwar Zakiyyah da Rumaisah, Hajiyar Abubakar da Umar, Innar Aliyu Abu turab, mun zo da babban al'amari ne me girgizarwa." Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mai da dubarta ga kofar dakin ta. Juyawa Gajiyah tayi zuwa ga kofar dakin. Inuwar mutum ne a wurin. Mikewa tayi ta nunawa Gajiyah barandar da yake dakin ta waje, anyi wurin domin shan iska ne. Tashi suka yi tare da nufar wurin. Sai da ta rufe kofar dakin ta, bayan ta leka bata ga kowa ba. Sannan ta nufi wurin su ta rufe kofar wurin shan iskar. "Ina jinki " taryan-taryan ta labarta mata, abin da Jikanta Kabiru ya gaya mata. Mikewa tayi tana kallon waje, ba zaka iya tantance abin da yake ranta ba. Domin wani irin fuska take da shi, na ba zaka iya gane fushinta da farar ba, duk da ta kasance mace mara yawan fara'a. Amma tana da faran-faran da mutane, yanayin ta ne kawai ba me yawan fara ba, amma idan ta zauna a cikin Yaranta har da dariya take yi, tana da wuyar sha'ani ce. "Gaskiya ka fada Kabiru?" "Na rantse da Allah gaskiyar kenan" "shi kena, amma Gajiyah me yasa kika zab'e fadar gaskiya bayan kowa yasan ke kina tare da Sultanah Babba ce" hawaye ne ya zubowa dattijuwan, ta saka hannu ta goge tana fadin. "Koda ni ban rayu ba, ina fatan shi din ya samu kyakkyawar rayuwa, Sultanah ban zabi haka domin nima mishi alfarma ba, asalima ina son nayi amfani da haka ne niman kusanci da Ubangiji na, nayi wanka da zunubi, a yanzu kuwa ni da banza daya ne, don Allah ki taya ni kare rayuwar shi, wallahi bani da wani abu da zan iya kare shi" "zaki iya tafiya, shi kuma ya zauna a bangaren auta. Domin tunda kika kawo shi ba zan yi sake da shi ba. Shi ne shaidana" "Na gode sosai Sultanah " har zasu tashi ta ce mishi. "zauna kai" komawa yayi ya zauna yana kallon kasa. "Zaki iya tafiya " zama yayi, ta zuba mishi idanu. Kan shi a kasa, kafin ta ce mishi. "Kana son zama a nan?" "Eh...eh... Sultanah " ya fada muryan shi yana rawa. Murmushi tayi tana kallon shi. *Idan na sake ya bi kakar shi* "Sultanah abubuwa daya sun faru a cikin masarautar nan don Allah ki hako wasu domin kyautatawa ce haka" kallon Gajiyah tayi sannan ta ce mata. "Ba zan iya hako abin da zai mai da kasa ya binne ni ba, wanke Yarona kawai nake son yi ba tada abun da ya wuce ba." "Idan kuma kina da alaka da hakan fa?" Gajiyah ta wurga mata tambayar. "An san da wuyar biri bai hana a daure shi a kugu ba, akan me zan saka kai na cikin abin da ya wuce babbar matsalata wanda ya kashe Yarinyar da babu ruwanta, sannan aka jinjinawa Abu Turab" "Sultanah" "don Allah ki je" sultanah ta fada. Har ta isa bakin kofar sai ta tsaya tana kallon Jikanta da Sultanah. "Wata rana zaki so ki san me ya faru, idan wannan lokacin yayi, ki ziyarci garin ka'injin don Allah " "Allah ya nuna mana," "Ga amanar shi nan" "Allah ya taya ni riko" ta fada. Tafiya Gajiyah tayi, bai zama dole ta rayu ba, amma ya zama dole ta gayawa Sultanah gaskiya, tana fita daga cikin sashin ta kalli Sarkin kofa ta ce mishi. "A gafarce ni mai kofa." "Ba kome, amma kin san zuwan kinan akwai hatsari ko?" Goya hannunta tayi a baya, "me yafi ciwo a ce kayi bauta a maida kai saniyar ware? Ka tab'a gane cewa kalilan ne a masarautar nan suka san amfanin mu? Ko kasan." "Gajiyah abu shida ke aiki a Masarautar nan, Kudi, mulki, hassada da makirci, mugunta da kwadayi, don Allah ki cire hannunki a wannan al'amarin" "Bakwai ne Sarkin kofa, fansa kowani bangare burin shi fansa" "don Allah ina baki shawaran ki cire hannunki a cikin wannan lamari, domin kin manta da Cin amana, wnada ka yarda da shi zai iya cin Amanar ka akan kuɗi da zai kare, akan dan abin da bai da tabbas, don Allah ki janye hannunki" tafiya tayi bata ce kome ba. *Haka ne duk abin da muka lissafo shi ne yake faruwa, idan har akwai abin da zai faru tow ba makawa yakin gaba da Sultanah ce, ita ce abin harin kowa ita da Yaranta maza uku, an fadi a kan Abu turab, shi ma ai don yana tare da ita ne, ta iya kare shi tun daga yarintar shi.* Wannan shi ne zancen zucin da take tabbas yaran sultanah sune ake hari kasancewar sune manyan...
ASHRAF, SANIN GAIBU,TSINTUWA is not free, Pay N400 ONE, TWO N800, THREE 1K to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza