NUFIN ALLAH! Chapter 17
📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo*
*Paid book:500*
*Chapter 17*
_Free page_
Su Inna Mairo ne suka fara fitowa falon bayan sun idar da sallar isha'i kamar yadda suka saba.Sun tadda Hannah da Nasreen zaune a falon suna hiransu kafin Gwaggon ta fito.Nasreen ta gabatarwa da Inna Mairo Hannah,tana sanar da ita cewa matar babban Yayansu Adnan ne.Suka gaisa da fara'a tana tambayar Hannah ina shi Adnan ɗin? Ta sanar da Inna Mairo cewa yana can Port Harcourt ɗin bai zo ba.Hannah ta dinga satan duban Inna Mairo da Najma, tana kallon tsabagen kamanninsu da juna.Sai dai kawai bambamcin kalar skin da ke garesu, kuma ita sai Najma da take baƙa kyawunta yafi birgeta fiye da Inna Mairo da ke jinta jajir da ita.Gwaggo ta fito ta samesu suna ta zantawa da juna, ta ƙariso mazauninta da ta saba zama cikin 2 seater ta zauna.Da zallar mamakin ganin Hannah take amsa gaisuwarta tare da tambayarta ita dawa ta zo garin? Hannah ta yi ƙasa da kai tana bai wa Gwaggo amsa da cewa, "Ni kaɗai na taho Gwaggo, shi zai zo daga baya ina ga zuwa jibi weekend!" Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Kuma shi ne ɗazu da mukai waya bai sanar min zaki zo ɗinba? Ya sako ki a jirgi ke kaɗai kika taho ko tsoro baki ji ba?" Hannah da Nasreen suka saki murmushi,Hannah na duban Gwaggo da girmamawa ta ce, "Gwaggo ai babu wani tsoro,tunda ba daga wata ƙasa na zo ba ni kaɗai ɗin,koma wata ƙasar ce ai babu wata damuwa." Gwaggo ta jinjina kai tare da taɓe baki ta ce, "Eh! Lallai zamani ba ƙarya bane ai, ku Yaran yanzu baku san tsoro ba sabida buɗewar ido da ya yi muku yawa." Ta ƙare maganar tana bin Hannah da wani kallo na ƙurilla don son gano ko abinda take hasashe da gaske ne a jikin Hannar? Don tun kallon farko da ta yiwa fuskarta fa tara zargin da wuya ba ciki ne da ita ba.Kamar Hannah ta gano manufar Gwaggo sai ta juyar da fuskarta baki ɗaya tana facing su Nasreen da ke ta faman hira da Najma.Har aka shirya abincin dinner a tsakiyar falon suna nan zaune, Gwaggo tayi musu tayin in zasu ci a haɗu duka aci tare da juna.Nasreen da bata faye cin abincin dare ba sai wajen 10pm tayi saurin girgiza kai tana faɗin, "Sai dai ko Anty Hannah Gwaggo." Hannah ta ita ma ta girgiza kai tana faɗin, "No! Na ƙoshi wallahi, ni da abinci sai can anjima kuma." Daga haka Najma da Inna Mairo tare da Gwaggo suka haɗu suna cin abincin hankali kwance.Nasreen da Hannah sai suka yi musu sai da safe suka fice, bayan Nasreen ta jaddadawa Najma cewa tana jiranta a ɓangarensu idan ta gama. Kai kawai Najma ta gyaɗa mata amma ba don zata je ɗin ba,don bata son ta zama mai yawan shigewa musamman da yau ɗin Anty Hannah ta zo.Wacce tun daga kallon da Momy ke mata da irin yadda Nasreen ta nuna ɗoki da murnar ganinta, ta gano irin soyayyar da suke mata.Shiyasa take ganin gara ta ɗan ja jikinta yau ɗin, don basu damar sakewa da surukar tasu,kar taje tana takurasu da ganinta a kusa da su.
Gwaggo bayan sun kammala da cin abincin sai ta koma daga gefe guda ta dannawa shalelenta AD Dukku kira.Bugu biyo ya ɗaga wayar cikin sassanyar muryarsa da yake haɗawa da ƴar shagwaɓar gata idan yana waya da ita.Bayan ta gama amsa gaisuwar da ya yi mata,sai kai tsaye ta jefa masa tambayar dake mintsininta, "Adnanu ya aka yi ka baro matarka ita kaɗai ta taho maimakon ku taho tare? Kasan fa nayi kewarka wata guda kenan baka zo dubamu ba,ince dai ko lafiya ta taho ita kaɗai ɗin."
AD Dukku daga ɓangarensa ya lumshe idanunsa,yana sake gyara kwanciyarsa akan sofa dake ɗakinsa. Domin tunda aka tashi office ya dawo gidan.Ya buɗe baki cikin ƙasa da muryarsa ya sanar da Gwaggo cewa Momy ce ta bai wa Hannah umurnin tahowa, sabida sun samu ƴar hatsaniya tsakaninsa da Hannar. Gwaggo ta buɗe baki cikin matuƙar mamaki ta ce, "To hatsaniyar uban me kuma kuka yi? Nifa ka fara bani haushi da wannan ƙiyayya da kake nunawa salihar baiwar Allah.Miye aibun Hannatu ne wai da ba za ka rungumi matarka ku zauna lafiya ba?" Gwaggo tayi maganar da ɗaga sautin muryarta, hakan ya sanya su Gwaggo da ke daga can cikin falon suna jiyo duk abinda take faɗi ɗin.Ta ɗanyi jim! Da alamu tana sauraran abinda yake faɗi mata ne,zuwa can kuma ta sake ɗaga sautin muryarta tana faɗin, "To ai shikenan, ni yanzu zan je wajen Zainabun inji dalilin da zaisa ta ce wa matarka ta zo ba tare da izininka ba.In banda ma shiga uku ina ruwanta da faɗarku da har zata saka ƴar mutane kamo hanya tazo gari ita kaɗai kamar wata wulaƙantatta." Ta dakata da maganar tana sauraren yadda AD Dukku ke narke mata murya yana nuna cewa bashi da wani laifi, Hannah ɗince ta kira Momy ta sanar da ita ƙarya da gaskiya don Momy ta ji zafinsa.Gwaggo ta dinga jinjina kai kamar yana gabanta,kafin ta sake faɗin, "Karka damu zan je yanzu na ce na sameta, kai dai kawai kaxo zuwa ranar sati ɗin ina son ganinka Adnanuna.Amma kuma zamu giwa ranar asabar ɗin, Gwaggonka Mairo da na sha baka labarin tana can,to ta dawo nan kaduna da zama zamu rakata kwaso kaya suyi sallama da mutanan arziƙinta kuma.Amma hakan ba matsala bace, ka dai zo ɗin kaji ko?" Ta sake yin shiru tana saurarensa daga ɓangarensa,kafin ta sake furta, "To shikenan sai ka iso ɗin, ina fata dai yanzu duk kana rage shashancin shaye-shayen nan na zamani daka koyo a turai,don sam bana so Adnanu.Don Allah ka nutsu ka zama mutumin kirki,karka ga ina kareka idan Iyayenka na kyararka nima kaina abin yana damuna a zuci." Ta kai ƙarshen maganar tana sake manne wayar a kunni,tana cigaba da sauraran tsarin da yake mata.Ta sauke wayar a kunni bayan ya kashe,tana mai miƙewa tsaye ta kallo side ɗin dasu Inna Mairo suke.Sun maida dukkanin hankulansu akan kallon TV, Najma kuma ta kan duba wayarta jefi-jefi.Gwaggo ta ɗaga murya ta kira sunan Najma tare da bata umurnin zuwa ɗakinta ta ɗakko mata mayafi.Najma ta miƙe ta wuce don zuwa ɗakkowa Gwaggon mayafin nata, ita kuma Gwaggo ta maida hankali wajen Inna Mairo tana faɗin."Mairo ɓangaren Zainab zani yanzu in jiyo dalilin da zai sanya ta saka ƴar mutane kamo hanya tazo gari bada izinin mijinta ba, ina na taɓa ganin anyi hakan ni Hauwa! In banda dai zamani da ya lalace ma, ina ruwanta da surukar ɗan fari har da zata dinga zaƙewa a lamuransu? To bari in je mata don ba zan bari ma sai gobe ba."
Inna Mairo tayi murmushi tana duban Gwaggo ta ce, "Allah sarki Gwaggo, watakila tana ganin hakan da tayi shi ne daidai ɗin.Amma dai gara kije ki ji ɗin zai fi." Gwaggo ta ɗan kyaɓe baki ta ce, "To ai hakan ma shine gaskiya da gaskiya Mairo, in je mata ɗin tun yanzu inji dalili da abinda ya faru ɗin." Najma da ta iso da mayafi a hannu,sai ta miƙawa Gwaggo tana faɗin, "Gashi Gwaggo." Gwaggo ta amsa mayafin tana faɗin, "Wuce mu je ki rakani ɓangaren Kabeeru Najma." Najma ta amsa da, "To." Tana bin bayan Gwaggo da bata bari ko mayafi ta saka akan rigar jikinta mara nauyi da ta saka ba. Suka isa ɓangaren su Momy tana cike da mamakin yadda Gwaggo ke ta faman mita ita kaɗai,don tunda suka fito take mita da magana ba tare da Najma ta ce komi ba. A nan main parlor ɗin suka tadda su Nasreen dukkansu har da Nabeela da ba a jima da maido ta gidan ba.Momy ta tarbi Gwaggo da kulawa tana faɗin, "Barka da shigowa Gwaggo, ga wuri nan zauna nan." Ta nunawa Gwaggo kujeran 2 seater ta zauna.Ta dubi Momy ɗin tana ɗan gimtse fuska ta ce, "Zainabu wajenki na zo, maza kai ni ɗaki muyi magana in kama kaina ba zama cikin Yara na xo yi ba." Momy ta dubi Gwaggo tana ji a jikinta cewa duk yadda aka yi Adnan ya kirata ya haɗosu kenan da Gwaggon.Ta miƙe tana duban Gwaggo ta ce, "To muje ɗakina Gwaggo." Daga haka suka yi gaba zuwa bedroom ɗin Momy ɗin, suka bar su Nasreen da bin bayansu da kallo, zuciyar Hannah na cigaba da doka mata.
Gwaggo ta dubi Momy bayan shigarsu ɗakin ta ce, "Zainabu miye naki na cewa Hannatu ta kamo hanya ta taho,don kawai sun sami saɓani da mijinta?" Momy ta danne ɓacin ran Adnan da ya taso mata,ta dubi Gwaggo kai tsaye ta ce, "Au! Bai faɗi miki ɓarnar da yake shirin saka Ƴar mutane su aikata ba Gwaggo?" Gwaggo ta haɗe fuska tamau ta ce, "Ina tambayarki maimakon amsa sai kuma ki jefoni da wata tambayar Zainab? To bai faɗi mini komi ba, shiyasa ai na zo inji daga bakinki." Momy ta sauke numfashi mai ɗumi, cikin kwantar da murya ta ce, "Gwaggo so yake ta zubda cikin da ta samu, sabida wai shi bai shiryama haihuwa yanzu ba.Ni kuma tunda ta sanar mini, shi ne nace ta dawo gabanmu don kada ya tirsasata su aikata ɓarna, tunda ya fahimci ta mato a kansa zata iya aikata komi don ta faranta masa.Don Allah Gwaggo ki nuna masa ɓacin ranki a wannan karon,don na san kema ba za ki so a aikata wannan ɗanyan ɓarnar ba." Gwaggo da tunda Momy ta fara magana ta shiga shock! Sai ta riƙe haɓa tana magana a firgice ta ce, "Shi Adinanun ne ya faɗi hakan Zainabu, da bakinsa ya furta cewa bai shirya haihuwa yanzu ba don ubanshi? To wallahi ya yi kaɗan, idan ƙwayoyin da yake sha ne suke gaya masa gaibu,to ya sani sai Hannatu ta haife wannan rabon da Allan ya nufeni da rahamar zan ga jininsa a duniya." Gwaggo ta ɗan numfasa kafin ta cigaba da faɗin, "Au shine har da narke mini kamar wani mai gaskiya, lallai ko zai san cewa bana bayansa a wannan karon.Yanzu dai jeki kirawo min Hannatun ta zo inji zance dalla-dalla daga bakinta." Momy ta saki murmushi a sace tana miƙewa ta fice don kiran Hannah.Gwaggo kuwa sai faman mita take yi tana tsinewa shaye-shayen ƙwayoyin da aka ce Adnan ɗin nayi.
Lokacin da Hannah ta shigo gefen da Momy ke zaune daga bed ta zauna tana yin ƙasa da kanta.Gwaggo ta zuba mata ido tana sake gano alamun mai ciki an tare da ita ɗin.Ta wanj yi ƙasa da murya tana duban Hannah kai tsaye ta ce, "Ke Hannatu da gaske ne Adnanu ne ya ce baya son cikin da kike ɗauke dashi?" Hannah ta gyaɗa kai cike da tsananin jin kunya.Gwaggo ta cigaba da faɗin, "To kuwa wallahi bai isa ba, ai duk laifinki ne da kike nuna masa shegiyar soyayyar da baki ganin duk wani aibunsa da tsiyar da yake shuka miki.Inba ya rainaki ya gano kin gama matowa a kansa ba, har ya iya kallon tsabar idonki ya ce baya son cikin alhali shi ya ɗirka miki,ko kuwa a ruwa kika sha cikin?" Hannah dai kunya kamar ta nitse, haka ta sake dankwafar da kai ƙasa tana sauraran masifar da Gwaggo ke mata.Daga ita har Momy suka yi har tayi mai isarta,ta miƙe tana duban Momy ta ce, "Ki sanar da Kabeeru da gaggawa, Yarinya ta dawo kenan har sai ta haife mana ɗan ko Ƴar sannan sai su ƙarata ta sake binsa can kudun.Amma yanzu tunda ya nuna baƙin cikinsa da hassadarsa akan samuwan cikin, ana bashi ita suka koma zai san yadda ya yi salwanyar da cikin tunda ita shashashace, ta riga ta nuna masa ta gama matowa a kansa gaba ɗaya.Ita ko irin ƴar jan ajinnan ta mata bata iya ba, kyawunsa gaba ɗaya na kula gigita yake,ta yadda idan waje duk take rasa nutsuwarta.Wallahi Hanantu ki yi hankali da zaƙewa a nuna wa namiji muguwar soyayya, inba haka ba kece a wahale a kuma gantale don duk iskancin da ɗebo a kanki zai riƙa saukewa." Gwaggo ta ƙare maganar tana yin gaba don fita daga ɗakin.Momy da Hannah sukai mata sai da safe, ta juyo tana makawa Momy harara ta ce, "Amma Zainab so kika yi ki rufeni,da tun farko baki je kin sanar min wannan iyashegenba.Yanzu gobe sai a buɗe mata ɓangarensu a gyare shi, tunda dama komi na nan kamar yau akai jeren wajen,tayi zamanta ta raini cikinta cikin salama.Ko Iyayenta ban yadda su ji wannan abin kunyar ba, sabida sai ai mata dariya gaskiya." Momy ta jinjina kai ta ce, "Dama nima shawarar dana yanke kenan Gwaggo, shi ma kuma Daddy haka ya ce tayi zamanta kawai." Gwaggo ta fice tana cewa, "To ai shikenan tunda basirarmu duk yazo ɗaya a nan,shi kuma Adinanun zai zo ya sameni har ɗakina." Ta ƙarisa ficewa tana barin su Momy da sakin dariya,don sun yi mamakin yadda Gwaggon ta rufe ido tana masifan jin zafin zancen zubda cikin. Falo Hannah ta koma ta samu Gwaggo ta tasa Najma sun koma ɓangarenta, don ta sanarwa Nasreen cewa gobe lafiyayyan ƙosan da Najma ta iya zata yi musu da safe.Don haka ba za ta kwana anan tana baccin asara da safe ba, har ta gagara komawa tayi musu ƙosan akan lokaci.Hannah ta zauna tana dariyar yadda Nasreen ke bata labarin abinda Gwaggon ta faɗi,ta cigaba da blushing tana cewa, "Nima har naji ina son naci ƙosan Sis,goben na je na samo wajen Gwaggon na ci." Nasreen ta taɓe baki cike da jin haushin hana Najma kwana da Gwaggo tayi ta ce, "Aiko dai zaki ci daɗi, don gaskiya ta iya suyan ƙosai sabida sana'arsu ce a can giwa ta ce." Hannah ta murmusa daidai wayarta na ɗaukar tsuwwa na shigowan kira ta ce, "Aiko da wuri zan aika a amso min ɗin." Daga haka ta ɗaga kiran ganin sunan Anty Laurah ce mai kiran.Sun ɗan jima suna magana, amma sam Hannah bata sanar mata cewa tana KD ba.Ta aje wayar tana kallo agogo zuciyarta na cike da tunanin kome yake can yana yi a yanzu? Ta ɗan lumshe ido tana jin wani zafi da kishi na sukan zuciyarta,don ta san yau ɗin watakila kwana ma zai yi a club tare da ƴan matansa tunda bata gidan baki ɗaya bare ya dawo mata cikin tsakiyar dare ya lalubeta kamar yadda ya saba.Ƙirjinta ta ji yana mata nauyi,sai tayi saurin tashi tana duban Nasreen da Nabeelah da hankalinsu ya koma kan wayoyinsu ta furta, "Gud night Sisis, zan kwanta bacci yazo." Nasreen sukai mata sai da safe ta nufi hanyar bedroom ɗin da Momy ta ce ta zauna a ciki.Su kuma suka cigaba da chart suna kuma kallo rabi da rabi.Kira da ya shigo wayar Nasreen na wani saurayinta Saheeb ya sanyata tashi ta wuce ɗaki, ta bar Nabeey a zaune tana kallo tana cigaba da chart.
*********
*Port Harcourt.*
Ƙarfe uku daidai na dare motar Adnan Dukku ya shigo gidansa.Ya ɓalle murfin motar ya fito bayan ya adanata a parking space, ya nufi cikin gidan yana jin kansa na sara masa sakamakon ƙwayar da ya sha da bai taɓa shan irin ta ba sai a yau ɗin da abokinsa US (Usman Sani) ya zo musu da ita.Shi ma kuma daga ingila ya taho da ƙwayar,wacce ba mai sanya buguwa bace sai dai ta sanyawa mutum ƙarfi da jin kansa a sama tamkar yafi kowa.Ƙarfin da take dashi ke sanya duk wanda ya fara shanta sai ya haɗu da ciwan kai mai tsanani kafin ta bi jikinsa ta fara aikin da ya dace.Ya kai kansa zuwa upstairs yana nufan room ɗinsa kai tsaye,domin burinsa bai wuce ya sakarwa kansa ruwa mai ɗumi ba.Kayan jikinsa da ke fidda mayataccen ƙamshin Leenah ya fidda,ya yi jifa dasu a tsakar ɗakin yana nufan hanyar bathroom ya sakarwa kansa ruwan sanyi.Sai da sanyin ruwan ya gama ratsa kwanyarsa lafin ya sakarwa jikinsa ruwa mai ɗumi,yana jin wani irin yanayi na bin jikinsa.Koda ya fito kayan baccinsa ya sanya, ya nufi wajen ƙaramin fridge ɗinsa ya ciro table water, sai da ya sha rabin gorar ya dire yana nufan bed kai tsaye don kwanciya. Ya lumshe idanunsa lokacin da kansa ke warwarewa daga caji da ta ɗauka, feeling ɗin da yake ji na tsananin son kusantar mace na sake ratsashi.Ya sake lumshe idanunsa yana ayyanawa a zuciyarsa da Hannah na nan da yanzu tana cikin jikinsa, don amfaninta kenan a garesa da zaran ya shigo a irin wannan yanayin da yake ciki.Tashi ya yi ya nufi side drawer ɗinsa yana ciro kwalin wani magani da ya jima bai yi amfani dashi ba, tun bayan fara sanin Hannah da ya yi a mace.Ya ɓalli biyu ya jefa a baki yana takowa inda ya aje ragowar table water ɗin ya ɗauka ya kora ruwan maganin suka wuce,ya aje goran yana sauke numfashi tamkar wanda yaci babu.Da ƙyar ya iya rintsawa a ƙarishen daren,yana mai yankewa kansa cewa dole zuwa jibi friday ya wuce KD don tinkaran koma miye akan cikin jikinta.
**********
*Kaduna.*
Washegary da wuri Najma ta wuce zuwa kitchen ɗin Gwaggo,suka haɗu da Tabawa don haɗa abincin breakfast.Lafiyayyan ƙosai da kunun tsamiya suka dama, sai aka soya egg da irish tare da dafa ruwan shayin da yaji kayan ƙamshi a dahuwar.Sosai ƙosan da Najma ta soya ɗin ya yi kyau da taushi, gashi ganin akwai wadatan kayan gayu na girki sai ta yi karanbanin yanka green pepe da wadatacciyar albasa a cikin ƙullun,ta saka curry kafin a soya.Sai ƙosan ya bada kala da flavour mai daɗi don green pepe akwai shi da daɗi a cikin wasu soya-soyen ga duk wacce ta ganewa sirrin.Ƙarfe tara suka kammala da komi Tabawa na faman yaba ƙoƙarin Najma da son aikinta,don tana da zafin nama da himma matuƙa da gaske. Najma ɗakinsu ta wuce don yin wanka ta shirya kafin Gwaggo ta fito, su haɗu suyi breakfast ɗin tare.Ta samu Inna Mairo a zaune tana sauraran karatu a cikin wayarta, ta gaidata tana mai wucewa bathroom ta yo wanka ta fito.A tsanake ta shirya cikin wata free gown na atamfa, wanda ɗinkin ya yi mata kyau a jiki sosai tare da fidda kyawunta.Bata shafawa fuskarta komi ba sai man leɓe data gogawa lips ɗinta,fuskarta sai ya yi fayau da asalin natural black beauty face ɗinta.Sassanyar ƙamshin turaren MISS DIOR da Nasreen ta bata ke tashi a jikinta,kamar yadda dukkanin ɗakin ma ya buɗe da ƙamshin mai sanyi.Inna Mairo ta ɗaga ido ta dubi Najma tana faɗin, "Najma kinga yadda ki ke ta sauyawa kuwa? Anya zuwa nan gaba ba zaki dinga yawo da dogon hijab har da niƙab ba? Ina tsoron kyawun mace ya cika bayyana Najma, domin ya kan zamewa wasu ƴan matan mummunan bazarana ga rayuwarsu.Nasihata a gareki kullum shi ne ki zama mai matuƙar kamun kai da takatsantsan wajen kare mutuncinki ta ɗiya mace,sannan ki nisanci sanya tufafin da zasu dinga bayyana surarki domin hakan ba wayewa bace.Ko kaɗan kada ki bari ruɗin duniya da zaman bariki su sanya ki watsar da tarbiyar da muka ginaki akai, domin daga ni har Malam burin mu ki zama nutsatstsiya mai tayamu kare mutuncinki da namu.A kowani mataki na rayuwa ki riƙa tuna cewa mutuncinki dana addininki shi ne abinda zaki fara karewa sama da komi a duniya.Sannan ki ji tsoran Allah wajen kiyaye kanki daga mazan da ba muharramanki ba, karki ruɗu da kalar rayuwar wasu ki ce kema zaki koyi dasu a abinda zai taɓa mutunci ko tarbiyarki mai nagarta.Don Allah Najma karki sauya akan kyawawan ɗabi'u da halayen da aka sanki dasu, sannan karki dinga manta asali da tushenki duk yadda rayuwa zata zo miki da sauyi.Ki dinga tuna cewa ke ɗin ba kowa bace ba kuma ƴar wani bace, face ƴar ƙauyen garin giwa." Inna Mairo ta ɗan dakata da maganar tana duban yadda Najma ta nutsu tana saurarenta.Ta ɗaura da cigaba da faɗin, "Ba ina miki wannan nasihar da wata manuface Najma, sai don ina tsoron sharrin zuciya da ruɗin duniya.waɗanda suke saurin sauya tunanin ɗan adam farat ɗaya! Dole sai ana yi ana taro ku tare da yi muku nasiha,don duniyar dukkaninta babu tabbas a cikinta.Ki riƙe gaskiya da amana, duk rintse karki yarda mutanen da suka aminta dake, suke nuna miki ƙauna tsakani da Allah su sameki da rashin gaskiya ko cin amana.Ki taimakeni ki tayani kyautata musu da yi musu biyayya, sannan ki guji shiga cikin lamarin da ba a sanya ki ciki ba.Ki nisanci ƙarya da ha'inci,duk da cewa ba halayyarki bace,amma ina so kiyi matuƙar takatsantsan Najma domin zama a ƙarƙashin wasu abu ne mai matuƙar wahala.Ki ninka haƙurinki domin dole za a saɓa miki kamar yadda kema zaki saɓa musu cikin rashin sani koda gangan,ina fata zaki kiyaye ki kuma nisanci son abin hannunsu.Dukkanin abinda aka ɗakko aka baki kiyi godia, wanda ba a baki ba ko ya shiga ranki ki kauda da kai karki yadda ki taɓa abinda ba a baki ba.Na sani baki da kwaɗayi, amma ina miki matashiya da ki ninka akan kyawawan ɗabi'unki da na sanki dashi, hakan zaisa na cigaba da alfahari da ke Najma kin ji ko?" Najma da dukkanin jikinta ya yi sanyi da nasihun Inna Mairo, sai ta gyaɗa kai murya a sanyaye ta ce, "Naji Inna, kuma In Sha Allah zan kiyaye dukkanin nasihunki.Allah ya barmu tare har mutuwa mu je mu tadda Malam a aljanna cikin aminci." Inna Mairo ta yi murmushi wani abu na motsa zuciyarta.Cikin sanyin murya ta furta,"Ameen Najma! Allah ya cigaba da haskaka makwancinsu,tashi muje kada Gwaggo tayi ta jiran mu." Suka fito daga ɗakin jere da juna,zukatansu na tuno musu da rayuwarsu a garin giwa tare da mutanen arziƙinsu Iyalan gidan Hakimi. Sun tadda Gwaggo har ta fito tana zaune wajen da suka saba cin abinci ta fara serving kanta.Suka zauna suna gaida Gwaggo a tare,ta ɗaga ido tayi musu duba ɗaya tana yaba kyawun da dukkaninsu suka yi cikin suturu masu kyau da ke jikinsu.Idanunta akan Najma ta furta, "Jikata ya gajiyan suya?" Najma ta saki wide smile tana faɗin, "Babu gajiya Gwaggo, Allah dai ya sanya ya yi miki daɗi,don nayi miki karambanin ƙara wani abin a ciki."
Gwaggo ta kai hannu tana buɗe kulolin har ta buɗo wanda ƙosan ke ciki, wani ƙamshi ya cika wajen mai daɗi.Ta ɗakko ɗaya ta kai baki tana faɗin, "To bari na ji wani karanbani ne kuma aka yi a cikin ƙosan." Ta tauna tattausan ƙosan da ke tashin ƙamshin green pepe da albasa tare da ƴar curry kaɗan da aka buga ƙullun dashi,wani irin daɗi ya ratsa harshenta zuwa kwanyarta.Ta lumshe ido tana buɗesu akan Najma ta ce, "Wayyo daɗi! Inji Yaro, gaskiya Najma kin iya ƙosai tamkar wata tsohuwar mace da hannunta ya nuna a iya tuya.Gaskiya dole Kabeeru ya yaba miki, aini ban taɓa sanin kin iya har hakan ba da kusan kullum dashi zan dinga karin safe,don ni Kabeeru ya gado a son karin safe da ƙosai ko waina da kunu." Daga Inna Mairo har Najma suka saki ƙaramin dariya, Najma na duban yadda Gwaggo ta sake jefa ƙosan a baki har da wani kanne ido.Ta sake sakin smile tana faɗin, "Allah sarki Gwaggo! Ai nima bansan kina so ba kuwa, da yake sana'arsa muke yi a ƙauye muke samun na rufin asiri lokacin." Gwaggo ta jinjina kai tana jin ciwon su dinga tuno rayuwar wahalar da sukai a baya,cikin kulawa da son kawar da maganar ta ce, "Gaskiya ni dai ke ce zaki dinga mana ƙosai ko idan watan azumi ya kamane, wannan irin ƙosai mai shegiyar daɗi haka." Najma suka sake sanya dariya,kafin tayi serving ɗinsu ita da Inna Mairo suka fara nasu karin.
Suna dab da kammalawa Nasreen da Hannah suka shigo cikin falon Gwaggon.Hannah ke gaba Nasreen na bayanta cikin shirin fita skull,suka zauna suna gaida su Gwaggo cike da ladabi.Najma ta gaida Hannah ta amsa da fara'a tana faɗin, "U look so fresh and beautiful Najma! Gaskiya na jima banga black beauty da skin mai kyau irin naki ba." Najma ta saki murmushi tana duban Nasreen da ta tsareta da ido ta ce, "Sis wannan kallon kuma fa?" Nasreen ta saki smile tana cewa, "Kyau kika min ba kaɗan ba Najma, anya nan gaba ba goslow zaki dinga haɗa mana a layi ba?" Najma ta jefa mata harara tana faɗin, "Kai Nasreen, wallahi kin cika neman magana." Hannah ta taya su yin dariyar idanunta na sauka akan ƙosan da Gwaggo ke ci baji ba gani.Gwaggo ta ɗago suka haɗa ido da Hannah, sai tayi saurin faɗin, "Hannatu ko zaki ci ƙosai a zubo miki, ko kema ƴar gayunce irin mijinki da sai abincin turawa yake karyawa dashi?" Hannah tayi ƙasa da kai tana faɗin, "Gwaggo ni kam babu ruwana ina ci sosai ma, musamman wannan ɗin da nake ganin kyawunsa tun a ido." Gwaggo ta zuba mata plate ta miƙa mata tana faɗin, "Maza sakko kici tunda zafinsa, ga kunu nan ki zuba shi ma idan kina so." Hannah da dama ƙosan ta biyo, don tunda akai zancensa jiya ta ji shi kaɗai take son ci.Shiyasa Nasreen na shiryawa ta ce zata yo nan ɗin ita ma tace da Momy zata zo ta gaida su Gwaggon,suka fito suka yo nan ba tare da ta tsaya yin breakfast a can ba.Sosai ta ci ƙosan tana yaba daɗinsa da ƙwarewar Najma a iya sarrafashi, Gwaggo ta cigaba da kwarzanta daɗinsa suna kwasan dariya.Nasreen ce ta yiwa Najma magana cewar zata wuce skull, idan ta dawo kuma zata rakata wata unguwa.Ta raka Nasreen ɗin har wajen motarta ta wuce skull, ita kuma ta juyo zuwa side Gwaggon.Tana shigowa Hannah na fitowa zata koma side ɗin Momy, ta yiwa Najma kallo ɗaya da murmushi akan fuskarta ta ce, "Najma naci ƙosai mai daɗi da yawa, gaskiya kin sama ladana thank u beauty!" Najma ta sakar mata smile tana faɗin, "Laah! Bakomi Anty, na gode nima da yabawa." Daga haka Hannah ta wuce ita kuma Najma ta shige daga ciki.Sai wajen sha ɗaya suka fito daga side ɗin Gwaggo zuwa na Momy don gaidata.Sun sameta tare da Nabeelah da Hannah zaune suna hiransu, suka gaisa a mutunce idanun Momy akan Najma ta furta, "Idon ki kenan daughter? Na fito jiya kawai sai na tadda Gwaggo ta tasa ƙeyarki kun koma can ɗin,ai gobe dai Daddy idan ya dawo zai yi mata magana da kansa cewa nan zaki dawo da zama dai." Najma da haka kawai bata son hakan a ranta sai ta saki murmushin yaƙe ba tare da ta yi magana ba, sai Inna Mairo ce ta ce, "Ai dama kun barta kawai a can ɗin, indai Najma ce ba za ta iya zaman waje ɗaya alhali tasan ina cikin gidan." Momy tayi dariya tana faɗin, "Aiko hakanan zata dawo nan ɗin, gara ta zauna cikin ƴan uwanta su riƙa yin komi tare hakan zai sake haifar da shaƙuwa a tsakaninsu......✍🏻
*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank*
*OR*
*PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻
*8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM*
*ACCOUNT NAME:OPAY*
*Evidence of payment to this number:****
🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*
*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA *** DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻
#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰